Showing 294001 words to 297000 words out of 346625 words

Chapter 99 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

Allah ya tsaga min? Yanxu ba don Aliyu ya gani ba shkkn tawa ta kare kenan a duniyar nan tunda an garkame baki? Bebiye fa xan koma" Jiddah dai sai kallonta take ta rasa ma me xata ce mata, Hajja ta kara rushewa da matsanancin kuka ta rike kai tace "Allah ya isa tsakanina da Hafsah, Allah ya isa wllh, Allah kadai yasan yanda xai yi da ita" bude kofar aka yi Abuturrab ya shigo, Hajja ta kuma sakar masa kuka tace "Toh wai garkame bakin na meye Hafsah tayi niyyar yi min Aliyu? Ina da wani mugun hali ne wanda ban sani bane ku ka ki fada min ku kuma, Wllh kwadon fa ya isa a garkame bakin mutane biyar da shi, amma wai ni kadae raina ta so garkame ma baki, wayyo duniya ina xa ki damuu...." Abuturrab yayi murmushi ya xauna yace "Toh ai babu xancen garkame baki yanxu tunda asiri ya tonu, kuma wa ya gaya maki bakinki xa a rufe, kika san ko soyayya tayi niyyar kullawa tsakaninku" Hajja tace "Huhuhu da uban wa xata yi soyayya? Sai dai tayi da uwarta dake kabari wllh" Abuturrab ya shafa kansa yace "Mu xa mu tafi sai da safe" Hajja ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh cikin kwalaben xata je ta kwana?" Yayi murmushi yace "Ga dai bangarena" Hajja tace "Shkkn ta tattara kayanta kawai ta mayar can, shi kuma Usman idan yan uwansa xai bi ya nemi taimako to duk ya bi, su hada masa taro da sisi don wllh shi xai siya mata wani kayan dakin ba wani ba, Maimoon tace min Miliyan biyar ne kayan dama" Abuturrab na kallon Jiddah yace "Mu tafi...." Jiddah ta kalli Hajja, Hajja tace "Tashi ki bi mijinki, amma anya Aliyu baxa a kira Hafsah aji dalilin garkame min baki da ta so yi ba kuwa, ko kuma in shirya gobe ka kai ni gun shegiyar yayarta kyauta dake can barnawa sai naji dalilin garkame min bakin da xa ayi" Shi dai Abuturrab bai tanka ta ba sai kallon Jiddah da taki tashi yake, ya karasa kusa da ita xai dago ta, xaro ido tayi ta mike da sauri, ya kama hannunta suka nufi kofa.... Xaune ya tadda Aneesah a main parlor da dogon Hijab dinta, tana ganinsu ta dauke kai, Jiddah ta xame hannunta daga rikon da yayi mata tana biye da shi a baya har suka fita parlon, mikewa Aneesah tayi ta bi bayansu kamar yanda Ummi ta umarceta, fuskar nan nata kamar bata ta6a dariya ba, suna fita kofar gida Abuturrab ya bude motarsa yana kallon Jiddah murya can kasa yace "Ki Shiga gaba" Ita dai bata ce komai ba ya xaga xai shiga driver seat, ta kai hannu xata bude gaban motar Aneesah ta rigata budewa ta shiga ta kulle fuskarta babu yabo babu fallasa, Abuturrab ya dinga kallonta, taki yarda ta kallesa, Jiddah dai ta koma baya ta bude motar a hankali ta shiga ta xauna, tada motar yayi suka bar layin, a wani eatry ya tsaya siya masu abinci, sannan suka wuce gida.... Abuturrab ya ajiye abincin hannunsa a parlor yana kallon Jiddah da ta nemi kujera ta xauna fuskarta babu walwala, tuni Aneesah ta haura upstairs, tayi tsaye a corridor ganin kofar dakinta a wangale, ta karasa da sauri tayi turus bakin kofa gabanta na faduwa ganin yanda dakinta ya dawo kaca kaca an tarwatse komai na ciki, bin dakin ta dinga yi da kallo ta kasa kwakkwaran motsi, can ta juya ta sauko downstairs bata ko kallesu ba, kamar xata tashi sama ta nufi waje, Abuturrab dake xaune kusa da Jiddah ya bi ta da kallo, takalminta ta dauko xata wuce sama yace "Idan kin gama abinda xa kiyi ki sakko, i have one or two things to say" Ta juya ta masa kallon gefen ido sannan tayi wucewarta sama, takalmin ta saka ta shiga cikin dakin tana takawa a hankali kar ta taka kwalba, ji tayi kamar ta rushe da kuka ganin yanda furnitures dinta suka koma, tayi saurin goge hawayen da ya kawo idonta ta dau wayarta ta fito daga dakin, ta dawo parlor ta nemi kujera ta xauna tana kallon hanyar dining, Abuturrab ya ta6e baki ya gyara xamansa yace "Dama ce maki xanyi you can use the visitor room upstairs har ayi clearing dakunan naku, Jiddah kuma xata tsaya bangarena till then...." Aneesah ta kallesa da sauri, calmly tace "A saboda me?" Yace "Saboda ita ce Uwar gida, kuma haka na shirya" Shiru Aneesah tayi ta kasa cewa komai, Sai kuma ta kallesa tace "She can use the room upstairs ni kuma xan tsaya a dakin dake nan kasa" Yace "Ohk then" Mikewa tayi ta bar masu parlon ta wuce sama. Duk wani abu da Abuturrab ya san Jiddah xata bukata ya shiga dakinta kamar dai yanda Aneesah tayi da takalmi, ya dauko mata sannan ya kai mata visitor room din, sannan ya sauko yana kallonta yace "Mu je ki ci abinci a sama" Tashi tayi ya dau ledan abincin ya bi bayanta, ta shiga dakin da ya nuna mata ta xauna gefen gadon dakin, ya ajiye mata leda daya na abincin sannan ya fita, yana jin Aneesah na ta share sharen kwalabe a dakinta yayi knocking tana bude kofar ya mika mata ledan hannunsa ba tare da ya kalleta ba, ta figi ledan sannan ta kulle dakinta, bangarensa ya tafi ya ajiye nasa abincin sannan ya koma dakin da Jiddah take, ruwan wanka ya hada mata a bathroom ya fito yana kallonta yace "Na sa maki ruwa kije kiyi wanka, or do u need any help" A takaice kamar jira take tace "No" ya rungume hannu yana kallonta, sai kuma yayi murmushi yace "Ko nayi wani laifi ne?" Karasawa yyi kusa da ita ya xauna gefenta ya jawota jikinsa a hankali yace "Tell me what happen wife, ko sbda ban bari kin bi Umma ba? To me xaki bi Umma kiyi bayan ga mijin ki?" Ya cire mata hijab din jikinta murya can kasa yace "Mu je to kiyi wanka" Da sauri tace "Xan iya da kai na" Yayi murmushi yayi kissing forehead dinta yace "Toh je kiyi..." Tashi tayi ta nufi bandaki ya bi ta da kallo har ta shiga ta kulle kofar sannan ya mike ya fita dakin, nasa bangaren ya koma... Sai wajen karfe sha daya saura Abuturrab ya fito daga bangaren nasa sanye da Pajamas dinsa, ga mamakinsa Aneesah na dakin nata har sannan ta ki sauka downstairs, ya kuma gane tana dakin nata ne ta dalilin waka da ta kunna, ya bude kofar dakin Jiddah ya ganta kwance gefen gado tana sanye da rigan baccinta dogo har kasa, ya kalli Abincin da ya ajiye mata tun daxu, da mamaki yace "Baki ci ba wife? Why? Ko baki son shinkafan ne? Tell me what u want to eat" Dagota yayi ya xauna kusa da ita yana kallonta da lumsassun idonsa, ya rungumeta a hankali yace "Jiddah" Tace "Uhm" yace "Ki sake jikinki da ni pls, ko da akwai wani abu dake xuciyarki game da ni ne har yanxu? Tell me plss" cikin sanyin murya tace "Ba komai" Yace "Har yanxu kina tuna da ko?" Ta lumshe idonta tace "Ehh" yace "Gaya min me kike tunawa..." A hankali tace "Ina tuna...." Sai kuma tayi shiru, ya kalleta, kin bude idonta tayi, underneath his breathe yace "Tell me plss" murmushi ya ga tayi sannan tace "Kawai na tuna lkcn da nace maka babu Awara" ya buda idonsa sosai yace "Really?" Tace "Uhm, da kuma lkcn da ka xo kace.... In yi hakuri" Murmushi kawai yake yana kallon kyakkyawan fuskarta, ya kai bakinsa kunnenta a hankali yace "Ni kuma ina tuna lkcn da na dinga ganin ki a sararin samaniya a duk sanda nake piloting jirgi, duk na waiga a sky ke nake gani" ta bude ido a hankali tana kallonsa, Dagota yayi ya dau abincin nata da bata ci ba ya fita dakin da ita yana rike da hannunta suka tafi bangarensa, a nan parlonsa ya xaunar da ita ya bude abincin ya dau cokali ya deba ya kai bakinta, ta kai hannu xata amshi cokalin tace "Xan ci da kai na" Yace "Aa ni xan baki" babu yanda ta iya haka ya dinga 6ata abincin da kansa, sai dai bata ci da yawa ba, ya kyaleta ta tafi bathroom ta wanke bakinta, kafin ta fito har yaje dakinta ya dauko mata drugs dinta, ya bata ta sha sannan ta kwanta, ya gama abinda xai yi a laptop dinsa ya mike ya kulle kofar dakin ya dawo ya kwanta kusa da ita, ganin kamar tayi bacci don idonta a lumshe suke ya kwanta side dinta not wanting to disturb her yana shakan kamshinta me dadi da saka nutsuwa, Lumshe ido yayi shi ma, yana tunanin da ya tafka asara babba in har ya rasa Jiddah, kasa daurewa yayi, yayi wrapping dinta jikinsa, lkci daya ya ga ta juyo ta rufe fuskarta a kirjinsa a hankali tace "I really appreciate the car, Allah ya kara budi da daukaka, Allah ya kare ka ya tsare ka duk inda xaka shiga, Allah ya bani ikon kyautata maka kamar yanda ka yi min tun daga watanni sha daya da suka wuce har xuwa yanxu, i know I can't pay u, i.... " Kasa ci gaba tayi Hawaye na sauka idonta, cikin rawan murya tace "U stoop too low for my sake, duk da bambanci me taxara dake tsakaninmu a komai na rayuwa, u neva left me, u were der throughout... Ur sacrifice will for ever remain in my memory, how can i ever pay for this?"




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;

Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697








Abuturrab was Speechless.... ya rungumeta sosai, wani sabon sonta na fixgarsa ya rufe ido cikin sanyayyan muryarsa yace "I have a lot to say to you but not today, i will reserve it for another sweet night, they are so many lovely night to come...." Ita dai bata bude idonta ba tana sauke numfashi a hankali. Washegari da asuba Abuturrab na dawowa masallaci har ya nufi bangarensa sae kuma ya dawo yana kallon kofar dakin Aneesah ya karasa ya bude kofar dakin yana kallon ciki, kwance ya ganta kan manyan duvets dinta guda biyu da ta shimfida a kasan tiles daga gefen gadonta, ya karasa cikin dakin ya kai hannu ya buga duvet din, ta bude ido yace "Sallah" Daga haka ya mike ya fita dakin ya koma bangarensa, xaune ya tadda Jiddah kan darduma tana azkar dinta a xuciya, ya xauna gefen gado ta daga kai a hankali ta kallesa, bayan wani lkci tace "Ina kwana" kallonta kawai yake, ta mike ta dauke darduman da tayi sallah ya tashi shi ma ya nufeta ya jawota jikinsa yace "Good morning Jiddatul Khair" daga kai tayi ta kallesa ya sakar mata murmushi yace "How was ur night?" A hankali tace "Alhmdlh" yace "Let sleep a little more" Kafin ta ce komai ya ja ta saman gadon suka kwanta, sae da yayi cuddling dinta iya son ransa sannan ya kyaleta, har bacci ya fara daukarta ta bude ido da sauri tana kallonsa taga ya koma baccin, kallon dogon hancinsa ta dinga yi da eyebrows dinsa, ta sauke idonta a hankali ta xame jikinta daga nasa ta sauka daga saman gadon ta fita parlonsa agogo ta kalla taga bakwai saura na safe, ta daure gashinta da yayi scatter waje daya sannan ta fita parlon ta sauka downstairs, sae da ta fara share ko ina a parlon tayi mopping, kayan kallon ma duk ta gogesu, parlon ya dawo wani fess da shi, da alamar an dade bai samu irin wannan gyaran ba, ta haura sama ta bude kofar dakinta a hankali tana kallon ciki, takalminta ta tafi ta dauko a downstairs sannan ta dawo dakin ta saka takalmin ta shiga cikin dakin da shi, burner dinta dake ajiye gefen madubi ta dauka sannan ta samu ta harhada turarrukan wuta a wani kwalba da bai karasa fashewa ba ta sauko downstairs ta jona burner din a socket, ta debi turaren ta xuba a ciki ta mike, kitchen ta wuce, sae da tayi minti daya tsaye tana kare ma kitchen din kallo snn ta girgixa kai, ta fara tidying din ko ina har cikin store ta fitar da duk kwalayen da babu komai ciki ta kofar backyard, bayan kitchen din ya dawo a bit tidy ta fara wanke wanken duk plates da cups, sai kusan karfe takwas da rabi ta gama da kitchen din, ta goge ko ina ta wanke abinda xata iya wankewa a jikin gas ta goge na gogewa, tayi dusting ko ina, kan kace me kitchen din ya dawo so sparkling kamar ba shi ba... gas ta kunna ta daura ruwan Lipton, ta duba taga babu kayan kamshi, kawai ta debi irish ta fara ferewa, dicing it almost equally, tana son making Crispy french fries na dankalin ne ba irin wanda aka saba soyawa ba, bayan ta wanke dankalin da ta yayyanka ta bar sa cikin ruwa ya d'an jiku na wasu mintuna sannan ta wuce sama, corridor din rooms da bata share ba ta share tayi mopping, sai kuma ta shiga part din Abuturrab, parlon kadai ta gyara tsaf nan ma ta goge da kayan kallon, ta koma downstairs ta dauko burnern turaren wuta ta jona a parlon nasa sannan ta sauka ta koma kitchen, paper towel ta shimfida saman tray, ta xuba dankalin da ta tsane daga ruwa ta dau wani paper towel din, patting the potatoes very dry, bayan nan ta daura veg oil a saman gas heating it for about just 300° Fahrenheit, wato man bai yi wani xafi ba, bayan nan ta xuba wasu quantity na dice Irish din a cikin man gyadan, ta soya dankalin for just 3mins sannan ta kwashe ta xuba su a kan wani paper towel din, mutum na iya ajiyesa a freezer a hakan har xuwa sanda xai yi amfani da shi even if not that day, amma tunda ita a lkcn xa a ci, barinsa kawai tayi ya huce, ta tafi tana yanke yanken abinda xata soya kwai da shi, bayan ta gama ta juye ruwan Lipton dake tafasa cikin flask, ta duba dankalin da ya d'an huce ta barbada masa a little quantity of salt sannan ta sake daura man gyadan a wuta ta bar shi yayi xafin 400° Fahrenheit sannan ta xuba irish din, ta soya shi dai dai yanda take so, cikin minti sha biyar ta gama soya har da eggs din sannan ta fita da warmer din dankali da kwan ta kai saman dining, ta dawo ta kara gyara kitchen din kamar bata yi girki a ciki ba ta koma sama, dakinta ta shiga da takalmi a kafarta ta tafi bandaki tayi wanka ta fito, bayan ta dau abubuwan da xata dauka ta koma can dakin baki ta shirya, bayan ta gama shafe shafenta ta dau doguwar riga na atamfa ta saka ta daura dankwali, sosai kayan yayi mata kyau ta dawo sak amaryarta, lallen da ya haska hannunta sai sheki yake gwanin sha'awa, babu abinda ta shafa a fuskarta banda kwalli sai man lebbe, amma kyan da tayi ba a cewa komai, ta kalli agogo dake nuna goma da minti biyar ta mike ta fita dakin, dae dae nan Aneesah ta fito daga nata dakin sanye da kayan bacci, Suna hada ido Jiddah ta dauke kanta kamar yanda Aneesan ma tayi da sauri, ko tsayawa bata yi ba ta sauka downstairs abun ta, kamar ance Jiddah ta juya taga Abuturrab shi ma ya shirya cikin kananun kaya lkci daya kamshin turarensa ya xagaye corridor din, ya d'an kalli Aneesah da har ta kai downstairs don bata gansa ba ma, ya karasa gun Jiddah ya rungumota jikinsa yayi mata light french kiss, underneath his breathe yace "U look beautiful" A hankali tace "Thank you" ya xame dankwalinta yayi kissing bak'in gashinta me tsantsi sai kuma ya sauke lips dinsa xuwa wuyanta, jin taku a stairs ya saketa da sauri ya koma baya, Aneesah ta hauro saman tayi masu kallo daya ta yi hanyar dakinta, ya bi ta da kallon gefen ido, kafin ta shiga dakin yace "Good morning" Ta watsa masa wani kallo tace "Same" Daga haka ta shige dakinta, tuni Jiddah ta sauka downstairs, murmushi yayi ya shafa kansa sannan shi ma ya sauka. Ko kadan Abuturrab bai yi mamakin abubuwan da Jiddah tayi ba, da yanda tayi transforming kitchen da parlon gida, he was so happy ya xauna gefenta yace "Allah ya maki albarka Wife, a haka gidan nan yake a ko da yaushe kafin ki bar sa" Ita dai ko kallonsa bata yi ba, ya bude warmer din ya dau irish daya ya kai baki, ya juya ido bayan few seconds yace "U made this or u bought it??" Still ta ki cewa komai, sauka kasa yayi ya xauna saman carpet ya tankwash kafa ya bude kwan ya dau


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login