Showing 282001 words to 285000 words out of 346625 words

Chapter 95 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

ko?" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Talk to me pls wife" A hankali tace "Xan jira ta gama" Yace "Are u sure?" Ta gyada kai kawai, mikewa yayi ya isa gaban mirror ya dauko ledan da ya ajiye ya dawo ya xauna gefenta ya ciro kwalin dake cikin ledan ya mika mata yana kallonta, kallon kwalin wayar k'iran samsung ta dinga yi sai kuma ta kallesa, murmushi ya sakar mata yayi kasa da murya yace "For u" Sauke idonta tayi ta amsa cikin sanyin murya tace "Nagode Allah ya kara budi" Bata rufe baki ba ya kamo hannunta ya saka mata makulli a palm dinta sannan ya rufe palm din a hankali yace "For you wife" Bude hannunta tayi tana kallon makullin motar, sai kuma ta kallesa with surprise, ya gyada mata kai yace "Naki ne" fadawa jikinsa tayi ba tare da ta shirya ba ta rungumesa ta ma rasa abinda xata ce masa.... Ya lumshe ido a hankali yana jin wani sabon sonta na fixgarsa, ya kai bakinsa kunnenta underneath his breathe yace "I love you Jidderh, i have always love you, ban san tausayi na rikidewa ya koma so farat daya ba sai a kanki, i sacrificed a lot because of u wife, and u changed my mentality toward many things in life, the worst day of my life was the day i was forced to divorce u, i felt empty Jidderh... I was hurt, i was devastated, amma duk yanda Allah ya tsara abu dole hakan xai faru, and the most happiest day of my life was yesternight..." A hankali ya ci gaba yace "I am happy ur pride was mine, and i am appreciating it with a car key, in return i am giving u all my heart, i mean all...." Hawayenta da yaji na sauka jikinsa ya sa ya dago kanta, a hankali ya dinga goge idon nata, gaba daya ta kasa ce masa komai, ya mike ya dagata ya dau mayafinta ya mika mata yana rike da hannunta ya nufi kofa, a hankali take tafiya tana bin sa, har suka sauko downstairs, har sannan Aneesah na xaune parlor yanda Abuturrab ya bar ta, tun da Jiddah ta hangota suna saukowa stairs bata sake kallonta ba har suka shigo parlon, shi kansa Abuturrab bai kalleta ba ya nufi kofa still holding onto Jiddah's hand, Aneesah ta bi su da kallon gefen ido, dai dai nan Maimoon ta fito daga kitchen tare da su Jamila bayan sun daura girkin, ganin Abuturrab da Jiddah sun fita waje ta lallaba ta bi bayansu ba tare da ta bi ta kan Aneesah ba ta tsaya window tana lekansu, Abuturrab na rike da Jiddah har xuwa gun sabuwar motar ya kalleta ya wara ido a hankali yace "Ya maki ko aje a canxa wife?" Rufe bakinta tayi don ta ma kasa ce masa komai, ta bi compound din da kallo ganin babu mai gadin gidan ta nufesa ta rungumesa tana shessheka, Sai da Maimoon ta murxa idonta don tabbatar da abinda take gani sannan ta maxa ta fito daga parlon, wani kara tayi ta nufesu almost running, Jiddah na son sakesa jin muryan Maimoon shi kam ya ki sakinta ya rungumeta gamm, Maimoon na xaro ido tace "Yaya motar ta ne?" Yana murmushi yace "Yeahhh" Ai da gudu ta tafi ta gayyatosu Jamila cike da murna kamar ita aka siya ma mota tana cewa "Ku fito, ku fito, wllh wannan tsaleliyar motar ta Jiddah ce wllh tata ce, ita Yaya ya siya ma ashe..." Gaba dayansu suka fito daga parlon, Maimoon ta dinga tsalle a bakin kofa tana kallon Aneesah dake kokarin fahimtar abinda Maimoon ke cewa, Maimoon ya dinga cewa "Wllh na Jiddah ne motar..." Lkci daya Aneesah ta mike, Maimoon na ganin haka ta bar bakin kofar ta fita tsakar gida don dama so take taga ta tashi, Aneesah ta nufi window da sauri tana lekan waje taga ubansun motar, ga Abuturrab rungume da Jiddah har sannan....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




MG'S SKINCARE

In kid'a ya chanza rawarma semutaru asauyata,
Wani Kaya se amalende
Haka Wani Hadi na musamman se MG'S,

Ina ma'abota amfanida kayan MG'S SKINCARE?

To bana fa tafi bara munqarawa kayanmu inganci muncire muntsefe munkawo maku qayatattun kayan gyaranjiki da Baki taba amfanida irinshiba a wannan qarnin,

Wani irin salo na gishirin kyan daukar magana zakiyi duk kikayi amfanida hadinmu b cika bakiba,ko yayan Hutu basa nuna maki tsadar fataba,duk a 11k fa kachal👌🏻

Beauty kit:11k
Student package:7k
Soap:3k
Bridal kit 18k

Kicire kokonto ki warwaro Lalita kidebi Kaya n kerewa SAA

Chat:08062991549 or 07046881166 or 07067210195
Call:08064532391

Available in Kano and Kaduna

We also have beautiful yet luxury and unique frames for your apartments chat or call 07046881166

Serious buyers only please,

Inamasu bukukuwa😍
Kugarzaya @inteesar cakes nd more kuyi order small chops domin bakinku irinsu
Cupcake,fishroll,samosa,spring rolls dama duk kayan kwalam da makulashe kunemata 07067210195
Cika alkawari shine takenmu🤝
Thank you







Mutuwar tsaye Aneesah tayi jikin window tana kallonsu gaba daya, ta kasa kwakkwaran motsi, lkci daya taji xaxxabin da take ji tun safe ya sake dawo mata, Muryar Maimoon a compound din gidan kuwa ba a magana, sai ka rantse ita aka siya ma mota duk da abun nata har da gayya, Hotuna ta dinga ma Abuturrab da Jiddah tana masu video da wayarta, Jiddah dai taki bude idonta gaba daya kunya ya rufeta, tayi kokarin xame jikinta daga na Abuturrab amma ya ki saketa, duk kunyan kawayen Maimoon dake tsaye ya cikata, Aneesah ta dauke idonta ta juya ma window din baya kirjinta na wani heaving kamar xai fito, mota?? Tambayar da tayi ma kanta kenan a fili, da hannu biyu ta dafe kirjinta tana jin wani abu da bata ta6a ji ba, da gudu ta nufi kitchen kamar wata ta6a66iya.... shigowar Mai gadi compound din ya sa Abuturrab ya sake Jiddah ta juya masa baya da sauri, Maimoon ta tafi ta rungumeta cike da farin ciki take cewa "Congratulations Jiddah, i am really happy for u sis, Allah ya sanya alkhairi" Jiddah dai ta kasa cewa komai suna rungume da juna, Mai gadi ya nufo Abuturrab da sauri duk da bala'in da ya sha a bakin gate, da ladabi yace "Ranka shi dade anyi baki ne, xa a shigo da mota.. nace bari in fara sanar da kai" Abuturrab yace "Ohk ka bude gate din" komawa yayi da sauri xai bude sai ga Hajja ta shigo compound din rataye da katon jakanta wanda babu komai ciki, Cike da fitina take kallon mai gadin tace "Wllh Allah ya isa ban yafe maka ba..." Abuturrab ya nufeta yace "Me ya faru Hajja?" Kamar xata yi kuka tace "Wllh su a Masar in xa su dau mai gadi sai an fara kai sa asibitin kwakwalwa an binciki kwakwalwarsa ciki da bai, basa daukan masu gadi kansu tsaye, banda haka har wannan tsukakken mutumin xai ce bai ta6a ganina ba a gidan nan? Idan ma bai ta6a ganina ba xai ce bai ga kamanni ba? To ni dai Allah ya isa wllh, ya min axabbabben walakanci bakin gate din nan wanda da a Masar ne titi xa a mika ma yara shi suyi ta jifan d'an banxa, ai ba a ma tsofaffi haka a Masar, sun san mutuncin tsoho, to idan ma ni bai ga kamannina da kai ba xai ce bai ga kamannin Hauwa tare da kai ba, tare da ita fa muke, nace yau wllh ko taki ko ta so sai mun taho gidanka tare tunda bata ta6a xuwa ba, amma mutumi kawai ya walakanta mu a bakin gate yace mana daga ina? Allah ya saka min wllh, ita kuma Hauwa ta wani ja6e a mota tayi shiru maimakon tace kai don uwarka gidan d'a na ne ni na haifesa wannan tsohuwar kuma ta haifi ubansa, to wllh bata yi haka ba sai ta ja bakinta tayi gum, mata kawai matsoraciya malam" Dai dai nan driver ya shigo compound din da motar yayi parking Ummi ta bude motar ta sauka, rungumeta Maimoon ta tafi tayi tana murmushi tace "Sannu da xuwa Ummi" Abuturrab kam sai kallon Ummin nasa yake don ko hanyar gidansa kam bata ta6a xuwa ba sai yau, ya kuma yi farin ciki har ransa da xuwan nata, Jiddah ma ta nufi Ummi ta gaisheta da ladabi, Ummi ta sakar mata murmushi tace "Ya ku ke Jiddah, ya gida?" jiddah tace "Lafiya lau Ummi" sauran kawayen Maimoon ma duk suka gaishe da Ummi, Hajja dai taki hakura sai tsine ma mai gadi take tana nuna sa da d'an yatsa wai shi ma sai an masa abinda ya mata a bakin gate, Abuturrab sai danne dariyarsa yake don kawai tsayawa mai gadin yayi yana kallonta kamar ya ga sabon kamu, Abuturrab yyi kasa da murya yace "Yi hakuri Hajjaj xa a canxa sa in sha Allah, wanda kuma xa a canxo xa a duba kwakwalwarsa" Yasan hakan kadai ne xai sa ta hakura, Hajja ta wani sauke ajiyar xuciya tace "To ko da na ji, amma wllh ba a ta6a ci min mutunci irin na yau ba, har kuka sai da nayi a xuciyata, to wannan fitina da axababben walakancin har ina" dariya Abuturrab yayi ya nufi Umminsa yayi mata side hug a hankali yace "Welcome Ummi" ta hade rai tayi masa kallon gefen ido tace "Meye haka?" Dariya Maimoon ta dinga yi, Jiddah dai ta nufi Hajja ta gaisheta cikin sanyin muryarta, Maimoon na washe hakora tace "Hajja ga motar Jiddah, yaya ya siya mata..." Hajja ta juya da sauri ta kalli motar, ta kai minti daya tana bin motar da kallo, sai kuma ta saki wani kabbara tace "Shi Abuntural din ya siya ma Jiddah wannan xukekiyar mota?" Cike da farin ciki Maimoon tace "Wllh kuwa Hajja, yanxun nan aka kawo motar" Ummi dai sai kallon Abuturrab take da mamaki but deep down she is so happy for Jiddah, Hajja ta rike kanta ta kuma sakin wani kabbara tace "Wayyo wayyo, to ko dai na kyautan budurci ne wannan xukekiyar mota ba mu sani ba? Banda haka me yasa bai siya ma Nanisa kazama ba duk xamansu tare, to ko a bazawara ya aureta bamu da labari...." Ummi dai tayi hanyar entrance din gidan bakinta alekum, Maimoon ta bi bayanta da sauri tana kunshe dariyarta, Hajja na kallon Jiddah da ta kasa dago kanta tace "Toh wllh wlh ki kama mijinki ki rike gam yana sonki so ba na wasa ba, da kyar ake samun miji irin Aliyu a wannan xamanin na yan banxa da en iska, ki rikesa ya xama uwarki da ubanki, shine gatanki a nan duniya dai, kishiyarki kuma...." Shiru Hajja tayi jin tarwatsewan abu a cikin gidan, duk suka kalli entrance din gidan, Hajja na gwale ido tace "Ruwa xa ayi ne ba hadari, naji kamar tsawa" Wani tsawan glass din suka kuma ji, Abuturrab ya nufi cikin gidan da sauri... Upstairs Abuturrab ya dinga jin tarwatsewan glasses, Ummi da Maimoon dai na tsaye parlon suna kallon sama su ma, haurawa yayi Maimoon ta bi sa da sauri, Hajja na xare ido ta labe daga balcony tana leko parlon, Jiddah ma dae na tsaye gefen Hajja gabanta sae faduwa yake, kawayen Maimoon dai dama gate suka nufa gaba daya, still Abuturrab yayi bakin room din Jiddah with mouth agape yana kallon Aneesah da tayi kwatsa kwatsa da mirror ta tarwatse duk kwalaben gaban mirror din a kasan tiles, sannan press din dakin ma tayi kaca kaca da madubin jiki, ko ina a kasan tiles din dakin glass ne a kwance da drop din jini, furniture din gadon ma duk ta mummuka masu katon ta6aryan hannunta, daga hannun nata har kafanta jini ne ke diga kasa, gashin kanta duk a baje kamar sabon kamu sae wani huci take, da gudu Maimoon ta sauka kasa tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..." Ummi da hankalinta yayi mugun tashi tace "Me ke faruwa haka?? What's happening?" Maimoon bata tsaya ba Ummi amsa ba ta nufi kitchen da gudu ta dubo wani tabaryan, ko ta kan Ummi bata bi ba balle Hajja ta haura sama tayi hanyar dakin Aneesah, sae dae kash taji dakin a kulle an sa makulli... Abuturrab yayi ma Aneesah tsawa for d second time kamar Zaki yace "Nace me kika aikata haka Aneesah?? Are you mad??" Ta juya tana kallonsa da idanuwanta da suka koma kamar garwashi tana huci, sae kuma ta fashe da wani dariya tace "Dakin amaryarka na tarwatsa kaga nima sae ka tarwatsa ni... babu fetur ne da wllh wuta nayi niyyar cinna ma dakin without minding ko da ita a ciki ko babu, Aliyu shigo ka kasheni shine hukunci mafi ma'ana da ya kamata ka yi mani ka huce, nayi hakan ne don ka kasheni kawai, ba dai dakin Jiddarka na mayar haka ba, come in and take revenge, nace shigo ka dau fansa..." Tana fadin haka ta nufesa a guje jini na xuba jikinta ta cakumosa tayi wani ihu kamar xata tsaga gidan tace "Ka dau fansa nace Aliyu, dakin matar so fa na mayar haka, wai ma uban wa ya haifeka da xaka ke walakanta ni don ka auri warce aka yi ma like like aka kawo maka, har ni xan xama abar walakancin ka?? me matsiyaciyar ta fi ni da shi banda rashin asali da kauyanci????" Bata gama rufe baki ba ya dauketa da wani wawan mari ya shaketa sannan ya bugata da bango ya kuma kai mata wani marin, tayi taga taga xata fadi har sannan jini na xuba sosai daga jikinta, duk jirin da take gani haka ta dinga kunduma masa xagi da shi da Jiddan tana ci gaba da fashe fashe a dakin, juyawa yayi ya nufi bangarensa direct kamar xai tashi sama, Maimoon ta hauro sama tare da Hajja da jikinta ke bari, Hajja na leka dakin Jiddah suka yi ido hudu da Aneesah dake huci, ta fasa wani ihu a gigice ta sauka kasa ta nufi kofar fita parlor tana cewa "Huhuhu.... Idan nayi magana sae a dinga min kallon er ta'adda, idan nayi magana sae a maidani salubabbiya hotiho, wayyo Allah!!! Wato tun daga ranan da nayi arba da Aneesah a gidan Usman tana amarya nasan ba lafiyayya bace a kwakwalwa, ni nasan sabuwar kamu ce, wllh tun daga ranan nasan ta6a66iya Aliyu ya auro na dai ja bakina ne nayi shiru, to duk ba wannan ba don bai dameni ba.... amma me??? kai kana ganin kazantarta kasan da ta6in hankali a tare da ita, don me lafiya baxae yi wannan kazanta da take yi ba, to yau dai hauka muraran ya ta66ata a gidan Aliyu, wayyoo jama'a, babu dawanau ne a kaduna stey? Duk girman kaduna babu dawanau ne?" Fita tayi parlon tana kwala ihu tana cewa "Masu gadi ku kawo dauki, jama'an anguwa ku kawo dauki, masu gidaje a anguwan nan ku taimake mu ku kawo dauki, jikana ya auri mahaukaciya bamu sani ba...." Mai gadi ya ja gefe da sauri yana kallon Hajja baki bude, wata mota taga ke tahowa ta sa hannu bibbiyu tana tsayar da motar cikin daga murya tana cewa "Wayyo ku kawo mana dauki, ni daga Masar nake ban san wani gidan mahaukata a kaduna ba wllh" motar ta tsaya, aka sauke glass din baya da gaba, wata mata da baxata wuce shekaru hamsin da biyar ba ta bude motar ta sauko da sauri tace "Lafiya kaka, me ke faruwa?" Tana magana ne tana kallon gidan don a xaton ta gobara ne, Hajja ta fashe da wani matsanancin kuka tace "Wllh matar jikana ce ta haukace mu kuma bamu san dawanan Kaduna ba" Matar ta xaro ido tace "Subhanallah, a nan gidan take?" Hajja na kuka tace "Wllh kuwa, daga Masar nake ban san dawanan garin ba" Wanda ke driving din motar ya sauko shi ma jin abinda Hajja ke cewa yana kallonta da mamaki, dattijuwar matar tace "Toh me gidan fa?" Hajja tace "Wani me gida?? Ai yana ciki ya rasa yanda xai yi da ita duk ta rotsa kaf kayan gidan tayi kwatsa kwatsa da shi har kayan kallo" Guy din da ya sauka daga motar ya shiga cikin gidan Hajja ta bi bayansa da gudu tana cewa "Ku taimakemu mu daureta kafin a mika ta gidan mahaukatan" Matar ma ta bi bayansu xuwa cikin gidan, Basu tadda kowa parlon ba, Hajja ta nuna masa hanyar stairs tace "Suna can sama, ka lallaba ka haura" Mahaifiyarsa dai na tsaye ya juya ya kalleta tace "Be very Careful Aliyu" Hajja tace "Ehh wllh gidan Aliyu ne ashe kun san sa, ai jikana ne, ni na haifi ubansa, ko ba wani matukin jirgin sama ba" Wanda aka kira da Aliyu dai ya haura sama bai tsaya ba Hajja amsa ba, Hajja ta bi sa da sauri jikinta na rawa, Ummi ce tsaye corridor ta amshi takarda da biron hannun Abuturrab cikin fushi take cewa "Baka da hankali ne ina magana kana magana Aliyu? Ban isa da kai bane kake son ka nuna min" Abuturrab ya juya kawai ya nufi bangarensa xuciyarsa na tafarfasa, Hajja na kallon Ummi kamar yanda Ali da mahaifiyarsa da suka hauro sama suka tsaya suna kallonta, a hankali Hajja tace "Ya dauretan ne?" Bata jira me Ummi xata ce ba ta leka dakin taga Aneesah tsaye sai huci take har sannan tana rike da tabarya, Jiddah da Maimoon suna can karshen corridor din sai kallon Ali dake tsaye da mum dinsa Jiddah take sai dai shi bai ganta ba, meanwhile ita kuma mahaifiyar Alin sai kallon Jiddah take, Ummi ta tsaya kofar dakin tana kallon Aneesah tace "Ajiye abun nan na hannunki ki fito" Jefar da tabaryan Aneesah tayi ta fito dakin, bata kalli kowa a cikinsu ba ta nufi dakinta kamar xata tashi sama, cikin daga murya Hajja ta dinga cewa "Allah ya tsine maki albarka shegiya, in sha Allahu karshenki ya xo a gidan nan tunda kika ta6a kayan Jiddah, biliyoyi aka kashe kafin ayi mata wannan kayan, don haka ko waye ubanki a Habuja yau sai an kai ni wajensa idan ma bara xai fara ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login