Showing 291001 words to 294000 words out of 346625 words
Chapter 98 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
sai dai ta takani ka saketa a gabana ka koma bayana ka mayar da ita? Duk xamana da Hauwa ko kallon banxa bata ta6a min ba balle ta mayar min da magana duk fitinata da bala'i na, to na ta6a ce maka ta min??" Hajja ta dinga matse hawaye tana kuka, Abba ya daga kai a hankali ya kalli Aunty yace "Ki je na sake ki Hafsah" Mikewa Aunty tayi xumbur don furucin nasa ya xo mata unexpected, tana kikkifta ido tace "Kayi me?" Abba na kallonta yace "Na sake ki" Girgixa kai ta shiga yi cikin tashin hankali tana nuna sa take cewa "Plss stop this joke Usman, I don't get ka sakeni? Kamar yaya kenan? A saboda me ka sakeni? I don't understand, Kasan kuwa me kake cewa? Shikenan fa igiyar, are u on ur right senses?" Abba dai bai ce mata komai ba, ta fashe da wani mahaukacin kuka tace "Usman ka sakeni fa kace? Ka mance igiyar saura daya ne? Are u for real? Ka datse aurenmu kenan kake nufi?" Jin Abba bai tanka ta ba ta dau jakarta da sauri tana goge hawayen idonta tace "Wait for it Usman" xata nufi kofa Abuturrab ya mike yace "kinyi mantuwa dakin Hajja daxu!!" Juyowa tayi tana kallonsa, ya nufeta sannan ya ciro handkerchief din ya ajiye kasa gabanta bayan ya bude abun ciki a sarari ya mike yana kallonta, kallon layan ta dinga yi with so much shock, kowa na parlon ma kallon layan yake a firgice, Hajja ta mike da sauri tace "Huhuhu meye wannan kamar laya, ina ka samo sa Aliyu?" Abuturrab yace "Daxu ta bar maki shi a daki kafin ta fito" Hajja ta bude baki a tsorace ta dafe kirji tace "Ta bar min shi??" Da sauri Aunty ta juya ta fice daga parlon har tana bugewa da kofa, Hajja ta saki salati ta dau hankicin ta kai har gaban Abba ta ajiye masa ta fashe da kuka tace "Wato bakina ya rufu in kasa ta6uka komai a rayuwata ta duniya, to sai dai bakin uwarta dake kabari ya rufu ba dai nawa ba, in ji kaga matar da kake aure shekara da shekaru Usman, inji yau ka gane ma idonka" Abba dai sai kallon layan yake da mamaki ko kiftawa babu, Ummi dai duk jikinta yayi sanyi, Umma kuma sai murmushi take me sauti tana girgixa kafa, Sai da Hajja ta bari Abba ya gama kare ma layar kallo snn ta nannade tace "Toh Alhamdulillah, Allah nagode maka da ka kawo mana karshen wannan annoba dake cikinmu shekara da shekaru, Allah nagode maka, in ji dai ka gani Usman, to haka ta kulle bakinka kana ta tafka tsiya kana walakanta matarka ta arxiki, kana walakanta uwarka" Umma ta daga hannu sama da karfi tace "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, dama Hausawa sun ce shi ramin karya kurarre ne, kuma na sake tabbatar da cewa mahakurci mawadaci" Ummi ta goge hawayen da ya kawo idonta ita dai bata ce komai ba, Hajja ta fashe da kuka sosai tace "Ina ma Nafisa da su Kabiru na nan su ga wannan rana ni 'ya su, yanxu ya Hafsah xata yi da hakki jama'a? Ya xata yi da hakkin Hauwa da 'ya yanta? Har ma da hakkina da na d'a na" Abba dai ya kasa cewa komai kansa a kasa, kana ganinsa kasan he is really shocked, Amma fa babu wanda ya kai Aneesah shock a parlon to aka saki Aunty balle ita karan kada miya?? Gaba daya hankalinta idan yayi dubu ya tashi, tana son Aliyu so me tsanani kuma bata fatan abinda xai rabata da shi, tana tsoron ace ta rabu da Aliyu tasan kilan mutuwa xata yi gaba daya, duk wannan abun da ake Jiddah ta ki dago kanta a parlon, Hajja na shessheka tace "Toh ai xuwan Jiddah pamilyn nan namu alkhairi ne, gashi dai a ta dalilin xuwanta abubuwa iri iri na boye da na fili suka dinga billowa har ya kai ga tonon asirin Hafsah, duk mugayen abubuwan da Hafsah ke yi shekara da shekaru bai bayyana ba sai xuwan Jiddah, mata ki raba d'a da uwarsa, ni gaya maku ne kawai banyi amma wllh akwai sanda Aliyu ya sameni wai shi fa bai yadda Hauwa bace mahaifiyarsa, na yi matukar girgixa da furucin nan nasa nace kai ko me yasa kace haka, sai ce min yayi shi baya jin ta kamar uwarsa a ransa, kuma sai ya ji bai son ganinta ma wani lkcn, wllh idan ba yanxu ba ban sanar ma kowa ba ni dai na dage masa da addu'a, komai sai yace Aunty, da xa ku ji uban dukiyar da yake narka ma Aunty a baya sai kun girgixa, har fili ya ta6a siya mata ya gaya min amma wai kar in gaya ma Hauwa, alhalin bai ta6a tsinana Hauwan da komai ba, kaiii Hafsah dole sai ta dawo ta nemi gafarar Hauwa da D'an ta idan ba haka ba garari kawai xata yi tayi a duniya ta rasa tudun dafawa" Ummi dai ta kasa controlling hawayen dake xuba idonta tana tuna abubuwa da yawa, Umma dai ta rungume hannunta kawai daga inda take xaune ita ma tana tuna irin takaici da bakin cikin da yayarta ta dinga kunsa a gidan nan for almost 20 years amma take ta hakuri, kullum sai dai tace watarana sai labari, gashi ko sau daya bata ta6a yarda wai asiri Aunty ke yi ba, gaskiyan Hajja shigowar Jiddah rayuwar Abuturrab ne mafarin samun bond da Umminsa, ta dalilinta suka fara creating bond da mahaifiyarsa, a da ko shawara bai yarda yayi da ita ba, komai Aunty, ita kadai tasan nawa yake samu wajen aiki, ko wani lamarinsa ita ce, Umma ta girgixa kai ta ji ta kara jin tsoron duniya, yanxu ya Hafsah xata yi da wa ennan hakkin? kin raba mata da mijinta hakan bai isheki ba kin rabata da d'anta kiri kiri komai yace sai ke, Hajja ma don kin sameta tsayayya ce banda haka da tuni kin rabata da d'an ta ita ma, Umma ta share hawayen da taji ya kawo idonta tana kara gode ma Allah da ya kawo karshen komai cikin sauki sannan a lokacin da ba ayi xato ba, kuma a gaban kowa, Abba ya dago a hankali bayan few minutes ya kalli Hajja yace "Hakuri xa ayi Hajja, Allah ya sa mu gama da duniya lafiya, ina ce shikenan ba wani abu kuma?" Kana jin yanda yayi maganan kasan watse taron yake son yi, he just want to be left alone, Hajja ta share idonta a hankali tace "Aa ba shikenan ba, Usman daxu ni da wannan mata Hauwa mun je gidan Aliyu, nice ma na tilastata muka tafi ka santa ba wani wayewa gareta irin na matan xamani ba kamar dai yanda kaga yar uwarta Ramlah take, to banda rashin wayewa ai babu wani me kunyan d'an fari a xamanin nan dai, ni kaina banyi wannan kauyancin ba a xamaninmu, ni dai na ja ta muka je ashe bala'i xa mu je mu tarar Usman, in gaya maka wannan yarinya me kama da Zabiya matar Aliyu tayi kwatsa kwatsa da kayan dakin Jiddah da aka kai mata ko sati bai yi ba, kuma na samu labarin kayan miliyan uku aka kai mata" Abba ya kalli Abuturrab yace "Where were u then?" Ya sunkuyar da kansa, Hajja na nuna Ummi tace "Wllh a kan idon Hauwa aka yi komai, ni kuma na baxama gari neman masu kawo mana dauki, da yake a Masar haka ake, kawai fita titi xaka yi ka sanar da abinda ya dameka a kawo maka dauki har cikin gida...." Sai kuma tayi shiru tayi tagumi, sai kuma tace "Kai ni ban ma son magana wllh, abinda ya dameni ya tsaya min a rai daban, yanxu me na ma Hafsah jama'a da xata garkame min baki? Me na mata xata ajiye min mummunan laya da garkamemen kwadon jaraba a jiki don a rufe bakin da nake ma annabina salati? Ba fa abinda nake sai salatin da zikiri da wannan bakin nawa" sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tace "Allah ya isa, Allah ya isa wllh, to yanxu da Aliyu bai gani ba kurma xan dawo ko bebiye?" Umma dai sai danne dariya take, Hajja ta rushe da wani kukan takaici tace "Wllh baxan bar xancen nan haka ba sai kace er banxa warce bata da gata? Allah sai an bi min hakkina ta fadi ma'anar layar nan da kwado da ta bar min a daki, so tayi in dawo kamar Hauwa babu uhm babu um um ko kuwa? Wlh abun ya gigita ni, sannan ban gaya maku ba har da wani farfesu ta kawo min da yake Allah bai yi ni me kwadayi ba nasa aka kai kwararo aka juye shege, to da na ci ya kenan bin ta xan tayi kamar jela a baya koko?" Hajja ta mike tana kuka tace "Tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin haka ba wllh, yanxu xuwa xanyi kaf in kira 'ya yana da 'ya yan mijina in sanar dasu wannan abu da ya faru, don a gaskiya idan abu ya sameni ba yarda xa su yi ba..." Hajja ta fyace majina tace "Sai kuma abu na karshe wannan yarinya Nanisa take ko wa?? To wllh ta fi karfin Aliyu, don idan ta samu waje xata yi fiye da yin Hafsah a gidan Aliyu, don dama bakinsu daya kuma er kawarta ce duk yan iska ne masu bin boka da malamai, don haka yanda aka sallami Hafsah to ita ma a sallameta don hada iri da su bashi da amfani, hada iri da su bala'i ne...." Aneesah ta fashe da matsanancin kuka tace "Don girman Allah kar a rabani da Aliyu, wllh ina sonsa kuma na dau alkawarin xan xauna lafiya da shi, don Allah ayi min afuwa kar a rabani da shi, wllh ina sonsa" kuka take sosai, Hajja ta sha kunu tace "Wllh baxa ki xauna da jikana ba ki kashesa ki kashe matarsa, ke yar banxa ce, ke yar da6a ce, banda d'an da6a wa xai yi abinda kika yi yau? Inaaa xama da irin ku sai tsinanne" Cikin kuka Aneesah tace "Sharrin Shaidan ne Hajja, don Allah ku rufa min asiri wllh baxan sake ba kar ku rabani da mijina" Hajja tace "Idan Hafsah tayi ta'amali da laya to fa wnn wllh har bokan xata iya dinga kawowa cikin gidan tana boyewa don naga idonta ya fi na Hafsah budewa, kun dai ga abinda Hafsah ta jefa min a daki daxu ban ji ba ban gani ba, wai kar inyi magana kamar ita ta halitto min bakina, to Allah yatsine mata albarka, in sha Allahu baxata gama da duniya lafiya ba, wnn bakin nawa da ya tsole mata ido shine ajalinta, bana komai fa sai salati da zikiri amma ta nemi garkame min baki" Hajja ta nemi waje ta fashe da matsanancin kukan takaici, Umma ce ta dinga bata hakuri, ta share idonta ta mike tace "Amma duk Usman ne ya ja mana, don da bai auro Hafsah ba baxata lika ma d'an sa Nanisa ba, don haka wannan yarinya Nanisa ba matar xama bace, kar tayi ma Aliyu fiye da yanda Hafsah tayi ma Usman, ni dai na baku shawara xanje in kwanta in nutsu ko xan gano dalilin wannan laya da kwado da aka bar min a daki" daga haka ta nufi kofa ta fita parlon. Aneesah na kuka cikin rawan murya tace "Abba don girman Allah ayi min afuwa wllh baxan sake ba, wannan ma sharrin shaidan ne" Umma sai hararanta take jin yanda ta iya cewa sharrin shaidan, Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Tashin hankali da fitina ba shi da amfani Aneesah, yanxu ke abinda kika yi yau kinga kyautuwansa? Riban me kika ci banda tashin hankali da ji ma kanki ciwo?" Aneesah dai sai girgixa kai take tana hawaye, Abuturrab ya hade rai don ko muryarta wllh ya ji bai son ji, Ummi tace "Ki tafi ki ba mijin ki hakuri" Tashi tayi ta tafi gabansa ta durkusa cikin rawan murya tace "Kayi hakuri Captain, na dau alkawarin baxan sake creating wani problem ba a xaman mu plss pardon me" kin kallonta yayi balle ya bata amsa, Abba ya sauke boyayyen ajiyar xuciya, nasiha ya shiga yi masu gaba daya su ukun, Ita dai Jiddah kanta na sunkuye, ya dau kusan 20mins yana nasihar daga karshe ya juya kan Abuturrab yace "And you... Kaji tsoron Allah ka xamo me adalci a tsakaninsu, that's all i have to say" Abuturrab ya dago kansa a hankali yace "Toh Ummi idan har tana son xama da ni, dole xan ja mata layi da some set of people, jan layi na har abada, that is only if she wish to stay with me..." A hankali Aneesah tace "In sha Allah" Yace "Better!!" Ta juya ta kalli Umma sannan ta koma kusa da ita ta durkusa cikin sanyin murya tace "Umma kiyi hakuri, hakan baxai sake faruwa ba in sha Allah" Umma tace "Ai ba kayana kika walakanta ba, me kayan xa ki ba hakuri" Ta kalli Jiddah, sunkuyar da kai tayi kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Kiyi hakuri... ki gafarceni" Jiddah ta girgixa mata kai kawai don bata ma san me xata ce ba, Ummi tace "Allah ya gafarta mana ga baki daya, Allah ya baku xaman lafiya dauwamamme, ya kada fitina" cikin sanyin murya Aneesah tace "Ameen"
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
FZ BEAUTY SUPPLEMENTS
Dealer in all kind of dietary supplements such for skin whitening, skin glowing, weight gain, slimming, flat tummy, infection killers, dark spots removers, fertility booster, Hips boosters, Breast firming and Enlarging, Teeth whitening, eye, joint, stretch marks, and for marital pleasure. All supplement are available for wholesale and retail. For more information contact FZ via wa.me/2348143821028
FZ Beauty Supplements
Dealer ce ta supplement masu qara fito da kyaun mace ko namiji, hadi da qarama garkuwar jiki kuzari. Muna sayarda Supplemnt kamar na qarin duwawu, akwai wanda zaya taimaka wurin dawoda martabar Nono, akwai na rage qiba da tumbi, akwai na rakwainuwa, akwai na tada komada, akwai masu saka hasken fata da qyalli, akwai na infection, akwai na saka hasken ido da hakori sannan akwai na gyaran turaka. Muna maraba da mai sayen daya ko sari. Wa.me/2348143821028
Bayan few seconds Abba ya kalli Umma yace "Furnitures din na nawa aka siya mata?" Umma ta gyara xama tace "2.3m" Abba yace "Shkkn, xa a san yanda xa ayi, Allah ya rufa asiri" a takaice Umma tace "Ameen" kallon Jiddah tayi tace "Tashi ki dauko min jakata a parlon Ummi mu tafi, dare na yi Jiddah..." A hankali Jiddah ta mike ta nufi kofa Abuturrab ya bi ta da kallo, sai kuma ya kalli Umma, bayan fitar Jiddah da few seconds ya kalli Abba yayi kasa da murya a hankali yace "Allah ya kara girma Abba, mun gode" Abba yace "Ameen" mikewa yayi ya nufi kofa da sauri, Aneesah ta bi sa da ido har ya fita, sai kuma ta daga kai ta kalli Ummi cikin sanyin murya tace "Nagode Ummi, Allah ya kara girma" Ummi tayi murmushi tace "Ameen, sai ayi ta hakuri kuma" mikewa tayi ta fita parlon ita ma, Umma dai ta ta6e baki ta kalli Abba ta ga Ummi yake kallo.... Jiddah na shiga parlon Ummi ta dau jakar Umma da wayarta dake ajiye saman kujera xata fito aka bude kofar parlon, ta daga kai da sauri, suna hada ido ta sauke nata idon har ya iso inda take tsaye, ya jawota kusa da shi yyi wrapping hannunsa daya a bayanta ya dago kanta yana kallonta yayi kasa da murya yace "How are u feeling now?" Ta dauke kanta tace "Fine" Da damuwa yace "Are u sure? Me kika ci a gidan Umma daxu? Where u able to eat?" Tace "Na ci" yace "Kina kai mata jakar ki fito mu wuce gida yanxu" Ta xaro ido tana kallonsa, ya hade rai yace "To bin ta xa ki yi?" Kafin tace komai aka bude kofar parlon, da sauri ta turasa ta koma baya, Aneesah ta shigo parlon babu ko sallama, kallo daya tayi masu ta wuce dakin Ummi fuskarta a daure ta kulle kofar, Abuturrab ya bi ta da wani harara, Jiddah dai bata ko kalleta ba ta bi gefensa xata wuce ya rikota da damuwa yace "Are u serious bin ta xa ki yi Jiddah? Kin ga fa gobe xan koma aiki" Ta kallesa a hankali tace "Toh ni baxan iya ce mata a'a ba" amsar jakar da wayar yayi a hannunta yace "Ki tafi dakin Hajja ki jira ni" Bai jira me xata ce ba ya nufi kofa ta kasa cewa komai ta bi sa da kallo har ya fita, direct parlon Abba ya koma ya shiga da sallama bai bari sun hada ido da Umma ba ya ajiye mata jakarta da wayarta a gefe kansa a kasa yayi masu sae da safe, daga haka ya fita daga dakin, Ummi ta bi sa da kallo sae kuma ta mike ta bi bayansa, tana fitowa Main parlor tace "Aliyu" Abuturrab da har ya nufi dakin Hajja ya juyo yana kallonta sannan ya dawo, tace "Tafiya xa ku yi gidan naka yanxu?" Ya sunkuyar da kai yace "Eh Ummi" tace "You should be taking them both then" Ya daga kai ya kalli Ummi amma ya kasa ce mata komai, Ummi tace "Ka tsaya kallona ko da matsala ne?" a hankali ya girgixa mata kai, tace "Toh sae da safe, sae ayi ta hakuri kuma, Allah ya baku xaman lafiya" ko kadan ransa bai so haka ba, bai yi niyyar komawa da Aneesah gidansa yau ba, amma babu yanda ya iya, Ummi ta tafi bangarenta to meet Aneesah, shi kuma ya tafi dakin Hajja, Hajja na xaune tana matsar kwalla a hankali tana kallon Jiddah tace "Ke tunda aka haifeki kin ta6a gani ko jin haka? Me na mata da ta nemi garkame min bakin da