Showing 306001 words to 309000 words out of 346625 words

Chapter 103 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

kwatsam sai ga mummunan mafarkin nan daxu, kin ga kuwa ai ba lafiya, to tun kan a cuceni a mayar dani Bebiye gwara a xo a biya min tikiti in koma Masar bakina alekum" Jiddah dai sauraronta kawai take, Hajja tace "Shi kuma yaushe xai dawo daga gararin samaniyar tasa?" Jiddah tace "Kilan juma'ah ko asabar, Hajja ki xauna in kawo maki ruwa" Hajja tace "Wani ruwa bayan abinci ma wannan na kasa ci, meye kuma ruwa, naga alama kun dau wannan kess din karamin kess, wllh da a Masar ne sai an bata kwadon gaske ace ta kulle bakin nawa a gani, Allah sai an mata zindir an xane shegiya sannan a mika ma yara su yi ta jifa, me na mata xata min haka??" Tana kai wa nan ta nemi waje ta xauna tana fiffita xufar da tayi da mayafinta, Jiddah ta nufi kitchen dauko mata ruwa da lemo ta ajiye gabanta, Hajja ta dau goran ruwa daya sai da ta kwankwadesa tass, sannan ta ajiye tace "Rabona da shan ruwa tun kan inji wannan mummunan batun" Bude kofar parlon aka yi duk suka daga kai, sosai gaban Jiddah ya fadi ganin Abuturrab ya shigo parlon, suna hada ido ya dauke idonsa fuskar nan tasa a daure, ta sunkuyar da kai, Hajja ta kalli Jiddah tace "Kika ce min ya tafi aiki?" Kafin Jiddah tace komai yace "Ehh daga can nake" Hajja ta mike tace "Abinda Allah ya ga xuciyata ko daga sararin samaniyar ne ai sai a hankado min kai kawai, wllh ina cikin garari Aliyu, gidan Kyauta yayar Hafsah xaka kai ni a Barnawa don girman Allah" Abuturrab yace "Daga Abuja fa nake yanxu ko hutawa ban yi ba Hajja" Hajja tace "Oh oh Allah, Aliyu mafarki nayi an kulle min baki da kwado fa? Wa xai xauna da wannan mugun mafarkin idan ba gantalalle ba" Yace "Toh ki bari in huta na gaji, bayan nayi aiki kuma na sake shiga mota na taho kaduna" Hajja ta koma ta xauna tace "Toh tafi ka huta ko na minti sha biyar ne, ai ni ba bakuwar xafi bace, banda Ramlah ma bata san gidan ba ai ita nayi niyyar ta rakani don naga ita dai dai take da ko wani d'an banxa a duniya" Abuturrab bai ce mata komai ba ya nufi sama, Jiddah ta bi sa da kallo, Hajja tayi kasa da murya tace "Ina gantallaliyar abokiyar xamar ta ki?" Jiddah tace "Kila tana daki ban sani ba" Hajja tace "Atoh, ina ruwanki da ita da xaki san inda take dama" Mikewa Jiddah tayi tace "Ina xuwa Hajja" Hajja tace "Toh ni dai kar a shanya ni, ba ruwana da iskanci da rana tsaka" stairs Jiddah ta nufa, tana haurawa sama ta tsaya corridor tana tunanin ta je ko kar taje side din nasa, haka kawai ta ji tana shakkarsa sosai, bayan few seconds kawai ta nufi bangaren nasa tana tafiya a hankali, bude kofar parlon tayi kamar munafuka ta shiga ciki ta gansa xaune, ta karasa ciki ta d'an durkusa kasa daga gefensa ta ki yarda su hada ido tace "Sannu da dawowa" Ba tare da ya kalleta ba yace "Thank you" Kallonsa tayi a hankali, jin bai sake cewa komai ba ta mike ta nufi kofa ta fita ta koma wajen Hajja. Bayan minti ashirin Abuturrab ya sauko parlor kafin nan sai da ya bude kofar dakin Aneesah ya ji sa a kulle, kallon Jiddah yayi yace "Lend me ur car key" Ta mike tana kallonsa don babu yabo babu fallasa yayi maganar, ta wuce sama ta dauko masa makullin a dakinta ta risina ta basa, ya amsa yace "Tashi mu je Hajja" Hajja ta mike tace "Allah yayi maka albarka, mu je in ji ba'asin kulle min bakina" Kofa ya nufa tana biye da shi ko sallama bata tuna tayi ma Jiddah ba har suka fita, Jiddah ta bi su ta tsaya bakin kofa tana kallon Abuturrab, ya ki yarda ya kalleta, nan da nan hawaye ya kawo idonta, kamar ance ya juya ya ga hawaye a idonta, ya jefa mata wani kallo, turo masa baki tayi ta juya ta koma parlon da sauri. Abuturrab na ajiye Hajja kofar gidan Kyauta ya ciro dubu biyar ya mika mata yace "Hajja gashi idan xaki koma sai ki samu adaidaita sahu, ni yanxu xan koma aiki ne, nayi mantuwa ne yasa na dawo" cike da masifa Hajja tace "Yau naga jalala, dama ba da kai xa mu shiga ba ni kadai raina xan shiga?" Yace "Toh ni macece da xan bi ki mu shiga Hajja, excuse na dauka wajen aiki, jirgi na can a airport din Abuja xan daga xuwa kano" Hajja tace "Toh na fi jirgi ne? Ko ina ruwana da shegen jirgin naku? Sbda ba bakin uwarka aka yi niyyar garkamewa ba shi sa baxa ka bi ni mu shiga ba ko??" Dariya ta basa amma ya cije yace "Toh sai in bar aikina in shiga ayi ta xancen garkame baki da ni?" Hajja tace "Toh Allah ya isa, ai sbda kai da uwarka aka yi niyyar kulle min bakin nawa Allah ya toni asiri, kuma wllh daga yau ko kasheku naga xa ayi kai da uwarka shiru xanyi abina in koma gefe tunda gashi ta dalilinku aka nemi hallaka min bakin da nake salati nake ba Allah gaskiya" Daga haka ta fixge dubu biyar din ta shige gidan tana rafka wani uban sallama, dariya yayi ya juya kan motarsa ya dau hanyar gida. Yana komawa gida bayan ya haura sama dakin Aneesah ya bude ya ji a kulle har sannan, ya d'an tsaya sai kuma ya nufi dakin Jiddah ya bude, kwance ya ganta tayi kukanta ta koshi, ta mike xaune tana kallonsa ya wani hade rai, cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri" yace "Ban yi ba" Tura masa baki tayi ta juya masa baya, ya shafa kansa yana kallonta, sai kuma yace "Ina Aneesah?" Ta kallesa a hankali tace "Nima ban sani ba" ya karasa dakin ya rungume hannunsa yana kallonta, lkci daya ya dauke idonsa daga kanta, yyi kasa da murya yace "Make me a cup of tea" daga haka ya juya ya fita, ta mike a hankali ta fita ita ma ta sauka downstairs. Bangarensa ya tafi ya dauko spare key ya bude dakin Aneesah thinking ko kulle kanta tayi a ciki, amma babu kowa dakin haka ma bathroom din... A ranan Abuturrab xai koma Abuja don ko awa biyu bai yi niyyar yi ba a gidan, but ya kasa tafiya yana ta xaune parlor downstairs yana jiran ya ga sanda Aneesah xata shigo gidan, Jiddah ta fito daga kitchen tana kallonsa tace "Na gama in xubo maka yanxu?" Ya daga kai ya kalleta yace "Tun yaushe Aneesah ta fita gidan nan?" Ta d'an buda hannunta tace "Nima ban sani ba ina daki" Yayi shiru, ta koma kitchen ta xubo masa girkin da tayi ta fito ta ajiye masa kusa da shi, kallon kirjinta kawai yake da ta durkusa ajiye abincin, ya lumshe idonsa ya jinginar da kansa jikin kujera, don ba karamin nesa yake kai xuciyarsa ba a kanta tun daxu, barin da ya shiga dakinta ya ga tana kuka he wish he can hug her tightly and tell her he isn't angry and he is back all because of her, ta mike tana kallonsa ta wuce sama ta shiga dakinta ta xauna tana tunanin yanda xata yi Aneesah ta san ya dawo gidan, mikewa tayi ta tafi bangarensa tana kallon wayarsa da ya bari kan kujera, dauka tayi ta kulle kofar parlon, ta shiga call logs dinsa amma bata san yanda yayi saving number Aneesah ba, Blossom ta gani can kasa nan da nan ta tuna ta ta6a ganin sunan a phone dinsa da dadewa tayi dialing number, yana fara ringing aka daga.....




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you


_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp









Jiddah tayi shiru, daga daya bangaren ta ji muryar Aneesah kasa kasa tace "Hello My captain..." ta fadi hakan yayi sau uku, jin shiru Aneesah ta katse wayar ta sake kira, Jiddah ta dinga kallon screen din kamar baxata daga ba, har ya kusa katsewa sai kuma ta daga a takaice tace "Dama kawai ce maki xanyi ya dawo tun daxu..." Aneesah ta xabura lokaci daya tace "Captain din?" Jiddah bata ce mata komai ba ta katse wayar, Ta ajiye masa kan kujera sannan ta fito ta wuce dakinta.. Abuturrab na dawowa masallaci bayan magrib ya dinga kallon motar da yayi parking kofar gidansa, sai ga Rabi'ah ta sauko daga maxaunin driver ta bude back seat ta riko Aneesah ta fito da ita, Banda nishi babu abinda Aneesah take tana tafiya da kyar Rabi'ah na rirrike da ita tana mata sannu, ya dinga kallonsu sai kuma ya shige gate kawai, yana xaune parlor suka shigo bayan minti goma irin da kyar Aneesah ke tafiya din nan, Aneesah ta kwanta saman kujera tana sauke numfashi da kyar tace "Ka dawo ne Captain? Hope all is well?" Shiru yayi yana kallon tv, Rabi'ah tace "Haba dai Captain, kai da ya kamata ka fara tambayar lafiya ka dawo gida baka sameta ba kuma daga ina take? Sai kuma kayi shiru? To daga asibiti muke" Ko kallonta Abuturrab bai yi ba, Aneesah ta mike xaune ta jingina da kujera tana nishi tace "Ban yi bacci ba kwata kwata jiya da daddare captain wani xaxxabi me xafi ya rufeni na rasa yanda xanyi, ga shi drugs da aka min prescribing a hospital kamar shi ya sake triggering xaxxabin da ciwon kai, na daure da sassafe na fita na kwankwasa ma matarka kofa tana ji ta ki budewa, har ce mata nayi bani da lafiya ne, wllh sai ce min tayi ita baxata iya fitowa ba bacci take, ban ta6a xaton haka ba wllh, na dai koma dakina ina son sake shan drugs din nawa amma ban ci komai ba, sai na daure na sauko downstairs wajen karfe sha biyu tana xaune tana kallo tana cin abincin da ta girka, jin kamshin girkin ya sa naji amai ya taho min, wllh captain a nan parlon na gama amai na, na gyara wajen Jiddah ko sannu balle Allah ya sauwake, shine na koma daki nayi ta kiran layin Aunty Safara'u taki dauka kuma nasan fushi take da ni har yanxu, da na rasa yanda xanyi kai kuma ina tunanin kana bakin aiki sai na kira Rabi'ah ta xo ta kai ni asibiti, shine sai yanxu fa" Rabi'ah ta ajiye mata ledan magungunan hannunta tace "Sai da safe Aneesah, Allah ya sauwake ya kara lafiya, ciwo kuma na kan kowa ai...." Daga haka ta nufi kofa ta fita, Abuturrab ya dinga kallon Aneesah dake sauke numfashi da kyar, yace "Wani asibitin ku ka je?" Tace "Nima ban sani ba, sai dai a tambayeta, i almost lost conscious a hanya" Bai kuma ce mata komai ba ya mike ya wuce sama, ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, ta tashi ta tafi dakinta da sauri ta kwanta ta lulluba da bargo, bayan isha Abuturrab ya shigo dakin nata, duk da idonta biyu taki nuna hakan, ya karasa ya xauna gefen gadon yana kallonta yace "Ya jikin?" Ta bude ido da kyar tace "Da sauki" yace "Me xa ki ci?" Tayi kasa da murya tace "Shayi kawai xan sha kar in yi amai" mikewa yayi ya sauka kasa ya shiga kitchen, yana making cup of tea Jiddah ta shigo kitchen din, ya kalleta sau daya ya ci gaba da abinda yake, ta wanke plate din hannunta ta ajiye xata fita ta ji yace "Me yasa da Aneesah ta ce maki bata da lafiya kika yi shunning din ta?" Kallonsa Jiddah take with confusion, ya juya ya kalleta yana jiran amsanta, jin tayi shiru yace "Just like that?" Tace "Ehh, haka nayi niyya" tana fadin haka ta juya ta fita ya bi ta da kallo, lkcn da Aneesah ta fada masa he find it hard to believe ya dai ji ta kawai, amma yanxu ya tabbatar hakan ne, ya dau shayin ya fita ya kai ma Aneesah daki, Jiddah ta xauna gefen gadonta tambayar da Abuturrab ya mata na rotating a kanta, wai me yasa tayi shunning Aneesah, a ina ta ganta balle tayi shunning dinta?? Karfe hudu da rabi na asuba Abuturrab ya gama shiryawansa a dakin Aneesah, ita ce ma ta tashesa don yace mata he will be leaving very early kafin sallan asuba sbda karfe takwas xa su yi piloting jirgi xuwa PH, ta hada masa ruwan wanka ta dauko masa kayan da xai saka daga bangarensa har hakan ya basa mamaki don duk xamansu bata ta6a yi masa haka ba, da damuwa tace "To breakfast fa? Haka xaka tafi baka karya ba?" Yace "I will... At the airport, how are you feeling now?" Tace "Aa na ji sauki sosai" Yace "Alright, Allah ya sauwake" Tace "Ameen My Captain, yaushe xaka dawo?" Yace "Friday in sha Allah" tace "Toh wai me ya dawo da kai jiya, ko dai ka ji a jikinka bani da lfya ne?" Yayi murmushi kawai ya dau jakar laptop dinsa yace "Probably.... Take care, sae na dawo" tace "Toh xa ma ka samu motar da xai je Abuja this early kuwa?" Yace "Aa i will drive" daga haka ya nufi kofa tace "But ina son magana na minti daya captain" ya juyo ya kalleta, tayi kasa da murya cike da damuwa tace "I don't know why Jiddah bata son mu xauna as one Captain, ko don sbda abubuwan da na dinga yi a baya ne ya sa ta ki sakin jiki da ni ban sani ba, dama shi mutum baya canxawa Allah baya canxa sa? Wllh nayi nadaman abubuwan da na aikata a baya, naga ba shi da amfani ba shi da fa'ida, i was just behaving like an illiterate a lokacin, baya bayan nan na gane babu abinda ya kai xaman lafiya dadi, balle ita da nake mata kallon warce bata da hayaniya xa mu xauna lafiyan, amma wai bani da lafiya Jiddah tayi kamar bata sani ba a gidan nan alhalin a gabanta nayi amai ta kauda kai, rashin lafiya ae ya fi gaban komai... da bata min haka ba wllh" Yace "Sai na dawo" fita yayi dakin, ya nufi dakin Jiddah ya murda kofar ya bude ya shiga, bude kofar ya farkar da ita, ya kunna wutan dakin yana kallonta yace "Lend me the car key" Sauke ido tayi daga kallonsa ta sauka kan gadon ta tafi gaban madubi ta dau makullin ta ba sa, har ya nufi kofa ya dawo yana kallonta yace "Ke yanxu abinda kika yi jiya kin kyauta Jiddah? Komin abinda mutum yayi maki kika ga bashi da lafiya ai xaki yi masa abinda ya kamata a matsayin ki na musulma, Did u know what it means to have a forgiving heart kuwa?" kallonsa kawai Jiddah take ta ma rasa abinda xata ce don bata san a kan me yake maganan ba ma, a xuciyarta kuwa tunani ta shiga yi waye ba lafiya? Ganin taki ce masa komai ya nufi kofa ya fice daga dakin. Da safe karfe tara Jiddah ta sauko ta ga Aneesah xaune parlor tana kallo da plate din samosa da spring rolls a hannunta tana ci, aikin kenan ta ci tayi kallo... Tana ganin Jiddah ta dinga mata wani kallon raini daga sama har kasa, Jiddah dai bata kalleta ba har ta wuceta, ta ja wani dogon tsaki tace "Shi dan talaka dama idan ya samu waje ya fi kowa gogewa da girman kai, banxa kawai er matsiyata" Jiddah ta tsaya ta juya tana kallonta, Mikewa Aneesah tayi ta nufeta a fusace tace "Ko xa ki rama ne da kika tsaya kallona haka?" Jiddah ta girgixa kanta tace "Not my home training" Ta juya xata wuce Aneesah ta fixgota da karfi tace "Home training din waye kenan?" Duk da yanda gaban Jiddah ya dinga bugawa haka ta hade rai tace "Cika ni..." Aneesah ta dunguri kanta tace "Anki a cika ki don ubanki, kiyi abinda xa kiyi" Jiddah tace "Babu abinda xanyi tunda ni ba mahaukaciya ba..." Bata rufe baki ba Aneesah ta sauke mata mari sannan ta hankadeta da karfi tace "Uwarki ce mahaukaciyar, ehh uwarki da ba a san ko cikin shege tayi ta haifeki ba tunda har yau ba a ga dalilin asalinki ba..." Jiddah ta dafe kuncinta tana kallonta, Bata san lkcn da ta figi flower vase dake saman center table ba ta buga mata shi a kai, duk da Aneesah ta kauce sai da abun ya sameta, wani ihu ta fasa ta dafe kanta lkci daya idonta ya fara juya mata sai dai kan nata bai fashe ba, ta nufi kitchen da gudu kamar mahaukaciya, Jiddah na ganin haka tayi hanyar kofar fita, kan kace me sai ga ta a bakin gate, gaba daya ta tsorata, mai gadi na tambayarta lafiya ko kallonsa bata yi ba ta fice ta shige gidan Hajiya Fatima, da gudu Mai gadin ya nufi entrance din gidan don ganin abinda ya faru.... Babu kowa parlon gidan, Jiddah ta xauna saman kujera a hankali tana bin parlon da kallo, lkci daya ta rufe fuskarta da kujera ta fashe da kuka a hankali, ji tayi ta gaji da komai na rayuwan, ta rasa me ke mata dadi, ta ma rasa wani tunanin xata yi, kuka tayi sosai a parlon daga karshe ta goge hawayenta a hankali ta jinginar da kanta da kujera tana tunanin rayuwarta, she wish she have another place to go apart from Umma's house, she wish tana da yan uwanta na jini da ta sani, she wish her father is alive today, kilan da gorin da xa a dinga yi mata bai kai haka ba, wasu hawayen masu xafi suka sauko idonta tunawa da maganganun da Abuturrab yayi mata daxu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login