Showing 159001 words to 162000 words out of 346625 words

Chapter 54 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

lafiyayyen lace, Sounding so fed up Maimoon tace "Wllh ke dai Jiddah kina da matsala, duk a nan wa kika ga ya wani dau mayafi xai yafa? ba fa a sa mayafi a kan irin wannan shigan wllh, tun daxu kike ta bamu matsala kin kama kin wanke make up bayan kowa na rike da alwalansa ke kince baki san xance ba, da ba don Hajja ba yanxu ai baxa ki samu wani make up din ba..." Jiddah da taki sauraronta tace "Ni dai baxan iya fita haka ba..." Maimoon ta fixge mayafin tace "U will just look odd among us, kawai fa mota xa mu shiga a ajiye mu a wajen mu shiga, idan xa mu dawo ma mota xa mu hau a dawo da mu gida ba wai titi xa mu bi muyi ta tafiya a kafa ba" Jiddah ta dinga kallonta alamar ita fa bata gamsu ba, duk kawayen amarya dake wajen kallon Jiddah kawai suke, irin kyan da tayi ba don anko ne jikinta ba bbu wanda dama xai ce ba ita bace bride din, ita Aneesah dama can dakin Aunty aka kai ta ana shiryata, Jiddah ta ta6a jelan tulin gashinta da ya leko ta head din tace "Yanxu har gashina haka xan bar shi a waje?" Wani harara Maimoon ta watsa mata tace "Ae kuma sae kiyi...." Daga haka ta nufi wayarta dake ring, Jiddah ta bi ta da ido, bude baki Maimoon tayi da mamaki tana kallon screen din wayarta, can ta nemi waje ta xauna a hankali tace "Toh wai ni me nayi ma Yaya Aliyu?" Sae da ya kusa katsewa ta daga ta kai kunne ta marairaice murya tace "Na'am Yaya?" Yace "Kuna ina?" Tace "Mun shirya xa mu fito yanxu" Yace "Ke da su wa?" Tace "Ni, Aunty Safiyya, Aisha, Sister Ramlah, Nafisah, Jiddah da wasu baki yan mata biyu?" Yace "Duk wani mota ne xai kwashe ku haka?" Ji tayi kamar tayi kuka ta dai dake tace "Aa dama saurayin Aunty Safiyya ne xai kai mu don ba mota" Yace "Duk ku takwas din mota daya xai kwasa?" Ta murguda baki tace "Aa Yousuf ma ae xai xo yace yana hanya" Abuturrab ya xauna da kyau a kan driver seat din da ya d'an kwantar yace "Shi kuma wa xai dauka?" Tace "Aa kawai dai xai xo tunda mota daya baxai ishemu ba, sai ya dauki duk wanda xai dauka" yace "Wa ya kira Yousuf din?" Tace "Waya suka yi da Jiddah" Abuturrab yace "Ohk... Idan kun kusa sai ki kirani xan baki ajiya ne" Tace "Toh" yace "Aneesah da frnds dinta sun bar gida ne yanxu?" Maimoon tace "Aa ba a gama shiryata ba" Yace "Ohk ki tabbatar basu riga ku fitowa daga gida ba in baki sakon da nace" A hankali tace "Toh" daga haka ya katse wayar, Maimoon ta wani turo baki tace "Toh wai ni me ya hadani da shi ne yau yake ta kirana haka" Jiddah dai bata ce komai ba ta karasa cusa mayafinta a jaka kafin Maimoon ta farga, kamar yanda ya fada Maimoon ta harhada tawagarsu ta kannin ango suka fito don Saurayin Safiyya ya iso, Safiyya da su Aisha da Ramlah suka shiga motarsa, Maimoon na ganin kiran Yousuf ta daga nan ya sanar masu ya iso, Babu yanda Jiddah ta iya haka ta shiga gaban mota, gaba daya a kunyace take saboda shigar da tayi, Maimoon dai ta shige bayan mota da Nafisah da wasu yan matan biyu, Yousuf ya amsa gaisuwansu gaba daya yana murmushi, bayan sun hau saman hanya ya d'an kalli Jiddah murya can kasa yace "Me yasa kika fito haka Jiddah?" Tana wasa da jakarta dake kan kafarta ta girgixa masa kai kawai, bai kuma cewa komai ba, sai da suka kusa event center din wayar Maimoon ya fara ring, tana ganin me kiranta ta jinginar da kanta da kujeran motar murya can kasa tace "Na shiga uku" Can dai ta daga ta kai kunne tace "Na'am yaya" Yace "Kuna ina?" Tace "Gashi mun kusa muna hanya" Yace "Ke da wa?" Tace "Nafisah da wasu yan uwan Aunty" Ya xauna da kyau yace "Sai wa?" Ta kalli Jiddah dake gaban mota tace "Jiddah" yace "Ohk, idan kun sauka ke da ita ku taho parking space xan bar fitila a kunne yanda xa ku ga motata" a hankali Maimoon tace "Toh" ya katse wayar. Yousuf na parking ya juya yana kallon Jiddah yace "I am not happy at how u dress today" Ta kallesa, Maimoon da ta galla masa wani harara ta fara kokarin sauka motar tace "Toh mun gode yaya yousuf, Jiddah mu je mu amso sakon...." Daga haka ta sauka, Jiddah na kallonsa a hankali tace "Kayi hakuri, mayafina na cikin jakana xan saka" Yace "Toh saka yanxu" Ta d'an kalli Maimoon dake tsaye ta wani sha kunu tana jiran saukowarta, Tace "Xan saka da gaske idan na sauka" yace "Wani sako xaku amso?" Jiddah ta buda hannu tace "Nima ban sani ba" Yace "To karfe nawa xan dawo daukanku?" Tace "Kai dama ba dinner din ka xo ba?" Ya girgixa kai yace "Aa ba shi na xo ba, anjima idan kun gama ki kirani in maida ku gida" Tace "Toh" Maimoon tace "Jiddah ya fara kira fa..." Jiddah tana kallon Yousuf tace "Toh xan kiraka mun gode" Ya bi ta da ido har ta sauka, tuni dama su Nafisah ma suka sauka, ya ja motarsa ya bar wajen.. Maimoon na dialing number Abuturrab ya daga yace "Wai baki da hankali ne kin bar ni mota Ina jira tun daxu??" Buda baki tayi, sai kuma ta hade rai tace "Ai ban san wani parking space din bane kayi parking" yace "Na dama idan kin shigo wajen... Kar ki bari in sake kiranki wllh" ta murguda baki tace "Ohk" daga haka ta katse waya, cike da masifa tace "Ni fa bana son harka da yaya Aliyu wllh, ni ban san inda ya samu number na ba, gashi sai kirana yake yi ni dai yana damuna, sae kace yanxu ba ni na kirasa ba" Nafisah tace "Toh ni dai xan jira bakin hall tunda gate pass dinku na wajena baxan je wajen ya Aliyu ba mood dina ya baci" daga haka ta wuce, Maimoon na kallon Jiddah tace "Toh kin tsaya mu tafi mana, masifa fa yake ta yi" Jiddah tace "Toh wai ni sai na bi ki?" Maimoon tace "Cewa yayi ni da ke mu taho ni dai kar kisa yayi min jaraba mu tafi ya bamu tsiyar da xai bamu mu shiga hall, gashi can ana ta yi ba mu" Jiddah dai bata ce komai ba ta bi bayanta amma ranta bai so ba, tun daga nesa Abuturrab ya hangosu da yanda duk attention din maxa ya koma kansu, ya xauna da kyau yana kara kare masu kallo kamar wanda ya ga wani mugun abu, gaba dayansu kuma takalmi me heel suka saka, Maimoon na isa dai dai parking space din ta tsaya jikin wata mota ta fara kiransa a waya tana cewa "Ni wllh abun nan duk ya isheni, gashi sai jaraba yake ma mutane a waya kamar me" Yana fara ring ta murguda baki tana gunguni, duk Abuturrab na kallonta, sai da kiranta ya shigo wayarsa snn ya dallara masu fitilar motarsa, Maimoon ta saita fuskarta tana kirkiran murmushi bayan ta hangosa cikin motar dake nesa da su sosai, ta kalli Jiddah tace "Mu je gashi can" Bin ta Jiddah tayi suka nufi motar dake can ciki sosai, sauka yyi daga motar yana kallon Jiddah daga sama har kasa, haka nan taji gabanta na faduwa taji kamar xata gurde kafa ta fadi, komai na shape din jikinta sai da gown din ya bayyana, suna kusa dab da shi ta makale jikin mota taki yarda ta karasa, Maimoon ma da ta sha jinin jikinta ganin kallon da yake masu ta tsaya d'an gaba da Jiddah tace "Yaya wani sako xaka bamu?" Calmly yace "Xo ki amsa" Ta dake ta karasa gabansa, xuciyarta na bugawa, ya kalli Jiddah yace "Ke can xan biyoki in baki?" Ta ki yarda su hada ido ta karaso gefensa a hankali ta tsaya, Yana kallon Maimoon da kyau yace "Wato don na kira ki nace xan baki sako shine kike murgude murgude kike xagina baki san duk ina kallonki ba" Ta xaro ido tace "Wllh ban xageka ba yaya neman..." Gwabje mata baki yyi da karfi, ta kai hannu bakinta da sauri tana kallonsa, ya hade rai yace "Bace gabana kar in taka ki..." Juyawa tayi ta bar wajen kamar xata tashi sama, Jiddah gabanta ya hau faduwa ta bi Maimoon da kallo, lkci daya ta juya da sauri kamar ya san abinda xata yi ya fixgota, tayi narai narai da ido tana kallonsa amma ta kasa cewa komai yana ganin ynda kirjinta ke heaving, strictly yace "Tun daga gida kika fito a haka da wannan shegun kayan?" Ido ta kafesa da shi, cikin tsawa yace "Ba magana nake maki ba?? Ke wato kina ganin matsayinki daya da su Maimoon ko?" Bata ce masa komai ba taga ya fixgota ya xaga ta daya side din motar ya bude back seat fuska daure yace "Shiga" Ta fashe da kuka tana kokarin kwace hannunta tace "Ni me yasa baxa ka daina takurani ba, bayan kace...." Bata rufe baki ba taji saukan mari, ta dafe kuncinta, bayan few seconds ta dago kai tana kallonsa ko kiftawa babu, turata yyi cikin motar yayi banging door din, ya xaga xuwa driver seat ya dau wayarsa dake ta ring sannan ya kulle motar dake a kunne ba tare da ya kashe Ac dake aiki ba ya bar wajen walking majestically, ta bi sa da kallo hawaye masu xafi na sauka idonta. Wani kallo Ahmad ya dinga masa yana wondering daga ina yake, don tuntuni suke ta kiransa amarya ta iso su shiga hall amma no answer, Aneesah dake xaune cikin mota dae sai kallonsa take don ba karamin kyau yayi mata ba, sai da ya karaso sannan aka bude mata motar ta fito tana kallonsa tana murmushi, tsayawa yayi gefenta ya d'an hade rai murya can kasa yace "Wannan kwalliyan fa kamar jan laka" tayi kasa da murya a hankali tace "Jan laka kuma Baby? Kana nufin ban yi kyau ba" Yana gyara hularsa yace "Aa baki yi ba gaskiya, u look odd" Ko ba a fada ba xaka san bata ji dadin abinda yace ba don nan da nan fara'arta ya gushe, kuma duk yana lura da hakan, hannunta ya rike cikin nasa a hankali yana murxawa yana murmushi yace "Wasa nake, you look sweet, u look like a... Quee..." Sai kuma yayi saurin cewa "Princess, yes my princess" Wani murmushi tayi tace "Aa queen din dai, the queen of ur kingdom my king" Yace "Noo princess din dai" Duk kasa kasa suke firan nasu gwanin sha'awa a wajen, har dai daga karshe Mc ya bukaci shigowarsu da frnds dinsu cikin hall din. Wajen Dinner kam ya cika, kuma ya hadu iya haduwa, abun ya kawatar da jama'a sosai, babu abun ciye ciyen da babu a wajen, iyayi kuwa wajen kawayen amarya ba a cewa komai, sai kai komo suke a inda El-Basheer ke xaune, idan ba kusa da shi ka je ba sae ka rantse balarabe ne xaune wajen, shi kam banda danna wayarsa babu abinda yake lkci lkci ne yake dago kai, Ahmad da ya kallesa sai yyi murmushi don yasan El-Basheer ya take Abuturrab wajen miskilanci, kuma in kaga yayi shiru haka to abu bai masa ba, bai burgesa ba ko kadan.... Irin rawan da Aneesah ta tika sai ya sa ka fara tantamar anya kuwa ita ce amaryar, cire kunya tayi abunta ta sha rawarta don a mentality dinta abu ne sau daya a lifetime, ba wani dinnern xata sake ba gwara tayi enjoying day dinta, su Aunty kirjin biki sai ji ake da jama'a ba a can ba a nan, daga yatsunta har kunne xuwa wuya gwalagwalai ne, Ummi ce kawai da Hajja basu je wajen ba amma har mahaifiyar Aneesah da kakarta sun xo dinner din daga Abuja, kaf family dinta babu wanda bai hallaci wnn dinner ba, shi ko uban gayyan was absentminded all through, Har Aneesah ta d'an cunkulesa a kafa tace "Wai tunanin me kake ne haka Babyna, naga kamar hankalinka baya tare da kai" Ya kalleta yace "Na gaji ne mana... abu kamar baxa a gama ba, this is going to 2hrs now" Turo baki tayi tace "Toh ko kwana xa ayi meye a ciki? ranan farin cikinmu ne fa, kuma sau daya xaka yi hakan a rayuwarka, ba wani dinnern xaka sake ba" ya kalleta bai dai ce komai ba, shi dai El-Basheer tun da aka shigo wajen ya baxa idon inda xai ga Jiddah amma bai ga alamarta ba, an kira kannin ango fage sun fito sun taka rawa anyi hotuna amma babu ita a ciki, can ya hango Maimoon sai tikar rawa take da su Nafisah as if their life depends on it, dangin amarya da aka kira ya sa suka bar stage din, El-Basheer ya mike ya nufi Maimoon kafin taje ta xauna tana ganinsa ta washe baki tace "Yaya Bash ba mu yi hoto ba" Yace "Xa mu yi, where is jiddah?" Ta d'an bude ido, sai kuma tace "Oho ni dai daxu Ya Aliyu yace muje mu amshi sako... Kuma ni na rigata shigowa hall, tun daxu nake dubata ban ganta ba wllh" yace "A ina Aliyun yace ku amshi sako?" Tace "Daxu ne a parking space, to ko gida ta kai masa sakon, ni dai ban sani ba, nayi ta duba ta ban ganta ba wllh" Bai ce mata komai ba ya koma ya xauna, Sai kallonsa kawai Abuturrab yake kamar yasan tambayar da yaje yayi ma Maimoon.... Sai karfe goma da wani abu aka tashi dinner din, outside d hall Abuturrab ya shafa kansa ganin motar da aka ajiye masa shi da Aneesah da xai maidasu gida, Ahmad na kallonsa yana jiran jin me xai ce don ya san da magana a bakinsa, Abuturrab na kallon Aneesah yace "Get in" Shiga motar tayi ya daga mata gown dinta dake jan kasa ya mika mata, ta amsa tana murmushi tana kallonsa, shiga motar yayi shi ma, Najeeb ya shiga driver seat ya tada motar suka fita hall din... kawayen Aneesah suka shiga motar Ahmad yayi gida da su su ma, Dai dai kofar gidansu Abuturrab Najeeb yayi parking, Najeeb yace "Xa mu jira frnds dinta yanxu sai su shiga da ita ko?" Abuturrab yace "Aa ba sai mun jirasu ba, ba dai kawai shiga ciki bane" cike da shagwaba Aneesah tace "Don Allah Baby ka jira su iso ni kunya nake ji wllh, sai su Ummi su ganmu haka mu biyu ai da kunya" wani kallon gefen ido yayi mata bai ce komai ba ya bude motar ya sauka, Najeeb couldn't help it but laugh ganin da gaske wucewa ciki Aliyu xai yi yace "Captain plss ka jira frnds dinta su xo xai fi" Abuturrab yace "Noo ai na barta ta jirasu, i have to go and ease my self" Daga haka yayi wucewarsa, Aneesah da ta sha kunu ta bi sa da wani irin kallo.... Can backyard din gidan Abuturrab ya tafi ya ja kujera ya xauna yana jiran su shisshiga, lkci lkci yake kallon agogon wrist dinsa, bayan some minutes ya mike ya fita gidan, da kafa ya karasa bakin hanya, ya samu adaidaita ya koma can wajen event center din, har sannan da akwai mutane wajen, kansa a kasa ya nufi parking space wanda motoci sun ragu sosai, direct gun motarsa ya nufa ya ciro makulli ya danna lock din motar snn ya bude back seat, xaune ya ganta ta hade kai da gwiwa kamar mai bacci, tana jin an bude motar ta dago da sauri, bayan ja har kumbura sai da idanuwanta suka yi don kuka, ta sauke kanta kasa yace "Fito" Ba musu ta fito daga motar ba tare da ta kallesa ba, fixgo hannunta yayi ganin wucewa xata yi, ta fashe da kuka sosai tana kiciniyar kwace hannunta tace "Ni ka kyaleni, ka sake min hannu" Kalle kallen wajen ya fara yi ganin jama'ah xata tara masa, ya ja ta xuwa daya side din wanda akwai wata mota a parke, ya jinginar da ita da motarsa yace "Baki da hankali ne kike cewa in kyaleki" kuka kawai take tana fixge fixge taki yarda ta kallesa, tsawa yayi mata yace "Ba magana nake maki ba" Ta kuma fashewa da wani kuka tace "Ni wllh ka sakeni... Ban son haka" da ta ga baxai saketa din ba ta kai bakinta kan hannunsa xata gatsa masa cixo ya xaro ido ya saki hannunta lkci daya ya rungumota jikinsa, nan ma ta hau kiciniyar kwace jikinta amma ta kasa, hakan yasa ta hakura amma bata fasa rusa masa kuka ba kamar ranta xai fita, kukan da take kuma bai hanata jin yanda xuciyarsa ke bugawa ba, lkci daya ta jika masa shaddar jikinsa da hawayenta...




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




*Free delivery anywhere*

It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;

Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login