Showing 318001 words to 321000 words out of 346625 words
Chapter 107 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
yayi ya shiga motarsa don dama Makullin motar na aljihunsa ya nufi gidansa, yana isa ya tadda Ahmad xaune cikin motar a kofar gidan, yayi parking ya sauko yana murmushi, Ahmad ma ya sauko yace "Wannan ai kanka ka siya ma sabuwar mota ba Jiddah ba, har Abuja fa naga kaje da motar, dama yaudara ce kawai kayi mana??" Abuturrab couldn't help it but laugh hard, Ahmad dai sai kallonsa yake, Abuturrab yayi patting dinsa yace "Idan ma tace bata son motar nan kuma wllh sai in canxa mata, ai aro nake yi ba komai ba, infact ko gidan nan Jiddah tace tana son in mallaka mata wllh i will do so without second thought, i will give her wholeheartedly, ba gida ko mota ba, ni kai na i belong to her, and her wish is always my command" Sake baki Ahmad yayi yana kallonsa, can ya fashe da dariya yace "Ita murhun? Ita me Awaran?" Lkci daya smile din fuskar Abuturrab yayi fading, Ahmad ya dinga dariya don ba da niyyar ya 6ata masa mood ya fadi haka ba, ya kama hannunsa suka shiga ciki yana cewa "Pulling my brothers leg" har suka shiga ciki kuma gaba daya Abuturrab ba shi da walwala duk yayi wani sanyi, Ahmad yace "I left Abuja all because of u now, don haka cheers and tell me what's up?" Abuturrab ya sauke idonsa sai kuma ya mike ya wuce sama, ba a dau lkci ba ya sauko rike da sachet din jiya da ya gani dakin Aneesah ya mika masa su yace "I need more explanation on this pls" Ahmad ya dinga juya abun a hannunsa da mamaki ya kalli Abuturrab yace "This is a prophylactic for ladies, a ina ka samo wannan?" A hankali Abuturrab yace "Dakin Aneesah" Ahmad ya bude ido sosai yana kallon Abuturrab, Abuturrab yace "Yea, i saw them yesterday" Ahmad yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to me take yi da su" Abuturrab ya jinginar da kansa da kujera, Ahmad yace "Did she know u saw it?" Abuturrab yace "I don't think so" Ahmad yayi shiru yana naxari, Abuturrab yace "kasan me ya faru?" Ahmad yace "No" A nutse Abuturrab ya shiga narrating masa yanda suka dinga yi da Aneesah har xuwa safiyan yau, da kuma lkcn da ta shigo gidan, Ahmad ya buda baki yana ta kallon Abuturrab da mamaki ko kiftawa baya yi, Abuturrab da yaji xuciyarsa na masa kuna, yayi kasa da murya yace "I'm really shock Ahmad, i couldn't sleep well yesternight, I'm still finding it hard to believe this, but i need more evidence before anything Ahmad, yanxu maganan da nake maka tana gidan Ummi taje ta shirya mata karya da gaskiya wai gidan kawarta ta tafi ta kwana... Ban ta6a sanin da gaske akwai karyan da ke girgixa mutum ba sai jiya, wllh i am shock, but all the same i am happy don duk karyan nan da ta dinga min a kan Jiddah ko sau daya ban fito na nuna ma Jiddah bacin rai na ba, I was super calm all that while, sai gashi tun ba aje ko ina ba...." Ahmad ya girgixa kai shi ma dai lamarin da alama ya girgixa sa yace "So what next Captain?" Abuturrab yace "Ba tace bata da lafiya ba? Dama nace ma Ummi xaka je ka dubata tunda mun riga munje asibiti, yanxu abinda nake so shine kawai mu siya alluran bacci mu je can gidan kayi mata, bayan tayi bacci xan yi unlocking wayarta da finger print dinta sai in binciki wayarta, and i am hoping we will find concrete evidence a wayar nata, yanxu if i should show this stuff to our parent the first thing that will come to der mind shine bata son haihuwa ne kawai, infact kowa ma haka xai yi tunani, kaga kuma ai ni bani da abinda xance..." Ahmad ya sauke wani ajiyar xuciya yace "Exactly, at first nima na xata haihuwan ne bata so, not until this ur story..." Abuturrab ya mike yace "Mu je" Tashi Ahmad that is just speechless yayi ya bi bayan Abuturrab suka fita, sai da suka fara biyawa Pharmacy ya siya alluran bacci sannan suka tafi can gidan.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_
Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*
If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp
Ahmad ya gaisa da Ummi sannan ya shiga hada alluran, Ummi ta mike bar masu parlon nata, Abuturrab dai na xaune har Ahmad ya gama ya mike, leading dinsa yayi xuwa bedroom din Ummi, ta blanket Aneesah ta lekosu a hankali don ganin wa ya shigo, sai da gabanta ya fadi da suka hada ido da Abuturrab sannan Ahmad, wani tsanarta yake ji har ransa, ya dai dake yace "Kince ma Ummi baki da lafiya bayan ni kince min kin ji sauki, so Ahmad is here xai dauraki kan wani treatment din...." Ta mike xaune tana sauke numfashi kamar gaske, cikin rawan murya tace "Wllh bana son inyi ta daga maka hankali ne kana wajen aiki My Captain, shi yasa nake ta ce maka ni naji sauki" hawaye ta fara yi tana kallonsa, Ko sauraron muryarta Abuturrab bai ma son yi, yana kallon Ahmad yace "Yi mata mu fita, i have somewhere to go m" Ta kalli Ahmad haka nan ta ji gabanta ya fadi, ta girgixa kai a hankali tace "Ni ban son wani allura gwara a bani drugs kawai in sha.... Ban son alluran" Ahmad yace "Alluran xai fi maki drugs din kuma ai" tana kara girgixa kai tace "Aa gaskiya gwara min kwaya baxan iya amsan wani allura ba bayan wa enda na amsa a baya" Kallonta kawai Abuturrab yake yi cike da mugun tsanarta, can ya juya ya fice daga dakin, da Ummi ya tafi ya hadata, Ummi ta shigo dakin tare da shi, tana kallon Aneesah tace "Ya haka ana nema maki sauki kuma kina cewa Aa Aneesah, tunda suna ga alluran ya fi sai ki bari ayi maki ai... Meye a cikin allura" Aneesah ta kasa cewa komai ta rasa me yasa gabanta ke faduwa, Ummi tace "Kiyi hakuri ayi maki kawai" Daga haka ta juya ta fita, Abuturrab ya fita shi ma, haka nan hankalinta bai kwanta ba Ahmad yayi mata alluran, sai wani hahhade masa rai take tana hararansa, dama kuma yana sane ko gaishesa bata yi ba, shima din bai ko kalleta ba bayan ya gama alluran ya juya ya fita xai yi disposing din syringe din, a parlor ya tadda Abuturrab xaune, Ahmad ya dage masa gira sannan ya fita, Abuturrab ya shafa kansa a hankali waiting to proceed for the worst, should he really do this? Yana gudun abinda xai daga masa hankali shi kam, ba a dau lkci ba Ahmad ya dawo parlon ya xauna shi ma, a hankali Abuturrab yace "So where did u leave ur wife?" Ahmad yace "Nayi dropping dinta gidan Umma" Yace "Ohk..." Ahmad na murmushi yace "Captain the once upon a time Hygienist.... Not anymore" Abuturrab ya kallesa da sauri yace "Har yanxu ma kuwa" sai kuma a hankali yace "Is just that one have to adapt to every situation he finds himself in life, i still appreciate Cleanliness, and it's still my priority...." Dariya Ahmad yayi yace "Gaskiya ne..." Lkci lkci Ahmad ke kallon agogon wrist dinsa har ya mike daga karshe ya nufi bedroom din Ummi ya tura kofar a hankali yana kallon Aneesah...., karasawa yayi ciki yaga she is already fast asleep, ya leko yana kallon Captain yayi masa alamar ya taho, captain ya mike ya shiga dakin gabansa na faduwa, jawo jakarta dake makale gefenta yayi ya bude zip din ya ciro wayar, ajiye wayar yayi ya hau bincika jakar, panties ya gani, da toothpaste and brush, with turarruka, sai kuma Rubber irin wanda ya gani a dakinta har biyu" Juyawa yayi ya kalli Ahmad dake tsaye yana kallon ikon Allah shi kam, Abuturrab ya dinga kallonta da wani expression, sai kuma ya mayar da kayan gaba daya cikin jakan ya kulle, ya dawo wayarta ya kamo hannunta a hankali ya manna finger print dinta a jiki, nan da nan wayar ya budu, sai da ya fara shiga settings yayi adding nasa finger print din yayi saving sannan yana kallon Ahmad yace "Mu je" Fita suka yi dakin xuwa cikin motar Ahmad, tun Abuturrab bai shiga wayar ba yaji xufa na keto masa all over, he don't even get why, ga gabansa da ya dinga faduwa babu kakkautawa, WhatsApp dinta ya fara shiga, Ahmad dai na xaune a maxaunin driver, shi kuma Abuturrab na xaune a kujera me xaman banxa. Alhaji Mukhtar ya fara cin karo as wanda suka yi chatting last, ya shiga chat din ya dinga scrolling yana karanta content din with mouth agape, magana ne a kan inda xa su hadu ya shigo kaduna state from Adamawa, take ce masa mai gidanta is around sai dai next week idan ya koma aiki, tunani Abuturrab ya dinga yi, su hadu su yi me? Wani business din take wanda bai sani bane, iyakar chat din kenan sai kuma dubu ashirin da tace ya tura mata, kuma ya tura mata din don ga receipt, wani chat din Barrister Ismail ya shiga, first abinda ya fara cin karo da shi shine compliment da yake mata a kan darensu na jiya how awesome it was, lkci daya jikin Abuturrab yayi sanyi qlau, ya duba date din chat din ya ga just 3 days ago ne, jinginar da kansa yayi da kujeran mota yana jin xuciyarsa na bugawa da karfi, Ahmad dai sai kallonsa yake kuma bai bukaci ya nuna masa komai a wayar ba cause it's more like his privacy, Abuturrab ya daure ya ci gaba da scrolling chat din, wanda duk erotic talks ne, wani video ya gani na minti daya da some seconds wanda tayi ma iya private part dinta ta tura masa, Abuturrab couldn't hold it any more ya fita chat din ya sauka Whatsapp din gaba daya, without looking at Ahmad a hankali yace "Na gama duba abinda xan duba Ahmad" Ahmad could sense how hurt he is from d way he sound, Ahmad ya kasa ce masa komai, Abuturrab ya kara jinginar da kansa jikin kujera ya runtse idonsa jin kansa yayi masa wani nauyi, Ahmad ya sauka motar yace "Mu Shiga ciki" Da kyar Abuturrab ya bude idonsa ya sauka daga motar, ganin abun yake kamar a mafarki, is this for real?? Ahmad ya xagayo yayi patting shoulder dinsa a hankali yace "It's well bro..." Abuturrab bai iya yace masa komai ba suka shiga gidan yana tafiya slowly. Parlor ya xauna yana kallon Ahmad alamar ya ma rasa abinda xai ce masa, Nafisah da ta shigo parlon xata tafi dakin Hajja ya bi da kallo yace "Ba ni takarda da biro" Ahmad yayi kasa da murya yace "I won't tell u no Aliyu.... Idan baka mance ba farkon aurenku na ta6a gaya maka in har mace ta saba biye biyen maxa a waje in har tayi aure idan ba wani ikon Allah ba it's hard ta iya bari, she is already used to different men, so daya baxai ta6a iya gamsar da ita ba, she can neva be contented with her husband, sai in Allah ya so ta da Rahama wllh, ban ce fa babu wa enda basu dainawa, but gaskiya sune wa enda Allah ya so da Rahamarsa kamar yanda na fada maka, don haka before coming to ur final decision, talk to Ummi first, convince her, and you can even go ahead and show her all this evidence, ba wani xancen jin kunya a issue din nan" Abuturrab ya kasa ce masa komai, duk jikinsa yayi sanyi ba kadan ba, this is the worst thing dat have happened to him na bacin rai da shock, matarsa ta sunna take harka da wasu mazan a waje, shi da yake namiji me yawo gari gari ya iya rike kansa... Ohh This is so sad, ya rike kansa with so many thoughts running his mind, can ya mike ya tafi dakin Hajja don Ummi na ciki, tun da ya shigo Ummi ke kallonsa ganin yanayinsa, Jiddah ma kallonsa take, Hajja kam dama shiru tayi ta hade rai taki kallonsa irin haushinsa take ji har sannan, Abuturrab ya shiga Whatsapp din ya mika ma Ummi, cike da karfin hali yace "Ki d'an duba Ummi" Daga haka ya juya ya fice daga dakin, Hajja ta dago da sauri tace "Ki duba me?" ummi dai sai kallon What'sapp din take bata ma san chat din wa xata shiga ba, kuma taga wayar kaman na Aneesah, Hajja ta mike a rikice tace "Ya xa ki min shiru Hauwa, matsala ya samu wajen aikin ne?" Ummi ta kalleta tace "Aa Hajja, magana ce ya bani in duba" Daga haka ta mike ta fita dakin ta koma parlonta, kamar hadin baki da Abuturrab iya chats din da ya shiga ita ma ta shiga a lkcn, and she couldn't scroll further, har ta fi sa shiga shock din ta kasa rufe baki, dai dai kan video din ita ma ta sauka what'sapp din gaba daya ta dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Abuturrab ya shigo parlon nata rike da paper da pen, Kasa kallonsa tayi, duk jikinta yayi sanyi qlau, ya xauna saman kujera yana kallonta yace "And i just have to do this Ummi, ni ba mazinaci bane, don haka baxa a so in ci gaba da rayuwa da mazinaciya ba...." Kai kawai Ummi ta iya gyada masa, ta ji tausayin d'an nata ya ratsata, Aneesah ta ci amanar aure, Cikin few minutes Abuturrab ya rubuta abinda xai rubuta a takardan ya mike yayi folding dinsa neatly ya shiga dakin ya ajiye mata a dai dai inda tana juyawa xata ga takardan sannan ya juya ya fita daga dakin, mika masa wayar Ummi da ta ma rasa abinda xata ce tayi, ya amsa yace "Xan tafi da wayar idan Abba ya dawo anjima xan dawo in basa shi ma..." Ummi tace "Aa, xan sanar masa da baki ba sai ka nuna masa wata waya ba" sae kuma kawai ya ajiye ma Ummi wayar yayi mata sallama ya fita ta bi sa da kallo. Abuturrab bai kara minti goma a gidan ba ya dau Jiddah Ahmad yayi dropping dinsu a gida, Ahmad na kallonsa bayan sun sauka yace "We will talk on phone Captain" Abuturrab ya gyada masa kai kawai, ko magana bai son yi, Ahmad yayi reverse ya bar anguwan, Tun da suka shiga parlor Jiddah ke kallon Abuturrab ganin bata ta6a ganinsa a wannan yanayin da yake ciki ba, gashi ya ki ce mata komai, har xata wuce sama ta kasa, ta dawo ta xauna dab da shi tana kallonsa a hankali tace "Are you okay?" Ya dinga kallonta bai ce komai ba ya sauke idonsa, da damuwa tace "You are not saying anything" Ya jawota jikinsa cikin sanyin murya yace "I am fully okay Jiddah, ki je ki huta probably anjima xa mu fita da su Mama" Kallonsa ta dinga yi, can ta mike ta wuce sama ya bi ta da kallo, kwanciya yayi kan 3 seater din yana jin kamar xaxxabi xai rufesa ya runtse idonsa. Kiran Magrib ya sa Abuturrab mikewa duk da ba bacci yayi ba, ya shiga bandakin dake downstairs ya fito ya tafi masallaci. Ana idarwa bayan ya dawo gida yayi minti goma xaune parlor still thinking, sai kuma ya tashi ya tafi dakin Jiddah, yana shiga dakin ya ji kamar an yaye masa damuwar da ta cika masa xuciya, xaune ya ganta can karshen gado ita ma ta yi sallan, tana ganinsa kuma ta dauke kai, ya karasa ya xauna kusa da ita yana murmushi ya kamo hannunta yace "U are sulking" xata kauda kai ya rike kanta giving her a deep kiss, don kansa ya gaji ya kyaleta, yana kallon fuskarta with much love yace "Tell me fushin me kike?" Tayi shiru bata ce komai ba, ya jawota jikinsa yace "I love you Jiddah, and I won't halt saying I am sorry over and over again, i am sorry wife...." Ta turo baki tana kallonsa tace "You are sorry for what?" Yayi kasa da murya yana murxa hannunta yace "For everything i have done to you hitherto...." Tayi murmushi a hankali ta kwanta kirjinsa cikin sanyin murya tace "You did nothing to me than molding me to who i am today, you influence me..." Ya rungumeta sosai yana shakan kamshinta me rikitarsa. Bayan isha Aneesah ta farka daga baccin da take, ta ji kanta yayi mata nauyi sosai, ta dinga bin dakin da kallo, sai kuma ta mike xaune da sauri idonta ya sauka kan farin takardan dake gefenta, dauka tayi tana jujjuya takardan that is folded neatly, haka nan kawai taji gabanta yayi mugun faduwa, sai kuma tayi tunanin ko maganin da Ahmad yayi mata prescribe ne, ta warware takardan da sauri tana kallon content din, "Ni Aliyu Usman na sake ki saki daya, na sake ki saki biyu Aneesah, duk xamanmu idan na ta6a wronging dinki in anyway, forgive me, nima ki je na yafe maki" Wani ihu ta kwala kamar xata tsaga gidan, ta sauka saman gadon dama Hijab dinta na jikinta har sannan, ta fito kamar mahaukaciya parlon Ummi taga babu kowa, main parlor ta fito taga Hajja xaune da Ummi sai Umma a parlon, ta rushe da wani matsanancin kuka ta nufi Ummi ta durkusa tana rike kafarta da karfi take cewa "Me nayi masa ya sakeni, saki ya rubuta min a takarda fa, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga ukuna, don girman Allah Ummi ku rufa min asiri, wllh ina son mijina, me nayi masa ya sakeni kina kallo" Tashi Hajja tayi tana d'an tattaka rawa tace "Rana dubu ta barawo, rana daya ta me kaya...." Haka ta dinga nanatawa tana