Showing 93001 words to 96000 words out of 346625 words

Chapter 32 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

iya xuwa wai gidansa El-Basheer, ni fa na tattare lamarin Abuturrab na watsar a gefe, i see no reason da xai dinga boye boyen cewar ya saki yarinyar nan, ko meye fa'idan xama gida daya da ita bayan ya saketa, who is he deceiving?? To wllh I've made up my mind cewar Abbansa na dawowa sati me xuwa xan sanar masa komai, wannan ae iskanci ne, to ko minti biyar ba ayi da muka gama waya da mahaifiyar Aneesah ba, labari ya je masu, kana tunanin xaka iya ci gaba da boye masu ne dama?? Wllh yanxu haka duk hankalina a tashe yake, nayi kokarin fahimtar da su ba auren amma ya faskara...." Kallonta kawai Abuturrab yake yi, shi na Aneesan ma bai damesa ba kamar na Abba da tace xata sanar ma ya saki Jiddah kuma yana xaune tare da ita, gaba daya yaji hankalinsa yyi mugun tashi, Waje ya nema ya xauna jin har kansa ya fara juya masa, El-Basheer yace "Ni banga abun boye boye a nan ba, let this be known to everyone that she is no longer ur wife, kana xaune gida daya da macen da ba muharramarka ba, who does that??" Abuturrab ya kalli Aunty da ta ci gaba da abinda take bbu fara'a fuskarta, yyi kasa da murya yace "Amma Aunty kinsan Abba won't be happy idan yaji na saketa, he will be highly disappointed at me, kuma ni sbda bana son bacin ranki ya sa na saketa wllh, idan kika gaya ma Abba cewar nayi hakan yanxu he won't take it likely with me, i am just confuse Aunty" Aunty ta juyo a fusace tace "Ni kuma dole in sanar masa duk abinda xae faru ya faru ba, are u this happy being with the girl da yasa ka daina dawowa weekend gidan nan sae dai ka sauka gidanka ka karashi weekend dinka ka wuce, haka xaman naka da ita yayi dadi duk da ba matarka bace ashe?? To kuwa xaka sha mamakina kuwa wllh" Ya girgixa kai yace "Aunty ni weekend din ma gaba daya na daina dawowa fa, Jiya ne kawai na dawo sbda El-Basheer yace min yana hanya" Aunty tace "Wato ita kadae ke yanda ta so a katon gidan? Ka sakar mata babban gida haka ta ci karenta ba babbaka, to baxai yiwu ba ne wllh" Shiru yyi bai ce komai ba, Aunty tace "Don kuwa da ta ci gaba da xaman gidan nan naka gwara ka dawo da ita nan, dama mai aiki xata tafi garinsu jibi, kaga ba wani xai ce ta bar nan gidan ba wataran..." Kallonta kawai Abuturrab ke yi gabansa na bugawa, tayi masa tsawa tace "Kallon ne amsan ka? Ko baxa kayi abinda nace bane??" Ya girgixa kai yace "Aunty can din ma ina assuring dinki ba sae wani yace ta tafi ba xata tafi, wllh ita kadai ce bbu kowa" Aunty ta kara masa wani tsawa tace "Nace ka dawo da ita gidan nan, ko ban isa ba??" Ya sunkuyar da kansa lkci daya jikinsa yyi sanyi, can ya kalleta cikin sanyi yace "Toh" Sannan ya mike ya nufi kofa ta bi sa da harara tana huci, El-Basheer ya d'an yi murmushi yace "But how can a normal human being do what Abuturrab did?" Cike da bacin rai Aunty tace "Atoh... Isn't this irritating Bash?? Wllh da lamarin nan nake kwana nake tashi a raina, ya ce ya saketa quite alright he did that, na sani, to kuma xaman me suke tare idan anyi magana yace Abbansa, ance masa da Abban nasa ya san ya saketa xae barsa ya ci gaba da xama gida daya da ita, ga yarinyar ido a bude, to xaman iskanci yake son fara yi da ita ko me, don dai shi ma ba saiti garesa ba kuma ba jin magana yake ba, ka sani, na sani, shi yasa bai dauki xaman da yake under same roof with her wani abu ba" El-Basheer ya mike yace "Allah ya kyauta" daga haka ya fita. Ko bangaren Ummi Abuturrab bai shiga ba ya fice daga gidan ya shiga motarsa ya jinginar da kansa da kujera yana jiran El-Basheer, dalilin da yasa bai son xuwa gidan kenan idan ya dawo weekend, ganin har bayan minti sha biyar El-Basheer bai fito ba Abuturrab yyi dialing numbersa, El-Basheer na dagawa, a fusace yace "Inyi tafiyata ne?" El-Basheer yyi murmushi ya katse wayar, kallon wayar Abuturrab ya dinga yi, sai ga text ya shigo masa, bude content din yyi, "C'mon wani irin gaisuwa kake son inyi ma Ummi, gaisuwan minti goma? Tunda kai kaki shigowa gaisheta ni baxan iya ba" Abuturrab ya mayar masa reply yace "Ka sameni a gida then" daga haka ya ajiye wayar ya tada motarsa ya bar anguwar. Yana parking ya shiga parlor ya xauna kujera ya jinginar da kansa ya lumshe ido yana jin ransa ba dadi, text ne ya shigo wayarsa ya bude ido a hankali ganin Aneesah ce tayi text din ya bude content din, "Abinda ka min was the least i expected from you Aliyu, ban yi xaton haka ko a mafarki ba, amma ka sani ka cuceni, ka ci amanata, ka yaudareni, ka ruguza min rayuwa, i gave u all my trust but u ended up betraying me, why Aliyu, did i deserve this harsh treatment from you?" Ko gama karanta text din bai yi ba yayi mata reply kamar haka "Since you never expect this from me... Then u consider me... Aure kuma sai idan kece kika ce baxa kiyi da ni ba, as for me you will be my first and last wife in sha Allah.... i will call u in 5 hours time in sha Allah" daga haka ya tura mata text din ya ajiye wayar ya mike ya wuce sama. Har bayan Magrib El-Basheer bai shigo gidan ba, hakan ya sa Abuturrab yyi dialing number sa, yana fara ring El-Basheer ya daga yace "Gobe xan shigo before leaving, Ummi tace i should spend the night here" Abuturrab yace "Ohk" daga haka ya katse wayar. Mikewa yyi ya wuce sama ya bude kofar dakin Jiddah, tun da ya dawo ko motsinta bai ji ba, tana xaune gaban mirror tana ma gashinta kitson kalaba, ganinsa ta dau hulanta ta saka, yana tsaye bakin kofa yace "Meye hakan kike yi?" Tace "Aa ina kitson gashin ne, yana karyewa idan ban yi kitso ba" Yace "Sai anyi kitson ne baxai karye ba?" Ta gyada masa kai, yace "Toh kwance wannan abinda kika yi, tunda a garinku ne aka ce maki xai karye idan ba ayi kitso ba, a tsefe xaki bar gashin, haka nake so" Ta kallesa da sauri, that was when he realized what he just said, lkci daya ya hade rai yace "Ko kina ganin kitso a gashin su Ramlah, mu a nan ba a kitso" Cikin sanyin murya tace "Toh" ta fara tsife dogon gashin nata da ta kitsa, har ta gama tsefe daya bata ji ya tafi ba, hakan yasa ta leko sa ta cikin gashinta da ya rufe mata fuskarta gaba daya, suna hada ido ya juya ya fita dakin. Ana kiran isha ta gama parking din dogon gashin nata ta kitse jelan sannan ta sa hularta. Karfe tara saura wayar da Abuturrab ya bata ya fara ring a gaban madubi, karasawa tayi ta dauka tana kallon number jikin screen din sannan tayi picking ta kai kunne, muryarsa taji yace "Ina jiranki a parlor" Daga haka ya katse wayar, ajiye wayar tayi ta sa Hijab dinta ta fita, shi kadae ne xaune parlon ta durkusa jikin kujera a hankali tace "Gani" Yace "Me kika ci?" Ta sunkuyar da kanta tace "Taliya na dafa" ya nuna mata ledan dake gefensa yace "dauka" mikewa tayi ta isa kusa da shi ta duka ta dau ledan, ya rike numfashinsa sbda wani kamshi na daban da ya doki hancinsa, ganin kwalin lemo a cikin ledan ta cire xata ajiye, ya saki breath dinsa ya hade rai yace "Har da shi xa ki tafi" Innocently tace "Ban iya sha ba" Yace "Haka xa ki je ki koyi sha yau, tunda ke yar kauye ce" Bata ce komai ba ta mayar da kwalin cikin ledan sannan ta mike ta nufi stairs, bin ta yyi da kallo tana isa stairs ta juyo suka hada ido, da sauri ya dauke idonsa, tace "Nagode" sannan ta wuce sama, jinginar da kansa yayi a hankali da kujera yana jin damuwa iri iri a ransa, gasasshiyar kaza ce da yaji Jiddah ta bude a dakinta, sai kamshi kazan yake, ta kalli kwalin hollandia din sannan ta bude ta d'an sha kadan, ji tayi yayi mata dadi a baki sbda gardinsa, ta lumshe ido ta kara sha sannan ta ajiye ta fara cin naman a hankali, lkci daya rayuwar da tayi a gidansu ya fado mata, tura kazan tayi tuna Babarsu da tayi.
Abuturrab na kwance wajajen sha daya a parlor, waya na kare kunnensa, he felt relieved bayan yayi convincing Aneesah a kan kaddara ce ya sa shi auren jiddah sannan kuma bashi da aurenta a kansa yanxu, daga daya bangaren cikin sanyin murya tace "Amma why is she still at ur resident My captain??" Yace "Ina kike son in kai ta yanxu?" Tace "Ni ko gidanmu ma ka kawota su Mummy baxa su ce Aa ba wllh, ni nasan karyar da xan masu, ka barta ta dawo gidanmu plss" Bai san lkcn da yyi wani murmushi ba, a hankali yace "Koh?" Ta marairaice tace "Sure dear" yace "I will think about that, xuwa nan da short period of time" tace "Do so fast plss Captain" daga kai yyi jin footstep a stairs, lkci daya yace "I call you in some minutes time" bai jira cewarta ba ya katse wayar, yayi kasa da idonsa kamar me bacci, A hankali Jiddah ke tafiya duk xatonta bacci yake hannunta rike da ledan kazan da ko yanka uku bata ci ba, to bata saba da shi ba shi yasa bata iya ci sosai ba, drink din ne ma ta d'an sha ba laifi, kitchen ta tafi ta ajiye ledan kazan a fridge ta ajiye lemon ma sannan ta fito, a hankali take tafiyar ta nufi stairs ya bi ta da kallo, nighty ne jikinta wanda ya wuce kneels dinta da hularta a kanta, sai da ta isa stairs ta juyo ta kallesa suka hada ido, sosai ta tsorata, yyi saurin mikewa xaune pretending to be awake at that moment yace "Me kike yi a nan" ta nuna masa kitchen tace "Na kai abu na ajiye" yace "Je ki dauko abinda kika ajiye" Tayi narai narai da ido ta ki motsawa daga inda take, ya hade rai yace "Baki ji abinda nace ba?" Da gudu ta wuce sama, ya mike tsaye da mamaki yana bin ta da kallo, har ta shige dakinta.


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems
[6/11, 7:21 PM] +234 803 540 6041: Har karfe daya da wani abu na dare Jiddah bata yi bacci ba, abu bai ta6a tsaya mata rai irin abubuwan da Abuturrab ya gaya mata ba, gashi har sannan ko digon hawaye bata yi ba, amma abun ya ki barin xuciyarta, da yake a kasan darduma ta kwanta kuma bai bi ta kanta ba yyi kwanciyarsa saman gado, ta mike xaune a hankali ta daura kanta bisa gwiwanta, sai a sannan hawaye ya shiga sauka idonta, gaba daya taji da ma ta hakura da aurenta da Iliya, taji ta gwammace gwara ta koma gidansu komin abinda xae faru, taji gwara ta gudu kawai, daga kai tayi hawaye na sauka idonta ta kallesa, duk da wutan dakin a kashe yake, tana ganinsa kwance saman gado. Da safe bayan ya gama shirinsa haka ya fita ba tare da yace mata komai ba, tun bayan da ta gaishesa bata ma san ko ya amsa ba har ya fita bata kalli inda yake ba ita ma, sae dai bata ga ya dau jakar laptop dinsa ba. Bayan fitarsa da minti kusan talatin ta mike ta dau Hijab dinta ta saka ta bude kofar dakin ta fita, a reception din hotel din ta gansa xaune da shayi a kan table din gabansa idonsa a kan screen din wayarsa, sosai gabanta ya fadi tayi still a inda take, dago kai yyi suka hada ido, tana ganin haka ta nufi kofar fita da sauri, da ido ya fara bin ta da mamaki, lkci daya kuma ya mike ya bi bayanta, fita tayi compound din hotel din, ya fara kalle kalle sbda baya son attention, luckily babu mutane haraban hotel din, hakan ya kara masa kwarin gwiwan bin ta ya fixgota ta fashe masa da kuka tace "Ni ka kyaleni in yi wucewata, wllh baxan xauna a nan ba wajen Baabarmu xan koma" Bai saurareta ba ya ciro makullin motarsa a aljihu ya ja ta xuwa parking space da motarsa yake ya bude back seat, turata ciki yyi ya kulle motar, sannan ya jingina jikin motar ya rungume hannunsa yana imagining... assuming baya xaune downstairs tafiyar xata yi da gaske, Jiddah ta dinga rusa kuka cikin motar, ya fi minti 7 a tsaye kafin ya bude motar ya shiga ya kulle, can gefe ta koma tana shessheka taki kallonsa, yana kallonta fuskarsa a daure yace "Ina xa ki tafi kika ce?" Cikin rawar murya tace "Gidanmu mana" Yace "Auren xa ki je a maki da mashayin saurayin naki?" Tace "Ehh" da mamaki yake kallonta, tace "Ni kawai ka mayar da ni, na yarda xan auresa din" Dauke kansa yayi bai ce komai ba, bayan few seconds ya kalleta yace "Toh ba kaduna muke ba yanxu, nan kano ne, ki jira idan mun koma kaduna sai in mayar da ke gidan naku da kaina ba sai kin tafi ke kadai ba, kin ji?" idonta ta fara gogewa tace "Yaushe xa mu koma kadunan?" Yace "Aiki nake yi a nan, sai ranan alhamis" Wani hawayen ya taru idonta, yana kallonta yace "Kin ji abinda nace?" Hawayen ya xubo mata tace "Har sai alhamis kuma?" Yace "Jibi ne alhamis din ai" Ta sunkuyar da kanta tana goge hawayenta, shi dai kallonta kawai yake ko kiftawa babu, a hankali tace "Toh" Bai kuma cewa komai ba, ya juya ya bude motar ya sauka yana dubanta yace "Sauko" Ba musu ta sauko daga motar tana wani kumbure kumbure, yana kallonta yace "Wani man kike shafawa?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Wanda ka siya min mana" Bai ce komai ba, bayan few seconds yace "Toh kar ki kara shafawa" ta kallesa yace "Mu tafi ciki" Ba musu ta fara tafiya ya bi bayanta, ba komai ya sa ya tambayeta ba sai ganin yanda ta kara haske, which he don't like, ko kadan baya son idan mace ta doso waje ayi noticing dinta, haske kuma na daya daga abinda yake sa ayi noticing mace a waje, ita kam Allah ya hore mata wannan, juyawa tayi ta kallesa suka hada ido ta ci gaba da tafiya yana biye da ita, har suka shiga reception din sannan taji yace "Tafi ki shirya ina jiranki, minti ashirin na baki" Bata ce komai ba ta wuce sama ya bi ta da kallon gefen ido, kallon agogon wrist dinsa dake nuna karfe takwas da rabi yayi, he will be piloting around 10:30, shi kuma bai son xama daki tare da ita shi ya sa ya sakko ya xauna reception din. Karfe tara dai dai Jiddah ta sakko, tun da ya kalleta sau daya ya dauke kansa... Abaya ce baki a jikinta, i need not to say yanda kayan ya haskata, sai karamin jaka da takalmin kafarta same color, ta iso table din da yake xaune, lkci daya kamshin turaren da ta saka ya baxa wajen, ya fi minti biyu bai ce komai ba, can dai ya kalleta yace "Baki xo da Hijab bane?" Ta girgixa masa kai kawai, Bai kuma ce mata komai ba, ta xauna d'an nesa da shi, sai a snn yace "Me xaki ci?" Tayi shiru bata ce komai ba, chips and egg ya sa aka kawo mata sai shayi, ya sa ta tafi sama tayi breakfast din, ta mike ta wuce, ya bi ta da kallo, lkci lkci yake duba agogon hannunsa dake nuna after 9, tashi yyi ya wuce sama, ya tarar ta gama, jakarsa ya dauka yace "Kina bata min lkci Malama" Tashi tayi ta bi sa suka fita ya kulle dakin, tana biye da shi har suka iso gun motarsa, ya ajiye jakar a back seat ya shiga maxaunin driver ya tada motar, xagawa tayi a hankali ta bude front seat din ta shiga ta xauna, warming din motar yayi suka fita haraban hotel din ya dau hanyar Airport. Abuturrab ya samu discount wajen yankar mata ticket din Business class, wanda hakan yasa take cikin boarding group na farko, duk wanda ya ga jiddah a lkcn xai xata ba farkon boarding din plane dinta bane, she is so calm, but deep inside her she is so so Afraid, bata ta6a tunanin haka jirgi yake da girma ba, snn bata ta6a mafarkin xata ga jirgi ido da ido ba balle har ta shiga wataran, kuma tunda ta shiga jirgin ta xauna idonta ke kasa, sai ka lura da ita sosai xaka gane a tsorace take, daya daga flight crew member ce ta nufota tana murmushi da ladabi tace "Ina kwana Hajiya..." Jiddah ta daga kai ta kalleta a hankali tace "Ina kwana" Cabin crew din na murmushi ta xauna kujeran gefenta tana kallonta ta buda mata ido sannan ta shiga fastening Seat belt dinta, wanda da alama Abuturrab ne ya sa ta gwada mata yanda zata saka seat belt din, Jiddah dai kallonta kawai take


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login