Showing 330001 words to 333000 words out of 346625 words
Chapter 111 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
mata Ramlah na ciki, Hajja na rike da jaririn tana shiryasa bayan ta gama masa wanka ta kankance ido tana cewa "Mata ki dinga abu isa isa da gadara kamar ni bare ce wajen Ramlar, toh dai ni na haifi uban Ramlah don haka ban ga ta inda kika fi ni kusanci da ita ba, kuma in don ta kece ma baxa ki gan ni gidan nan ba, to ina ruwana da wani Ahmad, ni sabida jikata na xo, daga nace a hada ma yaro gulucodi a fida sai ki kama min fitina, aa ni baxan biyeki ba aniyarki ta bi ki...." Ko kallonta Umma bata yi ba tana ta gyara sabon siff din baby, Ramlah kuma na kwance tana bacci kan gadon Umma, Hajja na ganin Jiddah tace "Xan dai ga uban da xai ce min haka xanyi ko ba haka xanyi ba idan matar Aliyu ta haihu... Ko ita Hauwan sai in tsine mata albarka idan tace xata min shisshigi a lkcn balle ke" kwafa tayi tace "Allah dai ya bamu lafiya ai kamar gobe ne, xan nuna ma kowa ni er banxa ce a lkcn" Jiddah ta durkusa ta gaida Hajja tana kallon kyakkyawan yaron hannunta, Hajja tace "Ga can jakata ki budu ki jera min kayana a kambodin Ramlah, atamfa a gefe, leshi a gefe, mayafan kuma ki saka su a tsakiya, basu fi kala ashirin ba kayan" Jiddah ta juya tana kallon katon jakan da Hajja ke nuna mata.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_
Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*
If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp
Jiddah dake xaune gefen gado rike da Babyn Ramlah a hannunta ta kauda kanta da sauri ganin abinda ke hannun Huraira me aikin Umma, Huraira ta karaso ta ajiye plate din tuwo da miyar agushi a kusa da Hajja, Hajja ta kalli Umma dake hada ma Ramlah shayi tace "Toh kin ga rashin d'a'an maimakon a bani girmana a xubo min abincin a cooler na tuwo da miya amma an kawo min tuwo a plate kamar almajira miya kuma na galantoyi a plate, to dai ya fi babu wai d'an agwai da bak'in da" Umma dai bata ce komai ba ta gama kada shayin ta mika ma Ramlah, Hajja ta kalli Jiddah da ke kallon wani side din daban aroma din miyan na damunta tace "Ki ajiye masu yaronsu kiyi ta kanki ki xo mu ci abinci, yaron da ake ta nuna mana fin karfi kamar d'an gwal..." Jiddah ta kasa juyowa ga amai dake taho mata, Kafin Hajja ta sake cewa komai ta kwantar da jaririn da sauri ta ajiye gyalenta xata fita Umma dake lura da ita ta nuna mata bandakinta tace "Shiga nan" Dawowa tayi ta shiga bandakin Umma da sauri ta hau kwarara amai, Hajja da ta bi ta da kallo ta saki baki har sai da Jiddah ta fito bayan minti biyar, kwanciya tayi saman carpet din dakin tana maida numfashi, Hajja tace "Sai dai da kika bari ya kai ki ya baro kenan er nan?" Jiddah ta daga kai a hankali tana kallon Hajja, Umma na kallon Jiddah tace "Ta shi ki dawo nan" Jiddah ta kalli gadon da Umma ke nuna mata sannan ta tashi da kyar ta hau ta kwanta Ramlah na mata sannu, Hajja ta kyabe baki tace "Toh ai shkkn kuma"
4months later...
Cikin bacci Jiddah ta ji ana jan hancinta a hankali, ta bude ido da kyar tana kallonsa, cikin shagwaba tace "Me yasa baka son ka dinga bari na ina bacci ne?" Ya marairaice mata yace "Baccin ya isa haka, tun safe fa, kin barni ni kadai kamar maraya...." Bai jira cewarta ba ya dagota xaune ta sakar masa kuka cike da shagwaba tana turasa tace "Ni wllh baka bari na inyi bacci" rikicewa yayi ya rungumeta sosai yace "I only want to show u something sai ki dawo ki ci gaba da baccin, i am so eager to show u" Tana kallonsa ta turo baki tace "Oya toh meye shi?" Dagota yayi suka mike tsaye, riga ce iya cinya a jikinta, idan kai ba me lura bane ba ma baxa ka san da wannan cikin na jikinta ba, sosai ta kara kyau tayi fresh, kuma ta d'an murmure kirjinta suka cicciko, da kansa ya daure mata gashinta sannan ya matso mata da takalman da take sa wa a daki ta saka yana rike da hannunta suka fita dakin, dakin Aneesah na da ya bude a hankali yana kallon Jiddah da murmushi fuskarsa, wara ido tayi ganin yanda aka gyara dakin for a new born, kamar dai irin gobe xata haihu din nan, gadon jaririn ciki kadai ma abun kallo ne... Dakin yayi masifaffen kyau, yana rike da hannunta suka shiga ciki ya bude press din kaya taga wasu uban kayan baby iri iri masu tsadan gaske, ya ja ta xuwa bathroom nan ma dai complete set iri biyu na kayan wankan jariri ne a ciki, ta juya ta kallesa tana wara ido, rungumesa tayi ta lumshe ido cikin sanyayyan muryarta tace "Thank you my world" Ya kankameta yace "Anything for u and my little pilot wife" Kissing lips dinsa tayi, sai kuma ta hade rai tace "little Pilot dinka kadai ka sani, don ni bani da kowa ko?" Dariya yayi yace "Ai sai mun gama da shi xa mu fara naki babynah" Turo baki tayi tace "Ka dai nuna yan ubanci tunda pilot din ka fara yi ma...." Yana murmushi yana shafa cikinta yace "Mama ta shigo daxu kina bacci" Tace "Me yasa baka tasheni ba?" Yace "Idan na tashe ki ai na tashi Lil pilot ne" Murmushi tayi tace "Toh in je gidan nata yanxu tunda baccin ya fita idona?" Yace "Ba ki ci abinci ba ai" Tace "Aa ban fara jin yunwa ba" Yace "Are u sure babynah?" Tace "Sure dear" Yayi pecking lips dinta yace "let me get you ur hijab, sai ki tafi amma kar ki dade plss, just 5mins ki gaisheta ki fito" Daga haka ya koma dakinta don dauko mata Hijab, ta dinga bin dakin da kallo tana kara jin son captain a ranta, tun bayan da aikinsa ya dawo twice to 3 times a week take samun kulawa na musamman daga garesa a ko da yaushe yana makale da ita, always there for her, komai shi yake mata, hakan yasa shakuwansu ya karu sosai... Ba a dau lkci ba ya dawo da hijab dinta da wata doguwar rigan, duk shi ya saka mata sannan ya rakata har bakin gate kafin ta fita ta kallesa cike da shagwaba tace "Plss ka dafa min white rice kafin in dawo ina son in ci da mai da ya ji" Yace "Right away baby" Daga haka ta fita shi kuma ya koma gidan ya shiga kitchen kamar Ummi ta sa shi aiki. Kasancewar ranan asabar ne su Khaleesat duk sun tafi makaranta, babu kowa downstairs sai mai aiki, bayan sun gaisa Jiddah ta xauna a parlon, mai aikin kuma ta tafi sama sanar ma Mama xuwanta, Jiddah na ta xaune ita daya parlon har taji shigowar mota compound din gidan, bayan few minutes aka bude kofar parlon ta daga kai, wani Dattijon da baxai wuce shekaru 73 ne ya shigo parlon da sallama hannunsa rike da karamin jaka, kallonsa Jiddah ta dinga yi babu ko kiftawa kamar idanuwanta xa su fito, can ta mike tsaye da sauri, ya karaso parlon shi ma dai yana kallonta, bata san sanda ta fasa wani kara a tsorace ba, dai dai fitowar Hajiya Fatima, tsaye Dattijon yayi daga inda yake yana kallon Jiddah da mamaki, Hajiya Fatima ta karaso da sauri tana kallon Jiddah tace "Lafiya Jiddah what happened?" Tana isowa dai dai wajen Jiddah taga ta sulale kasa, rikota tayi a raxane tana kiran sunanta tana kallon mai gidan nata, shi dai yana tsaye inda yake bai karaso ba yana ta kallonsu, Hajiya Fatima ta kallesa cikin tashin hankali tace "What just happened Yallabai, me ya faru da ita?" Yace "Shigowata kenan fa, and at first i tot Khadija ce, who is she? She just shouted after seeing me sai kuma tayi collapsing" Hajiya Fatima ta dinga kwala ma first daughter dinta kira, mai aiki dake tsaye gefe ita ma a tsorace ta tafi sama da gudu ta kira Aunty Rahama, Aunty Rahama na shigowa parlon ganin Jiddah kwance kasa a hannun mamanta ta xaro ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me ya faru mama, me ya sameta?" A rikice Hajiya Fatima tace "Ban sani ba wllh Rahama, ki dauko makullin mota mu tafi asibiti, Ali baya nan, quickly get the car key mu tafi asibiti kawai plss" Alhaji Ishaq dai na tsaye yana kallon ikon Allah, gaba daya mamaki ya gama cikasa, Da gudu Rahama ta tafi sama dauko makullin mota sai ga ta ta dawo har da mayafinta jikinta na rawa tace "Na dauko mu tafi Mama" Hajiya Fatima ta mike da sauri tana ce ma mai aiki tayi maxa maza ta dauko mata Hijab dinta, Aunty Rahama na daga Jiddah suka ga jini kwance a kasanta, Da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kin ga mama" Hajiya Fatima ta kwalo ido a tsorace tana kallon jinin tace "Na shiga uku na lalace, meye haka??" sai kuma ta fashe da kuka tana salati tace "Meye haka ni Fatima, me ya sameta" Alhaji Ishaq da shi ma hankalinsa ya tashi ya ajiye jakarsa da sauri yace "Ku fito da ita mu wuce asibiti, hurry pls" Juyawa yayi da sauri ya bar parlon. Hajiya Fatima na xaune a bakin emergency room tayi tagumi, ta dade bata shiga irin wannan tashin hankalin ba, ta ma rasa wani tunanin xata yi in particular, astagfirullah wannan kuma wani irin jarabawa ne a parlonta, sai a parlonta Jiddah xata fara bleeding? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Rahama na jingine da bango ita ma dai duk hankalinta a tashe fatan ta kada ace Jiddah tayi miscarrying cikin nan, Allah kada ya sa hakan, ko don yanda taga Captain ya kwallafa rai a cikin, don time to time ta kan shiga gidan idan ta dawo daga aiki, tunanin miscarriage ya dinga aika mata da wani goosebumps a jiki, she is so afraid, Alhaji Ishaq da Son dinsa Ali na can reception a xaune all disturbed also, bayan kusan minti talatin wata babban likita ta fito tana kallon Hajiya Fatima tace "Kece mahaifiyarta ai?" Hajiya Fatima ta mike da sauri gabanta na faduwa tace "Ni ce doctor, fatan dai babu matsala" Tace "Ki sameni a office" daga haka ta wuce, Rahama na kallon mum dinta sanin ba komai wani lkcn take iya dauka ba a ranta, ta dakatar da ita da sauri tace "Mama ki bari ni in je ko Ali, ke ba sai kin shiga ba ke" Hajiya Fatima tace "Aa babu komai xan je ni..." Daga haka ta bi bayan likitan da sauri xuwa office dinta, Likitan ta cire glasses din idonta tana kallon Mama tace "Ina shi me gidan nata?" Xuciyar Hajiya Fatima na bugawa da karfi tace "Fatan dai babu wata matsala doctor" likitan tace "Da akwai, don ta samu miscarriage, and she is still unconscious...." Da karfi Hajiya Fatima tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, miscarriage likita? Na shiga uku, yanxu cikin ya xube?" Sai kuma ta fashe da kuka, likitan tace "Kamata yayi kiyi fatan tayi gaining conscious Hajiya ba ki karkata kan miscarriage ba... Did she just slouch down, fall accidentally, or an gaya mata wani labari ne da ya girgixa ta ta fadi?" Kuka kawai Hajiya Fatima take ta ma kasa cewa likitan komai, ta furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya fi a kirga, likitan ta ajiye pen din hannunta tace "I need to talk to her husband, a turo min shi yanxu..." Cikin kuka Mama tace "Baya asibitin likita... Yanxu shkkn cikin ya 6are?" Likitan ta buga table din gabanta a hankali tace "Kiyi tunanin halin da er ki ke ciki tukun ba ciki ba Hajiya, kiyi hakuri ki d'an fita ki turo min wanda aka yi komai a gabansa, u aren't answering any of my questions Hajiya" Mama ta mike da kyar tana kuka ta fita, Rahama dake tsaye tana jiran fitowar mahaifiyarta ganin ta fito tana kuka a ranta ta shiga furta Innalillahi, shkkn abinda take ta gudu ya faru, Mama na kuka tace "Tayi miscarriage kuma wai she is still unconscious" Ita ma hawayen ta shiga yi tace "Mama ki kira mijinta kawai muna ta yin abubuwa gaban kanmu, a kirasa mama a sanar masa ya taho" Mama ta nemi waje ta xauna tana rusa kukan miscarriage din nan da aka yi a parlonta, Ali ya kasa cewa komai bayan yayarsa ta sanar masa abinda ke faruwa, Alhaji Ishaq dai na tsaye shi ma he is so Speechless, Rahama na goge idonta tace "Call him immediately Ali" daga haka ta juya ta bar wajen, Ali ya ciro wayarsa ya shiga neman number Abuturrab, ba karamin courage yayi gathering ba kafin yayi dialing number, yana fara ring Abuturrab ya daga, Ali yayi karfin halin cewa "ermm Captain dama Jiddah ce bata ji dadi ba, so we rushed her to the hospital immediately" Abuturrab ya mike tsaye daga xaunen da yake xuciyarsa na bugawa yace "Jiddah????" Ali ya runtse ido ya bude yace "Ehh" daga haka ya sanar masa da asibitin da suke ya katse wayar. Tun bayan da Abuturrab ya iso asibitin aka sanar masa abinda ake ciki, ya kasa cewa kowa komai, he was more than shock, yana xaune kan kujera a reception ya rike kansa ya kasa kallon kowa cikinsu, lkci daya idanuwansa suka kada, he was so hurt namijin kokari kawai yake, Alhaji Ishaq yace "Kayi hakuri, haka Allah ya kaddaro, ita kuma sai mu yi fatan Allah ya tashi kafadunta, ya bata lafiya" Hajiya Fatima dai na can gefe ta kasa kallon Abuturrab, tayi kuka har ta gaji er ta na taya ta, Ali yayi patting Shoulder din Abuturrab cikin kwantar da murya yace "U need to be strong Captain, Allahn da ya baku shi xai sake baku..." Abuturrab yayi karfin halin mikewa da kyar, gathering much courage yace "I want to see her plss" Ali yace "Likitan ta sanar min she is sleeping now, amma mu je office dinta mu ji ko xa a iya shiga ward din yanxu" kama hannun Abuturrab yayi xuwa office din likitan, likitan na kallon Abuturrab tace "Kai ne mijin nata?" Kai kawai ya iya gyada mata, tace "Ohk dama da akwai wani abu dake damun matarka ne, or did they break any shocking news to her?" Ya girgixa mata kai a hankali ya kasa cewa komai, tace "Toh Allah ya kiyaye, idan ta samu kanta sosai sai ayi mata wankin ciki, Allah ya kiyaye gaba" Ali yace "Doctor plss xa iya shiga a ganta yanxu?" Likitan tace "Alright shi dai mijin nata ya shiga ya dubata, amma yana dubata ya fito, she need much rest now" Ali yace "Toh mun gode Dr" ta fada masu ward din da Jiddah take, daga haka shi da Abuturrab da ya kasa cewa komai suka fita office din... Shi ya raka Abuturrab har dakin sannan ya xauna kujeran dake ajiye bakin ward din, Abuturrab ya tura kofar a hankali ya shiga ciki, yana isa kusa da gadon ya daura kansa saman pillon, he was really hurt, can ya dago kansa a hankali yana kallonta da idanuwansa da suka kada, cike da karfin hali yace "Get well soon wife, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" Xaunawa yayi kan kujeran dake ward din ya jinginar da kansa yana jin wani xafi da xuciyarsa ke masa bai ta6a xaton haka ba, can ya ciro wayarsa yayi dialing number Ummi, tana dagawa ya gaisheta, jin voice dinsa tace "Lafiya??" A hankali yace "Ummi muna hospital, Jiddah tayi miscarriage" a rikice Ummi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wani hospital din" Ya sanar mata ta katse wayar tana nanata furta Innalillahi a xuciyarta, can tayi dialing number Umma tana dagawa ta sanar mata sannan ta mike ta fita xuwa dakin Hajja, kwalema ta sameta tana yi da su Nafisah wai taga gilmawan kyankyaso a dakinta, Ummi tayi karfin halin cewa "Hajja yanxu Aliyu ya kirani wai Jiddah tayi 6ari suna asibiti" Hajja ta saki Tsintsiyar hannunta da karfi tace "Li eelafi quraysh, meye kuma 6ari?"
*Sorry for the silence yesterday, jiki da jini... Kuma aski in ya xo gaban goshi...*
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_
Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*
If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp
Kwanansu daya a hospital aka yi discharging Jiddah bayan an mata Dilation and Curettage, Aunty Rahama na rike da hannun Jiddah suka nufi motar Abuturrab, tuni ya fita da basket na abincin da aka kawo da safe daga gidan Umma, Hajja ta bi Aunty Rahama da kallo sai kuma ta kalli Umma dake yi ma nurses din reception sallama, tayi kasa da murya tace "Ita kuma wannan narkekiyar daga ina? Naga sai wani kai wa take tana komowa, a ina ku ka samo ta?" Umma tace "Makociyarsu ce" Hajja ta rike haba tace "A kasar nan dai naga kamar an maida kiba wata abar ado... Ita Jiddah ina ita ina wannan jigbegiyar mata da ta kusa haihuwanta, wnn ai ta fi ta wayewa da duniyanci, salon taje ta kwace mata miji mu shiga uku? Ai ba wani kiban a xo a gani ne da matar ba balle ace Aliyu baxai iya aurenta ba, tsaff xai aureta su xauna, sannan naga fuskarta na da kyau kamar dai yar yarinya, jikinta kuma luwi luwi alamar hutu ya xauna, to ni dai ba ruwana kilan baku xaunar