Showing 219001 words to 222000 words out of 346625 words

Chapter 74 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

girman Allah kayi hakuri yaya, naje kulle kofa ne sai ka gan ni..." Bai saurareta ba ya bude kofar kitchen din ya fita yana rike da hannunta.... Umma ce ta fito parlor tace "Au, tafiya yayi shashashan?" Babu kowa parlon balle a bata amsa, Ta wuce dakinsu Jiddah taga Jiddah kadai a dakin tace "Aliyun ya tafi ne?" Jiddah tace "Ina daki ban sani ba" Umma tace "Toh ga shi ki amso min kati na dubu daya a waje" Jiddah ta d'an xaro ido amma bata ce komai ba ta amshi kudin gabanta na faduwa, Umma na fita dakin ta saka hijab dinta ta fita ita ma, duk jikinta a sanyaye ta fita compound, tana isa gate ta leka waje ta ga motar Ahmad instead, amma Abuturrab ne a ciki Maimoon na tsaye daga window din kusa da shi ta daddage tana cewa "Ni dai wllh ka tura yanxu kafin ka tafi yaya, haka kawai idan ka je ka manta bayan na sanka da mantuwa, kawai bari in kira maka account number din ai yana kai na" Ko kallonsu Jiddah bata sake yi ba ta nufi kantin da xata amso kati, Abuturrab na danna wayarsa yace "Call the account number" tana washe baki ta shiga kira masa account number dinta har ta gama, snn ta fara kallon wayarta dake hannunta tana murmushi, cikin few seconds sai ga alert, ta duba da sauri taga dubu hamsin, wani tsalle ta doka tana tafe hannu sannan tayi masa blow din kisses tace "Nagode sosai yayana, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara maka budi, Allah ya kai mana kai lafiya ya dawo da kai lafiya" Komawa baya tayi ganin ya tada motarsa tana daga masa hannu har ya bar layin, baki har kunne ta shige cikin gida, Jiddah ma ta shiga gidan don duk tana kallon abinda Maimoon take a titi.... Dakin Umma jiddah ta tafi ta kai mata katin sannan ta fito ta shiga nasu dakin, gaban madubi ta tafi ta dau takardan da ta ajiye bayan ta shigo dakin daxu, daukan takardan tayi ta shiga warwarewa, haka kawai ta ji gabanta na faduwa, ganin ta kusa gama budesa ta rufe idonta, sai da ta warware gaba daya sannan ta bude idonta a hankali tana kallon content din takardan gabanta na faduwa, "Ni ba matarsa ba, ni ba muharramarsa ba... amma yake min wasu abubuwa da bai dace ba a addininmu, bayan duk wani da yasan karatun addinin nan namu yasan haramcin yin abinda yake yi, ya kuma san hukuncin wanda ya aikata hakan, kullum tunanina wanda xan kai ma kararsa... ya takura ni, ya takura ma rayuwata bayan kuma ya sakeni kowa kuma ya shaida ya sakeni....." Boldly daga kasan rubutun aka rubuta "Ur mentality Jidderh!!! And I know u might be questioning my fate, amma ki saka a ranki ba dai dai kike da sauran yan matan da ke gaban iyayensu ba yanxu, you ain't of the same level with them... abu kadan xa ki yi Allah yayi fushi da ke! ... no doubt na fi ki sanin addininmu, limit ur interaction with MALE, limit ur going out, and by so doing, u are respecting ur religion" Jiddah ta karanta content din takardan nan yayi sau biyar amma ba abinda ta gane, da ta dauko hanyar ganewa sai abun ya ruguje kan ta kai karshe, a hankali ta linke takardan ta yaga, sai da tayi masa pieces sannan ta tafi ta bude window ta watsar, Maimoon ta shigo dakin ta ajiye wayarta gaban mirror tace "Ke bikin kawar nan tawa fa sati me xuwa ne, ina ta son in kira Aunty Ramlah ince ta baki waya in gaya maki muna da biki, kuma ba karamin casu xa ayi ba, hope kun gama exams before then?" Jiddah ta tafi ta xauna gefen gado tana duba farcenta tace "Ban gama ba" Ta gefen ido Maimoon ta kalleta ta d'an ta6e baki ta nufi kofa tana cewa "Ko da yake ke ai sai da izini, mu din dai" Daga haka ta fice, Jiddah ta bi ta da kallo. Bayan sati daya Jiddah suka gama exams suka yi hutu ta dawo gidan Umma yin hutu... Ranan friday ita da Maimoon da Safiyya suka shirya xa su gaida Ummi, Da yake driver baya nan, Umma ta basu kudin adaidaita tana sake jaddada masu kar su kwana saboda Islamiyya gobe, Maimoon tace "Haba Umma karfe biyar na yi xa mu juyo, har sun nufi kofa Maimoon ta kalli Jiddah tace "Anya baxa ki sa Hijab ba Jiddah?" Safiyya tace "Saboda me?" Maimoon tace "A'a ba saboda komai ba, gani nayi ya fi mutunci" Daga sama har kasa Safiyya ta kalleta tace "Shi yasa naga kin sa Hijab din ke ai" Jiddah tayi ficewarta bata sake sauraron Maimoon ba, Safiyya tace "Duk wani harka na iyayi kin fi kowa iyawa" Maimoon tace "Aa daga magana sai cibi ya xama Kari, ni dai ba kawai suggestion na kawo ba" Safiyya tace "Why didn't u suggest that for ur self??" Maimoon tayi ficewarta tayi banxa da ita. Suna isa gidan direct bangaren Ummi suka wuce, Aneesah na xaune parlon da kanwar mamarta Safara'u da ta tare a gidanta tun bayan da Aliyu ya bar kasar, Ummi ma na parlon alamar dai su ma xuwansu kenan, Maimoon na ganin Aneesah ta hade rai tana kallon Ummi tace "Ummi ina yini?" Ummi tace "Lafiya lau Maimuna, daga gida ku ke haka?" Maimoon tace "Ehh wllh Ummi, Hajja na nan?" Ummi tace "Hajja ai tana Bauchi" Maimoon tace "Ohk" daga haka ta wuce dakin Ummi, Aneesah ta bi ta da kallo, Jiddah ma ta durkusa ta gaida Ummi, Ummi ta amsa da fara'a, wani kallo Aneesah ta dinga yi ma Jiddah kamar ta ga kashi, Jiddah ta kasa kin gaida Safara'u ganin babba ce, Aneesah na jin ta gaida Safara'u tayi ma Safara'un alamar kar ta amsa ta hanyar ta6a ta da sauri, ai ko Safara'u taki amsawa, Safiyya ta gaida Ummi sannan ta gaida Aneesah da Safara'u ta mike ta wuce dakin Ummi, Ummi na kallon jiddah tace "Tashi ki bi su ko" Mikewa jiddah tayi ta bi bayansu, Aneesah dai sai kallonta ta gefen ido take, ta rasa dalilin da yasa da taga Jiddah sai hankalinta ya d'an tashi, Safiya ce tsaye tana kallon Maimoon tace "Me yasa baki gaida Aunty Aneesah ba?" Maimoon da ke kwance kan gadon Ummi ta mike tace "Wacece kuma Anty Aneesah? Me na hada da ita da xan gaisheta?" Safiyya tace "Matar Yaya Aliyun??" Maimoon tayi wani dariya tace "Ta jira dai taga matar tasa ta ainahi... Wannan matar me yi ma mutane kallon rainin hankali da walakanci ne xan gaishe da, ji fa ranan da muka je gidanta abinda ta mana har xaki ce in gaisheta, a da nayi vow har in mutu baxan sake komawa gidan yaya Aliyu ba, amma dai nayi istigifari kwanan nan don can ne ma dabar mu idan Allah ya so nan ba da dadewa ba, sai ta raina kanta wllh, don ni tattara kayana ma xanyi in koma gidan sai dai in Umma ce ta hanani ko shi ya korani" Daga Safiyya har Jiddah dai kallonta kawai suke, ta murguda baki ta mike ta fice daga dakin yanda xata sake bin gaban Aneesah ba tare da ta gaisheta ba, ai ko Aneesah ta bi ta da kallo kasa kasa xuciyarta na tafarfasa har ta fita parlon. Kamar yanda suka sanar ma Umma karfe biyar suka fara shirin komawa gida, Ummi ta basu kudin mota sannan tace "Amma fa ku shiga ku sallami Aunty duk da bata dade da dawowa ba" Sallama suka mata suka fita, Jiddah tayi pretend kamar xata je ta sha ruwa, Maimoon da Safiyya suka shiga part din Aunty, Tana xaune parlonta da Aneesah da Safara'u, suna gaisheta ta mike rai bace tace "Wato ke Maimoon don baki da kunya baki gaji kunya ba ita Aneesar xa ki gani ki ki gaisarwa ki wuce don Ubanki??" Maimoon ta tsaya tana mata kallon tara saura amma taki cewa komai, Aunty na tafe hannu tace "Maxa fitar min daga parlor kada in rotsa maki kai, shegiya fitsararriya kawai" Aneesah tace "Ae kawai da kin kyaleni da ita Aunty, ita karamar alhaki ma?? Wllh so nayi watarana Allah ya kawota gidana in mata koran kare, uwar me gaisuwarta xai kare ni da shi dama?" Maimoon tayi wani dariya tace "A gidan yayan nawa xa ki yi min koran kare??" Aneesah ta mike tana huci tace "Kya dai je ki nemi yayanki amma ba Aliyu ba, idan kuma da akwai abinda ya fi koran kare wllh sai na aiwatar gareki in har rashin hankalinki ya ja ki xuwa gidana, don wannan gidan a yanxu ko shi Aliyun ba shi da wani say a kansa, yau da Ramlah ko Nafisah ko Aisha ce suka ki gaisheni shine xan ji takaici amma banda ke karere gayyar tsiya" Maimoon tayi wani shewa tace "To mu xuba dake shege ka fasa, kuma wannan gidan da kike takama da shi sai ya gagareki xama kwanan nan ba da wani dadewa ba wllh, abota xa ki kulla da sleepless night very soon..." Da gudu Maimoon ta fice daga parlon tana murguda baki ganin Aunty ta yo kanta tana kunduma mata wasu axababben xagi kamar bamagujiya, ita dai Safiyya na tsaye kamar shashasha, Safara'u kuwa sai dannan xuciyarta take tunda Aunty da Aneesah nayi ita bai kamata ta sa baki ba, Aunty tayi mata tsawa tace "Fita kema, gantalallu gayyar tsiya kawai...." Safiyya bata ce komai ba ta fita daga parlon, tuni Maimoon ta ja Jiddah suka fice daga gidan ranta fess ta fesa masu rashin kunya iya rashin kunya, sai da suka nufi titi Safiyya ke cewa "Wllh baki ji Maimoon, baki jin magana, Umma ta hanaki wannan halin kin ki, idan ma sun xageki meye na biyesu bayan kin san ba sa'anninki bane su??" Maimoon tana tafe hannu tace "Ba ruwana da tsufansu, ai ance respect begets respect, Respect should only be given to he who deserves ita, wato dai he who respect his or her self, basu yi respecting din kansu ba balle inyi respecting dinsu, haka kawai a xagi ubana dake kabari a kan wata banxa jaka can kaxama da ita kike expecting inyi shiru kamar ban san ciwon kai na ba?? To wllh ban rama yanda nake so ba ma, sai ranan da muka fara bata sleepless night a gidanta sannan xata gane ni ba kanwar lasa bace..." Wani shewa Maimoon tayi cike da farin ciki, Safiyya tace "Ke da wa xaki bata sleepless night din" Maimoon ta bude hannu tace "Ohoo a xuba ido a gani, shi sa Jiddah asirinta a rufe taki shiga nima da na sani wllh kawai ce ma Ummi xanyi to amma inyi wucewata, uwata ce ita da dole sai na gaisheta??" Safiyya tace "Ni dai ba ruwana ki daina wnn halin da kike...." Maimoon tayi gaba ta ki sauraran Safiyya kuma, Jiddah dai tafiyarta kawai take bata ce masu komai ba, a ranta kuwa taji dadin dubaran da tayi na shigewa kitchen da yau har da ita xa a hada a xage ubanta dake kabari. Bayan kwana biyu Jiddah na xaune kan darduma ta idar da isha Maimoon ta shigo rike da wayarta dake kare kunnenta, ta nufeta ta mika mata wayar tace "Kema ku gaisa, Safiyya ma sun gaisa, har da Umma ma sun gaisa" Jiddah na kallonta ta amshi wayar, screen din ta fara kalla ta ga "Yaya A" ta kai wayar kunne tayi shiru, Maimoon tace "Toh kiyi magana mana ai bai katse ba fa" daga daya bangaren taji yace "Shiru kika yi?" Lokaci daya ta dau muryarsa wanda hakan ya ja mata faduwar gaba, ta d'an hade rai a hnkli tace "Ina yini" Yace "How are you?" Tace "Lafiya" juyawa Maimoon tayi ta lallaba ta fita dakin....




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;

Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697



Kallon screen din wayar Jiddah tayi jin shirun yyi yawa, taga har sannan bai katse ba, ta d'an turo baki tace "Ina jin ka" Yace "Ohk... Ae ban san kina ji ba" mikewa tayi ta nufi kofa ta fita, ganin Maimoon a xaune parlor ta tafi ta dungurar mata da wayarta ta juya ta koma daki... Umma ce xaune parlor tare da Maimoon, Jiddah kuma na xaune dinning area rike da littafi a hannunta tana dubawa, Umma na kallon Maimoon tace "Ke a ina ku ka yi magana da shi kika san bashi da lafiya?" Maimoon tace "Ba muna chatting ba Umma, wani lokacin ma har video call muna yi" Umma ta kyabe baki tace "Toh Allah ya basa lafiya" Maimoon tace "Ameen, Umma har fa ya je asibiti yace min" Umma tace "Ikon Allah, kila change of weather ne, barin yanda ya dade bai fita waje ba, Allah ya basa lafiya" Maimoon tace "Dama nima nace change of weather gashi he still have some months kafin ya dawo" Umma tace "To kuma wannan shirin gulman da ku ka tsiri yi da shi na meye?" Dariya Maimoon tayi har da kwanciya, tace "Toh ba ya ga ya tafi inda baxae dinga ganin mu ba Umma, gashi bashi da kowa a can, kinga yanxu da a kasar nan ne bashi da lafiya ae da duk mun je duba sa har da abinci... To amma yanxu babu me kula da shi" Umma dai tayi dariya kawai, can tace "Dama yaje da matar tasa ne da sauki, to bai je ba, kuma ranan da Ummi tayi masa magana cewa yyi kawai bai da niyyar xuwa da ita ne but he is allowed to go with his wife" Maimoon ta rike ha6a tace "Toh ba sonta yake ba Umma, don dai kawai baxai yiwu ya tafi da warce yake son bane amma ni nasan da ya tafi da ita" Umma tace "Wacece ita warce yake son?" Maimoon ta d'an rufe baki tace "Aa wai imagining kawai nake" Umma ta tabe baki tace "Haka yace maki baya son matar tasa? Da baya sonta ai baxai aureta ba" Maimoon dai bata sake cewa komai ba sai murmushi take, Safiyya ta fito daga daki rike da wayar Maimoon dake ring ta mika mata sannan ta koma dakin, mikewa Maimoon tayi bayan ta saci kallon Umma ta wuce dakin da sauri, tsaye tayi bakin kofa dai dai nn wayar ya katse, tabe baki tayi sai gashi an sake kira ta daga ta kai kunne tare da sallama, cikin faram faram tace "Lafiya lau wllh Engineer, amma kuma bata dawo ba har yau fa...." ta d'an yi shiru sai kuma ta kyabe baki tace "Toh gaskiya nima ban sani ba dai, amma babu rana kam, kasan nace maka ta bar nan sbda karatu, mu ma sai season season muke ganinta..." Da sauri tace "Toh ae ita ma matar Ya Ahmad din ba wayar gareta ba ya fada cikin ruwa..." Ta d'an sosa kai tace "Toh ina jin dai nan da sati biyu ne xan je can gidan sbda kaga baxa mu je mu tarar ma yaya Ahmad a gidansa ba, amma dai idan naje din xan bata in sha Allah" Ta kara da cewa "Toh shkkn bye" katse wayar tayi ta juya xata fita Safiyya tace "Wacece bata nan?" Maimoon ta juyo ta kalleta bata amsata ba ta fita dakin Safiyya ta bi ta da kallo... Tunda Maimoon ta fito Jiddah ke kallonta, Umma da ta bi ta da kallo tace "Waye ya kiraki don munafurci kika shiga daki Maimoon?" Maimoon ta sosa kai tana er dariya tace "Aa Umma kawata ce ta kirani tace akwai gist daxu ina aiki ban samu mun yi waya ba sai yanxu ta sake kira" Wani kallo Umma ta dinga yi mata ta wuce kitchen da sauri tana dariya... Da daddare Jiddah na kwance amma ba bacci take ba, tana son yin baccin amma ta rasa abinda yasa ta kasa, sannan tana jin abu da ita kanta bata san meye ba ya tsaya mata a rai yana damunta, Maimoon ce ta shigo dakin bayan ta gama kallon da take a parlor, ajiye wayarta tayi gefen gado ta shiga bandaki, Jiddah ta bi ta da kallo, sae da taga ta kulle kofar bandakin sannan ta mike xaune ta jawo wayar a hankali don bai shiga lock ba, call logs ta fara shiga ta d'an yi scrolling sae kuma ta fita da sauri ta shiga application din WhatsApp, second to the last chat din da ta ga an sa Yaya A... Ta shiga tana sake kallon kofar bandakin, dai dai nan taji an bude kofar saboda rudewa kawai ta kashe wayar tana kan What'sapp din ta mayar da sauri ta ajiye ta kwanta ta rufe ido, Maimoon ta fito ta dau wayarta ta bude lock din, mamaki ne ya cikata tana kallon wayar ganin chat dinta da Abuturrab ne gaban screen din bayan ita ba kan WhatsApp take ba, ta kalli Jiddah da ta ki bude ido, kofa kawai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login