Showing 309001 words to 312000 words out of 346625 words

Chapter 104 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

bata san hawa ba bata san sauka ba, Rahama ce ta shigo parlon daga kitchen, da mamaki ta tsaya take kallon Jiddah, tace "Aa Jiddah? Yaushe kika shigo?" Jiddah ta daga kai a hankali tana kallonta ta kasa ce mata komai, tace "Bari in sanar ma Hajiya" juyawa tayi ta koma sama ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo da mum dinta, Hajiya fatima na kallon Jiddah ganin hula ne kawai a kanta ga shi doguwar riga ta saka, ta nufota tace "Lafiya Jiddah? Daga ina haka?" Jiddah bata san sanda ta fashe da kuka ba cikin sanyin murya tace "Nemana take da fada mama" Hajiya Fatima tace "Ikon Allah, amma wannan yarinya dai ina ga ta hada iri da maguzawa, bata da mafada ne ko hankali ne kawai yayi gardama? ina shi mai gidan naku?" Cikin rawar murya Jiddah tace "Ya koma aiki" Hajiya Fatima tace "Wannan wace irin fitinanniya ce kuwa? Taso mu je sama, shi ma yasan mara tarbiyar da ya ajiye gida ya xa ayi ya dinga barin ku ku biyu kadai a gida? Haba wannan ai ba dubara bane, yaushe aka gama wancan case din ina jin ko sati ba ayi ba, shi tunaninsa bai basa cewar bai kamata ya bar ku a gida tare ba tunda yasan matar tasa yar tasha ce? Wani bala'i ne wannan ke cin ta kamar jahila?" Dago Jiddah Hajiya Fatima tayi ta wuce sama da ita xuwa parlonta, Rahama ta bi bayansu ita ma ta ji ranta ya baci sosai, tace "Yarinyar nan na bukatar wa enda xa su koya mata hankali wllh, tana bukatar a koya mata lesson, ita ko kunya bata ji ba da er cikinta take tashin hankali kullum? Ko dai bata da saiti ne?" Hajiya fatima ta xauna bayan ta xaunar da Jiddah saman kujera, Rahama ma ta xauna, duk ranta ya gama baci, cikin fada tace "Allah Mama wannan ba karamin issue bane wllh, ya kamata ayi masu iyaka me karfi ko kuma a raba masu gida kada wataran ta illata ta tun da ba sa'arta bace karfinsu ba daya ba, yanxu me ya hadaku?" Jiddah ta share hawayen dake xubo mata tace "Kawai na sauko kasa shine ta fara xagina har da iyayena tana dungurina, kuma take tambayata ko xan rama ne nace mata ai ni ba mahaukaciya bace shine fa ta mareni" Kuka sosai Jiddah take tana kallonsu, Rahama tace "Kan bala'i, ta mareki? Sai kika yi me?" A hankali tace "Ni kuma na dau vase na kwala mata a kai na fito" Rahama tace "Good!!! Dai dai kenan da fuskarta kika saita kika maka mata vase din a kai tunda ita yar matsiyata ce bata san mutunci ba, banda jahili wa ke irin wannan kishin en kauyen da take? Ai kai ya waye yanxu matured kishi ake na kwalliya da kamshi da iya tarairayan miji, sai kuma kayi takama da kwallinka, wa ke irin wannan kishin na hauka a yanzu dai? Aa wllh babu sai a kauye" Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "A wani anguwan iyayenki suke Jiddah?" Jiddah ta d'an yi shiru, lkci daya wasu sabbin hawayen suka kawo idonta ta ma rasa abinda xata ce, Hajiya Fatima tace "Ko ba a kaduna suke ba?" Hawaye na sauka idonta cikin sanyin murya tace "Iyayena duk sun rasu" Hajiya Fatima tace "Hasbunallah!!" Allah ubangiji ya gafarta masu yayi masu Rahama" A hankali Jiddah tace "Ameen" Hajiya Fatima tace "Toh ina relatives dinki kuma suke?" Jiddah ta goge idonta cike da karfin hali tace "Wajen stepmom dita na taso" Rahama sai kallon Jiddah cike da tausayinta cause ta yanda tayi maganar xaka san she is hurt, a hankali Hajiya Fatima tace "Toh dangin mahaifiyarki da Mahaifinki fa?" Jiddah ta kalleta, bata san sanda wani kuka ya taho mata ba ta fashe da kuka sosai tace "Ban san su, i only know my step mum, ita kawai na sani, wajenta na taso" Duk suka yi shiru suna kallonta cike da tausayi, Hajiya Fatima tace "Ina ita stepmom din taki take?" Cikin rauni Jiddah tace "Hayin rigasa" Hajiya fatima tace "A can din Aliyun ya auro ki?" Jiddah ta kasa ce mata komai hawaye wani na bin wani a idonta, Hajiya Fatima tace "Ki daina kukan nan kiyi min magana Jiddah" Tayi kokarin daina kukan da take, cikin sanyin murya tace "Ina yi mata awara a bakin titi ya gan ni, a hayin rigasa...." Daga Hajiya Fatima har 'er ta where a bit shock, don dai a class din Abuturrab da kyansa, da kudinsa, da kuma profession dinsa, infact Abuturrab bai yi kama da wanda xai yi stooping kansa that low ba at all, Rahama a ranta ta dinga tunani to kyanta ne ya tafi da shi, ko haskenta? Ko da yake babu yanda Allah baya ikonsa, l Hajiya Fatima tace "Ikon Allah, a can ya auro ki kenan?" Jiddah ta girgixa kai tace "Ya dai taimakeni, kuma ba wai don ya aureni ya taimake ni ba, ya taimakeni ne saboda halin da ya ga nake ciki wajen stepmom dita" Hajiya Fatima tace "Kamar yaya kenan?" Cikin sanyin murya Jiddah ta fara basu labarin tun daga farkon haduwarta da Abuturrab har xuwa yanxu da ya sake aurenta for the second time ya hadasu da Aneesah, Rahama dai sai hmm take cause she is speechless, Hajiya Fatima kuwa tagumi tayi tana ta kallon Jiddah don labarinta ya sanyaya mata jiki, wani tausayinta ta dinga ji har kasan ranta, Rahama ta kara sauke ajiyar xuciya for the third time sannan tace "Yanxu na gano dalilin da ya sa ta sako ki gaba, na farko tana ganin baki da kowa baki da wani me tsaya maki banda dangin Aliyun, ta yanda idan ta tafka tsiyarta a kanki sai ace family issue ne kamar yanda aka yi last week ta lalata maki furnitures, na biyu kuma tana ganin ke ba class din kishinta bane, ta raina wacece ke, ta raina personality dinki, tana ganin ta fi ki komai ta fi ki gata, but she is mistaken, she is deceiving her self don ko nayi rantsuwa baxan yi kaffara ba kin fita value a wajen mijinku from the way i saw things..." Hajiya Fatima da tayi nisa a tunanin da take ta kalli Jiddah bayan ta sauke ajiyar xuciya tace "Ina gidanku yake a hayi Jiddah?" A hankali Jiddah ta gaya mata, Hajiya Fatima tace "Tashi ki sauka downstairs akwai breakfast a dining ki deba ki karya tukun" Jiddah ta mike a hankali ta juya ta fita daga parlon duk suka bi ta da kallo, Rahama tace "Mama don Allah kar ma ki nuna tana gidan nan, ki bar ta tayi xamanta a nan ta samu nutsuwa, kalli fa duk a firgice take kana ganinta kasan bata da rest of mind a gidan miji? For what reason? She is too young to be experiencing this bull shit, Wllh kawai don kin hanani shiga abinda babu ruwana ne banda haka sai na nuna ma kishiyarta karamin hauka take, Allah sai na rama mata marin" Hajiya Fatima tace "Aa bbu ruwanki, ki bar komai a hannu na kawai..." Rahama tace "Allah ya sa mai gadinsu bai ga shigowarta nan ba, a barta ta huta na kwana biyu wllh, shi ma banda dama ya so a cuceta ne ai yasan mahaukaciya ya ajiye a gida, ta yaya xai tafi ya barsu su biyu kadai, wato ya ba kura nama kenan, ko kanninsa baxai kawo gidan ba su xauna saboda Jiddan, haba tayi kankanta da yawa da fara fuskarta matsalan gidan aure, kamarta yanxu ai ya kamata ace karatu take ba wai facing marital crisis ba, gaskiya banji dadin wannan labarin ba, na tsani in ga ana walakanta 'ya mace, macen ma karama, idan bata samu kwanciyar hankali a gidan aure ba albarkacin shekarunta ai baxa a dinga musguna mata haka ba, no plss this is too bad..." Hajiya Fatima tace "Ke wannan ne ya fi damunki, ni damuwata ta yaya xa ace mutum bashi da dangin uwa bashi da dangin uba kamar daga sama ya fado? Ai idan tana son samun 'yan cin kanta dole sai ta san su waye danginta, idan ba haka ba no matter kwanciyar hankalin da xata samu dole sai an mata gorin dangi, kishiyarta baxata ta6a daina mata wannan gorin ba, kai har shi wataran wllh sai ya mata gori, ki kyale maxan nan kawai" Rahama tace "Gaskiya ne kuma, to yanxu ya xa ayi kenan mama?" Tace "Ni nasan yanda xanyi in sha Allah" Aneesah na xaune parlor da kawayenta su hudu tun bayan da ta kirasu ta sanar masu abinda ya faru suka yo xuga xuwa gidan, labarin yanda captain ya ji da ita daren jiya ta dinga basu, da irin yanda suka rabu yau da asuba, Fauziyya da Rabi'ah suka yi wani shewa suka ce "Gaba da gabanta, ba kin tsaya sanya ba da, kin xauna kina ta hauka da fashe fashe da dambe a asibiti, to ai yanxu kin fara ganin aiki da cikawa" ita dai sai wani blushing take, Wayarta ne ya fara ring tayi masu alama duk suyi shiru daga surutun da suke, lkci daya suka yi tsit, ta daga ta kai kunne a hankali ta rausaya murya tace "My Captain" Yace "How are you feeling?" Tayi fari da ido tace "Alhmdlh, da sauki, sai dai ciwon kan ne kawai bai tafi gaba daya ba" Yace "Toh Allah ya kara lafiya" Tana wani murmushi tace "Ameen, na ga sakon da ka turo daxu, nagode My captain" yace "You are wlcm" tace "Kana lagos ne?" Yace "Yeah... Kai ma Jiddah waya" Ta d'an yatsine fuska tace "Ai kam daxu na ga ta shirya ta ci kwalliya ta fita, bata ce min komai ba nima ban ce mata ba gaskiya, don abinda ta min jiya yayi min ciwo" Yace "Ta fita?? To where?" Tace "Aa ban sani ba karya haramun, na dai ji tana waya wai ga ta nan fitowa yanxun nan, har nake tunanin ashe tana da waya don ni ban ta6a ganinta da waya ba sai yau" Shiru yayi bayan few seconds yace "Sai anjima" Tace "Alright my captain" Daga haka ya katse wayar, ta fashe da dariya tana kallon kawayenta da suka hau hailing dinta, tayi kasa da murya tace "Kun ga anjima sai in ce masa an kawota an ajiye a mota naje raka Rabi'ah da ta xo dubani na gani da idona" Abuturrab na gama waya da Aneesah ya shiga kiran Maimoon, Maimoon na dagawa bayan ta gaishesa yace "Kina ina?" Tana magana kasa kasa tace "Islamiyya" Katse wayar yayi, ya ma rasa tunanin da xai yi, sai kuma ya hau kiran Umma, bayan sun gaisa tace "Ya su Jiddah?" He was short of word at first, sai kuma yace "Alhmdlh Umma" Tace "Ahmad ya gaya maka sun koma makaranta ko bai gaya maka ba" Yace "Ya gaya min" Tace "Toh yayi kyau" sallama yayi mata yace "Dama na kira ne in gaisheku" Tace "To madallah, Allah yayi albarka" ya amsa da Ameen ya katse wayar, Ummi ya kira nan ma sai da ta tambayesa Jiddah da Aneesah hakan ya nuna masa Jiddah bata gidan, yayi mata sallama ya katse wayar....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp









Aneesah na ta shiryawa a dakinta bayan magariba, ta dau duk wani abinda ta san xata bukata a er jakarta bata da yanda xata yi ne kawai amma yau kam bata yi niyyar fitar ba ma, wayarta ne ya fara ring, ta xaro ido ganin Abuturrab ne ke kiranta, ta dauka ta xauna gefen gado tayi kasa da murya tace "Hello my Captain" Yace "How are u doing?" Ta langwabar da murya tace "Alhmdlh wllh" yace "Ya jikin?" Tace "Aa naji sauki Alhamdulillah yanxu" Yace "Ohk, ta dawo gidan?" Tace "Ehh fa, Rabi'ah just left few minutes ago na fita in rakata motarta naga ita kuma an dawo da ita ta sauka daga wata mota" Yace "Motar??" Tace "That was what i saw, dama da baka tambaya ba ba ruwana ai tunda ban san wa ya sauketa ba, xai yiwu ko d'an uwansu ne" Yayi shirun kusan second ashirin, har sai da tace "Hello" Yace "Alright, sai mun yi magana" Tace "Ohk my captain" Katse wayar tayi, ta ajiye tayi shiru, anya ya kamata ta fita yau kuwa, kar ta fita ya dawo unexpected fah, but his schedules tomorrow are so tight don karfe bakwai da rabi take jin xa su yi piloting xuwa lagos, tana ta tunane tunane wayarta ya fara ring kuma, ta duba da sauri taga shi ne, ta daga ta kai kunne tace "Hello my Captain" Yace "Can u pls go give her d phone?" Sosai hankalinta ya d'an kwanta, which means baxai dawo din ba kenan, mikewa tayi sai kuma ta tuna fa bata ji shigowar Jiddah ba har yanxu, har kawayenta suka gama jiranta suka bar gidan bata dawo ba, kilan ma gidan Umma ta tafi, da sauri tace "Kana ganin babu matsala captain, kar in kai mata kuma fa ta xageni, kaga ni bana son fitina wllh" Yace "Ki kai mata" mikewa tayi tace "Toh" daga haka ta fita daga dakin ta nufi dakin Jiddah ta bude kofar a hankali ta leka ciki taga babu ita babu alamarta, kulle kofar tayi ta fara knocking ta yanda xai ji... tana cewa "Assalamualaikum, Jiddah xa ayi maki magana a waya, Jiddah, Jiddah..." Ta kira sunanta yayi sau biyar, sai kuma ta juya tace "Ka dai ga... Tana ji wllh taki cewa komai Captain, kofar ma ta sa key" Yace "Ohk, sai da safe" Tace "Toh Allah ya kai mu captain, goben xaka dawo ne?" Yace "No, sai friday da safe in sha Allah, i will be piloting all throughout" Tace "Toh shkkn Captain Allah ya kai mu Friday din, Allah ya tsare min kai, sai mun yi magana gobe" Yace "Ameen... In sha Allah" Daga haka ya katse wayar, tayi wani murmushi tana jujjuya wayar hannunta ta koma dakinta ta karasa shirinta a hanxarce, wardrobe dinta inda take ajiye bedsheets ta bude ta daga squeezed bedsheeta din nata ta dau wani sealed abu a leda ta cusa cikin handbag din nata, tana ganin xanuwan gadon suka xubo kasa ko bin ta kansu bata yi ba ta dau Hijab dogo ta saka ta boye handbag din ta cikin hijab din ta bude dakin ta fito ta kulle da makulli ta sauka downstairs, ta daga wayarta da ya fara ring tace "Gani nan tahowa na fito yanxu" daga haka ta katse wayar ta fito compound, sosai taji dadin ganin mai gadi yana sallah a compound din yayi backing dinta, ta lallaba tana tafiya a hankali ta nufi gate, ta bude ta fice daga gidan. Jiddah na xaune parlon Hajiya Fatima sanye da Hijab din Khaleesat, Hajiya Fatima ta gama waya da mai gidanta da baya kasar bayan ta nemi izininsa na cewa xata fita, ajiye wayar tayi ta kalli er ta Rahama tace "Toh yanxu ita haka xa a fita da ita babu izinin shi mijin nata?" Aunty Rahama tace "Atohh ai komai kamawa yake Mama, ba kuma fitar shiririta xa ayi ba, da ma dai ana son yasan tana nan ne sai ki amshi numbersa a wajenta ki kirasa, amma ni wllh bana son ma yasan tana gidan nan" Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh ko dai a amshi number tasa a wajenta sai a kirasa kar ma aje ayi ta nemanta mun ajiyeta a nan" Aunty Rahama tace "Mama don Allah mu je mu dawo, ayi ta nemanta din, yasan baya son ya nemeta me yasa xai barta da wnn rikakkiyar matar su biyu kadai a gida, ai shima yayi kuskure wllh, bai yi tunanin abinda xai je ya dawo ba" Mikewa tayi ya fita, mahaifiyarta ta bi bayanta, Jiddah dai kanta na kasa, Hajiya Fatima tace "Kina da number Aliyun ai ko?" Jiddah ta girgixa kai tace "Aa bani da shi" Tace "Toh tashi mu je" Mikewa tayi ta nufi kofa suka bi bayanta, Aliyu dake xaune parlor yana jiran fitowarsu tun daxu ya mike ya fita yana rike da makullin motarsa, Jiddah da Hajiya Fatima suka xauna back seat, Aunty Rahama kuma ta xauna a gaba, cikin minti ashirin suka isa hayin rigasa, Jiddah ta nuna masu hanyar gidan nasu, bayan Aliyu yayi parking ya juya yana kallon Mum dinsa, Hajiya Fatima na kallon Jiddah tace "Xa mu shiga ciki ke ki xauna a mota kin ji" a hankali Jiddah tace "Toh" Duk suka sauka motar har Aliyu suka bar ta ita kadai, Aunty Rahama ce tayi sallama kofar xauren gidan, wani d'an tsoho ya fito yana kallonsu yace "Wa ku ke nema?" Hajiya Fatima ta gaishesa tace "Sannu baba, matar gidan fa?" Ya d'an buda ido yace "Wai matata?" Sake lekowa waje yayi yana xaro ido ganin katuwar motar dake parke a firgice yace "Bayin Allah lafiya kuwa?" Hajiya Fatima tayi murmushi tace "lafiya lau baba, kar ka wani samu damuwa" Tsohon da ya ji hankalinsa ya kwanta yace "Toh bari ayi kiranta..." Juyawa yayi ya koma ciki sai gasu sun dawo tare da matar tasa, ita ma a tsorace take kallonsu tace "Lafiya??" cikin kwantar da murya Hajiya Fatima tace "Ba ke ce Malama Hafsatu ba" Da sauri matar tace "Aa bani bace ba wllh...." Tsohon yace "Hajiya siyan gidan muka yi, ko wata uku bamu yi da dawowa nan ba..." Matar tace "Kuma tunda muka dawo nan yan bashi ke xuwa neman matar nan da kika ambata, kusan kullum sai an xo mana nan... idan ku ma bashin ya kawo ku to kuwa ance bata ma garin ta gudu, ta cinye ma jama'a kudi ta tsere" Hajiya Fatima tace "Hasbunallah, yanxu bata garin nan kuma?" Matar ta tafe hannu tace "Wllh kuwa, wannan gidan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login