Showing 174001 words to 177000 words out of 346625 words
Chapter 59 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
ji da bak'in halinki... In dai jikana na so bbu ruwana da sarautarku ta karya can, yanxu fa sai tace ita a dole gimbiya take so ya aura don ita tana jikar sarkin Gombe, to ni ba ruwana bama haka, kowa mutum me daraja ne a wajenmu, kuma nasan Kabiru da Bashir baxa su watsa min duwatsu a ido ba..." Sai da Jiddah ta fara xuwa tayi ma Ummi sallama sannan ta fito main parlor, har sannan Abuturrab na tare da El-Basheer, Tana kallon El-Basheer tace "Sai da safe" Yace "Ohkk ba nan xaki kwana ba dama" Tayi murmushi ta girgixa masa kai tace "Kawo ni aka yi" Abuturrab ya daga kai ya kalleta, sai kuma ya mike ya fita daga parlon, El-Basheer yace "Driver kowa?" Ta gyada kai tace "Shi" El-Basheer yace "To mu je in rakaki" Bata ce komai ba ya mike suka fita parlon a tare, kofar gida suka tadda Abuturrab tsaye jikin motarsa, Jiddah na kallon El-Basheer tace "Nagode, sai da safe" Ya sakar mata murmushi yace "Aiitt, Allah ya tashe mu lfya" Bude back seat tayi ta shiga driver ya tada motar suka bar layin, El-Basheer na kallon Abuturrab yace "Ya ne, are you ready to go home now" Abuturrab yace "Yeah, Sai da safe" Daga haka ya shiga motarsa ya tada ya bar layin. Abuturrab na isa gida ya fi minti goma xaune cikin mota a parking space kafin ya sauka ya shiga cikin gidan, kulle kofar parlor yayi yana bin parlon da kallo, plates ne da suka ci cin cin, dubulan da su alkaki da frnds dinta da goran ruwa da lemo, ga bone din kaji a wani plate din a gefe, carpet din duk an marmasa cin cin da dubulan, haurawa sama yayi ya nufi bangarensa ya bude kofar parlon, nan ma dai ledojin souvenirs ne a tsakar parlon da souvenirs din a ciki, ya bude kofar bedroom dinsa, xaune ya ganta gaban mirror daure da towel tana ta shafe shafe, kamshin turare iri iri ya cika dakin, kallo daya tayi masa ta ci gaba da abinda take gently, yace "Aneesah what happened naga parlon downstairs so irritating sannan ga parlona duk wasu tarkacen ledoji, what's d meaning of that?" Tace "Ohh xan xo in kwashe souvenirs din but downstairs gaskiya sai gobe cause har yanxu jikina da gajiya sosai, baka ji bayana ba sai ciwo yake min wllh, I'm so stressed out" Calmly yace "No Aneesah, but u can't leave my parlor that way, I won't sleeo comfortable, ban sa6a ganin haka ba, Kuma ban ta6a kwana a haka ba" Tace "Captain ba wai fa nace baxanyi bane, xanyi amma gaskiya sai gobe, haba duk gajiyan bikin nan dake tare dani ka tsiro min aiki kuma da daddaren nan" Juyawa yayi ya fice daga dakin ya sauka downstairs, ya wuce kitchen ya dau sweeper da abun kwasar shara ya dawo parlon, sai da ya fara tattara duk plates din da robobin lemo ya kai kitchen sannan ya dawo ya share carpet din tass, ya kai ya xubar... Xaunawa yyi a parlon for kusan minti ashirin kafin daga karshe ya mike ya kashe wutan parlon ya wuce sama, har sannan ledojin souvenirs din na nan yanda ya barsu, ya kwashesu gaba daya ya bude kofar balcony dake parlon ya watsar da su nan ya tabbatar babu komai xaune parlornsa bayan furnitures sannan ya kulle kofar balcony din ya wuce daki, a gaban madubin ya sameta still, dakin sai wani fitinannen kamshi yake, ta saka wasu tsinanannun kayan bacci, yyi mata kallo daya ya fara cire shirt dinsa ya wuce bandaki. Daure da towel ya fito, yana goge gashin kansa da karamin towel din a hannunsa, Aneesah ta bi sa da kallo sae kuma ta mike ta nufesa ta rungumesa ta kwanta bayansa kamar me rada tace "In maka shafan cream din ne?" Ya dakatar da goge gashin nasa yace "I am not rubbing anything Aneesah" ta xagayo gabansa still holding onto him cike da kissa tana masa wani irin kallon so tace "Sai me Babynah?" Yana kallonta kafin yace komai ta lumshe ido ta fara sumbatar bakinsa, daukarta yayi bai direta ko ina ba sae saman gado, cikin cool voice dinsa yace "I'm not in the mood Aneesah, ni ma gajiyar biki bai sakeni ba har yanxu...." yana fadin haka ya lakaci hancinta ya mike daga kan gadon ya tafi ya dau pajamas dinsa ya fara sakawa, Aneesah ta bi sa da kallon mamaki har sannan tana kwance, can side din gadon ya tafi ya xauna bayan ya saka pajamas dinsa, ya juya ya kalleta yace "I need hot tea" Ta masa wani kallo ta mike tace "Baxan iya ba..." tana fadin haka ta fice daga dakin, a parlor ta dau wayarta ta fita ta koma wani daki ta kulle ta shiga kiran Aunty, Aunty na dagawa tace "Lafiya Aneesah????" Cikin rawar murya tace "Aunty wllh fa kawai walakanci Aliyu ke ji, kinga yau ma ba shi da niyya" Aunty ta bude baki tace "Ke kuma sae kace ba mace ba Aneesah, ae sae abun ya lalace ya gantale idan ya wuce yau" Aneesah ta marairaice tace "Toh ni ya xan yi masa Aunty, ji fa kudin da mutum ya kashe ma" Aunty tace "Xuwa xakiyi kiyi duk yanda xaki yi komai ya kankama, koma meye kiyi ni dai, sae da safe ni ba a bangarena nake ba" Daga haka Aunty ta katse wayar, Aneesah ta fi minti uku tsaye tana naxari sannan tayi wani murmushi ta fita dakin ta nufi bangarensa.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
*EXCLUSIVE FABRICS &MORE* provides you with exclusive, and Affordable fabrics such as laces, Ankara,materials shoes,bags and so much more on wholesale and retail EXQUISITE, AND AFFORDABLE
THANK U ❤️🤩
LOCATION: LAGOS
*EXCLUSIVE_FABRICS_AND_MORE* Na siyar da kaya kamar Laces, Atampopi, Materials, Jewelleries,👡👠👜👛da dai sauran su
Tana maraba da masu siyan daya koh sari
Location : Lagos
Tana aika kaya duk inda kake da yardan Allah 🤝🤝❤️🥰
09080058848
Bude kofar dakin nasa tayi ta shigo, ta gansa xaune daya side din gadon ya kunna laptop, ta kashe wutan daki ya daga kai yana kallon direction din da take, a nutse yace "Ban gama abinda nake ba Madam..." Barin wajen tayi ba tare da ta kunna ba ta taho ta hau saman gado, bai ce mata komai ba ya mike ya tafi ya kunna ya dawo ya ci gaba da danna laptop dinsa ya wani sha kunu kamar bai ta6a dariya ba, hakan ya sace mata gwiwan abinda tayi niyya, ta koma ta kwanta tayi lamo a kan gado... Har wajen sha biyu yana operating laptop bata ga alamar xai kwanta ba, ga bacci da ya fara damun idonta, nan duk ita jira take taga ya kashe laptop din ya kashe fitilun dakin sannan taga dubaran da xata iya amma shiru shiru har bacci yayi awon gaba da ita bata shirya ba, sai da ya tabbatar baccinta yayi nisa sannan ya kashe laptop dinsa ya rufe ya ajiye yana kallonta, dama akwai lkcn da xai yi aure da Aneesah gasu a daki daya yaji ba shi da feelings din yin komai tare da ita, he is getting irritated at the thought of having any affair with her, ya rasa dalili kuma upon how clean he knows she is, shi dai yasan duk xamansu tare da kwana gida tare da suke, bai ta6a sa ran xai yi tarayya da ita ba tare da sunyi aure ba, kawai sai d'an abinda ba ka rasa ba, but all of a sudden ya ji he is irritated at her, kashe wutan dakin yyi ya bude kofa ya fita ya koma parlor yayi kwanciyarsa saman 3 seater ya lumshe ido yasan this is just for a while Aneesah tana da tsaftar da baxai ji wani irritation ba.... Da asuba yana dawowa masallaci bai hau sama ba yayi kwanciyarsa downstairs, sai karfe tara ya koma sama ga mamakinsa sai ya ganta xaune tsakiyar gado tana danna waya ko kayan baccin bata cire ba balle ace tayi wanka ko ta gyara daki, yanxu bedroom dinsa ne har nine ba gyara?? kallo daya yayi ma idanuwanta ya san kuka ta ci ba kadan ba, ya karasa dakin ya d'an kakkabe gefen bedsheet din ya xauna yana kallonta yace "You are angry at me right?" Kauda kai tayi taki cewa komai, yayi kasa da murya yace "Toh kiyi hakuri, but ina son mu yi magana ta fahimta da ke Aneesah" Ganin bata da niyyar juyowa balle ta kallesa ya mike ya koma daya side din nan ma ya kakkabe ya xauna yana kallonta ya kamo hannunta yace "There is something serious i want us to discuss...." Ita dai taki cewa komai, kamar me rada yace "Kar ki ga kamar ko bana son having affair tare da ke...." Ta fixge hannunta ta katse sa cikin fushi tace "Don't tell me anything" yace "No i need to pls, kema kinsan duk xuwan da kike yi gidana can Abuja iyakar abinda ke hadani dake romance, just that, kuma ban ta6a tsallake hakan ba, and now u are mine completely and i can do whatever i want with u, but sai dai I don't know... may be i was suppose to have told u this long ago Aneesah...." Ya d'an yi shiru, ganin kallon da take masa with much interest din son jin abinda xai ce, yayi kasa da murya a hankali yace "I have issues Aneesah..." kallonsa take ko kiftawa babu, can tace "Issues din me?" Yana wasa da hannunta a hankali yace "Issues with having intercourse" Tayi masa wani kallo tace "You must be kidding Aliyu, ni din ce ban sanka ba??" Yace "Aa baki san ni ba, ni ne nasan kai na, domin kina gani na kamar lafiyayye xai iya kasancewa ba haka bane... Don't be deceived by what u saw" Da mamaki take kallonsa ta ma kasa cewa komai, ya langwabar da kai shi ma yana kallonta, ta girgixa kai da sauri tace "Ban gane ba Aliyu" yace "Meye baki gane ba?" Tace "Naga dai baka ta6a making Attempt din yi ba ai kaga ka kasa" Yace "Ehh ko ban ta6a making any attempt ba ai xan fahimci wanene ni with out making Attempt" Ta girgixa kai tace "Noo, ni ban ga haka a tare da kai ba, ko a sannan ma ni nasan karfin hali kawai kake yi kana kyaleni don kawai baka da yanda xaka yi kuma baka son kayi sabon Allah amma ba wai don kana da wani issues ba, u are more than healthy" Ya d'an yi murmushi yace "I am sorry i am telling u this late Aneesah, amma ina da issues wanda nake neman magani a kai har yanxu... I am sorry i am letting u know it now" Buda ido tayi sosai tana kallonsa, can tace "Wai kai a ina ka ta6a making Attempt kaga kana da issues?" Yace "Aneesah nace maki ba sai nayi making any attempt ba, i knew my self, i knew my issues long ago, yanxu dai ina son wannan ya xama babban sirrinmu ni dake plss Aneesah, nasan kin aureni ne ba don komai na ba sai don sona da kike, in sha Allah xan fara neman magani daga yanxu, komai xai dai daita in sha Allah, kinji my wife??" Kasa daina kallonsa Aneesah tayi da mugun mamaki, is Aliyu kidding her? Mutumin da take tsoro saboda yanda take ganin yanayinsa a duk sanda suke tare shine yanxu xai ce mata yana da issues, mutumin da duk da sonsa da maitarsa da take wani bangare na xuciyarta na mugun tsoron ranan haduwarsu tunda ta gama sanin komai game da shi... kamar ya san tunanin da take yayi kasa da murya yace "I don't know if i have deceived u with what u saw or what u imagine, kinsan babu yanda Allah baya abunsa, amma ni ai nasan baxaki ki xama da ni duk da wnn matsalar tawa ba Aneesah, nasan kina sona ne so na tsakani da Allah" Sounding so pissed off tace "Wai ban gane kana da matsala ba, matsalar me takamaimai, don ni a sanin da na maka ban sanka a me wata matsala ba, dama wai mutum na sanin yana da matsala bai yi making any effort ba?" Cikin sanyin murya yace "Dama abinda na guda kenan ya sa ban sanar maki ba tun farko, i was afraid kar kice xaki bar ni, but sai gashi maganganunki sun nuna hakan" Jawota yyi jikinsa yace "Kinga ba wai fa yana nufin i can't touch you ba, it's just that I can't make love with u, amma komai kike so ni xan maki...." Lamo tayi jikinsa ita dai tana sake jin wutan sonsa na ruruwa a xuciyarta, a hankali yace "Say something Aneesah" Aneesah dai ta fada duniyar tunanin da ta tafi, ko ba komai tension guda daya ya sauka a kanta, cause she can't imagine dama idan Abuturrab ya gane she isn't a virgin, tun da aka kawota da wannan xullumin take xaune a gidan, shi sa take son ayi a wuce wajen hankalinta ya kwanta, tun ana sauran kwanaki bikin take ta fatan duk abinda suka yi da kudin da suka kashe bai tafi in vain ba, Girgixa kai tayi tana d'an murmushi tace "Ni kai nake so kuma xan xauna da kai a ko yaya kake my captain, amma kuma ai hakan baxai sa kace baxa ka dinga ta6ani ba ko?" Murmushi yyi duk da bata ganin fuskarsa yace "Sure xan maki duk abinda kike so mana Wife" Tayi kasa da murya tace "To amma kasan akwai abubuwan da idan ana yi ma mace xai sa tayi loosing virginity dinta ko?" Yace "Abubuwa kamar me?" Dago kai tayi ta kallesa ya wara mata ido yana sauraronta, a kunne ta rada masa, yace "Toh shkkn baxan maki shi ba, because i want to know u a virgin" Gabanta taji ya fadi sosai, ta girgixa kai tace "Toh idan baka min ba ai kuma baka fita hakkina ba tunda ba dayan xaka dinga yi ba" Shi dai murmushi kawai yake yaki yace mata komai, ta shige jikinsa kamar xasu hade waje daya, nan da nan yaji kamar kunnasa take son yi, ya d'an koma baya, cike da shagwaba tace "Kayi shiru" Yace "Ohk i want this as a secret between we both Aneesah, sannan duk wata bukatarki na yau da kullum xan maki duk don ki kwantar da hankalinki kiyi hakuri da yanda kika sameni" Ta lumshe idonta tace "In sha Allah my captain, i love you so much" Ya sauke wani boyayen ajiyar xuciya, yana sake kallon agogo wai har karfe goma saura mace na saman gadonta, kwantar da ita yayi ya mike yace "I want to take my bath, kinsan yau xan koma gun aiki fa" Ta xaro ido tace "Kai da ya kamata ka dau sati captain? Ko basu san aure kayi ba" Yace "No iyakar kwanakin da aka bani kenan, kinsan my first marriage an bani almost 2 weeks, and this is my second marriage...." Da mamaki take kallonsa kafin ta katse sa da sauri tace "Kai har kana da wani first marriage da kake tutiya da shi Captain?" Yace "Ohh toh ya xan kirasa? Aure ne shi ma ai" Ta hade rai tace "Wannan kuma ya rage naka, amma take note aurenmu shine first and last marriage dinka" Yana cire jallabiyar jikinsa yace "Toh ai wajen aiki babu ruwansu, a first marriage dina suka san wancan hutun da suka bani, wannan kuma second marriage..." Kallonsa kawai take from head to toe babu ko kiftawa, don Abuturrab ya kai namiji wanda ko wace mace xata so shi a matsayin mijinta, daga sama har kasa kawai take kallonsa tana sake imagining din discuss dinsu, wai yana da issues, Issues a hakan da take ganinsa? Kamar ya san tunanin da take ya juya yayi shigewarsa bandaki ya kulle, ta sauke wani ajiyar xuciya tana jin wani shaukinsa na taso mata, ta kwanta gefen gado hade da lumshe ido. Jiddah na tsaye dakinsu tana jera kayansu da mai wanki da guga ya kawo a press, Maimoon ce kwance dakin tana baccin wahala saboda cramps da ya sakota gaba ko boko bata je ba ranan, Jiddah kuma shigowarta kenan malamarta ta wuce, shine take gyaran kayan kafin Mu'allimarta na Islamiyya ta xo, Umma ce ta bude kofar dakin, tana kallon Maimoon tace "Ta samu bacci kenan" Jiddah tace "Ehh tayi bacci" Umma ta kalli Jiddah na few seconds kafin tace "Jiddah ki xo daki ki sameni idan kin gama" Jiddah tace "Toh" Umma ta juya ta fita, sai da Jiddah ta gama jera kayan nasu sannan ta fita xuwa dakin Umma, Umma na xaune kan arm chair dake dakin, Jiddah ta xauna saman carpet, duk da yanda gabanta ke faduwa don yawanci kiran Umma baya wuce warning xata mata, shima warning din a kan Abuturrab, to amma ai yau kusan wata kenan bata gansa da idonta ba, a hankali tace "Umma gani" Umma na kallonta tace "Jiddah baki ta6a xuwa kin sameni kince kina son Pad xakiyi al'ada ba" Jiddah ta sunkuyar da kanta a hankali amma bata ce komai ba, Umma tace "Ko baki fara ba ne?" Ta girgixa kai tace "Aa na ta6a yi sau biyu kuma ban sake yi ba" Umma tace "A ina kika ta6a yi?" Ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Ya dade, tun ina gun Baabarmu, lkcn ban daina xuwa islamiyya ba" Umma tace "Xai kai wata nawa?" Jiddah ta buda ido sosai tace "Umma xai yi kusan shekara biyu" Umma ta gyada kai tace "Ikon Allah, kuma shine baki sake ba har yau?" Jiddah tace "Eh" Umma tace "Toh tashi ki tafi" Mikewa tayi ta juya ta fita dakin, Umma ta bi ta da kallo tana tunanin meye ma'anar hakan, Jiddah na fita ta sauke ajiyar xuciya ita ko fata ta sake yi bata yi har abada, don bata mance wahalan da ta sha ba har sai