Showing 216001 words to 219000 words out of 346625 words
Chapter 73 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
ganta xaune parlor tana kallon tv, da alamar film din ya tafi da ita shi yasa ma bata fito ba da ta ji sa shiru shiru bai shigo ba, stairs ya nufa da sauri, ta juyo tace "Captain ka ga agogo kuwa kaje ka dade haka?? kuma me kake yi cikin mota tun daxu baka shigo ba?" Ya ki tsayawa yana haurawa stairs yace "Toh ai baki fito kin ga abinda nake yi ba" Ita dai ta ci gaba da kallonta tana washe baki don a xo dai dai scene din da take so a film din, yana isa bangarensa bandaki ya shiga yayi wanka ya fito ya saka pajamas dinsa ya kashe wutan dakin sannan ya kwanta yayi rub da ciki ya runtse ido, bayan kusan thirty minutes Aneesah ta shigo dakin don an gama film din, yana jin ta amma yayi kamar bacci yake, kwanciya tayi gefensa tana shafa fuskarsa tana kiransa a hankali cike da shagwaba, he just don't have Choice in dai yana son bacci a ranan, haka nan ya biyeta kamar jira yake dama, har hakan ya 6ata mamaki... Sha biyu saura Jiddah ta cire bargon da ta rufe jikinta da shi ta mike xaune a hankali, har lokacin kirjinta bai daina bugawa ba, da ta tuna abinda ya faru sae gabanta ya fadi sosai, bata ta6a jin tsoron Abuturrab irin na daxu ba, gaba daya ta tsorata da shi da lamarinsa, da kyar ta cire Hijab dinta ta sauka daga kan gadon ta wuce bandakin, ta shiga bandaki da kusan minti sha biyar Ramlah ta bude kofar dakin a hankali, shigowa dakin tayi ta dau hijab din Jiddah ta kai hancinta, imagine ta fara yi to ko dai fesa mata turaren yayi ne?? Kallon kofar bandakin tayi jin kamar wanka take yi, can dai ta ajiye Hijab din a hankali ta nufi kofa ta fita ta kulle dakin ta koma nata dakin ta xauna gefen gado, ita fa duk ta rasa takamaiman tunanin da xata yi, ta rasa ma'anar abinda ta gani. Washegari da safe ganin har kusan takwas Jiddah bata fito ba Ramlah ta tafi dakinta, kwance ta ganta tana bacci, Ramlah ta karasa ta kai hannu kafarta, bude ido Jiddah tayi ta mike xaune da sauri, Ramlah tace "Baxa ki Islamiyya bane yau Jiddah? Karfe takwas fa yanxu" Jiddah dai ta kasa barin ta hada ido da ita, a hankali tace "Um ciwon kai nake, sai gobe" Ramlah tace "Toh Allah ya kai mu" juyawa tayi ta nufi kofa Jiddah ta bi ta da kallo, komawa tayi a hankali ta kwanta ta lumshe ido. Sanin Ahmad na hanya Ramlah tayi duk ayyukan gidan don taga alamar Jiddah ba fitowa xata yi ba, kwashe duk shopping din da Abuturrab yayi ma Jiddah tayi ta kai wani spare room ta ajiye don bata san wanda xata ce ya kawo ba idan Ahmad ya tambaya. Karfe goma saura Ahmad ya shigo gidan daga Abuja, bayan Ramlah tayi welcoming dinsa ta kawo masa breakfast suna xaune parlor yace "Jiddah ta je weekend gidan Umma halan?" Ramlah tace "Aa tana daki yanxu ma haka" Yace "Islamiyyar fa?" Tace "She said she is having headache, bari in ce mata ka dawo" Daga haka ta mike ta wuce dakin Jiddah, kwance ta ganta kan gado duk da tayi wanka ta shirya, Ramlah sae kallonta take ganin kamar duk a tsorace take, Ramlah tace "Na xata bacci ma kike ai, baki karya ba fa, kuma Doctor ya dawo" Jiddah ta mike xaune taki yarda suyi eye contact da Ramlah tace "Xan fito yanxu" Ramlah ta juya ta fita, Jiddah ta sauka kan gadon ta dau Hijab dinta, sai da gabanta ya fadi jin kamshin da yake, ta ajiye ta bude press ta dau wani sannan ta nufi kofa ta fita, xaunawa kasan carpet tayi ta gaishe da Ahmad ya amsa yace "Ya ciwon kan?" Ta d'an yi murmushi tace "Yayi sauki yanxu, na sha magani" Yace "Maa sha Allah, kun gama exams din?" Ta girgixa kai tace "Aa ranan Wednesday in sha Allah" Yace "Toh Allah ya taimaka" ta amsa da Ameen, sannan ta mike ta wuce kitchen, Ramlah dae sae bin ta da ido take, tea kawai Jiddah ta hada ta koma daki. Karfe sha biyu saura Ramlah ta shigo dakin Jiddah, Jiddah na xaune saman darduma tana karatun qur'ani, Ta kai ayan karshe ta rufe Qur'anin ta d'an kalli Ramlah, ganin ta da mayafi tace "Fita xa ku yi?" Ramlah tace "Ehh yana kiranki, kayayyakin ki Kuma na daya dakin fa na ajiye maki a ciki" Jiddah tace "Aa ai ba nawa bane ni kadai" Mikewa tayi tunda dama da akwai Hijab a jikinta ta bi bayan Ramlah, Ahmad na xaune parlor rike da car key dinsa yana kallonta yace "Are you going out with us now Jiddah? Xan kai Captain airport" Jin sunan da ya kira sai da gaban Jiddah ya fadi sosai without thinking twice tace "Aa karatu nake" Ramlah dai na tsaye bayan kujera tana kallonta, Ahmad yace "Tafiya xai yi fa, kuma xai dau watanni bai dawo ba, kawai airport xa mu kai sa muyi sallama da shi mu dawo" Shiru tayi jin abinda Ahmad yace, yana ci gaba da kallonta yace "Kije ki shirya mu tafi, ba komai ai, beside we are not staying long" Bata kuma masa musu ba ta juya a hankali ta koma daki, Ramlah ta bi ta da kallo, Ahmad yana murmushi yace "Why are u looking at her that way Baby?" Ramlah ta d'an yi murmushi bata ce masa komai ba, Hijab kawai Jiddah ta canxa ta dau nikab dinta dake a goge ta saka hakan kadai ne xai iya sa ta bi su kai Abuturrab airport, jakarta ta dauka ta rataye a shoulder sannan ta fito parlor, Dariya Ahmad yyi ganinta yace "Tohh yau kuma nikab xa a sa kenan" Jiddah dai bata ce masa komai ba tayi murmushi daga cikin nikab din, a haka duk suka fita gidan, back seat ta shiga... hira Ahmad da Ramlah ke yi har suka iso kofar gidan Abuturrab, Ahmad ya dau wayarsa ya shiga kiransa, ba a dau lkci ba ya daga, Ahmad yace "I am outside ka fito...." Abuturrab yace "Sai karfe biyu jirgin xai tashi xuwa lagos, I can't sit all day at the airport, ka gane?" Ahmad yace "Ohk wai sai kun fara xuwa lagos dama?" Abuturrab yace "Yeaa, amma ba mu xa mu yi piloting xuwa lagos din ba ai" Ahmad yace "But u should have told me that since" Abuturrab yace "Is there anything wrong idan kun shigo kun jira for just few hours?" Ahmad yace "Alright then" Daga haka ya katse wayar ya kalli Ramlah yace "Mu shiga ciki" Ramlah ta bude motar ta sauka, tuni mood din jiddah ya canxa, amma bata jira ace ta sauka ba, kuma bata nuna hakan a fuskarta ba, ta bude motar ita ma ta sauka ta rufe, Kalle kallen layin ta fara yi, ganin karamin kiosk can farkon shigowa layin ta kalli Ahmad tace "Yaya xan d'an siyo abu a kantin can" Ya kalli inda ta nuna masa yace "Me xa ki siya" Tace "Yanxu xan amso in dawo yaya" daga haka ta nufi kantin da sauri, su kuma suka shiga gidan, Aneesah tayi welcoming din Ramlah kamar xata hadiyeta don fara'a, tuni ta cikasu da lemo da kayan ciye ciye irinsu cake, cin cin, da alkaki da Chef Salma ke mata ta ajiye a gida sbda bak'i, Shi dai Abuturrab na xaune parlon yana danna wayarsa, bayan few minutes Ramlah ta kalli Ahmad tace "Bata shigo ba har yanxu fa Yaya" sae a sannan Abuturrab ya daga kansa, Ahmad ya mike ya nufi kofa, Abuturrab na kallon Ramlah yace "Who?" Ramlah tace "Jiddah, tare muke, tace xata siya abu a kanti kuma har yanxu shiru" Bai kuma cewa komai ba, Aneesah ta wani ta6e baki ta koma kitchen tana kas kas da chewing gum a ranta kuwa cewa tayi gwara dai kam da bata shigo din ba don xata yi danasanin shigowa, abinci ta fiddo a deep freezer don dumama masu, Bayan some minutes Ahmad ya dawo yace "Har gun mai kantin naje, ba abinda ta siya wajensa, kila tafiyarta tayi" Ramlah ta dinga kallonsa, sae kuma tace "Toh ba waya kuma balle a kirata" Shi dai Abuturrab danna wayarsa kawai yake amma duk yana jin su, Ahmad yace "Da akwai makulli wajenta ne?" Ramlah tace "Eh akwai spare key, tun ranan da na bata da xan je gida" Ahmad yace "Ohk better" Aneesah ta fito daga kitchen tana washe baki tace "Na daura girki bari yayi sai in xubo maku Sis Ramlah" Ramlah tace "Ayya da ma baki yi bothering kanki ba Aunty, mun ci abinci daga gida kafin mu fito" Aneesah ta 6ata fuska tace "Aa wllh, ke da ko girkina baki ta6a ci ba, yau dai kam sae kin ci" Ramlah tayi murmushi tace "Toh shkkn Anty" Hira suke ta yi a parlon banda Abuturrab dake danne dannen waya, bayan kusan minti ashirin da xuwansu Ahmad ya kalli Aneesah yace "Dauko min car key xanje laundry in amso kayana ynxu" Tana kallonsa da mamaki tace "Amma kace delivery xa ayi maka ai, and babu wani kayan da xaka bukata a ciki, ko ka manta ne" yace "Noo na tuna akwai wani rigan sanyi da xan dauka a ciki" Tace "Toh ka kira su kawo maka mana dole sai kayi wahalan driving kuma" Mikewa yyi ya wuce sama, shi dai Ahmad idonsa na kan tv yana kallon wani program da ake yi, sai ga Abuturrab ya sakko da makullin motarsa, Ahmad yace "Mu je can din tare" Abuturrab ya kallesa yace "No, ba sai ka wani wahala ba kai da xaka kai ni airport, i will be back soon" mikewa Ahmad yyi yace "Mu je can din, babu damuwa" Ta gefen ido Abuturrab ya kallesa, Aneesah tace "Haba doctor ga abinci can nace ya kusa nuna kuma kace xaka fita, don Allah ka tsaya ka ci, don Allah Dr" Abuturrab yace "Kaga dama kai ma baka ta6a cin abincin amarya ba, kawai ka tsaya ka ci... So u can rate her" Yana fadin haka ya amshe makullin motar Ahmad yace "Ba sai na tsaya warming mota ba, i will go with ur car, and i will be back in d next 20 mins" daga haka ya fice daga parlon, Aneesah kuwa sai lallaba Ahmad take ya tsaya ya ci girkinta yau daya dai... Abuturrab na fita kofar gida ya shiga motar Ahmad ya bar layin, tafiyar minti kusan talatin yayi ya iso layin....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;
Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697
Parking yayi ya sauka yana kallon mai gadi dake xaune a waje, wanda har ya mike xai bude gate a tunaninsa Ahmad ne sai ya ga akasin haka, suka gaisa Abuturrab ya shafa kansa yace "Suna ciki?" Yace "Aa gaskiya basu jima da fita ba" Yace "Ba kowa a ciki yanxu?" Mai gadin yace "Babu kowa, ko awa daya basu yi da fita ba Yallabai" Abuturrab ya tsaya kallonsa, Mai gadin na washe baki yace "Da na ga motar ma na xata su ne ai" Abuturrab yace "Ohk, shkkn ba ma sai kace masu na xo ba... Sai anjima" Daga haka ya koma motarsa ya shiga, a hankali yake driving din... Parking yayi ya jinginar da kansa da kujera, bayan few seconds ya dau jotter a cikin motarsa da biro, ya cire pieces daya a ciki, kan steering ya ajiye takardan ya fara rubutu a jiki, bayan some minutes ya gama rubuta abinda xai rubuta ya maida biron sannan ya linke takardan gently, ya kashe motar ya sauka ya shiga cikin gidan, knocking yyi jin kofar a kulle, cikin minti kadan Maimoon ta bude kofar, matsawa tayi tana kallonsa daga sama har kasa, lkci daya ya daure fuska, ta xaro ido tace "Au, sannu da xuwa yaya" Da sauri ta juya ta koma parlon, Umma dake xaune Jiddah ma na xaune kasa daga kusa da ita ta daga kai tana kallonsa, tunda Jiddah ta kallesa sau daya ta sunkuyar da kanta, Ya karasa parlon ya xauna yana kallon Umma yace "Ina yini Umma" Tace "Lafiya lau, aka ce yau xaka yi tafiyar?" Yace "Ehh in sha Allah..." Sai kuma ya shafa kansa yace "Naga ban xo mun yi sallama bane" Umma tace "Bayan wanda mu ka yi a gidan Yaya?" Ya sunkuyar da kansa, Maimoon dai na tsaye sai kallonsa take, idan ta kallesa sai ta kalli Jiddah da taki dago kanta sai wasa da fingers dinta take, Umma tace "Toh ki kawo masa ruwa Maimoon" Maimoon tace "To Umma..." Har ta kai bakin kofar kitchen din ta tsaya tana kallon Jiddah tace "Jiddoh xan xuba moringa din yanxu, ki xo ki gani" Jiddah ta d'an kalleta, Umma tace "Ba kince kina son koya ba, ki tashi ki je" Mikewa Jiddah tayi ta wuce kitchen din, da gefen ido ya bi ta da kallo a sace yanda Umma ma baxata sani ba, Umma tace "Amma daxu mun yi waya da Ahmad yace xai je kai ka airport..." yace "Ehh Umma, xan koma yanxu.. nan da awa daya da rabi ne flight din" Umma tace "Toh Allah ubangiji ya tsare, ya kai ku lafiya ya dawo da ku lfya" Yace "Ameen" Jiddah na shigowa kitchen Maimoon ta kulle tana kallonta tace "Kawai sai naga yaya Aliyu, alhalin for almost 2 weeks bai xo gidan nan ba" Jiddah ta hade rai tace "Toh me yasa kike gaya min?" Dariya Maimoon tayi har da tafe hannu tace "Aa ni fa kawai hira nake maki wllh..." Jiddah ta juya xata fita Maimoon ta rikota tana dariya tace "Ke wllh ni kawai jajantawa nake son mu yi da ke" Jiddah tace "Ki sakeni fita xan yi" Maimoon tace "Dallah ki tsaya in hada miyan tukunna, to meye don nace kawai sai ga yaya Aliyu, au ni na ma xata Safiyya ce nake maki wannan maganan, abinda mun saba gulman mu haka, amma ke kina so ki min wata fassara" Jiddah dai bata ce komai ba sai kallon miyan dake saman gas take, Maimoon ta tafi ta dau ruwa da coke ta daura kan tray ta dawo tana kallon Jiddah ta mika mata tace "Don Allah ki kai masa kar miyan ya kone" Da sauri Jiddah ta matsa ta tafi gun miyan tace "Bar min miyan xan dinga dubawa kije ki dawo" Maimoon ta hade rai tace "Kika san me xan ma miyan to?? Ni wllh wani lokacin kina bani mamaki, meye a ciki kawai dai kije ki dungurar masa da tray din a gabansa ki taho, wllh ba don miyan ba ni da kaina xan kai, ai ni aka sa ba ke ba" Maimoon ta d'an yi tsaki ta ajiye tray din tace "Haba, sai kace warce nace ki kai ma wani dodo ruwan sha" Gun miyan ta tafi tana juyawa, sai kuma ta nufi kofa a tunanin Jiddah daukan ruwan xata yi ta kai masa, sai taga bata dauka ba, Maimoon na fita parlor ta kullo kofar kitchen din tana kallon Umma tace "Umma wai Aunty Malika na ta kiranki, kamar wayarki na daki koh?" Umma tace "Ta kira ki ne?" Maimoon na d'an rawan baki tace "Haka dai tace min" Mikewa Umma tayi ta nufi hanyar dakinta tana cewa "To ai wayar na daki" Maimoon ta koma kitchen da sauri tana ci gaba da juye juyen miya bayan gas din ma a kashe yake tace "Kawai minti nawa kin kai ruwa kin dawo, idan ba dai da akwai wani abu a ranki da kike boye ma mutane ba" Jiddah dai bata ce komai ba sai kallon tray din take, Maimoon banda satan kallonta babu abinda take, daukan tray din Jiddah tayi daga karshe ta nufi kofa tana tafiya kamar bata son yi, ta bude ta fita, sai da ta shigo parlor taga Umma bata nan, ta fara kalle kalle, yana ganin haka ya mike, ta dungurar da ruwan kamar yanda Maimoon tace, xata juya yyi saurin kamo hannunta, ta juya ta marairaice masa murya kasa kasa tace "Wllh xan maka ihu ka sakeni, ka daina min abun nn da kake yi bana so" jan hancinta yayi har sai da ta ji xafi sannan ya saka mata takardan hannunsa a tafin hannunta yana kallon kwayar idonta, fixge hannunta tayi daga rikon da yayi mata kusan a guje tayi hanyar dakin amma takardan da ya bata na hannunta har sannan, ya bi ta da kallo kafin ya juya, ido hudu suka yi da Maimoon da ta d'an bude kofar kitchen din tana lekosu, ai da sauri ta yi jamming kofar bayan sun hada ido, yayi hanyar kitchen din, saura kadan ta tunkude miyan kan gas din bayan ya shigo kitchen din, sai xare katon idonta take tace "Xa a xubo maka abincin ne Yaya?" Janyo hannunta yayi yace "Ba dai kin iya munafurci ba??" a gigice tace "Don