Showing 171001 words to 174000 words out of 346625 words
Chapter 58 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
ya karasa cikin parlon yana kallonsu Fauziyya with smile on his face yace "Kun yini lafiya" Fauziyya tace "Lafiya lau ango, jiya kuma sai muka ji ku shiru shiru kai da abokanka..." Abuturrab yace "Ohh yeah, toh kun ki bar min mata ku tafi, and all my frnds that are suppose to escort me sun koma saboda aiki, shi yasa nace to bari dai nasan xuwa yau xa ku tafi ku bar min amaryata, na daga kafa jiya, amma ashe i am mistaken kuna nan dai" Dariya duk suka yi banda Aneesah da ta kauda kanta imagining how to punish him, Fauziyya tace "Da ka kwantar da hankalinka ma yanxu shiryawa muke xa mu wuce in sha Allahu" Yyi murmushi yace "Toh ba sai na haura sama ba kenan bari in jira ku a mota, sai in ajiye ku train station...." Naja tace "Mun ko gode Captain" Ya d'an saci kallon Aneesah suka hada ido ya kashe mata one eye, ta wani sha kunu, ya juya ya fita parlon, har bakin motarsa ta raka kawayen nata da jakunkunan kayansu, a kan kafada ta yafa gyalen yyi mata kallo daya ya kauda kai duk kawayenta suka shiga motar suka sallami juna sannan ya kalleta sai na dawo, bata tanka sa ba ta shige gate din gidan, ya ja motarsa ya wuce. Aneesah na komawa ciki ta haura sama ta shiga parlonsa ta dau wayarta ta kira Aunty, aunty na dagawa tace "Ya dawo?" Tace "Ehh yanxu ya shigo, amma ya tafi kai su Fauziyya tashan jirgin kasa" Aunty tace "Toh kar ki wani nuna masa komai, kiyi kamar abinda yayi jiya bai baki haushi ba kinji, kiyi hakuri... Sannan ki kula duk yanda Safara'u ta ce maki haka xaki yi anjima kada ki yarda mistake ya shiga..." Aneesah tayi kasa da murya tace "Amma Aunty he is so smart kin sani" Aunty tace "Smart din banxa, ke dai kiyi abinda aka ce maki kawai" tace "Toh shkkn" Aunty tace "Yanxu dai kawai muyi waya gobe" Aneesah tace "Allah ya kai mu" Daga haka ta katse wayar, shiru tayi tana naxari iri iri a ranta, can tayi murmushi ta mike ta shiga daki. Abuturrab na ajiye su a train station din rigasa ya ciro dubu ashirin din da yayi withdraw kafin ya je gida ya mika masu, nan kuma yayi masu sallama yayi wucewarsa ba tare da ya damu yasan ko akwai jirgin ko babu ba, a ransa yace idan ma babu sai su wuce park, a hankali yake driving ya shiga d'an layin wanda ke shimfide da kwalta, dai dai layin gidan mai anguwa ya samu waje yayi parking sannan ya sauka ya karasa layin da kafarsa, saman tabarman dake kofar gidan ya xauna bayan ya gaisa da dattijan da suka wayesa a wajen, yana jiran mai anguwan da aka ce masa ya shiga gida ya fito yanxu, wani dattijo yace "Ya iyalin naka?" Abuturrab yace "Lafiya lau Alhmdlh" Dattijon yace "Madallah, Allah ya maka albarka" Abuturrab ya sunkui da kansa yace "Ameen" ba a dau lkci ba mai anguwan ya fito, ganin Abuturrab yace "Ikon Allah, sannu da xuwa Malam Ali" Abuturrab ya gaishesa da ladabi bayan ya xauna, mai anguwa yace "Ya kaje gida ranan? Nayi ta kiran layinka baya shiga kuwa" Abuturrab yace "Allah sarki, Ina jin na kashe wayar ne" Mai anguwa yace "Toh madallah, ya aiki fa...." Abuturrab yace "Aiki Alhmdlh, Dama na xo tasha ne shine nace bari in karaso mu gaisa" Mai anguwa yace "Ai ko mun gode Malam Ali, ya iyalin taka dai?" Yace "Lafiya lau" Mai anguwa yace "Toh Allah ya kauda fitina, ya ci gaba sa baku xaman lafiya" Abuturrab ya amsa da "Ameen" sannan ya ciro kudi aljihunsa ya ajiye nan gabansa yace "Toh xan koma in sha Allah, sai kuma wani lkcn" Mai anguwa ya rike ha6a yace "Baka gajiya Malam Ali??"
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
*EXCLUSIVE FABRICS &MORE* provides you with exclusive, and Affordable fabrics such as laces, Ankara,materials shoes,bags and so much more on wholesale and retail EXQUISITE, AND AFFORDABLE
THANK U ❤️🤩
LOCATION: LAGOS
*EXCLUSIVE_FABRICS_AND_MORE* Na siyar da kaya kamar Laces, Atampopi, Materials, Jewelleries,👡👠👜👛da dai sauran su
Tana maraba da masu siyan daya koh sari
Location : Lagos
Tana aika kaya duk inda kake da yardan Allah 🤝🤝❤️🥰
09080058848
Abuturrab yyi parking kofar gidansu ya kashe motarsa ya sauka, suka gaisa da Mai gadi sannan ya shiga cikin gidan, bbu kowa parlon duk yan biki sun watse, ya wuce dakin Hajja ya bude kofar ganin Mahaifiyar El-Basheer xaune dakin ya sa shi yin sallama, Hajja dai kallo daya tayi masa ta ci gaba da xancenta tana cewa "Wllh baki ganta ba, babu sa wa babu hanawa, don dai kawai ni ina komai cikin sirri ne banda haka da har sunan yarinyar sai in fada maki ynxu, kuma ni ba abinda yasa na kara samun kwarin gwiwa sai ganin yanda Bashir din yayi na'am da xancen nawa, wllh ko musu d'an arxikin bai yi ba, da dai su o'o ne har ubana dake rami sai ya xaga, shi sa kika ga nayi ta ja baya da bikin nan ba ruwana aje a kunyata ma yarana ni a banxa, ai xamana Masar ya koya min iya xaman duniya, nasan yanda xan xauna da ko wani gantallale lafiya babu me jin kanmu" Murmushi kawai Hajiya Safinah mahaifiyar El-Basheer ke yi, Abuturrab ya karaso ya xauna kasa yace "Ina yini Mummy?" Da fara'arta tace "Lafiya lau Captain, yanxu muka dawo daga can gidan naka ai tare da Hajiya Hafsah, amaryar taka tace mana kaje kai kawayenta tasha ko?" Yace "Ehh" tace "Toh maa sha Allah, Allah ya bada xaman lafiya, ya kauda fitina tsakaninku" Yayi kasa da kai yace "Ameen" Sai a sannan ya kalli Hajja yace "Ina yini" Da sauri tace "Aa, ka dai gane ma idonka, lafiya lau na wuni wllh" Ya mata wani kallo ta gefen ido, Hajja tace "Kina ji na Safinah" Mummy tace "Ina ji Hajja" Tace "Kar ki dau maganata da wasa, tunda dai gobe xa ki koma kina isa gida, ko da mijinki na xaune fada ki yi sallama ki shiga kiyi masa duk bayanin nan da na maki, kinga ai tunda aka samu wannan mutumi yyi aure shi ma Bashir ya kamata yayi auren" Mummy tace "Haka ne Hajja" Hajja tace "Atoh, da a Masar ne ma wace shegiya xata kallesu duk sun tsofe a gida, mu fa a Masar sai ki ga d'an yaro shekara ashirin da biyu yayi aurensa gwanin ban sha'awa wllh" Mummy na gyada kai tace "Ikon Allah" Hajja tace "To ba ruwana wllh, idan xa ki dau maganata da muhimmanci ki dauka, ni anjima ma sai in sa a kira min waya in sa cikin dubara a turo yarinyar kamar dai xata kawo min sako sai ki ganta" Mummy tayi dariya tace "To ae Shikenan Hajja bari in je can bangaren Hajiya Hauwa" Hajja tace "Toh shkkn, xuwa nan da magariba xa ki ga an turo min yarinyar in sha Allah" Mummy dai na murmushi ta mike ta fita, Hajja ta kalli Abuturrab dake danna wayarsa tace "Har yanxu kuna can gwamutse da kawayen amaryar?" Yace "Toh ina ruwanki?" Yana fadin haka ya mike ya nufi kofa tace "Ji shashasha, to ni ina ruwana in ma shekara xa su yi a gidanka? Ba dai mun maka me wuyar mun aurar da kai sauran Bashir ba, sae kaje can ka karata da mummunar matarka sae haske kamar jinjirar xabiya, ni sai na ga wani kallon tara saura quarter ma take ma mutane kamar" Tuni Abuturrab ya fice daga dakin ya kulle mata kofa, wayarta ta dauka ta mike tace "Bari in je a kira min Ramlah, kawai ce mata xanyi ta xuba abinci ta ba yarinyar ta hadata da direba a kawo min kuma daga nan ina son ta wanke min bandaki, don duk ta fi sauran yan matan iyawa, kinga babu wanda xai xargi komai, daga nan tana xuwa sai in nuna ma Safinah" Tsaye Abuturrab yayi bakin kofa yana kallon Aunty, tace "Idan baxa ka karaso ciki ka kulle min kofa ba gwara ka fita don Allah Aliyu, bana son walakanci" Bai ce komai ba ya kulle kofar sannan ya karasa cikin dakin, tace "Yanxu kai abinda kayi jiya a tunaninka ya dace kenan Aliyu?" Yace "Aunty ni fa banyi komai ba, i instructed her to tell her frnds to come out so i can drop them home amma taki, ni kuma bana son tashin hankali kawai na bar masu gidan gaba daya na tafi hotel na kwana, a ina aka ta6a cewa sai kawayen amarya sun kwana gidan amarya ranan da aka kai ta?" Aunty ta jefa masa wani kallo tace "Ance din, ina ruwan ka da kawayenta dake daki daban ku kuna daki daban, yan matan da suka taso tun daga Abuja suka xo sun cancanci wannan walakancin a wajenka Aliyu? Tun da yan matan nan suka xo garin nan Hajja ke hantarar su, dalilin ma da yasa nace su kwana can din kenan, duka duka dai ai ba can xa su dauwama a gidan naka ba banda rashin hakuri irin naka, kuma banda ma kana son a tafi da matarka a baki meye na barin gidan?? wani ango ne ka ta6a jin yayi hakan" Abuturrab dai bai kuma ce mata komai ba, Aunty tace "Toh a gaskiya ka shiga hankalinka, kada in sake jin makamancin hakan, Aneesah dai ba abar rainawarka bace kasan daga irin gidan da ta fito kasan wacece ita, yar asali ce me dangi gabas da yamma kudu da arewa, kar kaga ka ta6a aure a gantale kun rabu a gantale, to ita wannan ba gantallaliya bace da danginta, yar usuli ce" Kallonta kawai Abuturrab yake babu ko kiftawa, Ta mike tana gyara daurin dankwalinta tace "Yanxu idan kaje sai kasan yanda xaka bata hakuri ta hakura, ni ma kuma dama na bata hakurin" Sauke hannunta tayi a fusace tana kallonsa tace "Wai ya haka ina magana ka kafe ni da ido kayi shiru kamar baka jin abinda nake cewa, are you okay??" Sauke idonsa yayi yace "Na ji ki" Daga haka ya juya ya fita daga dakin ta bi sa da wani irin kallo. Umma ta ajiye wayar hannunta tana kallon Aunty Nafisah da mamaki tace "Wai ki ji Hajja in ba Jiddah abinci tare da driver ta kai mata...." Aunty Nafisah tace "Ikon Allah, ba dai gidan xan tafi ba yanxu sai in tafi mata da shi kawai" Umma tace "Kin ji yanda ta dage kuwa, na ma ce mata karatu jiddan take Maimoon su taho da drivern, amma wai Jiddar ta taho da takardun kawai" Aunty Nafisah tace "Ki bar Hajja kawai ana magariba xan tafi tare da abincin in kai mata" Umma tace "To amma ki kirata ki sanar mata dai tukun kar tace an mata ba dai dai ba, ko ya kika ga" Aunty Nafisah ta dau wayarta ta shiga kiran Hajja, Hajja na dagawa tace "Hajjaju yanxu xan bar gidan Hajiya Ramlah sai in taho maki da abincin...." Hajja ta katseta a fusace tace "Oh oh naga bala'i, ni dai na shiga uku, ita katuwar ce ta tsara maki haka Nafisah? Yanxu ke fisabilillahi tare dake muka xauna a Masar, ke kinga suna haka? Me yasa xaki taho kasar mutane ki ari halin da ba taki ba ki dinga yin abun da ba ayi a Masar? Ga dai abinda nace ina so sai ayi ta min hanya hanya? Ita Ramlan don bata san ciwona ba har da cewa xata ba direba shi kadai ya kawo min abincin da xan ci, me na hada da direban xa a basa abinda xan xuba a ciki ya kawo min, dama mutum na yarda ya ci gaibu? Toh shkkn babu damuwa, ni baxan sake ce maku komai ba" Daga haka ta katse wayarta, Umma dai sai murmushi take, Aunty Nafisah tace "Toh Allah ya kyauta, baxan ma koma gidan ba yau sai gobe, a ba Jiddar ta kai mata" Umma tace "To ai nace ki bari goben kika ki, ai shkkn bari in ba Jiddan ta kai, amma tana mika mata driver ya juyo da ita don tana da karatu gobe" Hijab har kasa Jiddah ta saka, tana rike da warmer din tuwo da miya da xata kai ma Hajja, gaba daya mood dinta ya canxa jin aiken da Umma tayi mata, babban damuwarta kar ta je ta hadu da Aunty, a sanyaye ta shiga bayan motar ta xauna har suka isa gidan bata da walwala, driver yayi parking kofar gida, ta sauka a hankali hannunta rike da warmer din ta shiga compound din gidan, a hankali ta bude kofar parlon tana leka ciki, ido hudu tayi da Abuturrab dake gidan har sannan suna xaune parlon da El-Basheer da ya takarkare yana masa labarin ball, ta karaso cikin parlon, El-Basheer ya juya yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi da ladabi tace "Ina yini" murmushi ya sakar mata yace "Lafiya lau Jiddah, how are you doing?" Tace "Alhmdlh" yace "Daga ina kike haka?" Tace "Gida" Yace "That's cool..." Bata ko kalli Abuturrab da ya bi ta da kallon gefen ido ba tayi hanyar dakin Hajja, shi ma El-Basheer din da kallo ya bi ta, da sallama ta bude kofar dakin Hajja, Hajja ta amsa ta washe baki ganinta tana cewa "Sannu da xuwa Jiddah" Aisha dake xaune dakin ta bi Jiddah da wani kallo, Jiddah ta tsugunna ta ajiye warmer din hannunta tana kallon Hajja tace "Ina yini Hajja?" Hajja tace "Lafiya lau, shinkafa ta baki ki kawo ko me?" Jiddah ta girgixa kai tace "Aa tuwo ne" Hajja tace "Atoh da kyau, dama shi nake marmari" Mikewa Aisha tayi ta fita daga dakin, Hajja tace "Dama ba wani amfani take min ba, yar kazar da Bashir ya kawo min take ma ni kuma na boye kayana karkashin gado, tunda ba uwarta bace ta siyo min, shi wan nata Salem tun saukana daga Masar har yau ban gansa ba ance yana Benue, to ni ina ruwana kuma" Ita dai Jiddah bata ce komai ba, Hajja tace "Yanxun nan Bashir din ya fita ai da kun gaisa wllh" Jiddah tace "Ai mun gaisa" Hajja tace "Haba" Gyada mata kai Jiddah tayi, Hajja tace "A ina kika gansa?" jiddah tace "A parlor" Hajja tayi kasa da murya tace "Shi da wa?" Jiddah tace "Ya Aliyu" Hajja ta wani kyabe baki tace "Ashe bai tafi ba kenan, in gaya maki ni dai babu xagin da bai min ba daxu, amma ban biyesa ba don ba shine gabana ba wllh, ni tunda naje Masar na koyi xama da ko wani fitsararre, iyakar hakuri da kauda kai na koyo kam ba laifi a Masar" Jiddah ta d'an yi murmushi kawai, Hajja tace "Toh ba ruwana dai da wannan, yanxu ki tashi ki tafi bangaren warcan matar da ku ke ce ma Ummi, kiyi sallama sai ki durkusa ki gaishesu da ladabi gaba daya sannan kice don Allah Maman Bauchi kike nema, Idan aka nuna maki ita aka ce gata sai kice mata dama Hajja ce tace in kira ki, Shkkn sai ki taso abun ki ki fito kinji?" Jiddah tace "Toh" Hajja tace "Toh tashi kije" Mikewa tayi ta fita dakin, suka hada ido da Abuturrab a parlor ta dauke kanta tayi hanyar bangaren Ummi, El-Basheer ya shafa kansa yace "Kasan mene Captain" Abuturrab ya kallesa yace "Idan magana ce da ya shafi koma waye na cikin gidan nan I'm not interested Yarima" El-Basheer yace "A kan Jiddah ne maganar" Mikewa Abuturrab yayi ya wuce dinning area, El-Basheer ya bi sa da kallo yana murmushi... Duk yanda Hajja tace haka Jiddah tayi, Ummi na murmushi ta nuna Mummy tace "Gata nan" Jiddah ta kalleta sannan ta sunkuyar da kanta, Mummy tace "Ki ce mata gani nan xuwa" Jiddah tace "Toh" sannan ta mike ta fita parlon, muryar Aunty ta ji a main parlor tana cewa "Har gashi xa ayi isha baka tafi ba ka bar yar mutane ita daya a gida Aliyu, Wai me yasa bakwa gaya masa gaskiya Bashir" El-Basheer yace "No nayi masa magana Aunty, har ce masa nayi ya tashi in rakasa yace aa yana jiran wani abu ne, ina ta xuba ido in ga me yake jira" Abuturrab na kallon Aunty daga dinning area da yake xaune yace "Yanxu xan wuce, dama gidan akwai wasu coursemates dinta ne amma nasan may be sun tafi yanxu, i will be on my way" Jiddah dai tayi sum sum ta shige dakin Hajja kafin Aunty ta ganta gabanta na faduwa. Tana shiga dakin Hajja ba a dau lkci ba sai ga Mummy ta shigo ta nemi waje ta xauna tana kallon Hajja tace "Ga ni" Hajja na Murmushi tace "Toh xancen da muka yi daxu dake dai da yamma... kin tuna?" Mummy ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Na tuna" Hajja tayi dariya tace "Toh shine, ai dama na maki alkawari xaki santa yau din nan" Mummy dai sai d'an Murmushi take tana kallon Jiddah dake xaune kasan carpet kasa kasa, Jiddah tace "Hajja ana jirana a waje" Hajja tace "Direba ko?" jiddah tace "Ehh" Hajja tace "To yi maxa tashi kije, kice da Ramlah na gode, Allah ya tashe mu lafiya" Jiddah ta mike tace "Ameen" Sallama tayi ma Mummy sannan ta fita dakin, Hajja tace "Toh ita ce dae Jiddar" Mummy tace "Maa sha Allah" Hajja tace "Aa ba haka xaki ce ba" Mummy tace "To ya xan ce" Hajja ta marairaice tace "Yau naga jaraba, sai kice ehh ai kuwa tayi Allah ya tabbatar da alkhairi Hajja, haka ake magana me ma'ana" Mummy tace "Gaskiya ne tayi kam, Allah ya tabbatar da alkhairi" Hajja tayi Murmushi tace "Yauwa ko ke fa, in sha Allahu satin da xa a shiga xan xo bauchi gun kabiru" Mummy tace "Toh Allah ya kai mu, bari in je Hajja" Daga haka ta mike ta fita dakin, Hajja ta ta6e baki tace "Oho dai, kya