Showing 39001 words to 42000 words out of 346625 words

Chapter 14 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

kusa da shi ta durkusa ta ajiye spoon din, sai kuma tace "In xuba maka?" Bata jira yace komai ba ta fara dibar masa awaran a plate sannan ta mika masa, calmly yace "Kwashe su nace baxan ci ba" Sauke idonta tayi a hankali sannan ta juye ta mayar cikin warmer din ta dau tray din ta mike ta wuce kitchen. Tana fitowa ta nufi kofa xata fita ya bi ta fa kallo yace "Kee, ina xaki?" Ta juyo tace "Xan xauna a waje ne" Authoritatively yace "Dawo nan ki xauna" a hankali ta dawo parlon ta koma ta rakube inda take xaune da farko ta xauna, ya ci gaba da shan shayinsa har ya gama ya ajiye mug din ya kalli agogo dake nuna sha biyu saura, mikewa yayi ya nufi kofa ya fita parlon, sai da ya shiga motarsa sannan ya kira Umma yace mata ya tafi. Yana cikin driving wayarsa ya fara ring, kallon wayar yayi ganin me kiransa ya nemi suitable place yayi parking sannan ya daga wayar, Daga daya bangaren aka ce "Captain da kansa barka da wuni..." Abuturrab yace "Ya kake Mu'axxam?" Mu'axxam yace "Alhmdlh Oga, Kayi scarce kawai wannan satin, daxu nake tambayarka Umar ke cewa ai baka shigo ba satin nan baka jin dadi" Abuturrab yace "Ehh ina kaduna" Mu'axxam yace "Toh ya jikin Captain!" Abuturrab yace "Alhmdlh" Mu'axxam yace "To maa sha Allah ranka shi dade" Abuturrab ya jinginar da kansa da kujeran motarsa a hankali yace "Kana ji na Mu'axxam?" Mu'axxam yace "Ina jin ka Oga" Abuturrab yace "Kana da mata ne?" Mu'axxam yayi dariya yace "Aa tukunna dai Oga Allah bai kawo lkcn ba" Abuturrab ya gyara xamansa yace "Ohk, wata yarinya na sama maka ko hakan yayi maka?" Mu'axxam yace "Ikon Allah, Oga ai baxa ka min xabin da xai cutar da ni ba nasani wllh" Abuturrab yace "To kar ka damu, in sha Allah xan maka duk wani abu da ya kamata na auren tunda nasan kilan ba wai ka shirya bane yanxu ae" Mu'axxam yace "Allah sarki Oga, amma wllh nayi farin ciki da wannan labarin naka, naji dadi sosai, dama tuntuni nake son yin auren amma babu halin yi sbda kasan komai yanxu tsada, shi kansa auren tsada, duk da iyayen nawa sun ma riga mu gidan gaskiya sai kanni da yayyi, da dangi, amma ginin da nake yi a kauyenmu shi ke cinye min kudi wllh...." Abuturrab yace "Babu damuwa, Allah xai rufa asiri, amma xuwa ranan alhamis ko Juma'ah ka dau leave din kwana biyu ka xo kaduna, a nan yarinyar take, but before then ma xa mu yi magana" Mu'axxam yace "In sha Allahu kuwa Oga, Allah ubangiji ya saka maka da alkhairi, ya biya maka bukatunka na alkhairi, ya ji kan iyaye da kakanni, wllh nayi farin ciki sosai Oga" Abuturrab yace "Maa sha Allah, xa mu yi magana" Daga haka ya katse wayar, wani ajiyar xuciya ya sauke... this is now almost settled saura mutanen Hayi kuma yanxu, tada motar yayi ya ci gaba da driving din nasa. Kawu Jibril sai muxurai yake daga inda yake xaune jin abinda Abuturrab ke cewa, Hansai ta marairaice tana wuri wuri da ido tace "Ni kuwa Alhaji sai nake ga fa kamar idan mun koma gun 'yan sandan nan maganar nan babba xata xama, Iliya fa bai bari mun yi baccin kirki ba daren jiya a gidan nan, ni har na sadakar jiya xan mutu, saboda ka sanar min da xuwanka yasa na koma can gida karfe goma nayi ta jiranka sai gashi ka xo bayan azahar sannan na kawo ka wajen kawun nawa" Abuturrab yace "Ae baraxanar da yake maku ne dalilin da yasa xa aje police station din yanxu ba wani abu ba..." Abokin Kawu Jibril dake xaune tare da su yace "Ni da xa aji ta nawa kawai a tafi wajen me unguwar yankin nan gaba daya, naga yana fada aji, idan abun ya gagaresa shi sai mu koma gun 'yan sanda don gaskiya wannan yaro Iliya d'an iska ne wllh, iyayensa ma ba isa suka yi da shi ba balle wani, amma gwara a fara sako mai anguwa a lamarin nan sannan ya kai mana gaban hukuma koko ya ku ka ga?" Hansai tace "Wallahi haka ma yafi, mu je aji ta bakin me anguwan tukunna" Kallonsu kawai Abuturrab yake with surprise, su fa ko damuwa da 6atan yarinyar basa yi, damuwarsu da tashin hankalinsu Iliya da ya sako su gaba, Kawu Jibril yace "Ko ya kace Alhaji??" D'an murmushi yayi yace "Ehh hakan yayi, aje wajen nasa" Hansai ta mike tana gyara takurarren mayafinta tace "Ba sai mun sha wahalan neman abun hawa ba da motarsa ya xo babba ce duk xata kwashe mu" Abuturrab bai ce komai ba ya mike shi ma duk suka bi bayansa xuwa kofar gida, sai bayan da suka shiga motar, Hansai tace "Ita Jiddah ganinta me sauki ne wllh, nasan tsoro ne yasa ta buya wani gun, amma ko ni daya sai in samota ai, bari dai a gama da tantirin nan" Ta madubi Abuturrab ya kalleta yace "Kinsan inda take kenan?" Da sauri Hansai tace "Aa amma nasan tana nan cikin hayi babu inda xata, kasanta da shige shige da yawace yawace tunda ba jin magana take ba, baxata rasa wanda xai boyeta ba na kwanakin nan kam" Abuturrab bai kuma cewa komai ba har dai suka isa gidan mai unguwar, xuwansu ya sa shi fitowa xuwa kan tabarmansa dake shimfide a waje da wasu dattijai uku ke xaune, Bayan an gaisa Kawu Jibril yace "Toh gashi dai mun xo gareka mai unguwa...." Sanin kawun nata bai iya magana ba yasa Hansai ta amshe bayan ta maka masa harara, ta marairaice tace "Mai unguwa muna cikin tashin hankali da fargaba wallahi, don a gaskiya bamu da wani tsaro xaman mu a hayi" Mai Anguwa yace "Ikon Allah, me ke faruwa? Har kin fita takaba ne Hansai?" Hansai ta sinne kai taki basa amsansa na karshe, Nan dai ta kwashe duk abinda ke faruwa karya da gaskiya ta sanar masa tana matsar kwalla da kyar, kallonta kawai Abuturrab ke yi da mamaki don maganganu da yawa ta canxa a kan yanda shi ta gaya masa, Mai Anguwa na jinjina kai yace "Ikon Allah Iliya dai guda, d'an gidan Malam Kabiru?" Hansai na shessheka tace "Shi wllh" Yace "Toh yanxu ke kin tabbata yarinyar na nan cikin garin nan, don lafiyarta shine babban abin dubawa yanxu..." Hansai tayi saurin cewa "Tana nan anguwar wllh Mai anguwa, ai nasan babu inda xata, kawai tsorata tayi yasa ta buya, yanxu idan na dage na kwalo mata kira xata fito wllh, kawai dai a gama da xancen yaron nan iliya tukun" Mai Anguwa ya girgixa kai yace "Toh yanxu xa a min kiran shi mahaifin Iliyan da shi kansa iliyan" Hansai ta xaro ido a mugun tsorace, Mai anguwan yace "Amma ke kika haifi yarinyar?" Hansai tace "Ehh 'ya ta ce" Yace "Yanxu ki rasa wanda xaki yarda ya nemi auren yar ki sai wannan takadirin Iliya? Waye bai san halinsa ba a garin nan, garin yaya har kika amince ya auri yar ki, duk uwa ta gari ai baxata so ma yar ta wannan yaro ba" Hansai ta fara matsar kwalla tace "Wallahi mahaifinta ya rasu, yarinyar nema take ta gagareni, baxan boye maka ba wllh bin maxa take, to shi nan rufa mana asiri yayi xai aureta, bayan haka kuma da tsohon bashi tsakaninsa da mahaifinta ina jin, kuma ni bani da halin biya gaskiya shi sa kawai na sadaukar ai ba a cire ran shiryuwar d'an mutum, ni ban cire ran shi ma xai shiryu ba sannan ai gwara shi kiriniya kawai yake yi, ita fa bin maxa take wllh, duk iya bakin kokarina kan yarinyar nan ya ci tura, tsoro nake kada ta jajibo min abun kunya shi sa da ya billo da xancen aurenta bani da yanda xan yi na hakura, don kowa tsoronta yake sbda halinta, sannan yana da xuciya yaron, me yi ne shi wllh" Sake baki mai Anguwa yyi yana kallonta, Abuturrab ma kallonta yake ko kiftawa babu with shock, ta sharce majina tace "Amma tunda abu ya xo da haka in da wani shawara da taimakon da xaka mana kawai kayi mai anguwa mun baka wuka da nama don a gaskiya muna cikin hatsari" Ya sauke wani ajiyar xuciya yace "Ikon Allah, to yanxu dai xan sa ayi kiran mahaifin yaron da shi kansa yaron sai a san abun yi, idan naga sulhun baxai yiwu ba sai kawai ku tafi wajen yan sanda su ma idan abun baxai sulhuntu a gunsu ba kotu xa su tura ku, amma abu me sauki a mayar ma yaron nan kudadensa ita kuma yarinya a nema mata mai hankali wanda yaji xai iya ya aureta...." Hansai ta fashe da kuka tace "Duk ba sai an kai ga haka ba wllh, Allah xai dubemu maganar ta mutu cikin ruwan sanyi, banda ta lalata rayuwarta idonta ya bude da maxa me xai sa in yi sha'awar yi mata aure bayan abinda xan kai ta da shi ma bani da shi, duka duka shekarta fa sha bakwai, har nawa take xan dage sai na mata aure banda ta lalace" Kawu Jibril dai ba baki sai idanuwa, sauran dattijan dake xaune gun sai kallon Hansai suke wasun su na tirr da ita a xuciya, don ko min lalacewar naka baxa hadasa da lalatattce ba da yayi fice a gari, Abuturrab ya d'an yi murmushi shi dai bai ce komai ba yana kara jinjina halin Hansai a ransa. Sai da suka yi la'asar Mahaifin iliya ya iso, sai ga iliya ma da abokansa yan daba irinsa sun iso wajen, Mai anguwa ya dakatar da abokan dake kokarin xaunawa kan takalmansu don tabarman ya cika yace "Ku yi hakuri yan samari kuyi jiransa ga benchi can" Suna gunguni suka bar wajen, Abuturrab ya kafe iliya da ido, ba lebbensa ba hatta fuskarsa ya dafe saboda xuke xuke.....


07087865788📚✍🏻Kashe Ac din dakin Aunty tayi ta sauke curtains ta dawo ta xauna kusa da shi tace "Sannu, ko dai a kira Dr? amma daga ina kake haka?" Girgixa mata kai kawai yayi don bai jin ma xai iya magana, ta mike ta fita don daukan wayarta ta kira Dr din, Tana cikin dialing number likitan ta kalli Ummi tace "Baya jin dadi ne wllh" Ummi tace "Ikon Allah, to Allah ya sauwake" Aunty na gama kiran likitan ta koma daki..... Abu kamar wasa Abuturrab har da karin ruwa, he was so weak and sick, sae bayan isha family Dr din nasu ya bar gidan. Karfe goma da yan mintuna wayar Abuturrab dake gaban mirror din dakin Aunty ya fara ring Aunty ta dau wayar ganin Ahmad ne ta kyabe baki ta dauka don tun daxu yake kira, bayan ya gaisheta yace "Ya tashi Aunty?" A takaice tace "Aa..... ko minti sha biyar ban yi da fitowa daga dakin ba" Ahmad ya d'an yi shiru sannan yace "Amma jikin da sauki?" Tace "Eh toh amma har yanxu his temperature is high" Yace "Toh Allah ya sauwake, likitan ya tafi?" Aunty tace "Ehh" Yace "Toh Allah ya bashi lafiya" Aunty tace "Ameen" daga yayi mata sallama ya katse wayar, Aunty ta ajiye wayar ta koma bangaren Abuturrab ta bude kofar dakinsa, tsaye taga Ummi a dakin kusa da shi tana kallonsa, Aunty tace "Ya tashi ne?" Ummi ta juyo tace "Aa" Aunty ta karasa kusa da shi ta xauna ta sauke duvet din tana kallonsa ta kai hannu goshinsa, taji har sannan da xafi, juyawa Ummi tayi ta fita daga dakin... a hankali Abuturrab ya bude idonsa da yayi masa nauyi sbda ciwon kai, ji yake kamar ana sara masa goshinsa, Aunty tace "Sannu son, ya jikin?" Bai iya ya bata amsa ba ya sake lumshe ido, tace "Baka ci komai ba, in hado maka shayi?" Girgixa mata kai yayi, bai sake bude idonsa ba har ta ga alamar ya koma bacci, ta mike ta fita daga dakin ta kulle masa kofar. Can cikin dare Abuturrab ya farka, da kyar ya mike xaune coz he was pressed, ko hasken fitilan dakin bai so don kara masa ciwon kai yake yi, ya kalli drip din hannunsa da ya kusa rabi, ya mike tsaye da kyar yana jin jiri ya kashe ruwan ya bar cannula din kadai a hannunsa bayan yyi disconnecting dinsa daga jikin ruwan, kamar me counting steps dinsa ya nufi bandaki ya shiga duk da jirin da yake ji, da alwalansa ya fito ya xauna gefen gado ya dafe kansa, ko kadan bai son tuna komai da ya faru yau, it's making him down and weak, Bude kofar dakin aka yi Aunty ta shigo ya daga kai da sauri, tace "Ka tashi Abuturrab, sannu ya jikin" A hankali yace "Alhmdlh" Ta karasa kusa da shi tana dialing number Ahmad don kiransa ne ma ya tasheta yana fara ring tace "Duk abokinka ya takurani gashi nan ni dai" Tana fadin haka ta mika ma Abuturrab wayar, ya amsa ya kai kunne yyi shiru, daga daya bangaren Ahmad yace "How are you feeling captain?" Cikin sanyin murya yace "Alhmdlh" Ahmad yace "Ka samu ka ci wani abun kuwa?" Abuturrab yace "I will take tea now" Ahmad yace "Do so plss, Dr Shariff din ya baka drugs ne?" Abuturrab yace "I just woke up ban sani ba" Ahmad yace "Ohk, ruwan yayi rabi yanxu?" Abuturrab ya kalli drip din sannan yace "Almost" Ahmad yace "Toh Allah ya sauwake" Abuturrab yace "Ameen" sallama Ahmad yyi masa ya katse wayar, ba a dau lkci ba Aunty ta dawo dakin rike da cup din tea ta mika ma Abuturrab tace "Gashi ka samu ka sha" Ba musu ya amsa, tana nan tsaye sai da ta tabbatar ya sha shayin sannan ta amshi cup din ta fita, Mikewa yayi ya koma bathroom ya wanke bakinsa ya fito ya dau pray mat ya shimfida ya hau sannan ya tada sllh, ko da Aunty ta dawo dakin ganin yana sallah ta koma dakinta, ya jima xaune kan darduma daga bisanni ya mike a hankali ya dauke darduman ya koma kan gado, mayar da ruwan yyi ya kashe wuta ya kwanta ya lullube jikinsa yana jin kamar wani sabon xaxxabin xai sake rufesa. Da asuba duk yanda Abuturrab ya so tashi yin sllh kasawa yyi, Karfe shidda da yan mintuna Aunty ta shigo dakin, ta kunna wuta ta karasa gun gadon ta cire duvet din da ya rufe har kansa da shi, bude ido yyi a hankali, tace "Ka samu kayi sallah kuwa?" Girgixa mata kai yayi, tace "Da ka daure ka tashi, amma how are you feeling now?" A hankali yace "Alhamdulillah" mikewa yyi xaune, tace "Let me get u something to take sai ka sha magungunan idan ka idar da sallahn" Fita tayi dakin, yayi karfin halin tashi ya cire ruwan da ya rage kiris ya kare sannan ya shiga bandaki, yana sallah ta dawo dakin, ta ajiye masa cup din shayi da ledan drugs din ta nemi waje ta xauna har ya idar da sallahn sannan ta sa ya dau shayin da ta hada masa ya sha.... Karfe goma na safen Abuturrab na bedroom dinsa hannunsa rike da bowl din pepper soup, Ummi ce tsaye dakin tana kallonsa, ko minti biyar ba ayi da fitan family Dr dinsu daga dakin ba, bayan few minutes ya d'an kalli Ummin tasa, ji yayi gabansa ya fadi sosai, a hankali yace "Why don't u sit Ummi?" Ummi tace "Am okay here" Ba tare da ya kalleta ba yace "Aunty fa?" Tace "She is in the kitchen" Bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da shan pepper soup din hannunsa a hankali, Ummi tace "Kun yi magana da Abban naka? Ya kira kana bacci daxu" Ya gyada kai yace "Ehh Aunty ta bani mun yi waya" Tace "Ohk" Juyawa tayi ta fita dakin ya bi ta da kallo, lkci daya jikinsa yyi sanyi, ya ajiye bowl din hannunsa ya jingina da gadon da yake xaune, he needs someone to talk to about this unfavorable issue, he needs to share this with someone that's understandable, who will this be, rike kansa yayi yana nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.... Xuwa yamma Abuturrab ya d'an samu saukin ciwon kan dake damunsa, ya fito wanka kenan yana goge kansa da karamin towel din hannunsa aka bude kofar dakin, Ahmad ne ya shigo dakin hade da sallama, ganin Abuturrab a tsaye, ya tsaya daga bakin kofar ya rike waist dinsa yace "This is better, and I'm glad i saw u this way" Abuturrab bai ce masa komai ba, Ahmad ya d'an yi murmushi yace "Medical report dae ya xama na gaske yanxu kenan" Abuturrab ya kallesa yace "Ka taho min dashi?" Ahmad ya karasa ya xauna gefen gado yace "How are you feeling now?" Abuturrab ya nufi gaban mirror a hankali yace "Alhamdulillah" Ahmad yace "But dama baka jin dadi ne, coz naga sickness din yyi striking dinka so hard, you look lean...." Ta madubi Abuturrab ke kallonsa bai ce komai ba, Ahmad yace "Ba shiru xaka min ba, i left my work for ur sake na biyo train" Abuturrab yace "Da baka dawo ba ma ni xan kiraka ka dawo, i have been expecting you" Ahmad yace "Hope you are feeling much better now?" A hankali Abuturrab yace "Not at all.... We need to talk Ahmad" Keenly Ahmad ke kallonsa cause he can see how worried and confuse he looks, Mikewa Ahmad yyi ya karasa kusa da shi yace "Tell me what's wrong Captain?" Kasa ce masa komai Abuturrab yayi, Ahmad ya koma ya xauna yace "To ka gama shiryawa mu yi magana" Yana kallon Abuturrab har ya gama shiryawa ya dawo ya xauna gefen gadon shi ma, Ahmad yace "Me ke faruwa tell me" Abuturrab ya shafa kansa a hankali kamar me tunanin ta inda xai fara, bude kofar dakin aka yi Aunty ta shigo rike da bowl din fruit salad biyu, murmushi tayi ganin Abuturrab tace "Alhmdlh, son jiki yayi kyau,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login