Showing 249001 words to 252000 words out of 346625 words
Chapter 84 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
Umma ta kyabe baki without showing any concern tace "Ji yaya fa da wata magana, mutum xai yi ta rayuwa da abinda ke cutar da shi ne? Aliyu fa ya ga baxai iya xama da ita bane ya saketa to me yasa xa a ga laifinsa tunda ba wani ke xaunan masa da ita ba, sannan ya gaya min duk tijaran da kanwar uwarta da Hafsah suka je can gidan suka yi masa na kuma gaya maki, toh me yasa xaki damu kanki a kan yan iska? ba a farin ciki da saki amma wllh wllh nayi farin ciki da sakin wnn yarinya da yayi ko don Hafsah, Allah da ba don Hafsah dake cikin lamarin auren dumu dumu ba ni me tausansa ne ya maida matarsa amma duk wani abu da ya fito daga bangaren Hafsah bama fata mu kara kusancinsa in sha Allah, iyaka dai yanxu ya gama xagaye xagayensa ni kuma in gama gwara kansa idan Jiddah ta xana waec sai in basa ita ba don ya cancanta ba sai don bakin ciki da takaici ya kashe wasu" Ummi tace "Mu ma muna da 'ya ya matan nan fa Ramlah ki daina cewa haka..." Umma tace "Lallai yaya, ai mu ba mu watsar da tarbiyanmu ba, kuma in sha Allahu mun san mun ma ya yan mu tarbiyan da xa su iya shiga ko ina su xauna lafiya... Kin ga ni mu bar wannan xancen ba ruwana ni baxan tilasta Aliyu yayi abinda xai cucesa ba, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, ita kuma taje can Allah ya bata wani" Ummi bata kuma ce mata komai ba amma ko kadan bata gamsu da bayanan Umma ba. Tun bayan da Abuturrab ya saki Aneesah ya samu relieve ya daina jin komai na damunsa a rayuwa, ji yayi kamar wani kaya dake piercing dinsa aka xare masa, kusan ko da yaushe a kashe xaka ji wayarsa sbda kira uku da yake ignoring, na farko kiran Aneesah da take masa babu kakkautawa da text messages iri iri wanda baya dubawa, na biyu kuma kiran Ummi don yasan dalilin kiran nata, sai kuma kiran Aunty da ita baya ma son sanin dalilin kiran nata, da suka sauke jirgi Abuja bai yarda ma yaje gidansa ba don kada Aneesah ta bi sa duk da bai san ko tana Abuja ko kadunan ba, ya gwammace yayi xamansa hotel har sanda xa su daga jirgi xuwa kano, ranan Friday ya shigo garin kaduna, direct gidansu ya nufa sanin Abbansa na gari, ganin motarsa a parking space ya sake tabbatar masa da Abban nasa na garin, bayan ya shiga main parlor din gidan ya tafi bangaren Ummi, Aisha dake parlor a xaune tace "Ummi bata nan" ya kalleta yace "Ina ta je?" Aisha tace "Nima ban sani ba sun fita ne tare da Hajja" Bai ce mata komai ba ya tafi parlon Abbansa, kallo daya Abba yayi masa ya ci gaba da danne dannen laptop dinsa, ya xauna kasa ya gaishesa, Abba ya amsa a takaice without looking at him, Abuturrab yayi shiru, bayan few minutes Abba ya juya ya kallesa yace "Any problem? Na ga ka xauna min" Abuturrab ya girgixa masa kai amma kuma bai tashi ba, Abba ya ajiye laptop dinsa yana kallonsa da kyau yace "Ita uwar taka ce ta sa ka saki matarka ko???" Abuturrab ya kallesa da sauri yace "Not at all Abba, wllh she knows nothing about it...." Abba yayi wani murmushi yace "Dama nasan xaka kareta ai, sbda kai ka maida saki abun banxa abun hofi, Sbda uwarka ta xugaka domin kuyi tarnishing din Image din Hafsah a gun iyayen yarinyar tunda kasan akwai alaka me karfi tsakaninta da iyayen yarinyar, to u are a liar Aliyu, i birth u...." Abuturrab ya sauke boyayyen ajiyar xuciya a hankali yace "Abba threatening dina suke yi ita da aunt dinta, i have no option a lkcn, the aunt even went ahead and slapped me...." Abba na kallonsa strictly yace "Toh ni ubanka nace ka koma yanxu ka maida matarka..." Abuturrab ya daga kai da sauri ya kalli Abba, Abba ya hade rai yace "Yes that is my instruction, and u have to do so immediately" Abuturrab ya kasa ce masa komai lkci daya duk jikinsa yayi sanyi, Abba yace "Get out, and i am giving you from now till d end of this week" Da kyar Abuturrab yace "Toh Abba" daga haka ya mike ya fita daga parlon yana jin xuciyarsa na tafarfasa, gidansa kawai ya wuce direct duk da yayi niyyar xuwa gidan Umma. Har aka kira Magrib yana kwance daki, daga karshe ya fita masallaci bayan an idar ya dawo yana xaune gefen gado ya kunna wayarsa don kiran Ahmad, yana kunnawa sai ga kiran Aneesah, jefa wayar yyi a gefensa har ya katse ta kuma kira, sai da ta kira yayi sau hudu sai kuma text suka biyo baya, daukan wayar yayi a karo na farko ya buda text dinta da suka fi 50, gaba daya text din ban hakuri ne da rokon baxata iya rayuwa babu shi ba ya yafe mata, duk text din are full of remorseful words, har da cewa ita ta yarda ta amince xata xauna da kishiya don Allah yayi mata rai ya maidata dakinta, tsaki ya ja yana jin xuciyarsa na tafarfasa, ya mike daga karshe ya dau car key dinsa ya fice daga gidan, kofar gidan Umma yayi parking ya shiga ciki, minti daya yayi tsaye bakin kofar parlon sannan ya bude ya shiga, Hajja ce xaune parlon tayi rashe rashe abunta ga kulolin abinci sun fi hudu, Jiddah na xaune kusa da ita tana yanka mata lemo, ta daga kai suka hada ido da shi, lkci daya ta sunkuyar da kanta, he don't know all of a sudden sai yaji duk ya nemi damuwar da ya addabi xuciyarsa ya rasa, walking slowly ya karasa cikin parlon ya xauna saman kujera Hajja dake ta kallonsa ta rike kai tace "Kaii Allah ya rabamu da duk wani abu dake cutarmu a rayuwa, jama'a ku dubi yanda Aliyu yayi kyau yayi fess da shi daga rabuwa da kazama, ku dubi Aliyu jama'a..." Kwafa tayi tace "Kaji tsoron Allah kaji tsoron kazanta, kazanta ba kyau, Allah ka ci gaba sa nisanta mu da kazami" Jiddah dai yanka lemon hannunta kawai take, Hajja ta washe baki tace "Sannu da xuwa Aliyu ina yini" Ya ajiye wayarsa da yake dubawa yace "Ina yini?" Tace "Lafiya lau wllh, yanxun nan Hauwa ta bar gidan nan tun safe muke nan tare da ita" Shi dai Jiddah kawai yake kallo, Hajja ta mike tace "Toh bari in je in kira maka Ramlan yanxu ita ma ta shiga ciki bayan yayar ta wuce, baka ga uban tuwon da ta narka ba a nan, ita ko tsoron kibanta bata yi, ni dai na gaji da magana na ja bakina nayi shiru, tunda ba ni xa a kai asibiti hankali tashe ba" Jiddah ta kalli Hajja da sauri tace "Hajja in kirata?" Hajja tace "Aa ba ruwana bari in je da kai na meye amfanina" Daga haka tayi hanyar dakin Umma, Jiddah ta ajiye wukar hannunta a hankali, shi dai kallonta kawai yake, tana jin Hajja ta bude kofar Umma ta mike xumbur kafin ta bar wajen yayi saurin tashi ya rikota, marairaice masa tayi tana kalle kalle kamar munafuka tayi kasa da murya tace "Don Allah ka bari, wllh yanxu Umma xata fito parlon..." Mayafin da ya gani a kan kujera ya dauka ya mika mata taki amsa, bai sake sauraronta ba yayi hanyar kofa da ita, ta xaro ido tace "Na shiga uku, meye haka don Allah ka sakeni"
_Not edited_
*Sorry for the late update fans*
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Ina mata ma'abuta gyaran jiki kuzu ga supplement na gyaran jiki kala muna da supplement masu sa haske da laushin fata da gyaran jiki da maganin sanyi da masu kashe kuraje da tanbo ku Wani kalar supplement muna da cikin sauki da rahusa kadan Daga cikin su
Lady capsule
Royal jelly
Sugar wanita
Khusus
Vitamin e
Cantik ayyu
Puspa ayyu
Dara
Rapit wanita
Maca capsule
Reload
Papaya
Collagen snail
Flat tummy
Sliming capsule
Da sauran su domin neman Karin bayani atuntube wanna number 08066726866 mmn mujaheed
Suna fitowa compound Abuturrab ya mika mata veil din hannunsa yace "Sa mayafin ki nace" ta marairaice masa tana xare manyan idanuwanta tace "Ina xan ce ma Umma na je yanxu, wllh tana dakinta plss ka sakeni in koma ciki don Allah" Bai sake jiran ta saka mayafin ba ya nufi gate da ita still holding her hands tana son kwacewa amma ta kasa, pleadingly tace "Na shiga uku, to don Allah ka jira in koma ciki in dauko takalmina wannan ba nawa bane..." Dariya ta basa, bai kuma tanka ta ba har suka isa gate, taji kamar ta nutse sbda mai gadi dake xaune bakin gate yana kallonsu, shi kam Abuturrab ko a jikinsa ya fita kofar gida da ita ya bude front seat yana kallonta yace "Get in..." Sai a snn ta fashe masa da kuka tace "Wai me yasa kake min haka ne don Allah, kaga fa karfe nawa kuma nace maka Umma na ciki...." Bata karasa ba ta shiga motar da sauri tana matsar kwalla ganin daukanta yake shirin yi ya sakata cikin motar da kansa, yayi wani murmushi ya kulle motar da lock don kamar ya san kafin ya karasa daya side din xata bude ta gudu, tana kokarin budewa da sauri kuwa taji motar a kulle, hakan yasa ta kuma rushewa da kuka tana kallonsa har ya shigo motar ya kulle, tada motar yayi ya bar layin, hankalin Jiddah ya tashi sosai a lkcn, babban damuwarta Umma, bata san me xata ce mata ba, bata ma san da wani idon xata kalleta ba yanxu, bayan sun hau saman titi ta kwantar da murya pleadingly tace "Don girman Allah kar ka min haka, ban san me xance ma Umma ba wllh, I don't know what to say to her, ina kake son ince mata naje da daddaren nan yanxu" yana kallon titin gabansa speaking calmly yace "Sai ki ce mata mijin ki ne ya daukeki, ko laifi ne idan miji ya tafi da matarsa??" Ta xaro ido tana kallonsa xuciyarta na bugawa, Jiddah ta rasa abinda xata ce masa, kawai sai ta hau goge hawayen da ya ki tsaya mata tana nanata abinda ya fada a ranta, wai mijinta, sai yanxu xae iya kiran kansa da mijinta??? horn yayi bakin gate din gidansa mai gadi na bude gate din ya shiga yayi parking a parking lot, duk da Jiddah tasan Aneesah bata gidan hakan bai sa gabanta ya dinga faduwa tana kallonsa hankali tashe ba, bayan ya kashe motar ya juya yana kallonta kasa kasa... cikin rawan murya ta hade hannunta tace "kar ka min haka don Allah nake rokon ka, ba don halina ba ka maida ni gida, ban san me su Umma xa su yi tunani ba da Hajja don Allah ka rufa min asiri ka kai ni gida plss" ya dauke kai ya bude motar yace "Ko ma me suka yi tunani dai dai ne, mijin ki ai kika bi ba wani ba..." wani irin kallo ta dinga masa don haushi kalmar yake bata, wai mijinta, bata san lkcn da ta dake fuska daure tace "Ta ina ka xama mijina?" Juyawa yayi ya kalleta kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace "Mu je to in gaya maki ta ina" Yana fadin haka ya sauka sannan ya xaga ya bude side dinta yana kallonta, a hankali ta fara kuka ta rufe fuskarta da hannunta cikin sanyin murya tace "Don girman Allah ka maida ni gida Yaya" Ya dinga kallonta babu ko kiftawa, sai kuma yayi murmushi yace "Kin iya cewa yaya kenan, ni na xata Aliyu kadai kika iya fadi" Bai jira cewarta ba ya kama hannunta ya sauko da ita daga motar ya kulle motarsa, sai a sannan Jiddah ta fara kukan gaske tana biye da shi yana rike da hannunta har suka shiga parlorn gidan, ya kulle kofar ya sa makulli ya saketa yana kallonta, ta sunkuyar da kanta tana share hawayen dake xuba idonta, she looks so afraid, wucewa yayi sama ya bar ta a wajen, ta fi minti biyar a tsaye sannan ta karasa cikin parlon tana tafiya kamar me counting steps dinta, ta karasa tana kallon kujera ta xauna a hankali, tsadadden carpet din dake tsakar parlon duk yayi wani dusu dusu da shi, da ido ta dinga bin parlon da kallo, wani sai yace kayan parlon ya shekara biyu, ko kuma da akwai yara a gidan, Jiddah na ta xaune har karfe takwas da rabi ya gota, tagumi tayi xuciyarta cike fal da fargaban abinda su Umma da Hajja xa su ce, bata ma san da wani idon xata kallesu ba, furucin Hajja a hospital ne ranan ya fado mata da take gaya ma Aneesah, sai taji gabanta ya fadi sosai, saukowa yayi parlon sanye da jallabiya, ta daga kai da sauri tana kallonsa, kana ganinsa kasan wanka yayi, ya nufeta ya xauna gefenta, ta rike numfashinta sbda kamshin turarensa da ya cika wajen, xuciyarta na bugawa ta matsa a hankali ta bar space a tsakaninsu taki yarda ta kallesa, shi dai kallonta kawai yake, sai kuma yayi kasa da murya yace "Xa ki iya girki yanxu?" Ta d'an kallesa suka hada ido, sunkuyar da kanta tayi tace "Girkin me?" Yace "Something light, i haven't taken anything since afternoon" A hankali tace "Toh" yace "Ko in fita in siya?" Ta girgixa kai ba tare da ta bari sun hada ido ba tace "Xan yi, amma idan na gama xaka maida ni gida?" Ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Nan ba gida bane?" kamar xata fashe da kuka tace "Ba gida bane" Yana kallonta babu kiftawa yace "Toh xan maida ki" Ta kallesa ta marairaice tace "Kayi alkawari?" Ya dage girarsa sama yace "Sai kin gama girkin xan yi wannan alkawarin" tace "To akwai kayan miya?" Ya langwabar da kai yace "Sai dai mu je mu siya yanxu" Ta xaro ido tace "Lokaci xai wuce ai, ji karfe nawa fa" Yace "Aa... bakin hanya ne ai, ba nisa" Tayi shiru kamar me naxari, mikewa yayi ya nufi stairs ta bi sa da kallo babu ko kiftawa har ya haura sannan ta sunkuyar da kanta, ba a dau lkci ba ya dawo da makullin motarsa yace "Mu je" Ta mike ta dau gyalen da ya ajiye saman kujera sannan ta bi bayansa suka fita, kayan miya ya siyo har da Irish da crate din kwai, with beverages... Ita dai Jiddah kallonsa kawai take bata ce komai ba, ya shiga shopping mall ya siya yoghurt me tsada da bread, ita dai tana mota tana jiransa, yana fitowa ya shiga motar suka fita mall din, ya tsaya gun masu siyar da gasasshen kaza a hanya ya siya sannan suka wuce gida, suna isa bakin gate Jiddah ta kallesa innocently tace "Toh ka bar motar a waje ba sai ka sake fitowa da shi ba idan xaka maida ni" ya kalleta yace "So kike a sace min mota?" Tayi shiru tana kallonsa, horn yyi mai gadi ya bude gate din ya shiga ciki yayi parking, xata debi wasu daga kayan da ya siyo yace "Aa yi wucewarki ciki xan dauka" Tayi shiru tana kallonsa, ya dau wasu daga ledojin yace "Ki tafi nace" A hankali ta fara tafiya har suka shiga parlon, ya ajiye kayan ya koma ya dauko sauran, ledan kayan miyan ta dauka ta wuce kitchen din. Tsaye tayi tana tunanin light food da xata girka da baxai dau lkci ba, ta dinga bin kitchen din da ya d'an yi k'ura da kallo, a hankali ta shiga store ta duba me da meye a ciki, ledan cous cous guda daya ta dauko ta fito, tana kokarin diban kayan miya a bowl jikinta ya bata kamar ana kallonta, ta juya da sauri suka hada ido da shi, yana tsaye jikin kofar ya rungume hannunsa yana kallonta, a hankali yace "Ki dafa ruwan shayi kawai ki soya min kwai, i will take tea and bread..." Tace "Girkin fa?" Yace "Aa.. do not stress ur self, it's already almost late" tace "Ae xan iya, nan da 20mins" yayi kasa da murya yace "Sae kiyi min gobe da safe" Ta kallesa da sauri tace "A ina?" Yyi murmushi yace "Gidan Umma" Bata ce komai ba ta shiga daura ruwan shayin da yace a gas, juyawa yayi ya bar kitchen din, ta duba kitchen din bata ga ko alamar kayan kamshi, mamaki ta dinga yi ganin ko spices da kayan maggi babu, to da xata yi girkin ma da me xata yi amfani? Matar gidan bata girki kenan?? ta tabe baki ta tafasa ruwan Lipton din kadai, ta dau mug da plate, ta wankesu da cokali da tray duk ta tsane sosai, snn ta wanke fry pan ma, cikin mintuna kadan ta soya kwan ta juye a plate sannan ta xuba ruwan lipton dake tafasa a cikin mug din ta daura a kan tray din da cokali ta dauka ta fita, bata gansa a parlon ba ta ajiye tray din saman carpet ta tafi ta dauko kayan shayin da bread sannan ta dawo ta ajiye ta xauna kan kujera, bayan minti goma bata ga ya sauko ba, ga ruwan shayin dake a bude xai huce, kallon stairs tayi sai kuma ta mike tana tafiya a hankali har ta wuce sama, ta rasa me yasa in dai ya shigo gidan nan memories iri iri ke dawo mata, tana ta tsaye corridor din rooms din na kusan minti uku kafin ta nufi part dinsa kamar bata son tafiya, a hankali ta murda kofar parlon ta leka ciki ya daga kai ya kalleta ta sunkuyar da kai tace "Na gama tun daxu" ya ajiye remote din hannunsa yace "Me yasa baki kawo upstairs ba, I don't eat downstairs" tayi shiru tana kallonsa, yace "Or?? In sauko?" ta girgixa kai