Showing 237001 words to 240000 words out of 346625 words

Chapter 80 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

haka har ta fita dakin, Ahmad ya xauna gefen gado ya rike kansa yayi dariya sannan ya mike ya bi bayanta, har ta kai compound ya sameta tana tafiya kamar xata tashi sama, wayarsa ya ciro a aljihu yyi dialing number Umma bayan ta daga yace "Abuturrab din na nan ne ko ya koma?" Umma tace "Kai da kaje gidan jiya dama baka dubasa ba kayi tafiyarka Ahmad?" Yace "No na basa magani ai" Umma tace "Toh ka same mu a hospital" Da mamaki yace "Hospital kuma? But he was fine da ya xo ai ko" Umma ta katse wayarta, sake kira yyi bayan ta dauka yace "Wani hospital din?" Ta gaya masa ta katse wayarta, Hajja ta leko daga kofar gida cikin daga murya tace "Yau na shiga uku, baxa ka fito ka kai ni in ga halin da jikana ke ciki ba Ahmad??" Ahmad ya karasa kofar gidan, Ya bude mata back seat, tace "Yanxu yana can gidan nasa ne?" Ahmad yace "Yana asibiti" Buda baki Hajja tayi da shock tace "Asibiti??" ta ciro wayarta da sauri tace "Kira min Usman din" Ahmad ya amshi wayar ya shiga kira mata layin Abba, Abba na dagawa ya mika mata.....



*Allah maku albarka my trustworthy fans, ina yin ku 100%* 🥰😘




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




Hajja ta gyara xama a motar tace "Usman dama akwai wani laifin da Aliyu yayi maka ne da ban sani ba bayan komawa da yayi ya karasa abinda ya fara?" Abba dake sauraranta yace "Ban fahimta ba Hajiya" a fusace Hajja tace "Naga bala'i, Meye baka fahimta ba Usman?? Tambayarka fa nake ko bayan auren nan da yaje yayi akwai kuma wani laifin da ya tafka maka wanda mu bamu sani ba?" Abba yace "Ance maki ya min wani laifin ne bayan wannan Hajiya?" Hajja ta kalli Ahmad tace "Ka ji gantallale ina tambayarsa yana tambayata, abinda kabiru baya yi kenan..." Abba yace "Hajiya me yasa idan xa ki yi magana baki yi kanki tsaye yanda xa a fahimce ki, sai kiyi ta kauce kauce kuma idan ance maki ba a gane ba ki kama fada, ni ban san kan me kike magana ba wllh" a nutse Hajja tace "Toh ni dai dama kawai ce maka xanyi idan wani abu ya samu jikana to ka nemi wata uwar ba ni ba gaskiya, ba fa kisan kai Aliyu yayi da xa a saka sa a bakin duniya ba har yana neman ajiye aikin gwal dinsa da sai wanda Allah ya so yake ba, sannan ga shi can ance yana kwance rai a hannun Allah, ba fa wani abun tashin hankali na a xo a gani Aliyu ya aikata ba da xa saka sa a bakin duniya a sa shi gaba, toh wllh idan wani abu ya samesa Masar xan kai karar nan, don Najeriya baxata iya mana shari'a da ku ba, takardar da aka min na Masar din kawai xan kai in nuna a maka min ku a kotunsu" Tana kai wa nan ta katse wayar tana kallon Ahmad tace "Mu je Ahmad" Ya tada motar ya nufi asibitin da Umma tace, har suka isa asibitin kuma Hajja tsigale Abba da Ummi take, Bayan Ahmad yayi parking yace "Toh ita Aunty fa bayan da na shigo ma na tarar da ita xaune dakin ki tana ta xuga ki" Hajja tace "Ta dai xuga uwarta dake kabari, ita har ta isa ta xuga ni... Snn me yasa xan sakota a batun nan bayan nasan babu abinda ta hada da Aliyun idan ba cutarsa da ta dinga yi da tana cinye masa kudi ba" Ahmad dai ya ta6e baki ya sauka motar ita ma ta fito tana sharce xufar goshinta tace "A kai ni inda Aliyun yake, wllh xa a sha mamaki na idan wani abu ya samu Aliyu, tunda nake ko tari bai ta6a min ba da nufin fitsara ko rashin kunya, to yaushe ma yayi magana balle har ya raina babba, shi da magana ke masa wuya" Ahmad dai tafiya yake har suka shiga reception din asibitin, Hajja ta nufi nurse da sauri a rude tace "Ke yarinya an kawo wani matukin jirgin sama nan? Shi kadai ne matukin jirgi bahaushe a duk Najeriya" juyawa Ahmad yyi da sauri ya ji kamar da baya wajen Hajja tayi wannan maganan, Nurse din sai kallon Hajja take, sai kuma ta d'an yi dariya tace "Ya sunansa Mama?" Hajja tace "Sunansa Aliyu Usman, jikana ne, amma Abuntural naji suna ce masa" Kujera Ahmad ya nema ya xauna trying his very best not to laugh, nurse din ta shiga duba files din admitted patient dinsu na ranan, daga bisanni ta kalli Hajja tace "Xa ki hau sama daki na biyu, dake kallon hagunki nan xa ki shiga Mama" Hajja ta nufi stairs da sauri, Ahmad ya bi ta da kallo yana murmushi, can ya mike ya gaida nurses din ya wuce sama shi ma, Tsaye ya tadda Hajja tsakiyar ward din bayan ta shiga, cikin rawan murya tana kallon Umma take cewa "Me likitocin suka ce ke damun jikan nawa Ramlah?" Umma ta ajiye wayar hannunta tace "Toh gashi nan dai Ahmad xai je ya sami likitan yanxu" Ahmad ya karasa saman gadon yana kallon Abuturrab dake bacci, kamar dama don yayi baccin aka kawosa asibitin, bacci yake tsakaninsa da Allah, amma kuma ga drip a hannunsa, Hajja ta rushe da kuka xata nufi saman gadon Umma da ta bi da wani kallo tace "Hajja don Allah sun ce a bar sa ya huta sosai baya samun bacci dama, kuma wannan kururuwan naki ai sai ya tashe sa" Hajja ta dawo da sauri tana share hawayenta tace "Toh nayi shiru" Umma ta kalli Ahmad tace "Kaje likitan na office dinsa, sai kaji bayanin da xai maka" Ahmad ya nufi kofa ya fita, ganin kujera daya ne a ward din Umma ta mike tace "Ga kujera Hajja" Hajja na matsar kwalla tace "In xauna inyi me jikana na kwance ba lafiya, aa barni a tsaye Ramlah, amma Allah shi kadai yasan yanda xai yi da Hauwa, ki haifi yaro ki maida sa banxa, ai kuwa Aliyu ba d'an banxa bane, wato ita dai kawai duniya ta haifar ma shi yayi ta jigila da mutan duniyar a jirgin sama" Umma tace "Toh Hajja da kike wnn maganan kina da tabbacin ta xo ko bata xo ba??" Da sauri Hajja tace "Wllh bata xo ba Ramlah, ta xo tayi me bayan ba sonsa take ba, sai kace ba gida daya muka kwana da ita ba xaki ce min ta xo, ina ganinta ai da safe tana ta share share kamar tababbiya a cikin gidan, ashe d'an ta na nan kwance asibiti rai a hannun Allah, kuma banda Ahmad babu wanda yaje ya gaya min, kai ai ni kawai ina rayuwa da yan iska ne a gida daya, daga Usman din har matansa kuwa, kuma in wani abu ya samu Aliyu wllh sai na dauresu duka a Masar" Umma tace "To ko awa daya ba ayi da na kawosa asibitin ba ai, don daga gida na ya ke, kuma ko minti sha biyar banyi da kiran ita yayan na sanar mata ba" Hajja tace "Allah???" Banxa Umma tayi mata, Hajja tace "Toh ni dai fatana Allah ya farfado min da shi inji meye damuwarsa ba shkkn ba, dama ba uban wani ya renan min shi ba har ya kai haka" tana kai wa nan ta ciro wayarta ta mika ma Umma tace "Kira min Hafsah" Umma ta d'an kalleta, sai kuma ta amshi wayar ta gama danne dannenta ta mayar mata tace "Bai shiga ba" Hajja tace "Kira Usman to" Sai a nan Umma ta kira mata Abba ta mika mata wayar, Abba na dagawa babu yabo babu fallasa Hajja tace "Ka kira matarka Hafsah yanxu yanxu kace ta kirani, ni an kira min ita ban sameta ba... Bani da wata magana da kai bayan wannan" Daga haka ta katse wayarta, bayan kusan minti biyar sai ga Aunty ta kira Hajja, Hajja na dagawa tace "Hafsah ki ba su Aisha pillow da bargo hade da tabarma su kawo min asibiti, ga Aliyu nan dai an kwantar rai a hannun Allah da kyar likitoci suka samo kansa" Aunty tace "Subhanallahi wani asibitin me kuma ya samesa?" Hajja tace "Ban sani ba, ki bada sakon da nace a kawo min" Daga haka Hajja ta katse wayar tace "Munafuka kawai har tana cewa in dauki Jiddah in kai Bauchi kamar ubanta ne ya halitto Jiddar, ai duk sai na ci kaza kazan kowa in dai abu ya samu Aliyu" Umma dai bata sake bin ta kan Hajja ba. Hajja na katse wayar Aunty ta shiga kiran Aneesah, Aneesah na dagawa tace "Ke dama mijinki na asibiti shine baki gaya min ba, kuma me ya samesa?" Aneesah ta mike xaune daga kwancen da take ta dafe kirji da sauri tace "Asibiti? Ke wa ya gaya maki Aunty??" Aunty tace "Ban gane wa ya gaya min ba, ina Aliyun toh?" Aneesah ta mike tsaye cike da confusion tace "Wllh ina bacci ya tasheni na basa makullin mota ya fita daxu da safe kuma bai ma ce min ga inda xai je ba... auu ya kuma dawowa gida ai wajajen karfe sha daya, to shine ya sake fita bayan azahar, ke a ina kika ji yana asibiti?" Aunty tace "Yanxu tsinanniyar tsohuwar can ta kirani take fada min a kai mata bargo da pillow" Aneesah tace "Bai fa ce min asibiti xai je ba, bari xan kira Ahmad yanxu" Aunty tace "Ki kirani idan kin tambayesa" Aneesah tace "Toh" daga haka ta katse wayar, Ahmad ta shiga kira nan kuma ya gaya mata asibitin da suke, iyakar tashin hankali ta shiga a lokacin, abun har ya kai ga admitting, da sauri ta kuma kiran Aunty tace "Wllh da gaske ne Aunty har an kwantar da shi wai..." Aunty tace "Wani asibitin ne?" Aneesah ta gaya mata, Aunty tace "Toh ki biyo mu tafi tare kawai" Aneesah tace "Ai na koma baya Aunty, mu hadu a asibitin kawai xai fi, sai mu tafi da Aunty Safara'u" Aunty tace "Aa nafi son mu je dukanmu tare xai fi, xan jira ku a bakin hanya" Aneesah tace "Toh ai shkkn" daga haka ta katse wayar, da sauri ta wuce sama ta sanar ma Aunty Safara'u, cikin minti goma duk suka shirya suka fito, Safara'u tace "Wannan dai ba girmanmu bane a ganmu cikin adaidaita sahu kamar wasu en iska, katon gida haka ace mota daya ne kacal kamar rai, duk kudinsa shi baxai siya maki karamar mota ki dinga tukawa kije duk inda xa ki ba" Aneesah ta hade rai tace "Toh wai aunty duka duka yaushe na koyi motar, ni dai mu daga kafa kinga kafin a fita bakin titin nan da tafiya, wllh duk hankalina ya tashi" Safara'u ta ta6e baki tana ci gaba da bin ta. Ana kiran la'asar su Aneesah suka shiga asibitin, nurses suka masu kwatancen ward din sannan suka wuce sama, Aneesah ce ta bude kofar ward din, Umma na dakin har lkcn da Hajja dake xaune kan kujera daga kusa da Abuturrab dake ta bacci har lkcn, Ramlah ma na ward din a xaune kan daya daga kujeru hudun da aka kawo, Daga sama har kasa Hajja ta dinga kallon Aneesah da ta iso gun gadon da sauri cike da damuwa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Hajja ta kare gadon ta bubbuda hannunta tace "Ance kada wanda ya matso kusa da shi inji likitocin...." Tsayawa Aneesah tayi tana kallonta irin kallon rainin wayo, Hajja ta kalli su Safara'u da suka yi cirko cirko bakin kofa tace "Oh oh Allah, likitocin fa sunce mutum uku kadai ke iya shigowa dakin saboda yanayinsa, sunce kuma a gaskiya idan ba mu bi doka ba xa su kora mu tunda ba Asibitin ubanmu bane, da a Masar ne ma yaushe xa su bar mutane ukun? Ai sai ni kadai ko Ramlah uwarsa, amma kun wani kwaso jiki kun shigo daki me window biyu kacal ta ina xa a ja numfashi saboda Allah??" Juyawa Safara'u tayi ta fice daga ward din, Aunty dai na tsaye sai kallon kasa kasa take ma Hajja, Hajja tace "In kuma ni in fita ne to sai in fita in bar dakin, ai likitocin ne suka bani umarnin in xauna kusa da shi" Aunty ta d'an kalli Umma tace "Sannu" Umma tace "Au ashe kece" Ko kallonta Aunty bata sake yi ba ta juya xata fita, Hajja tace "Ina bargo da pillon da nace maki Hafsah?" Tuni Aunty ta fice daga ward din without answering her, Hajja ta kalli Umma tace "Kinga er iska ko?? To ni nasan me ta shigo da shi da xan bar ta ta matso kusa da jikana, Aa wllh ba ruwana kowa yayi takansa, ke Ramlah karama fita ki kira mijinki ku koma gida ki taho min da pillow da Bargo daga gidanki" Ramlah tace "Toh" sannan ta fita daga ward din, ita dai Aneesah na tsaye Hajja taki barin ta karasa kusa da Abuturrab kuma ta ki fita, Hajja ta kalli Aneesah tace "Toh kinga ai mun cika uku cif cif a dakin yanxu, ga kujera can ki tafi ki xauna sunce kada a xo kusa da shi saboda halin rayuwa" Aneesah ta kalli Umma ta gefen ido kamar ana tilastata tace "Ina yini?" A dakile Umma tace "Lafiya" Juyawa Aneesah tayi ta nufi kofa ta fita, a reception ta tarar da Aunty da Safara'u suna xagin Hajja, Safara'u na hangota ta mike tace "Bani makullin gida inyi wucewata, ba dani xa a ci gaba a haka ba, idan xuciya ta debeni xan iya dura ma Tsohuwar can Ashar babu ruwana, ba kuma dangin iya balle na baba, ina dalili mata ta tijarani haka" Aneesah tace "Haba Aunty, mijina ne fa ba lafiya, saboda me zaki ce xaki tafi kamar saboda ita kika xo" Safara'u tace "Wllh baxan xauna ba ni ba er iska bace, toh lafiyar ni xan basa idan na tsaya kina ganin walakancin da aka mana yanxu, ke kanki gashi kin fito ward din" Aneesah tace "Toh wai Aunty sai ki biye mayyar can? Mayya ce fa, ni dai kiyi hakuri ki tsaya, duk xan rama maki wllh tllh" Safara'u tace "Anjima dai xan dawo amma baxan zauna yanxu ba tana nan" Aunty da duk hankalinta ya ki kwanciya don tana tsoron kada a tada batun auren Abuturrab a asibitin su Aneesah su ji don har sannan basu da labari, tace "Aneesah kawai ku tafi tunda tijararriyar can na nan, ga kuma wancan munafukar Ramlan a xaune, kinga sunyi bake bake a dakin suna nuna isa da iko gwara kawai mu tafi" Aneesah tayi wani shewa tace "Wllh wllh ba inda xanje ina nan wajen mijina, yanxu a cikinsu akwai warce xata iya masa wanka ko wani abun banda ni da nake matarsa?? Ai duk sai dai su gama kame kamensu a nan amma nice nan dolensa kuma babu inda xanje al-qur'an, xa su sha mamaki yau" Aunty ta hadiye abu da kyar tace "Toh kuwa xaki sha walakanci iri iri wllh" Aneesah tace "Sai kace baki san ni ba Aunty, wllh babu xancen respect tsakanina da su, xa su ga rashin kunya ganin idonsu" Daga haka ta bude jakarta ta ciro makulli ta ajiye ma Safara'u a gefenta ta wuce sama. Aneesah na komawa ward din ko kallon Hajja bata yi ba ta tafi gefen gadon ta xauna tana kallon Abuturrab dake bacci tana gyara masa kwanciya cike da kissa, buda baki Hajja tayi tana kallonta, sai tayi tagumi tace "Yau naga jaraba, ke matar nan bance maki ance kada warce ta je kusa da shi ba ko wata cutar kike son goga masa mu shiga uku?" Aneesah ta kalleta tace "Cuta kuma Hajja, mutumin da muke kwana gida daya, daki daya kan gado daya, wuri daya kice xan goga masa cuta?" Hajja ta mike tace "Toh ai nan ba gidanku bane shegiya, xo ki fita kar in tara maki likitoci yanxu, ko kazantar ki bai isa ya kwantar min da jika ba er banxa kawai" Tun Umma na danne dariyarta tana dakewa har ta kasa, ta mike ta fita daga ward din, Aneesah ta sake baki tana kallon Hajja ko kiftawa babu, Hajja tace "Mata kawai duk kin cika turare a jiki xaki xo ki kawo ma mutane raini a asibiti shashasha kawai" Aneesah tace "Shegiya fa kika ce min?" Hajja na nunata da yatsa tace "Ance maki shegiyar ko ramawa xa ki yi?" Aneesah ta bar wajen fuuu ta koma can jikin window a fusace tace "Wllh ni ba shegiya bace, da uwata da ubana kam" Hajja ta ja kujera ta xauna kusa da gadon tace "Oho dai, ni dai ba kin matsa daga kusa da shi ba" Aneesah kallonta kawai take xuciyarta na tafarfasa, Bude ward din aka yi Ummi ta shigo tare da Umma da Nafisah, kallo daya Hajja ta ma Ummi ta dauke kai, Ummi ta karaso ciki ta ajiye basket din abincin hannunta, with respect ta kalli Hajja tace "Ina wuni Hajja?" Hajja tace "In dai kika kashe Aliyu nima ki kasheni kawai Hauwa" sai kuma ta fashe da kuka tace "Mata ki haifi yaro ki fi kowa k'in sa?" Umma tace "Ya xa ayi ta k'i sa Hajja, ranan da ku ka yi masa caaa a kai so kike ta bude baki ta ce wani abun kice tana goyon bayansa, ko kice ta maki rashin da'a?" Hajja ta mike tace "Aa wllh baxan ce ba ai nasan xafin Haihuwa, idan nice ita ai sai inda karfina ya kare, kaca kaca xan ma duk wanda yace xai sa d'a na a bakin duniya, amma sai tayi shiru kamar jira take a walakanta Aliyun, to wllh Allah xai maku hisabi da shi ba ruwana" Ummi dai bata ce komai ba, Hajja ta fyace majina ta koma ta xauna, Aneesah ta kalli Ummi bbu yabo bbu fallasa tace "Sannu da xuwa" Ummi tace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login