Showing 195001 words to 198000 words out of 346625 words
Chapter 66 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
kyar. Bayan ya shirya ko sallama bai mata ba ya fice daga gidan cikin motarsa, yana driving ya kara dialing number Ahmad, bayan Ahmad ya daga yace "Ahmad i still have more questions" Ahmad yace "Alright go on" Abuturrab yace "Kace not everyone ke shedding blood due to reasons u listed.... haka ko?" Ahmad yace "Yes" Abuturrab yace "But how about if u just find ur self in without any stress, me hakan ke nufi, or ana samun irin wannan cases din gun warce bata ta6a sex ba?" Ahmad yace "Noo!! if u should go in freely, to ko ma wacece ta ta6a sex wllh, continuously ma kuwa, and probably for long take abunta shi sa ma kayi noticing hakan lkci daya...." Abuturrab dai yayi shiru yana sauraronsa, Ahmad yace "And let me tell u something, in dai mace ta sa6a sex before marriage to memory din wanda ta sa6a da shi din will remain in her brain, da kyar ta iya rabuwa da shi duk da fa ga mijinta, yawancinsu basa iya tsayawa a matrimonial home dinsu without following men outside, it's just like a curse, ko da sun dau vow din repenting to ina gaya maka na yan shekaru ne... xa su koma idan ba Allah ne ya so su da Rahama ba" Shi dai Abuturrab bai ce komai ba, Ahmad yace "Are u okay now?" Abuturrab yace "Sure nagode, i am on my way to kano, thank you... Sai anjima" Ahmad yace "Alright safe trip" Katse wayar yayi ya ci gaba da tukinsa. Tun da Aneesah taji fitar motarsa a gidan ta hau kiran Aunty, Aunty na dagawa ta fashe da kuka tace "Aunty na shiga uku..." Aunty dake kwance kan gadonta ta mike xaune da sauri tace "Me ya faru?" Cikin kuka tace "Wllh kawai daren jiya Aliyu ya far min, duk yanda nayi kokarin stopping dinsa hakan bai yiwu ba har sae da yayi" Aunty ta bude baki tace "Yayi?? To sai aka yi yaya ynxu?" Tana kuka tace "Tun jiyan ya ki kulani bai ma kwana dakin ba, sae yau da safe ya xo daukan kaya yake ce min i betrayed his trust, kinga wllh ynxu ma haka ya tafi kano ko sallama bai min ba" Aunty ta saki salati tace "To garin yaya hakan ya faru, garin yaya kika yarda kinsan halin da kike ciki Aneesah?" Kuka kawai take tace "Wllh he forced him self in me Aunty, nayi kokarin preventing hakan amma ni ba karfinmu daya ba" Aunty tace "Tabdi, to ni yanxu me xance??" Aneesah ta dinga goge idonta ko da wasa bata ce ma Aunty turaren da ta bata ne ya fashe ba, Aunty tace "Toh abinda xai faru duk inda xaki nemo kudi ki nemo a samu a rufe bakinsa kawai" Aneesah tace "Sai in dau zinarina in siyar, I can't imagine Aliyu yace xai rabu dani sabida haka, wllh ina sonsa sosai Aunty" Aunty tace "Ya rabu da ke?? Ji wani mugun alkaba'i, ke fata kike ya rabu dake ma kenan? Akan wannan d'an abun xai rabu dake kamar warce ta kashe mutum? Mata nawa ne aka aurar bbu budurcinsu kuma suna xaune qlau da mazajensu? Rabu da d'an iska xai ma sakko ne, ke dai kawai ki siyar da zinarin ki turo min kudin a tura benue" Aneesah tace "Toh Aunty, ynxu xan fita kasuwa in siyar sae in tura maki kudin" Aunty tace "To yi maxa, kar ki wani damu abunki, ubansa ma yayi hakuri da hakan balle shi gantalalle, shaff mancewa xai yi idan na sa ayi aikin..." Aneesah tace "Toh nagode Aunty, bari inje, xan kiraki" Aunty tace "To yi maxa" daga haka ta katse wayar, ko wanka Aneesah bata yi ba tun daren jiyan balle aje ga sallah, ta saka doguwar rigar atamfa ta xumbula hijab dinta sannan ta saka zinarin a jaka ta fita daga gidan. A ranan Ahmad ya kai Jiddah makaranta kamar yanda ya ce da Umma, Tunda yyi duk registration din da komai ya tafi ya barta kawai ta fara karatu Monday din... Da yamma karfe hudu da kansa yaje daukota daga school din, amma sanin halin Ummarsa sae ya wuce da ita can gida kawai, Umma tayi farin cikin fara makarantar Jiddah sosai, ita dai Jiddah na xaune kasa kan carpet tana murmushi, Umma tace "Toh tashi kiyi sallah ki ci abinci" mikewa tayi ta wuce dakinsu, Ahmad ya kalli Umma yace "Kince daga nan xata dinga tafiya ko Umma?" Umma tace "Eh xata dinga xuwa daga nan" Yyi murmushi yace "Ga dai sauki amma ke baki so Umma" Umma tace "Saukin me?" Yace "Kashe transport" Umma tace "Kai yanxu ka bada shawarar a bar kamarta da Ramlah a gida kai kana can gun aiki, to wa xai dinga gaya masu gaskiya ko ya sa su kan hanya, shiririta kenan kawai" Yace "Kema dai kinsan Ramlah bata da shiririta Umma, sannan Jiddah ma na da hankali da nutsuwa sosai, kinga from monday to Friday idan taje schl sae ta xo nan Friday din da yamma ta maki weekend, ina ga xae fi wllh" Umma tace "Shkkn kuma babu me sa mata ido kan karatun?" Yace "A nan ma kinsan bbu me sa mata ido amma take yin karatunta wholeheartedly" Umma ta ta6e baki tace "Toh ae shkkn, sae ta tafi can din, amma friday ta dawo nan tayi weekend" Yace "In sha Allah Umma" Sae kusan biyar da rabi suka bar gidan suka koma gidan Ahmad, a hanya yake bata hakuri kan gidan Iya da bai kai ta ba tunda ta koma schl, Jiddah tayi murmushi kawai tace "Toh Allah ya kai mu wani lkcn" Ranan friday Abuturrab na shigowa garin kaduna gidan Umma ya nufa direct, yana parking a kofar gida ya shiga cikin gidan, Umma ce xaune parlor suna hira da Huraira, yayi sallama ya shiga parlorn, sanye yake da fararen shadda da suka amshesa sosai, sae da Huraira ta gaishesa sannan ta bar parlon, Ya xauna saman kujera yana kallon Umma yace "Ina yini" Umma na kallonsa tace "Lafiya lau, daga ina haka?" Yace "Daga gida" Tace "Madallah, ya kwana biyu?" Yace "Alhmdlh..." Sallama aka yi bakin kofar Umma ta daga kai tare da amsa sallaman, ta shigo parlon sanye da hijab dinta gogagge har kasa da jakarta a hannu, ta gefen ido yake kallonta har ta karaso cikin parlon ta nufi Umma ta durkusa nan kasa kusa da ita a hankali tace "Umma ina yini" Umma tayi murmushi tace "Lafiya lau Jiddah ya karatun?" Ta sunkuyar da kanta tace "Alhmdlh Umma" Abuturrab dai kallonta kawai yake, Umma tace "Ya su Ramlar" Jiddah na wasa da fingers dinta tace "Tana gaisheku..." Umma tace "Ahmad din ya shigo ne?" Jiddah ta girgixa mata kai tace "Aa" tunda ta lura da cewar Abuturrab ne xaune parlon duk da ba wai kallonsa tayi ba taki yarda ta dago kanta gaba daya, Umma tace "Toh yayi kyau, kije ki xuba abinci ki ci" Tace "Umma na ci abinci" Umma tace "Ohk to kice ma Huraira ta kawo ma Aliyu ruwa" Mikewa Jiddah tayi still bata yarda ta kalli direction din da yake ba ta wuce kitchen din, satan kallonta yake har ta shiga kitchen din, sai kuma ya kalli Umma yaga wani kallo da take masa...
*Sorry for the late night update*
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
FZ BEAUTY SUPPLEMENTS
Dealer in all kind of dietary supplements such for skin whitening, skin glowing, weight gain, slimming, flat tummy, infection killers, dark spots removers, fertility booster, Hips boosters, Breast firming and Enlarging, Teeth whitening, eye, joint, stretch marks, and for marital pleasure. All supplement are available for wholesale and retail. For more information contact FZ via wa.me/2348143821028
Abuturrab ya dauke kansa, Umma tace "A hado maka da abinci ne?" Girgixa kai yayi yace "Aa" Jiddah na ba Huraira sakon Umma ta fito ta wuce dakinsu, Huraira ta fito da ruwan ta ajiye ma Abuturrab, knocking aka yi bakin kofa Huraira ta karasa bakin kofar ganin driver ne ta kalli Umma tace "Umma Musan ya dawo" Umma tace "Ohk to ya jirani" Huraira ta koma ta gaya ma drivern abinda Umma tace, Abuturrab ya dau bottle water ya bude yana kallon Umma yace "Umma fita xa ki yi?" Umma tace "Ehh yanxu kuwa" Tana fadin haka ta mike ta wuce dakinta ta dau hijab da purse dinta, tana fitowa parlon shi dai bin ta kawai yake da kallo, ta xauna saman kujera ta kira Huraira, Huraira na xuwa tace "Kira min Jiddah" kallonta kawai Abuturrab yake, Huraira ta wuce daki sai ga ta sun fito tare da Jiddah, Umma tace "Dauko Hijab dinki ki rakani" Jiddah tace "Toh" sannan ta juya, Abuturrab dai sai kallon small mum din tasa yake, banda danna wayarta babu abinda take, Can ya shafa kansa a hankali yace "Umma ina xa ku?" Tace "Kwana biyu banje na gaida Yaya ba, can xanje yanxu" Yace "Nima can, xan tafi na dai fara xuwa nan in gaisheki ne" Umma tace "Allah sarki, ai ka kyauta" Yace "Toh in ajiye ku can din?" Umma tace "Idan ka ajiye mu wa xai maido mu, gwara mu tafi da driver ko awa nawa xanyi xai jira in gama sannan ya maido mu gida" Abuturrab yace "Ae xan kai har bayan isha a can, duk sanda xa ku dawo sai in dawo da ku sannan in wuce gidana" Umma tace "Toh ai shkkn idan ba takura" Umma ta mike ta wuce kitchen don juye pepper soup din da tayi ma Ummi, Jiddah ta fito daki sanye da hijab din da ta xo da shi, hada ido suka yi da shi, ta juya da sauri ta wuce kitchen, babu 6ata lkci Umma ta fito kitchen Jiddah na biye da ita rike da warmer din pepper soup, Abuturrab ya mike yace "Ina jira a mota Umma" Umma tace "Eh yanxu xa mu fito" Umma ta gama ba Huraira instructions din da xata bata sannan suka fito parlon da Jiddah, driver dake tsaye parking space Umma ta nufa tace "Musa kawai kayi tafiyarka na samu ma wanda xai ajiye ni can gidan" cike da ladabi Musa yace "Toh shkkn Hajiya, Allah ya tsare" Umma tace "Ameen, sai gobe kenan" Daga haka ta nufi gate Jiddah na biye da ita a baya being very careful kar ta 6ata hijab dinta da abinda ke cikin warmer din hannunta, back seat Umma ta bude ta shiga, Jiddah ta shiga bayan ita ma ta kulle motar, Umma na kallonsa tace "Idan ka samu wajen siyar da fruits a hanya" Yace "Ohk" daga haka ya tada motar ya bar layin. Dai dai wajen masu siyar da fruits yayi parking kamar yanda Umma ta umarcesa, Umma ta ciro kudi ta mika masa tace "Apples kawai sai grapes" Ya kalli kudin ya sauka motar yace "Akwai kudi a jikina" daga haka ya kulle motar ya tafi gun masu fruits din, bayan some minutes ya dawo, ya bude back seat yana mika ma Umma ledan amma Jiddah yake kallo, Umma ta kallesa tace "To ita kake ba ledan ko ni Aliyu? idan ita ce sai ka xaga ta can mana" Tana fadin haka ta amshe ledan xata rufo door din motar, shi dai bai ce komai ba ya koma driver seat, Jiddah dai na makale at the far end of d car don bata ma son su hada ido mistakenly ta madubi. A kofar gidansu yayi parking, Umma ta sauka, Jiddah ma ta sauka rike da warmer din ta bi bayan Umma da sauri, Direct bangaren Ummi suka tafi, Jiddah dai na xaune kasa bayan sun gaisa da Ummi da ta fito daga daki, Ummi tace "Toh ki xauna kujera mana Jiddah" Murmushi kawai Jiddah tayi bata ce komai ba, Umma tace "Ko a gida ma kafin ta xauna a kujera sau daya tayi xamanta a carpet ya fi a kirga" Ummi tace "Ikon Allah, to ina su Maimoon?" Umma tace "Suna dawowa boko suka tafi gidan Hajiya Zainab" Ummi tace "Haba, tana garin nan dama?" Umma tace "Aa last week ta shigo" Ummi tace "Allah sarki" Umma tace "Jiddah kuma ai nace maki tana gidan Ramlah ta fara karatu ko?" Ummi tace "Ehh haka kika ce, Allah ya bada ilimi me albarka da amfani" Umma tace "Ameen, Hajiya Hajja fa? Kwana biyu ba a je min ba" Ummi tayi murmushi tace "Shekaranjiya ta tada rigiman a kai ta gombe wajen mai martaba, amma yau kuma wai sai naji suna hanya kilan ma sun kusa, mun yi magana da El-Basheer din da safe" Umma ta tabe baki tace "Toh Allah ya kyauta, meye amfanin tafiya me nisan da ko kwana uku baxa ayi ba" Dariya kawai Ummi tayi, aka bude kofar Abuturrab ya shigo da sallama, xaunawa yayi ya gaida Umminsa, Ummi ta amsa tana kallonsa, Umma tace "Shi ya kawo mu, yaje can gida gaisheni shine yace bari ya ajiye mu tunda nan xa mu xo" Ummi tace "Maa sha Allah, Ina matar taka??" Yace "Tana gida" Ummi tace "Toh yayi kyau, shekaranjiya ma ai ina jin ta xo nan wajen Hafsah, amma ni dai ban ganta ba su Nafisah ke gaya min" Abuturrab dai yyi shiru bai ce komai ba, Umma dai ta ta6e baki tana kallon Tv, Ya kalli Ummi yace "Ummi akwai abinci?" Umma ta wani kallesa tace "Amma da nayi maka magana a can gidan me ka ce min?" Murmushi kawai yayi, Ummi ta kalli Jiddah tace "Akwai abinci kitchen ki dibar masa Jiddah" Sosai gaban Jiddah ya fadi ta kalli Ummi, Umma dai bata ce komai ba, Jiddah ta mike a hankali ta nufi kofa, Abuturrab na kallon Umminsa yace "Aunty na nan?" Ummi tace "Sai kaje ka duba" Bai ce komai ba, sai kuma ya mike yace "Bari in gaisheta in dawo yanxu" Daga haka ya nufi kofa daga Ummi har Umma suka bi sa da kallo, Umma tace "Mu je ciki akwai magana yaya" Ummi ta mike tace "Toh" a tare suka shiga bedroom din Ummi... Abuturrab na fitowa bangaren Ummi kitchen ya nufa direct, Jiddah ta juya da sauri jin an shigo kitchen din, suna hada ido ta juya masa baya, kana ganinta kasan duk a tsorace take ta ma rasa me take yi, sai kuma ta tuna miyan ganyen xata xuba a bowl, tana cikin xubawa taji muryarsa yace "Saboda nace ki daina gaisheni shi yasa idan kika gan ni sai ki min kallon banxa ki wuce right?" Kasa ce masa komai tayi amma banda bugawa babu abinda xuciyarta yake gashi taki juyowa, bude kitchen din aka yi ta juya da sauri, Mai aikin gidan ce ta shigo ganin Abuturrab ta koma xata fita, da sauri Jiddah ta ajiye bowl din miyar hannunta ta fice ta kofar da tagani a kitchen din wanda ke a bude, da mamaki ya bi ta da kallo, har ta xagayo gaban compound din gidan waige waige take ko ya biyota amma bata ga haka ba, mai gadi ya bude gate sai ga mota ya shigo, ko parking din motar ba a yi ba, motar na tsaye tsakar compound din aka bude back seat sae ga Hajja ta sauko da katon jakarta, Jiddah ta karasa gunta don amsan jakarta, Hajja sae kallonta take can tace "Wannan kafafuwa naki haka kamar a Masar, kinsan su ma haka kafafuwansu yake farare tass da yake larabawa ne, to ke kuma ba balarabiya ba sae dai ko sadaka yalla" Jiddah dai tayi murmushi ta amshi jakar Hajja tace "Sannu da dawowa Hajja" Hajja tace "Yauwa wajen d'ana sarkin Bauchi naje, ai da ke nayi niyyar xuwa Usman ya hanani wai inyi ta kaina, banda haka da na kai ki kinga ikon Allah, to ina takalman naki kike yawo haka ke kuwa? Ita mace ae ba a santa da yawo babu takalmi ba, barin ke da taki kafar kamar ta 'yan Masar" El-Basheer ya sauko daga mota yana kallon Jiddah, Jiddah ta d'an kallesa tace "Ina yini?" Yayi murmushi yace "Lafiya lau Jiddah, how are you doing?" Tace "Alhmdlh" Hajja tace "To ki tsaya ku gaisa a tsanake idan kun gama sai ki taho min da jakata kin ji" Daga haka tayi wucewarta, Jiddah ta d'an kallesa, Murmushi yayi yace "Ya karatu?" Tace "Lafiya lau" yana kallon kafafuwanta yace "Ina takalmanki" Tace "Aa ta kofar kitchen na fito ne" Yace "To muje ciki" Tana gaba yana biye da ita suka wuce parlor din gidan, Abuturrab na xaune parlor Hajja na tsaye sai basa labari take, shi kam ko kallonta baya yi banda danna wayarsa da yake, Jiddah ta shigo parlon tare da El-Basheer, Hajja ta kallesu tace "Har kun gama gaisawa?" Jiddah dai bata ce komai ba tayi hanyar dakin Hajja da jakarta bayan ta saci kallon Abuturrab, Hajja ta bi bayanta murya can kasa tana cewa "Ki daina abu kamar er kauye 'yar nan, kamata yyi ki buda baki kuyi tadi da shi sosai, ba wai ki ta sunkuyar da kai kina murmushi ba, ubansa fa shine sarkin Bauchi gaba daya, kuma ni na haifi uban, na ya6a da hankalinki ne shi sa nake ta cusa masa ke, amma naga ke kuma kina abu kamar wawa, haba kar kyanki ya tashi a banxa mana er nan" El-Basheer na kallon Abuturrab da ya ki dago kai yace "Na kira ka daxu wayarka a kashe" Abuturrab ya kallesa yace "Ohk kilan na kashe then, ya hanya" El-Basheer yace "Wannan mata ta fiye fitina wllh, i have to drive her all the way from kano, and in sha Allah gobe xan koma Bauchi" Abuturrab ya mike yace "Toh muje can gidana, tafiya xan yi nima" El-Basheer ya d'an buda ido yace "Ae ban gaisa da su Ummi da Aunty ba" Abuturrab yace "Duk basa nan, if u are going mu tafi yanxu don ni tafiya xanyi, gobe idan xaka koma Bauchin sai kaxo kayi masu sallama da safe" El-Basheer ya d'an shafa kansa yace "Ohk, i can even still come back at night in gaisa da su" Abuturrab yace