Showing 228001 words to 231000 words out of 346625 words

Chapter 77 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

Allah ku yi hakuri Abba, i know i wronged u all, but this the only way out for me, Abba baxai saurareni ba, so is Ummi... No one will give me a listening ear" Alhaji Lawal yace "Ohk ni kuma sbda ka yi shegen raina ni yanxu kake tunanin xan baka listening ear?? No... I am not giving u dat, and i am sorry babu wani abu da xan iya yi" Abuturrab ya kasa ce masa komai, Alhaji Lawal yace "I can't do anything about this... ina ce ita wannan yarinya idan ban mance ba babu irin hakuri da ban bakin da bamu baka ba a kan ka xauna da ita, ashe ka maida mu shashashai ne a lkcn ka je ka saketa kuna ta xama tare duk don sbda kana ganin ita ba class dinka bace or whatever, bugu da kari kuma u bluntly admitted baka sonta, to yanxun da ka koma ka aikata shirmen da ka aikata son nata ka fara yi kenan???" Nan ma dai Abuturrab bai ce komai ba, Alhaji Lawal ya daka masa tsawa yace "Bude baki ka bani amsa my frnd.. i am talking to u" A hankali yace "Ina son xama da ita yanxu Abba" Alhaji Lawal yace "U are very stupid, ae ba tambayar da nayi maka ba kenan.." Kasa basa amsa Abuturrab yayi nan ma, Ganin yanda Uncle din nasa ke kallonsa ya sunkuyar da kai, Alhaji Lawal yace "Toh ka saka a ranka cewar kamar yanda muka xaunar da kai kwanaki muka baka takarda da biro ka datse auren naku wannan karon ma hakan ne xai faru, mu ba 'yan banxa bane da xaka dinga controlling dinmu yanda ka so, kana aikata duk abinda ya xo kanka without our consent, we birth u..." Abuturrab ya marairaice masa yace "Abba don girman Allah ku yi hakuri, wllh ban koma na aureta da nufin in cuceta bane wannan karan, wancan lokacin ma kuskure aka samu, don Allah Abba kayi hakuri, i mean no harm to her..." Alhaji Lawal yace "Da nufin me ka koma ka aureta yanxu? Bani amsar tambayar nan" Abuturrab yace "Ina son xama da ita ne na har abada" Alhaji Lawal ya girgixa kai yace "Kamar dai yanda na fada you are very stupid, kawai ka koma ka aurota saboda kana son ku xauna tare har abada, wait!! are u mad??" Abuturrab yace "Abba ni dama fa ban ta6a buda baki nace bana sonta ba, kawai sharrin shaidan ne da kuma yanda kowa baya son auren shi yasa na aikata abinda na aikata, amma wllh ban ta6a cewa bana sonta ba" on a serious note Alhaji Lawal yace "Daga Hajja a rashin alkibla sai kai, anyway... I am so dedicated today, don haka idan Allah ya amince mana gobe xan shiga kadunan, xaka iya tafiyar ka sae na xo goben..." A hankali Abuturrab yace "Xan jira mu tafi tare goben in sha Allah" Alhaji Lawal yace "Allah ya kai mu" Godiya Abuturrab yayi ma uncle din nasa sanan ya mike ya nufi kofa hoping this will be the only challenge he is to face till end, Alhaji Lawal ya bi sa da kallo har ya fita yana mamakin karfin hali da taurin xuciya irin na Abuturrab, kiri kiri yayi ta abu ba tsoro. Abuturrab ya fi minti daya tsaye kofar parlon Abbansa ya kasa bude kofan, bai ta6a jin mugun shakkan Abbansa irin na lkcn ba, bai san me ya sa wnn karan ko Aunty baya jin ta kamar yanda yake jin Abbansa, ga bugun xuciyarsa da ya tsananta, it's been long da ya shiga yanayin nan da yake ciki yanxu, muryan Umma yaji a bayansa ta rike ha6a tace "Kai kuma yaushe a gari??" Ya juya da sauri, yyi feigning smile yace "Good evening Umma" tace "Saukan yaushe?" Ya d'an fara kame kame kafin yace "Jiya" tace "Ikon Allah, to sannu da dawowa..." Bude kofar parlon tayi, lkci daya fara'ar da ke fuskarta ya bace, ta wani sha kunu ta shiga parlon, tunda aka kirata aka ce ta xo gidan tayi tunanin xancen baxai wuce na auren da suke shirin laka6a ma Jiddah ba, kuma ta sha alwashin yau kam sae inda strength dinta ya kare, dai dai take da kowa, ganin Hajja xaune parlon ta wani kara daure fuska ta nemi waje ta xauna, Abuturrab ya shiga parlon kansa a kasa gabansa na mugun faduwa, xaunawa yyi saman carpet ya kasa kallon kowa, a hankali ya fara gaida Hajja kafin sauran occupant din parlon, Hajja dae fuskar nan nata babu ya6o bbu fallasa, Umma ma babu yabo babu fallasan tace "Ina yini Hajja" Hajja ta rike kanta tace "huhuhu wllh tun da naje Masar na samu saukin gaishe gaishen jaraban nan, yo kowa na ta kansa ina batun wani gaisuwa, su basa haka a can wllh, duk wayayyu ne, a kasar nan kowa sae yace sae ya gaisheka alhalin wani gaisuwar ma bai kai ciki ba, to ni dai na yafe, ko Usman ma ban amsa gaisuwarsa ba balle wani...." Ko kallonta Umma bata sake yi ba tana jan counter dinta... Alhaji Umar ne ya bude wajen da addu'a, sannan bbu 6ata lkci kuma babu boye boye in Brief Alhaji Lawal ya maimaita masu duk abinda Abuturrab ya sanar masa jiya a Zaria, Babu wanda bai girgixa ba a parlon, Abba dai kallon ceiling kawai yake, gaba daya sauran mutanan parlon kallon Abuturrab suke irin kallon tsoro, babu ko kiftawa, shi ko kansa na sunkuye xuciyarsa na bugawa, Hajja dae sae wani murmushi take me sauti irin na bosawa tana girgixa kafa da kai, Bayan shirun kusan minti biyu da ya ziyarci parlon, Aunty ta mike duk ta hada xufa daga sama har kasa tana girgixa kai tayi wani murmushin takaici tana nuna Abuturrab tace "Wllh karya kake Aliyu, karya kake baka isa ka kunyata ni ka toxarta ni, ka walakanta ni a idon duniya ba wllh... Karyanka ta sha karya wllh" kofa ta nufa ta fice daga parlon da sauri, Umma da Ummi har sannan hangame baki suka yi suna kallon Abuturrab, Hajja na kallon Abba a hankali tace "Yau da ace a Masar ne idan ba a garkame d'an ka a kurkuku ba shegiya nake Usman, ae wannan shine ta'addanci mafi muni da mutum xai yi a hukuntasa a kasar Masar, kai ba a ma ta6a haka a can ba wllh, Aliyu dai ya fita sahun mutanen kwarai, Aliyu mutumin banxa ne... Kiri kiri ya nuna ma d'an uwansa na jini bakin ciki, da hassada, ba fa son yarinyar yake ba kawai bakin ciki ya mayar da shi gun danginta ya sake aurota a gantale, su ma dai dangin nata matsiyata ne, kawai sun mayar da 'ya kaza don yaje yyi masu fafan yana tukin jirgin sama, to meye kuma tukin jirgin sama Allah na tuba abinda matsayinsa da d'an acaba da d'an taxi daya a idon duniya, wato sbda hassada sai ya ga ta yanda yarima zai aureta ko??" Cije yatsa Hajja tayi sae kuma ta rushe da kuka tace "Wllh mun fi awa biyu da mutumin nan muna garari a hayin rigasa, katon ya gilla min karya wai an rushe gidansu Jiddah daga karshe ma gaya maka ne kawai ban yi ba Usman wllh a tsakiyar titi ya yasar dani yyi wucewarsa kamar mara galihu duk na hada xufa, har ya kai ya kawo mutane suka xata almajira ce idan an xo wucewa sae a mika min ashirin, goma...." Sosai Hajja take kuka tace "Ni a tarihin duniya ma ban ta6a jin an haifi me hali irin na Aliyu ba, kuma a bisa dokan Masar duk wanda xai iya aikata abinda ya aikata to xae iya kashe rai babu ko darrr, shi yasa ma ake garkamesa a gidan gyaran hali, ni dae xan xuba ido kawai in ga hukuncin da xaka dauka a kan wannan d'a naka Usman, dalilin abun nan da Aliyu ya aikata sae zumunci ya tarwatse ya daidaice ya lalace wllh, don ba Yarima kadai ba.. hatta mutan Bauchi sae sun kullaci Aliyu, daga nan kuma sae a fara gaba tsakanin Bauchi da kaduna, to wa xai so haka??" Ta kara fashewa da matsanancin kuka tana kwance ha6ar xaninta tana salallami, ta mike ta fice daga parlon tace "Tirrrrrr" A karo na farko Abba ya kalli Abuturrab da har sannan ya ki raising kansa, Abba ya gyara xama speaking calmly yace "Yanxu kai ka tabbatar ka koma an sake daura maku aure da yarinyar nan Aliyu? Are u very sure about this" Sai a sannan Abuturrab ya daga kansa ya kalli Abbansa amma ya kasa cewa komai, Abba yace "I'm asking you...." A hankali yace "Ehh Abba" Abba yace "To da yaushe kaje aka mayar da auren?" Cikin sanyin murya Abuturrab yace "Before i got married to my recent wife..." Abba ya gyada kai yace "Ohkk that's good, wani sadakin ka kai kenan?" Abuturrab ya sunkuyar da kansa yace "Ehh" Abba yace "Nawa ka kai?" Abuturrab ya share xufar forehead dinsa yace "150k" Abba ya gyada kai cike da gamsuwa yace "Ohkk that's fine" Ummi ta rike ha6a tana kallon Aliyu da abinda ya fi mamaki, Umma kam dariya ma abun ya fara bata sai taji kamar film, hakan yasa bata san sanda ta dinga murmushi ba tana gyada kai, Mikewa Abba yayi Abuturrab ya bi sa da kallo kamar idanuwansa xa su fito ganin ya nufi bedroom dinsa, kallon Ummi yayi ya marairaice mata amma ya kasa cewa komai, gaba daya hankalinsa ya tashi sosai, ita kuwa sai kallonsa take har sannan tana rike da ha6a, Abba ya fito daga dakinsa rike da paper and pen, Alhaji Lawal ya dakatar da shi yace "Let's talk first Alhaji Usman" Abba ya ajiye takardan hannunsa gaban Abuturrab kafin yace komai Abuturrab ya hade hannayensa cikin breaking voice yace "I am sorry Abba, wllh i can't, i can't plsss...." Ai bai jira mai Abba xai kuma cewa ba ya mike ya fice daga parlon, duk suka bi sa da kallo. Babu yanda Alhaji Lawal bai yi kokarin ganin yayi convincing Abba yayi hakuri da abinda Abuturrab ya aikata ba, he should calm down before making any decision... but all his effort prove abortive, har Alhaji Umar ya sa baki don ganin Abba ya janye wannan kudirin da ya dauka amma Abba ya ki sauraron kowa, kana ganinsa kasan ya hau sama sosai, Ummi dai sai kallonsa take haka ma Umma dake parlon har sannan, Alhaji Umar yace "Ka fahimce ni Alhaji Usman ba don muna tsoronsa ya sa xa mu saurara masa ba, akwai abubuwan dubawa da yawa...." Abba ya dakatar dashi yana girgixa kai yace "Kasan Allah Umar?? Wllh wllh sai ya saketa, wllh baxai xauna da ita ba, xan nuna masa i birth him...." Yana kai wa nan ya mike ya fice daga parlon......



*Masu neman littafin Jiddatul Khair complete sae ku yi payment ku xo ku sameni da evidence* ๐Ÿ‘‡๐Ÿป

Wa.me/+2347087865788



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



Allah ubangiji ya maimaita mana๐Ÿ˜‡



Abuturrab na bedroom din Umminsa ta shigo, tun da ta gansa ta dauke kai ta tafi gaban mirror tana cire jewelries dinta, bayan ta gama ta nufi kofa xata fita yyi karfin halin cewa "Ummi" juyowa tayi ta kallesa, ya sauka kasa on his knees ya hade hannayensa pleadingly yace "Ummi don Allah ki ma Abba magana, interpose pls, nasan ke baxa ki juya min baya ba, pls don't say no to me Ummi, don girman Allah don't let him force me do wat will ruin me, baxan iya ba..." Ummi dake ta kallonsa tace "Ikon Allah!! Aliyu lkcn da kake abubuwan ka kana shawara da ni ne?" Yace "Ummi i don't know how to open up to you about this, i don't know where to start from, and I don't know how u will take it, idan ban yi hakan da nayi ba i might ruin my self, don girman Allah kiyi hakuri ki yafe min Ummi, i only did what will favor me till end" Ummi tayi wani murmushi ta girgixa kai tace "Aliyu kenan, but i am sorry i can't nd won't do anything about this, wannan batun ya fi karfina coz Abbanka ya dauka da xafi kuma ko na minti daya ban ga laifinsa ba duk abinda ya aiwatar dai dai ne, he is doing what is right, i see no reason we will birth a child dat will keep on controlling us" tana kai wa nan ta fice daga dakin, ya bi ta da kallo xuciyarsa na bugawa yana jin wasu xufan na keto masa a forehead, dafe kansa yyi na kusan minti goma, daga karshe ya mike ko minti daya bai kara a gidan ba ya fice... Tun da Umma ta koma gida take xaune dakinta ta ma rasa takamaiman tunanin da xata yi, ita wllh sai take ga kamar a mafarki duk abubuwan nan suke faruwa, lkci lkci take bude baki ta rike ha6a tana sake imagining da jinjina halin Abuturrab, yanxu komawa yayi ya sake auran yarinyar nan duk ya maida su shashashai gantalallu, ta ma rasa ko takaici take ji, haushi take ji, ko bakin cikin abinda Abuturrab ya aikata take, ko a tarihi bata ta6a jin shigen abinda Abuturrab yayi ba, wato yaron nan yayi mugun rainasu bai daukesu bakin komai ba, baya kuma tsoro ko shakkan kowa, tafe hannu tayi tana salati. Bayan magrib tana xaune kan darduma hannunta rike da carbi tayi nisa tunanin da take tana kallon Jiddah dake jera mata goggagun kayanta da me wanki da guga ya kawo a press, to meye manufarsa a kan marainiyar nan kuma yanxu?? Me yake nufi da su for the second time, wato idan ba a dau kwakkwaran mataki kan wnn abinda yaje yyi ba sun xama shashashan da gaske kawai, Ko kadan bata ji haushin reaction din Abba ba this time around kuma she is supporting him 100%, Aliyu xai gane ba shi da wayo.... bude kofar bedroom din aka yi amma ba duka ba, kuma ba a shigo ba, daga Umma har Jiddah kallon kofar suke, sai kuma aka yi sallama kasa kasa, still not coming inside the room, Lkci daya Jiddah ta dau muryarsa, kamar yanda Umma ma ta dau muryan amma sai ta hade rai tace "Waye wannan?" Shigowa dakin yayi kansa a kasa bayan yyi pushing door din slowly, Umma har ta mance rabon da ya shigo mata daki, Jiddah dai bata yarda ta kalli kofar ba don kamar kuwa ta san kallonta yake, Umma ta buda hannu da sauri tace "Ya aka yi xaka shigo min daki babu sallama?" Ya sauke idonsa daga kallon Jiddah ya karasa cikin dakin yana tafiya a hankali ya xauna nan saman carpet, yyi kasa da murya yace "Ina yini Umma?" As if in a hurry tace "Lafiya lau, ya aka yi?" Shiru yayi ya sunkuyar da kansa, Jiddah ta bar gyaran da take ta rufe press din ta nufi kofa ta fita, sannan ta kullo masu kofar. Cikin sanyin murya Abuturrab yace "Umma i know i wronged u all, kuma ni bani da bakin da xan baku hakuri, coz i don't deserve being forgiven, But Umma i want u all to get this... A Mistake repeated more than once is a DECISION, No mistake is repeated twice because the second time it's not longer a mistake but a CHOICE, this is my Decision and my Choice Umma" Ya hade Palm dinsa gathering much courage yace "This shouldn't be used against me plss, ku yi hakuri ku sassauta min, I don't have the strength to bear being denied my Choice, kuyi hakuri don Allah Umma..." Umma da ke ta masa kallon mamaki ta dakatar da shi tace "Ur Decision and Choice?? Lokacin da kayi watsi da namu decision din mun hakura ko bamu hakura ba Aliyu?? Kai don baka da kunya da tsoron Allah har xaka iya sake komawa a aura maka Jiddah?? Yarinyar da kafi karfinta? Yarinyar da ba class dinka ba? Yarinyar da ka dinga kunyan nuna ma duniya cewar ita ce matarka? Yarinyar da kayi ma sakin walakanci ka toxartata? Tsakaninka da ita fa abinci da suturan sakawa shi ma duk don kada Allah ya tambayeka ne... Get out from my sight plss Aliyu " Abuturrab ya girgixa mata kai ya marairaice yace "Noo plss Umma, kar ki min haka ke ma, i have no back up" Cikin tsawa Umma "Ohk so kake ince ka dau Jiddah ku tafi ko me? Haka kake son ji??" Ya girgixa kai cikin sanyin murya yace "Aa Umma, so nake kawai ki taimaka ki sa baki Ummi da Abba su sassauta min, don nasan baxan iya tsallake hukunci daga garesu ba, su yi min komai amma kada su ce in sake sakinta don girman Allah" Umma tace "Kaga ka xo kawai ka sa min ciwon kai Malam, ba don halina ba tashi kaje sae da safe i need rest, kuma kada ka sake xuwa min gida da batun Jiddah, ko me kake son fada kaje ka samu ubanka ko Ummi, but don't come to my house again, get out pls..." kallonta ya dinga yi, ta mike ta cire hijab dinta ta linke ta xauna gefen gado tana ci gaba da jan carbinta fuskarta a daure, a sanyaye ya mike ya yi mata sae da safe ya nufi kofa ya fita. A kofar gida Abuturrab yyi parking ya shiga cikin gida, wani kamshin bala'i ne ke tashi tun daga balcony har cikin gidan, ya bude kofar parlon ya shiga, ko ina na parlon sae walkiya yake don neatness, ya xauna saman kujera ya jinginar da kansa dake sara masa ya runtse ido xuciyarsa na bugawa, ya fi minti talatin a haka, sae ga Aneesah xata tafi kitchen da cup din hade hadenta na Maman Farida me kayan yan gayu da ta gama sha๐Ÿ™„, ta xaro ido ganinsa ta ajiye cup din a kasan parlon ta nufesa da sauri tace "My captain? Yaushe ka shigo?" K'in bude ido yyi, ta xube


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login