Showing 327001 words to 330000 words out of 346625 words
Chapter 110 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
ma Jiddah hoton mahaifiyarta da kakarta ba, cause bai son duk wani abu da xai sa ta kuka, barin yanda ya ga duk bata da wani kuzari, don ko d'an aikin da take yi ma yau bata yi ba, shi ma kuma bai tasheta tayi ba breakfast din ma shi ya tafasa ruwan shayi dama da akwai bread, sai karfe sha daya ya tasheta ya sa ta shirya suka taho gidan Umma don yana son kai ma Umma hoton, tana biye da shi suka shiga parlon da sallama Umma dake xaune da Ahmad ta amsa sallaman tana kallonsu, har ranta taji dadin fresh din da taga Jiddah tayi, Jiddah dai ta sunkuyar da kanta ta karasa parlon ta xauna amma gaba daya she was uncomfortable da aroma din abinci dake shigowa parlon don a bude kitchen din yake, tun tana daurewa har ta kasa ta mike da sauri tayi hanyar dakinsu Maimoon, Umma ta bi ta da kallo tace "Lafiya?" Tashi Abuturrab yayi amma sai ya ji kunyan Umma bai bi ta ba, shi kam Ahmad bin ta yayi da kallo, Umma ta mike ta bi bayanta da sauri, Ahmad ya kalli Abuturrab yace "Toh ka kyauta"
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Abuturrab na kallon Ahmad confounded yace "For What?" Ahmad ya ki ce masa komai, hakan yasa ya nufi dakinsu Maimoon amma ya kasa shiga ciki ya tsaya nan bakin kofar dakin, dariya kawai yake ba Ahmad ganin yanda duk ya wani damu, lkci lkci Ahmad ke juyawa ya kallesa yana tsaye har sannan a bakin kofar gashi ya kasa shiga, bayan 10-15 minutes Umma ta fito daga dakin, da sauri Abuturrab ya koma baya yana shafa kansa, Umma tayi masa kallo daya ta karasa cikin parlon ta xauna fuskarta babu yabo babu fallasa, ya d'an saci kallonta sannan ya shiga dakin bayan ya bude kofar a hankali ya rufe, kwance ya same Jiddah kan gado tayi backing dinsa, ya xagaya inda take ya durkusa da damuwa yace "Did u throw up baby?" A hankali ta bude ido tana kallonsa, ya dagota xaune ya xauna gefenta yace "Amai kika yi?" Ta gyada masa kai, da mamaki yace "But u ate nothing today, u took just Lipton... are okay?" Ta kwantar da kanta jikin shoulder dinsa cikin sanyin murya tace "Bana son kamshin miyan da ake yi ne, but i am okay" Da mamaki yace "Why? What about the Aroma?" Ta buda hannu tace "Nima ban sani ba, pls mu wuce gida" kamar xata masa kuka tayi maganan, Yace "Right away baby, bari in yi magana da Umma sai mu wuce" Ta gyada masa kai kawai, ya kwantar da ita gently yana kissing dogon hancinta sannan lips dinta yace "I love you" Lumshe ido tayi, tayi murmushi kawai, xai tashi ta rikosa murya can kasa tace "I want shawarma pls" Ya koma jikinta ya shafa belly dinta ya kwantar da murya yace "Right away baby" Daga haka ya mike ya fita dakin. Umma na kallonsa bayan ya shigo parlon tace "Kun je asibiti ne?" Yace "Aa Umma she is fine da muka fito gida, may be there is something she perceived that she doesn't like, but she isn't sick" Umma dai ta ta6e baki tace "Na ga alama ai" shi dai Ahmad kansa na kasa yana murmushi, Abuturrab ya mike ya ciro hoto a aljihunsa ya mika ma Umma, Umma ta amsa tana kallon hoton, sai kuma ta kallesa tace "Who are they?" Yace "Jiddah's Mum and Grandmum" Umma na kallonsa da mamaki tace "Ina ka samo?" Yace "Jiya mun je can wajen stepmom dinta shine ta bamu" Umma tace "Ikon Allah, toh ta gaya maku wani abu a kansu ne?" Yace "She knows nothing, ta dai bamu hoton kawai..." Umma tace "Allah sarki, but this will be too hard, Ta ina kake ga xa a fara yanxu?" A hankali yace "I don't know too Umma, nima naga da kamar wuya lamarin" Umma dai tayi shiru, can tace "Toh Allah ya kawo mana komai cikin sauki kawai, i will keep d picture with me" Yace "To Umma" Tace "Allah ya sa a dace" Yace "Ameen" Ahmad dai sai kallonsa yake, Abuturrab ya shafa kansa yana kallon Umma yace "Xa mu koma yanxu Umma" Umma tace "Toh na hanaku komawa ne.... Nayi ta xuba maka ido in ga gudun ruwanka a kan karatun ta naga kamar baka san a saka maka ido ba, gaya min me kake nufi da rashin barinta ta koma makaranta?" Yayi shiru sai kuma ya sunkuyar da kai yace "Xata fara Umma" Umma tace "Aa ka ajiyeta kayi ta kallo dai, shashasha kawai, kai da baka yi karatun ba xaka kai matsayin da kake yau, ance maka kowa ke karatu don aiki? To wllh kayi gaggawar mayar min da yarinya makaranta" a hankali yace "Toh Umma" Sannan ya mike, shi dai yasan iyakar to din nan bakinsa... Dakin su Maimoon ya nufa ya bude dakin, Bacci ya sameta tana yi ya karasa ya xauna kusa da ita yana shafa fuskarta ta bude ido da sauri kama hannunsa tayi kamar xata yi kuka tace "Are we not going home now?" Yace "We are baby" Ya dagota ya dau veil dinta ya mika mata ta amsa suka fito parlor, Jiddah ta gaida Ahmad ya amsa da murmushi fuskarsa yace "Ya jiki?" Abuturrab ya kallesa yace "She isn't sick" Ahmad ya gyada kai yace "Ohh yes" Abuturrab yayi ma Umma sallama, Jiddah ta karasa kusa da Umma ta durkusa tace "Umma xa mu tafi" Umma tace "Toh Allah ya tsare, ki dinga daurewa kina cin abinci ko yaya ne, kuma ki dinga kama jiki ba wannan lagwai lagwai da kike ba..." Cikin sanyi tace "Toh Umma" Umma tace "Allah ya kara lafiya" Shi dai Abuturrab kallon Umma yake, why are they even thinking she is sick, Jiddah ta kalli Umma tace "Su Maimoon fa?" Umma tace "Sun je saloon" Jiddah tace "Umma wai number me turaren da kika siya min ake tambayata" Umma tace "Wa ke tambayar ki?" Murmushi tayi tace "Wata Mama ce, she is our neighbor, ta shigo shekaranjiya shine tace kamshin yayi mata dadi in bata number me turaren" Umma tayi dariya tace "Lallai kam, ni ina xan rike number me turare, kije daki akwai wani container na turaren in jin akwai number me turaren a jiki" Tashi tayi ta tafi daki sai ga ta ta fito da daya daga container din turaren dake dakin Umma wanda a jiki aka rubuta _S_Square-Incense_ , tana kallon Abuturrab dake tsaye tace "Xaka min saving number a wayarka sai in ba mama pls" Ya ciro wayarsa yana kallonta kiris ya rage yace "Ur wish is my command Baby" kawai ya kalli Umma sai yayi maza yayi shiru, a hankali yace "Alright" Jiddah ta maida idonta kan container ta kira masa number 07030037697.... Bayan yayi saving yace "Done" Mayar ma Umma container din tayi sannan ta fito, suka kara ma Umma sallama, Jiddah na kallon Ahmad tace "Yaya Aunty Ramlah fah?" Yace "Tana gida, kin ki xuwa mana ai" Tana murmushi tace "Xan xo" yace "Ai kam xaki xo kwanan nan ai ko babu niyya" Ahmad ya rakasu har bakin mota, bayan Jiddah ta shiga front seat yana kallon Abuturrab yyi lowering voice dinsa yace "Reduce bothering her or u loose the Baby" Abuturrab ya kallesa da mamaki yace "Which Baby?" Ahmad ya daga kafada yana murmushi yace "Sai mun yi waya" Daga haka ya shige gidan, Abuturrab ya tabe baki ya xaga ya shiga motar suka bar anguwan. Sai da ya biya ya siya mata shawarma da tace tana so ya hada har da ice cream sannan suka dau hanyar gida... A hankali yake tafiya a motar ganin kamar Aneesah a kofar gidansa, ai ko yana isa dai dai gate din nasa ya ga ita ce, horn yayi mai gadi ya leko ganin motarsa ya bude gate din, Aneesah ta taso ta nufo motar da sauri, yayi zooming off into the compound, mai gadi na hanata ta hankade sa ta shige cikin gidan, Abuturrab yayi parking a parking space ya bude motar ya sauka, kasa karasawa kusa da shi Aneesah tayi hawaye na sauka idonta ta durkusa tace "Don girman Allah ka tsaya ka saurareni ko na minti biyu ne Aliyu" Abuturrab ya nufi mai gadi yana kwala masa kira a fusace, mai gadin ya taho da gudu bayan ya rufe gate din yana amsa kiran, Abuturrab na huci yace "Me nace maka a kan matar nan Salisu?" Mai gadin yace "Wllh wllh bude maka gate da nayi ne ya bata daman shigowa ciki amma kusan kullum sai ta xo kofar gidan nan har ma ta yini, ko da wasa ban ta6a bude mata gate din ba yallabai" Abuturrab ya juya yana kallon Aneesah dake durkushe tana hawaye da white bandage a hannunta, strictly yace "Look Madam.. i will assume ban ta6a sanin ki ba a rayuwata, and i think i have to report you to the police to stay away from my house because i don't know who u are, i don't know what u are up to, this my take on you... don haka tun muna mu biyu tashi ki fitar min daga gida kada in nuna maki the other bad side of me.... About ur luggages or whatever xan fito da su nan tsakar gida kusa da parking space a rufe su da sheath and anytime aka ganki da babban mota sai a bude maku gate ku kwashi kayan ku" kuka kawai take tana girgixa masa kai tace "Aliyu ka bani minti biyu don darajan iyayenka ka saurareni" Fiercely yace "Get.. out... Of my house" Ta ki tashi tana rusa kuka tana kallon Jiddah tace "Don Allah ki sa baki ya saurareni Jiddah...." a guje ta mike ganin ya nufota, tayi gate da gudu ta fita mai gadi ya kulle gate din, juyawa Abuturrab yayi yaga Jiddah tsaye, ta juya a hankali ta nufi entrance din gidan, ya bude motar ya dau abubuwan da ya siyo sannan ya bi bayanta. Bayan isha Jiddah na kwance jikin Abuturrab dake kallon wrestling a parlor, bata dade da tashi daga baccin da take tun yamma ba, ya dago kanta da damuwa yace "Baby duk yau fa baki ci komai ba, nace ki gaya min me kike son ci kada dare yayi in fita in samo maki plss" Tace "Bayan shawarman da na ci?" Yace "Noo u ate just a bite..." tace "Hakan da na ci ya isheni" Yace "I'm beginning to think if u are really okay..." Tace "Toh kasan me xan ci?" Ya xaunar da ita da kyau yace "Tell me wife, ko kano ne xan je yanxu in samo maki abinda kike so in dawo" Murmushi tayi, tayi lamo jikinsa tace "Indomie nake so with plenty Scotch bonnet pepper, with onion" Yace "Ohk xa mu iya samu a restaurant ai, bari inje in nemo maki in dawo yanxu" Ta dago kanta tayi masa wani kallo tace "Ni dai kai nake so ka dafa min, idan aka siyo a waje baxan iya ci ba" Ya d'an buda ido da mamaki yace "Really" Ta marairaice masa, ya lumshe ido ya bude yace "But idan bai yi dadi ba fa kinsan ni ba girki na iya ba baby, ba gwara in je in samo maki me dadi a duk inda yake ba yanxu" Kwanciya tayi kan kujera ta turo baki tace "Baxan ci ba" Yayi shiru yana kallonta, sai kuma a hankali yace "Ohk... But I don't know all the ingredients u listed..." tace "I will show u" tashi yayi ya nufi kitchen ta mike ta bi bayansa, tana tsaye ta jingina da cabinet ya dauko indomie din a store, ta nuna masa albasa da uban tarugun da take son yayi mata amfani da, yayi ta kallonsu yace "Are they not too much, anyway ya xan yi masu yanxu?" Tace "Wankesu xaka yi" Da wani expression yace "With gloves or what?" Tace "Ka ta6a ganin an wanke pepper da gloves?" Innocently yace "But it's harmful for the bare hands, ba yaji garesa ba? Ba shine tattasai da ake cewa ba" Tace "To da hannun xaka wanke ka cire duk hancin, ka yanka albasan" Ya fi minti daya yana bin tarugun da kallo sai kuma ya dauka yaje sink yana wankewa a hankali, tace "And baka sa ruwan indomie din ba a wuta ai" Yace "Ohk" dawowa yayi ya kunna gas ya daura ruwa a tukunya ya rufe, ya ga ta fita ta ya bi ta da kallo yana mamakin wannan aikin da ta sa shi da bai ta6a yi ba a rayuwarsa, bai ma ta6a tunanin akwai ranan da xai shiga kitchen da sunan ya sarfa abinci ba sai first night dinsu da ya shiga ya soya kwai sannan yau da tace dole shi xai yi mata indomie, ya langwabe kai yace "And i have to make it very delicious for her" Dawowa kitchen din ya ga tayi da kujeran dinning ya dinga kallonta da mamaki, ta ajiye ta xauna tsakiyar kitchen din tana kallonsa, bayan ya wanke pepper din ya juya ya kalleta yace "Toh ya xan yi da shi?" Hannu ta buda alamar bata sani ba, ya ciro wayarsa a aljihu ya shiga google... Sosai Abuturrab ya wahala kafin ya hada wannan indomie na yan gayu da Jiddah ta sa shi, idonsa sai yaji yake masa sbda albasa, ita dai ko uffan bata ce ba sai bin sa take da kallo, duk yayi kaca kaca da waje kamar kwali biyu na indomie ya dafa, ta dinga kallon indomien da ya juye a plate sai uban ruwan da ya cika kamar farfesu ga Indomien har yayi extra done, da liquid soap ya dinga wanke hannunsa a sink sannan ya juya yana kallonta a hankali yace "Na gama baby" ta tashi tace "Toh ka kawo" daga haka ta fita ta tafi parlor ta xauna, ya sauke ajiyar xuciya ya fitar da kujeran da ta shigo da ya mayar dinning sannan ya dawo ya dau indomie bayan ya saka fork a ciki ya fita ya kai mata ya ajiye gabanta, ya koma fridge ya dauko ruwa da lemon five alive ya dawo ya ajiye yana kallonta, daukan fork din tayi ta fara cin indomie din a hankali, ko taste din kirki babu sbda uban ruwan da ya cika, haka tayi ta cin abunta, ya ji dadi sosai ya xauna saman kujera yana kallonta, sai da ta ci rabin indomie din taji xuciyarta ya fara tashi ta jinginar da kanta da kujera yace "Baby what?" Ta kallesa sai kuma ta tashi ta tafi kujeran da yake ta xauna ta kwanta kusa da shi tace "Amai nake ji" Ya rungumeta yana buga bayanta gently yace "Amai kuma baby bai maki dadi bane" Tace "Yayi" haka ya dinga yi mata har taji aman ya daina damunta, ta lumshe ido jikinsa tace "Yayi min dadi sosai" murmushin jin ddi yayi yana shafa gashinta yace "I am happy my baby like it" Da safe Abuturrab ya tashi da farin ciki wanda baya misaltuwa don faduwa ce ta xo mashi dai dai da xama, Jiddah na bacci ya shirya ya tafi gida wajen Umminsa... bayan ya gaisheta ta amsa tana kallonsa ganin how good his mood was, tace "Ina Jiddar?" Yace "Tana gida Ummi" Ummi tace "Toh maa sha Allah, baka koma aiki bane?" Yace "Dama na xo ne in gaya maki aikin da na nema few years back na samu offer dinsu sun turo min ta mail... daxu na gani da asuba" Da mamaki Ummi tace "Wani aiki?" Yace "Piloting also, a private pilot, ko kin mance sanda nayi applying?" Ummi tayi shiru sai kuma tace "License or certificate din fa Aliyu, isn't it cost?" Yace "Nahh, i got that since Ummi, may be u forgot" Tace "So u mean u are tired of being an Airline transport pilot?" A hankali yace "I need more time for my self and family Ummi, i have served them in the sky for long, so xanyi resigning yanxu..." Ummi tace "Toh Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi a gareka" Yace "Ameen Ummi" Wayarta ne ya fara ring ta dauka ganin Umma ke kiranta ta daga ta kai kunne, bayan sun gaisa Umma tace "Toh munyi grandson" Ummi tace "A'a toh Alhmdlh, Alhmdlh, yaushe ta sauka?" Umma tace "Few minutes ago" Ummi tace "Toh Allah ubangiji ya raya mana, Allah yayi masu albarka" Bayan sunyi sallama Ummi ta kalli Abuturrab tace "Ramlah ta haihu" Yace "Maa sha Allah, Allah ya raya, i left my phone at home kilan Ahmad din ma ya kirani" Ummi ta mike tace "Bari in sanar ma Hajja" Daga haka ta fita daga parlon. A ranan kamar yanda Abuturrab ya fada da rana ya kira masu fitar da kayan Aneesah ya sa aka ajiye mata su kusa da parking space sannan aka lullube da Sheath din, Jiddah dai na xaune parlor don ya sa ta shirya xa su fita amma bai ce mata ga inda xa su ba, tana ta kallon yanda ake fitar da kayan Aneesah, har lkcn she is speechless she don't even know what to say to Aliyu, she don't know why she felt bad about everything that have happen, duk da bai gaya mata abinda ya sa shi sakin Aneesah ba amma har ranta bata ji dadi ba, bayan yan fitar da kayan sun gama ya sallamesu sun wuce ya dau makullin motarsa ya sauko downstairs yana kallon Jiddah ya nufeta, yana jan hancinta yace "Mu je ki ga baby" Tace "Wani baby?" Ya kashe mata ido yace "Ramlah ta haihu" tashi tayi da sauri tana wara ido tace "Don Allah da gaske?" Yace "Yea" kasa boye farin cikinta tayi tace "Shine baka gaya min tun daxu ba... Ni dai don Allah mu je ka kai ni" ya kama hannunta suka fita daga gidan, da yake an sallamesu asibiti gidan Umma suka wuce, Jiddah ta wuce dakin Umma direct bayan Maimoon ta sanar