Showing 264001 words to 267000 words out of 346625 words
Chapter 89 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
silar rabata da Abuturrab, Sosai xuciyarta ke k'una, can ta ja tsaki tana kallon Aneesah tace "Toh kukan uban meye haka? Shi kike ma kukan ko ita?" Aneesah dae bata ce masu komai ba kuka kawai take tana jin dama duk mafarki take yi wnn bakar rana da take witnessing, yanxu kishiyarta a ka kawo mata gida tana ji tana gani, a d'an tsawace Falmata tace "Baxa ki tashi kije ba, ni fa wllh sai in tattara kayana gobe in bar gidan nan idan baxa ki bi abubuwan da aka daura ki a kai ba don xaman lafiyan ki, wannan wacce irin yarinya ce haka don Allah" Aneesah ta goge idonta ta dake ta mike da kyar ta wuce saman duk suka bi ta da wani kallo, Aunty ta ja tsaki tace "Ni abinda ke min takaici da ita trusting dinmu da ta kasa yi har yanxu, shekarana ashirin da shidda tare da mahaifinsa sai yanda nace a gidan wllh, ko uwarsa da ta kusa shekara talatin da takwas bata isa bane, idan nace eh toh eh ne, Aa kuma Aa, to kuma waye Aliyu karamin alhaki?" Wani dariya Aunty tayi tace "Toh ko abinda ya faru kwanan nan da yanda ubansa ya birkice ma ya isa a san ba da wasa nake xama gidan ba, kwanansa biyar a Abuja shi ma sai da na dinga lallabasa ya tafi sabida aiki, to kuma waye Aliyu" Safara'u tace "Dalla rabu da ita har mijina ya mutu wllh ko kallon wata Mace bai yi da sha'awan aure, ita Aneesah ta cika hanzari ne sannan ga uban son da ta dauka ta daura masa duk shi ke cutanta" Aneesah na haurawa sama ta goge idonta sosai, tsaye tayi kofar dakin Jiddah dake ta xuba kamshi don tun daga bakin stairs ake jin kamshin, ta dake, ta danna xuciyarta ta kwankwasa kofar ta koma gefe, bayan wani lkci jin ba a amsa ba ta sake kwankwasawa sai kuma ta murda kofar ta ji a kulle, Abuturrab dake duke gaban Jiddah da ta ki daina kukan da take don ganin mutanen da tayi a parlor ya kara tsoratata, ya daga kai yana kallon kofar, lkci daya tayi tsit ita ma tana kallon kofar, gaba daya a tsorace take, mikewa yayi ya nufi kofar babu yabo babu fallasa yace "Waye?" Aneesah ta dake tace "It's me Captain" bude kofar yayi yana kallonta, tun da Jiddah ta kalleta sau daya ta dauke kai, Abuturrab ya juya ya koma ya xauna gefen gado, ta bi bayansa tana tafiya a hankali tace "Sorry for the interruption..." Ba dai wanda ya tanka ta, tana murmushi tace "Sannu da xuwa amarya" Jiddah ta hade rai ta d'an ja mayafinta ta rufe fuskarta, Aneesah ta xauna saman kujera daya dake cikin dakin, tana kirkiran murmushin karfin hali a hankali tace "Welcome to our home Jiddah, Allah ubangiji ya hade kanmu ya bamu xaman lafiya, ya kauda fitina tsakaninmu..." Ko dagowa Jiddah bata yi ba balle ta amsa mata, Aneesah tayi karfin halin cewa "Kin yi shiru... I only came to welcome u for being part of us, and i thought u will also welcome...." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka ba tare da ta shirya hakan ba, shi dai Abuturrab kallonta kawai yake, ta tashi ta nufi kofa da sauri ta fita daga dakin, Abuturrab ya kalli Jiddah kamar baxai tashi ba sai kuma ya mike ya bi bayan Aneesah, sai a sannan Jiddah ta daga kanta ta bi sa da wani kallo, yana fita dakin ta tashi ta karasa tayi locking kofar da makulli. Aneesah ta shige dakinta hakan ya sa ya bi ta cikin dakin, kuka take kamar ranta xai fita, ya tsaya bakin kofa yana kallonta yace "What's the meaning of that?" Girgixa masa kai kawai tayi, ganin yanda take kukan ya karasa cikin dakin, ta hade kanta da gado cikin kuka sosai tace "Captain baka ce min xaka min kishiya ba, baka ce min xa mu xauna tare ba, u once told me baka da burin mata biyu a rayuwanka, kullum cikin nuna min kake babu komai tsakaninka da Jiddah tun aurenku na farko, you deceived me all this while, me yasa baka gaya min gaskiya ba tun a farko in cire ran cewar ni kadai ce, me yasa tun sannan baka gaya min ba in hakura da tunanin ni kadai ce Captain, ka bar ni na sakankance, sannan ka dawo ka min haka? this is too painful to bear..." Yayi shiru yana kallonta, sai kuma ya xauna gefen gadon yana kallonta a hankali yace "We plan... But God plans best Aneesah, we were together before i met Jiddah, and i am sorry i never bargained for this, kaddara ta ce a haka, Allah ya rubuto min dole xan auri Jiddah kuma xan yi rayuwa da ita, and i am sorry to let u know that i can't live without her, babu yanda xanyi ita matata ce kamar yanda kike matata kema..." kuka kawai take kamar ranta xai fita, ya dagota ya jawota jikinsa yace "I am sorry all this happened Aneesah, ke ma kuma ba wai bana sonki bane, da bana sonki baxan aureki har in kai warhaka dake ba, i married u because i love u too" Ita dai kuka kawai take, ya rungumeta yace "Is that okay now?" Girgixa masa kai kawai take hawaye masu xafi na xuba idonta tace "Kasan ina sonka so me tsanani Captain..." yace "Yea na sani, kuma sai ki so abinda nima nake so ku xauna lafiya" Kai kawai ta gyada masa bata iya tace komai ba, yace "Kuma in sha Allah xan kwatanta adalci a tsakaninku" Sai da Abuturrab ya tabbatar ta daina kukan sannan ya mike yace "Yaushe su Aunty xa su bar gidan nan?" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, shiru yayi na wani d'an lokaci sai kuma yace "Sai da safe" Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo wasu sabbin hawayen na sauka idonta har ya fita ya kulle kofar, dakin Jiddah ya nufa yana murda kofar ya ji a kulle, ya kwankwasa Jiddah dake kwance taki motsawa balle ta tashi ta bude, kwankwasawa ya sake yi gently amma taki budewa. Juyawa yayi ya tafi bangarensa, wanka yayi ya sauya xuwa Pajamas sannan ya xauna yana danna laptop dinsa, yana son shan shayi but come to think of the set of people sitting down at the parlor ya sa shi kin fita yayi making tea din, kuma bai son ya sa Aneesah tayi masa, ma'anar abinda Jiddah tayi ne ya kasa ganewa har lkcn, ya dai ci gaba da operating laptop dinsa kawai, he doesn't even know if he is angry or not... Sai kusan karfe sha daya da rabi su Aunty suka hauro sama jin Aneesah shiru shiru kamar an aiki bawa garinsu, Aunty ta gama kare ma kofar dakin Jiddah kallo sai kuma tayi wani murmushi ta nufi dakin Aneesah, su Safara'u na biye da ita a baya suka bude kofar, kwance suka sameta tayi bacci da hawaye a fuskarta, Safara'u ta rike ha6a tace "Toh Allah ubangiji ya sa dai ba xubda mutuncinta da kimarta taje tayi a gabansu ba, kai wannan yarinya dai bata yo mu ba wllh yanda kika san ba jinin mu ba, ko kadan bata da xuciya sai hauka da shashanci" Aunty ta tada Aneesah tace "Shine kika shanya mu a parlor kamar yan iska, ya ake ciki?" Ta murxa ido a hankali, agogo ta kalla taga karfe sha biyu saura da sauri ta dira daga kan gadon ta fita dakin hawaye na taruwa idonta, duk suka bi ta da kallo Falmata tace "Toh wajen ubanwa xata, idan kun bibiya wllh bata yi abinda ku ka ce ba, xuwa tayi ta sha kukanta ta koshi ta kwanta, wnn fitina har ina ni falmata, anya xa ayi abun arxiki da er nan kuwa?" Aneesah na fita ta dinga kallon dakin Jiddah wasu hawaye na xuba idonta, she just can't imagine this, yanxu Aliyu na dakin kenan a nan xai kwana, jingina tayi da bango ta dinga rera kuka a hankali tana jin xuciyarta na mata xafi, kamar ance ta kalli part dinsa taga hasken wutan parlor na reflecting don an kashe fitilar corridor din wajen, da sauri ta karasa xuciyarta na bugawa, tura kofar tayi ta gansa xaune parlon ya daga kai yana kallonta, ta karasa ta xauna kasan carpet ta marairaice masa tace "I am not feeling okay captain, wllh ji nake kamar xaxxabi xai rufeni" yace "Toh sai ki sha paracetamol ai" Tayi shiru bata ce komai ba, amma tana son gano ko Jiddah na dakin ko bata nan, bayan few seconds a hankali tace "paracetamol dake gidan nan na bedroom din ka ai" bai ce komai ba ya mike ya nufi dakin ya shiga, da sauri ta tashi ta tafi tana leka cikin dakin taga babu jiddah, alamar dai tana can dakinta, ji tayi hankalinta ya d'an kwanta, to kenan ba a dakinta xai kwana ba? ta koma ta xauna tayi jigum xuciyarta babu dadi, fitowa yayi daga dakin rike da paracetamol din da wani spare key, ta dinga kallonsa ya mika mata paracetamol din ta amsa yace "Idan kin sha sai ki tafi ki kwanta, sai da safe" bata iya ta ce masa komai ba ya kashe laptop dinsa ya ajiye sannan ya nufi kofa, ji tayi kamar xuciyarta xai daina aiki kwata kwata at that moment, har sai da ya fita parlon sannan ta fashe da kuka sai kuma ta mike da gudu ta nufi kofar tana lekansa taga hanyar dakin Jiddah ya nufa, tana ta lekensa har ya bude kofar da makullin hannunsa sannan ya shiga ya kulle.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_
Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*
If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp
Abuturrab ya bi ta da kallo ganin da speed din da tayi use ta shige bandaki ta kulle kofar, ya karasa cikin dakin ya tsaya kusa da window ya rungume hannunsa, lkci lkci kuma yake kallon kofar bandakin, at first he pretend he isn't angry at all, yayi iya kokarin ganin bai ji haushin hakan da tayi ba, but he realize he was only deceiving himself cause he was jet angry, few days ago tayi masa rashin kunya, daxu kuma ya fita kafin ya shigo ta kulle kofa da makulli another rashin kunya, yanxu kuma ya shigo ta shige bandaki ta kulle... kallon kofar bandakin yayi for almost 3 minutes, kawai ya ji dole ma sae yayi maganinta yau, kofar ya nufa ya murda duk da ya san ta sa makulli, Jiddah dake tsaye jikin washing machine din bandakin ta wani harari kofar ta juya masa baya kamar irin yana ganinta din nan, calmly yace "Xo ki bude kofar nan right away" K'in cewa komai tayi, yace "Ba ki ji na ne?" Tayi masa shiru still, yace "Don't allow me to get that door open my self" Tace "Toh ni me xan maka idan na bude kofar, ka tafi wajen matarka mana, ai na xata a can ya kamata ka kwana tunda ka bi ta..." Shiru yayi na kusan one minute abinda ta fada na rotating a kansa, can yace "Ohk fine" Tana jin ya bude kofar dakin ya kulle, tayi ta tunanin to fita yayi? ita dai tana ta tsaye bandakin ta gaji da tsayuwa daga karshe ta durkusa, tana nan a haka har bacci ya fara damunta, xaro ido tayi ganin duhu ya gauraye bandakin lkci daya, hasken wata kadai ke reflecting ta window, mikewa tayi ta karasa kofar bandakin gabanta na faduwa ta murda makullin a hankali ta bude, without making any sound ta fito cikin dakin, ji tayi an fixgota da karfi, sbda rudewa da yanda ta gigice bata san sanda ta tsala wani ihu da karfi ba jikinta na rawa ta fara basa hakuri, da sauri ya rufe bakinta don bai ta6a xaton xata yi wannan ihun ba yace "Baki da hankali ne, baki san dare ne ba" Kuka ta fara yi tana son kwace kanta amma ya ki saketa, ba Aneesah da Falmata dake daki daya ba, har su Aunty da Safara'u dake room din karshe sae da suka ji wannan ihu na Jiddah duk da sun fara bacci ma, ita dama Aneesah ba baccin take ba falmata ce ke bacci, tun bayan da taga Abuturrab ya shiga dakin Jiddah ya kulle almost an hour ago ta wuce dakinta hawaye na xuba idonta kamar famfo, shine tun sannan take ta juye juye kan gado abin duniya yabi ya dameta, taji kamar da gaske xaxxabin karyan da ta ce masa na neman rufeta, sae kuma ga wannan ihun Jiddah da ya kara gigitata, sauka tayi daga kan gadonta ta xauna kasa tana jin kamar mashi ake soka mata a kirji ta dinga rera kuka tana imagining ihun meye Jiddah tayi, Falmata dae na kwance tana jin ta, ita ma dai takaicin ne ya cikata ta dinga jin kamar ita aka ma wannan kishiya... Ganin yanda Jiddah ta tsorata ya sa Abuturrab ya ji gwara ya kara tsoratata ya fidda rainin tsakaninsu ko xata shiga hankalinta da shi, don ya ga wani tashe raini take ji, ai kam Jiddah ta tsorata iya tsorata don taga sababbin al'amarin da kanta ya kasa iya dauka daga Abuturrab, taga abinda ya fi karfin tunaninta, bata ta6a sanin haka Abuturrab yake ba, gashi ya ki bata daman ko tari, roko ne fal bakinta da take son yi masa ko xai tausaya mata ya kyaleta amma yaki bata chance din hakan, Bai yi tunanin tsoronta ya kai haka ba, duk da babu abinda yayi niyyar mata without her consent amma sai yaga yana neman crossing boundaries dinsa shima, he was finding it hard to control himself anymore, ba karamin namijin kokari yayi ba na ganin ya kyaleta ya koma can end din gadon yayi kwanciyar upside down, ai tana samun wannan opportunity din saketa da yayi ta dira daga saman gadon ta kwala wani ihun ta fashe da kuka tana kiran Umma, ta kira Umma yayi sau biyar, gaba daya tayi mugun tsorata, bata ta6a xaton abinda ya mata ba, shi kam ina ya ga strength din hanata kukan nata da kiraye kirayen sunan Umma, kyaleta kawai yayi tayi me isarta, daga karshe ma tashi yayi ya shige bandaki ya kulle, wannan dare dai daga Aneesah har su Aunty kusan kwanan xaune suka yi, Aneesah ta ji dama ta mutu kafin safiya da wannan mugun abinda taji ma kunnenta, Falmata kuwa sae cewa take da gangan Jiddah ta dinga wannan abun duk karya ce, abu ne da aka kissa mata tun daga gida, Abuturrab ya fi awa daya a bandakin kafin ya fito wajajen karfe uku saura, switch din dakin ya kunna ya ganta kwance kasan tiles ta takure waje daya tana bacci, bai san lkcn da yayi murmushi ba ya kashe wutan ya nufeta ya duka a hankali ya kai hannu xae dauketa, wani ihun ta sakar masa a raxane, ya rufe bakinta da sauri murya can kasa yace "Ba abinda xan maki..." Daukanta yayi ya kwantar da ita saman gadon ya lullubeta da blanket, ita dai jikinta banda bari babu abinda yake, ta gama tsorata da lamarin Abuturrab, don ma ta saki jiki tayi bacci without fear, far end of the bed ya tafi ya kwanta ya juya mata baya, kasa bacci yayi gaba daya daren nan, tunaninsa kawai ya ranan da xae san jiddah xai kasance, gaba daya ya gama gano cewar raguwa ce kuma matsoraciya, ba ma wannan ba he couldn't find any way duk kokarinsa, unlike Aneesah... which the case is different on that very day... Da asuba a kan kunnen Aneesah ya bude kofa ya tafi masallaci, bai kuma tafi masallacin ba sae da ya sa ma kofar dakin Jiddah key, bayan ya gama azkar dinsa a masallaci ya shigo gidan, bude kofar dakin yayi ya ga har sannan Jiddah bata tashi ba duk da ya tasheta tayi sallah kafin ya fita, karasawa yayi ya xauna gefen gadon yana kallonta ya kai hannu fuskarta yana shafawa gently, sae kuma ya ta6a forehead dinta ya ji da dumi, a firgice ta mike xaune ta koma baya yace "Are you okay?" Ta kasa kallonsa xata sauka saman gadon ya jawota, ji yayi jikinta da xafi ta marairaice masa tace "Xan je in yi sallah" yana kallon duk jikinta yace "Are u feeling pain anywhere?" Girgixa masa kai tayi bata yarda sun hada ido ba ta wuce bandaki da sauri, gaba daya she looks afraid, ya bi ta da kallo, toh ae shi kuma ba irin wannan tsoron nasa yake son ta dinga yi ba, yana ta xaune har ta fito bandaki ta tada sallah... Bayan ta idar ta ki daga kai ta kallesa, a hankali yace "Jidderh" Kamar jira take ta fashe masa da kuka taki yarda ta kallesa, yayi kasa da murya yace "Ki je kiyi wanka ki shirya" ita dai bata ce komai ba, ya mike ya fita dakin sannan ya kulle da makulli ya tafi da makullin bangarensa, wanka yayi ya shirya cikin kananun kaya ya dau jakar laptop dinsa da makullin mota sannan ya fito, yana xaune dakin nata ya jira har ta gama shiryawa, ko da wasa bata yarda ta shirya a gabansa ba, a bandaki tayi komai, shi dai kawai murmushi yake yana danna wayarsa, bayan ta fito ya sa ta hada kayanta kala uku a karamin jaka ya amshi jakar sannan suka fito dakin, kulle kofa yayi ya sauka downstairs tana biye da shi, babu kowa a parlon infact kamar ba mutane gidan ma gaba daya, Jiddah dai ta xauna kan kujera har sannan taki yarda su hada ido da shi, shi kam sai kallonta yake don hakan da take dariya yake basa, Wayarsa ya ciro ya shiga kiran Aneesah, Aneesah dake xaune dakin