Showing 9001 words to 12000 words out of 346625 words

Chapter 4 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

ni iyantama, kaiii Hansai da kyar taga annabin rahama, da tasan abun arxiki ne iliya wllh baxa ta so ki da shi ba sai dai Bibalo amma da yake tasan waye shi sai cusa maki shi take alallai adole...." Jiddah dai kuka kawai take, Iyah tace "To dai ba ruwana nawa ido tunda 'ya yana sun hanani shiga maganan da bai shafeni ba, barin ma na gidan Hansai matar da bata gaji mutunci ba" tana fadin haka ta tafi ta ci gaba da abinda take, a hankali Jiddah ta mike tana share idonta ta fita gidan kada Hansai ta koma taga bata nan.

Abuturrab na xaune parlon Umma tare da Ahmad suna cin abinci a tare, Umma dake xaune tana kallo tace "Toh ba dole ku yi shiru ba dama" murmushi kawai Abuturrab yyi, Ahmad yace "Ni xan kawo maki ita ai ta gaisheki Umma...." Umma ta katse sa tace "Ka kawo min wa?" Bai kuma cewa komai, Abuturrab yace "Warce xai aura wai Umma" Umma tace "Akwai wata da xai aura bayan Ramlah ban sani ba?" A tare suka kalleta, Ahmad dai ya ci gaba da cin abincin gabansa bai ce komai ba, Umma tace "Ban da dai ku yaran yanxu abinda ku ke hange daban gida bai koshi ba ai ba a kai waje ba, is there anything wrong with Ramlah da baxaka iya aure ba?" Still Ahmad bai ce komai ba, Umma tace "Ni baxan yi abinda xai cutar da kai ba, meye da Ramlan da baka sonta ka gaya min" Jin bashi da abun ce mata ta mike ta fita daga parlon, Abuturrab dai sai kallon Ahmad yake, bayan few seconds Ahmad ya dago ya kallesa, d'an murmushi kawai yyi ya ci gaba da cin abincinsa, calmly Abuturrab yace "I dont want to believe kayi ma Umma shiru ne saboda Ramlah kanwata ce" Ahmad ya d'an kallesa sai dai he was mute, Abuturrab ya girgixa kai yace "Don't be quiet because of me, coz if i were in ur shoes i wont keep quiet, baka son Ramlah ga warce kake so to meye na yin shiru? Abinda ake tunanin shi xai karfafa xumunci shi ke 6ata shi, meet Umma.... Pour out ur mind to her, tell her who u intend marrying" Murmushi kawai Ahmad yyi ya maida dubansa kan TV, mikewa Abuturrab yyi yace "Xan amsan ma Ummi drugs a pharmacy so i will be on my way now" Ahmad yace "Alright, anjima da daddare xan shigo in sha Allah" Abuturrab yace "Ok then" daga haka ya fita parlon, amma sai da ya fara shiga main parlor yyi ma kanwar Mahaifiyarsa sallama sannan ya fita gidan. Abuturrab na bedroom dinsa bayan magrib Ahmad ya shigo, Ramlah ce biye a bayansa hannunta rike da cup din shayi da xata kai ma yayanta kamar yanda ya sa ta, Ahmad ya xauna gefen gado, Abuturrab na kallon Ramlah bayan ta ajiye shayin yace "Aunty ta dawo?" Ta girgixa kai tace "Aa bata dawo ba" Yace "Ohk" Ta kalli Ahmad dake danna wayarsa tace "Ya Ahmad su Umma fa?" Ya kalleta yace "She is fine, ya school?" tace "Lafiya lau, ya su Siyama" Yace "Alhmdlh" tace "Kai ma in hado maka shayin?" Yace "Aa sai kace nine Abuturrab" Dariya tayi, Abuturrab dai bai ce masu komai ba, ta nufi kofa, bayan ta fita Abuturrab yace "Mun yi waya da El-Basheer daxu yana gaisheka" Ahmad yace "Oh Yarima, kwana biyu bamu yi magana da shi ba ma" Abuturrab yace "Xai shigo Kadunan amma may be kana Abuja lkcn" Ahmad yace "Allah sarki, Allah ya kawosa lfya" Abuturrab yace "Did u talk to Umma?" Ahmad yace "About what?" Abuturrab yace "Ohh har ka manta" Ahmad yyi murmushi yace "No i dont need to, tunda ga abinda Umma take so, in sha Allah hakan xa ayi" Abuturrab ya mike a fusace yace "What nonsense, why will u say so bayan kai ba son hakan kake ba" Ahmad yace "Tunda Umma tana so nima dole in so" Abuturrab yyi masa kallo yace "Why just speak like an illiterate now?" Ahmad yace "Wait Captain, is there anything wrong with Umma's choice?" Abuturrab yace "Yes tunda ba son choice din kake ba" Dariya Ahmad yyi yace "Mun ta6a magana da kai nace bana son Ramlah? Asali ma duk cikin cousins dina babu wanda muke shiri da irin Ramlah, Ramlah was kinda brought up in our home since she was 2, tunda takwaran Umma ce kuma rainonta ce ita shi yasa take son ta hadamu, fine if Ramlah is okay with that ni bani da damuwa" Tsaki Abuturrab yyi ya koma ya xauna, Can yace "Ita kuma Maryam din dama yaudaranta kake kenan?" Ahmad yace "Idan wani xai min wnn kallon banda kai Abuturrab, it's just that my Umma's choice is my choice" Abuturrab ya jawo wayarsa dake ring ganin Aneesah ke kiransa ya katse ya shiga kiranta, Ahmad ya mike yace "Bari in gaida Ummi" daga haka ya fita dakin....


07087865788โœ๐Ÿป๐Ÿ’–๐Ÿ’–Jiddatul~Khair๐Ÿ’–๐Ÿ’–





_By khaleesat Haiydar_๐Ÿ“šโœ๐Ÿป





4......

Jiddah ce xaune kusa da Abbanta dake kwance tsakar gida saman tabarma da wani pillow da ya yakune, hawan jininsa ne ya tashi tun daren jiya, magunguna ne ajiye daga gefensa wanda da kudin da take tarawa wajen Iyah ta samu ta siyo masa magungunan, ko bi ta kan inda ta samo maganin Hansai dake ta yankan dafaffen awaranta bata yi ba, Sosai Abban nata ke jin jiki shi yasa duk hankalinta ya tashi, Hansai dai sai ta6e baki take, lkci lkci kuma tayi tsaki har ta gama abinda take yi ta mike tace "Yau ai sai ki xuba ruwa kasa ki sha tunda baxaki siyar min da awara ba kin wani makale kusa dashi wai bai da lafiya, to a duniyar nan yanxu wake da lafiya? Kowa ba lallaba kansa kawai yake yi ba, idan ka xauna ka fake da ciwo ai sai yunwa ta kar ka, ko da yake shi kwanciyar tasa ma da rashinta duk daya ai, Atoh duk daya mana tunda mace ce ke rike da gidan" Daga haka ta daura roban fentin dafaffen awaranta a kai da jarkan man gyada tace "Idan kinga dama in Bibalo ta dawo kice ta sameni bakin titi, tun safe ni ko ganin gilmawarta ban yi ba ko ina taje oho" kofa ta nufa da xaninta da yyi dukundukun xata fita, Jiddah ta goge hawayen dake makale idonta tana kallon Abbanta a hankali tace "Sannu Abba...." Bai iya yace mata komai ba, Hansai ta saka kai xata fita suka kusa cin karo da Iyah, Hansai ta koma baya tana washe baki tace "Sannu da xuwa Iyah" Iyah tace "Yauwa Hansatu, ya me jiki naji ance Isuhu bai ji dadi ba" Hansatu tace "Wllh da sauki kuwa, ga magungunan da na siya masa can ma, to ko kwayan hatsi bamu da shi a gidan shine nace Jiddah ta xauna tare da shi in fita in siyar da awaran nan, ba wata me yawa bace ta dubu uku ce kawai don dai a samu na cin abincin yau da gobe, kinga ai ba a xauna dukka ana jinya ba" Iyah tace "Gaskiya ne, Allah dai ya rufa asiri, yi maxa yamman ma tayi, Allah ya bada sa'a" Hansai tace "Ameen" Daga haka ta fita gidan, Iyah ta karasa ta dau kujeran tsugunno ta xauna tace "Sannu Isuhu" Da kyar ya gyada mata kai, Iyah ta rike ha6a tace "Farin mutum bafillatani duk ya kode kamar bai ta6a haske a rayuwarsa ba, Allah dai ya baka lafiya ya rabaka da cutan nan" Nan ma dai ya gyada mata kai, Iyah ta kalli Jiddah tace "Ya sha magungunan kuwa?" Jiddah ta gyada mata kai, Iyah tace "Toh Allah ya yaye masa" A hankali Jiddah tace "Ameen" Iyah ta bi d'an kuturun tsakar gidan wanda hansai ta mayar kamar na mahaukata da tarkacenta da kallo snn ta ta6e baki ta maida dubanta kansa tace "Amma kana ji na Isuhu" shi dai kallonta kawai yake yana numfashi da kyar, tace "Don muhammadurrasulillahi S.A.W.... ba a dai san gawan fari ba amma ka dubi Allah ka gaya ma wnn yarinya Jiddah inda dangin uwarta suke taje ta nemo su a fadin duniyar nan" Ya sauke numfashi da kyar muryarsa baya fita sosai yace "Iyah Mahaifiyar Hauwa 'yar Nijar ce...." Iyah tace "Kullum xancen ka kenan Mahaifiyarta yar Nijar ce, to a Nijar din bata da dangi ne Isuhu?" Ya sauke wani numfashin yace "Ni dai kowa yasan ni maraya ne ina almajiranci Uban gidana Alhaji Auwal ya daukeni ya rike kamar d'an sa sbda duk safiya xan wanke masa mota in share masa tsakar gida har ma in je masa aike, ni ban san garinsu Amina mahaifiyar Jiddah ba a Nijar din, ni dai tace min su 'yan Nijar ne, rana daya uwarta ta daukota suka dawo Nigeria wanda babu tantama kurciya aka mata, ko da suka dawo Nigeria basu walakanta ba don wata Hajiya ta amshe su hannu bibbiyu kakar Jiddah na masu aiki...." Iyah tace "To kai duk a ina kasan wannan labarin da ka kunshe ma cikin ka isuhu?" Yace "Mahaifiyar Jiddah ta bani labarin" Iyah tace "Toh ina ji" a hankali yace "A haka har Allah yayi haduwata da Mahaifiyar jiddah ranan naje kasuwa mai dakin uban gidana ta aikeni, ita kuma Jiddah Mahaifiyar ta aiketa, ban wani sha wahalan samun Mahaifiyar Jiddah ba sbda uban gidana ne ya tsaya min kan komai, a gidan da muka xauna wanda uban gidana ya kama mana haya a lkcn, muka hadu da Hansatu tana xuwa gun kanwar Mahaifiyarta, suka shaku sosai da Amina Mahaifiyar Jiddah duk da ko a lokacin Hansatu xata yi Shekara kusan talatin da wani abu amma bata ta6a aure ba, a lkcn kuma aurenmu ko shekara bai yi ba da Aminatu, ni dai nasan watarana na dawo daga kasuwa Amina ta sani gaba ai sai na auri Hansatu sun xauna tare yau Hansatu ta 6ata labarinta da irin tsananin da ake mata a gida duk don bata samu mijin aure ba kuma taji tausayinta sosai, wllh wllh Auren Hansatu kaddara ce daga Allah amma Amina ce sila, ta takurani, hatta iyayen gidana basu amince da auren ba a sannan, amma sbda son da nake ma Aminatu bana kuma son bacin ranta na lallabasu sai dai sun nuna min babu ruwansu a batun auren kuma babu biyar dinsu a auren, yawanci xannuwan da nayi ma Hansatu na lefe ma xannuwan Aminatu ce ta bani, kinji dalilin auren Hansatu, ni baxan ce sun yi xaman tashin hankali ba gaskiya don ko hakan ya faru Amina bata ta6a nuna min ba don har yau ban ga mace me hakurin Amina a duniya ba duk da xaman mu bai yi nisa ba don ta haifi Jiddah da shekara daya ta rasu, a lkcn Hansatu na da cikin Bibalo kin ji yanda rikon Jiddah ya koma gun Hansatu tun ba a yayeta ba, Uban gidana ya so Jiddah ta dawo wajensu bayan rasuwar Mahaifiyarta amma Hansatu ta saka mana kuka xa a rabata da jiddah, ita a bar mata ita xata raineta kamar yanda xata raini Habiba su taso tare, hatta Mahaifiyar Amina ta so amsan Jiddah bayan rasuwar 'yar ta, Amma Hansatu ta bi ta da dadin baki taki bata, ashe ita ma ba mai tsawon rai bace, don bayan rasuwan Amina da shekara uku ita ma ta rasu...." Jiddah dai kallon Abban nata kawai take don bai ta6a bata labarin nan ba sai yau, ta dai sha jin mutane na cewa Hansatu ba baabarta bace amma bata yrda sbda ita ta taso ta gani, Iyah sai girgixa kai take tana cewa "Allah me girma, ashe dai Hansatu baxata wanye lafiya da duniya ba... wuhuhu, Allahu akbar, To su iyayen gidan naka suna ina suka bar ka ka walakanta ka gantale haka, ai ko ba komai nasan sun ci moriyarka dai ba adadi" lkci daya Hawaye ya kawo idonsa yace "Hansatu ce dae ta rabamu, Alhaji Auwal ya bani kudi miliyan 2 in kai masa banki ban samu xuwa bankin a ranan ba sbda ruwan da aka yi kamar da bakin kwarya ina tsoron bin hanya da kudi haka, sae na dawo gida da kudin, Hansatu ta xare dubu dari biyu a ciki, kudi ko sama ko kasa, sbda Alhaji Auwal din yace bai yrda ba bayan na sanar masa 6atan kudin da naga bani da mafita, shine matar nan taje har gida ta ci masu mutunci ba na wasa ba, basu yi mata komai ba amma shine har yau, kudi kuma yace ya yafe min ya dai amshi sauran kudinsa, to kinji abinda ya faru... Wnn gidan ma da muke ciki ai shi ya siya min wllh, yau shekara bakwai kenan da ya bar kaduna suna Abuja da iyalansa" Iyah tayi tagumi tace "Yau naga tsinanniyar mata, dama ance ita ta talauta ka da ba haka kake ba, ilai ga magana ta fito...." Yace "Duk ta bi ta siyar min da filayena biyu da gonata daya, da wnn gidan kadai na tsira...." jiddah ta goge hawayen dake makale idonta duk jikinta yyi sanyi, Iyah tace "In sha Allahu xa mu ga karshenta kuwa, abinda Allah baya bacci, ynxu damuwata inda wnn yarinya jiddah xata samo danginta, to gidan da kakarta tayi aikatau a ina yake?" Yace "Wnn ai sun fi shekara sha biyar da barin kaduna, idan ko ba barin kaduna suka yi ba to sun sauya wani gidan ne don xuwana biyu duk akan haka amma aka sanar min sun tashi" Iyah tace "Abu ya lalace kuwa, banda haka ai baxata rasa basu labarin kanta da garinsu ba, kaga da ko su sai suyi ma jiddah hanyar xuwa dangin uwarta ita ma ta dawo mutum, amma ina mutum a nan ba dangi" girgixa kai kawai yyi, Iyah tace "Toh Allah ya rufa asiri, xaka ci tuwon masara da miyar kubewa in tafi in yi maka yanxu?" Jiddah tace "Xai ci iyah, tun safe bai ci komai ba sae kunu da ya sha" Mikewa Iyah tayi tace "Toh bari in je in hura gawayi yanxu ina da komai a gida, yanxun nan xan gama, to ae mayyar ba wani damuwa da rayuwarsa tayi ba, ehh Hansatu ba" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta ta ido har ta fita, murya can kasa yace "Kiyi ta hakuri kin ji Jiddah, wataran sai labari, nasan ban ta6a cutan wani tsawon rayuwata ba, ina fatan Allah ya dubi hakan, albarkacin hakan kada ya bari ki walakanta, Allah ya yanke maki wnn wahala da kike sha cikin gaggawa yayi maki abinda yafi alkhairi a rayuwarki, ina maki addu'an Allah ya baki hakuri da juriya da kauda kai irin na Mahaifiyarki Amina, kar ki kaga ana maki abubuwa ina shiru Jiddah, har gobe bani da kamar ki a duniya jiddah tun bayan rasuwar mahaifiyarki, Ban yi shiru a kan batun aurenki da wannan takadirin yaron da take ba, don har yanxu ban furta komai ba hakan ba yana nufin na aminta da auren bane, idan anyi duniya domin manzon Allah xaki auri mijin da xai kula dake yayi maki abubuwan da mu muka kasa maki, xaki auri wanda xai rike ki bisa gaskiya, wanda xai yanke maki wannan wahala da kike ciki in sha Allah" Hawaye ya shiga sakko mata ta kasa ce ma Abban nata komai, amma taji hankalinta ya kwanta sosai, da kyar ya ci gaba "In sha Allahu wannan takadirin ba mijin ki bane Jiddah..." ta gyada masa kai tana gyara masa kwanciyar kansa, ya lumshe ido yace "Tashi ki je kiyi wanke wanken da ta sa ki kar ta dawo kin ji" Ta goge idonta cikin sanyin murya tace "To Abbana Allah ya baka lafiya" Yace "Ameen Jiddah" Mikewa tayi ta tafi gun uban kwanukan da Hansai ta tula bakin kwararo k'uda sai fareti suke a kai, sbda yawan kwanukan sai kusan la'asar ta gama ta mike ta dau buta ta xuba ruwa jin ana kiran sllh ta ajiye inda Abbanta ke alwala ta koma kusa da shi ta durkusa tace "Abba ka daure ka tashi kayi alwala" Jin yyi shiru ta kai hannu jikinsa tace "Abba la'asar yyi...." hannunsa taga ya xamo kasa daga jikinsa, ta kamo hannun tace "Abba...." Shiru bai amsa ba, komin bacci ko rashin lafiya shi din ba me nauyin bacci bane, hakan yasa ta sake kiransa nan ma shiru, jijjigasa tayi taga dayan hannun ma ya xame, bata san lkcn da ta kwala wani ihu da karfi ba kan kace me mutane suka shigo gidan da sauri jikinta na rawa tace "Ku taimakeni Abbana yaki tashi" Wani makocinsu wanda har da shi ya shigo ya kai hannu jikinsa lkci daya ya saki salati yace "Isuhu ai rai yyi halinsa" Daga wnn Jiddah bata sake jin komai ba ta dai bude ido ta ganta kwance saman tabarma dare yyi ga mutane cike tsakar gidan. Bayan kwana uku, Jiddah na xaune tsakar gida da idonta da yyi bulu bulu ga wani rama da tayi don har sannan bata iya cin komai, Hansai sai faman yankan awara take tana cewa "Ke kadai aka ma mutuwa idan ba munafurci ba, Ita Bibalo ba ubanta ne ya rasu ba halan, munafuka kawai me neman suna, kin taso kin fita da kayan awara bakin titi ko sai na taso na nakada maki shegen duka, idan bamu yi awara ba yau ubanki xa mu kwakulo a kabari mu ci?" Hawaye kawai Jiddah take ta mike ta dau kaskon awara da coal pot da wasu kananun kayan ta fita xuwa bakin titi, Hansai tace "Ni wllh idan ba binsa kabarin kika yi ba bansan kina yi ba, bayan mutuwan da yyi ya bar ni da wahalan yi maki kayan aure duk da dai katifa da robobin kitchen kadai Allah xai hore min inyi maki, to ince me wnn wahalan da ya bar ni da shi, ina ta sintirin xuwa gidan Saude xaman makoki miji ya rasu ashe nima nawa na kan hanya xai tafi ya bar ni da wahala, to banda dai dama ya gaji da duniyar daga tashin hawan jini sai mutuwa Allah na tuba, shi dai yaji da munafurcinsa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login