Showing 189001 words to 192000 words out of 346625 words

Chapter 64 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

Umma tace "A gaida Ramlah" daga nan suka fita gidan, Suna shiga motar Ahmad yaga missed calls din Abuturrab har uku a wayarsa da ya bari a cikin mota, Sai da ya tada motar yyi reverse sannan yayi dialing number Abuturrab din, yana dagawa Ahmad ya kai kunne yace "Ya aka yi?" Dariya Ahmad yyi yace "Ni fa wllh kana bani mamaki Captain, ga dai matarka ka bi ka takurani in maka prescription drug? Are u even okay?" Jiddah dake xaune gefensa cikin motar taji gabanta ya fadi jin sunan da ya ambato, Ahmad yace "Toh ka taho gida ka amsa, ina driving yanxu..." Daga haka ya katse wayar yana maida hankalinsa kan titi, sai da suka yi nisa yace "Kin ma san gidana kuwa Jiddah?" Ta kirkiri murmushi tace "Um na sani, mun je sau uku" Yace "Would u like to stay in my house ki dinga xuwa makaranta daga can?" Jiddah ta d'an buda ido ta kallesa, yace "Yea, sai ki xauna ke da Ramlah koh??"



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




MG'S SKINCARE

In akaji gangami labarin kidane,sun shahara sun tumbatsa sunkai sunwuce tunanin duk wani meson Adama dashi aharkar gyaranfata d walwalinta,

Yar uwa haske ko qyalqyale kikeso kiyi Abu yaci tura?
Kyan fuskarda ko yar uwarki mace kance dama dama kikeso?
Kokuma ke kuraje d tabbuna suka lahanta mki fuska har ake ganinki d wani idon n daban,
Nankarwace tayimiki zanen kura a kyakyawar fatarki?
Kokumade Mai kikashafa be amshekiba yasa duk kika koma ruwa biyu Nan fari Nan baqi?

To duk kuzo insha Allah kudai naku y qare gdan kukazo,

Munkawo shahararrun kayangyaran jiki
Sabulu,
Man shafawa,
Man fuska,
Scrub,
Cleanser,
Glow oil,
Dukdan qawarmaku d matsaltsalunku,

Da 11k kachal zatasa kihaske kizama kalar madara qirar models,

Set 11k
Sabulu 3k
Student package:7k
Munakuma bayarwa in pieces duk afarashin mesauki.kayanmu bbu fariya ko tutiya angwada andawo,ankumayi farinciki d hkan,Kuna iya samummu d wadannan numbobin,
WhatsApp,
08062991549 or 07046881166 or 07067210195
Call only
08064532391
Instagram: glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Idanba wadannan numbobinba to gaskiya b mg's bane, available in Kaduna and Kano only, thanks for always trusting us,our returning customers we really do appreciate wadanda sukeda burin Siya munamaku fatan alkhairi ubangiji ybaku yenda zakuyi,Allah Kuma yqaro mna dukiya me amfani ta hanyar halalinmu.


Murmushi kawai Jiddah tayi bata ce komai ba, Ahmad bai kuma ce mata komai ba shi ma, suna isa wani babban pharmacy yayi parking yana kallonta yace "I am coming let me get u pain reliever, Umma tace kina ciwon ciki ko?" Ta gyada masa kai ya kashe motar ya sauka ya shiga cikin pharmacy din, ba a wani dau lkci sosai ba ya fito da ledan magani, ya shiga motar yana kallonta ya ajiye mata kusa da ita yace "Ko kina bukatar wani abun daban, akwai Supermarket a nan..." Ta girgixa kai tace "Aa bana bukatar komai" Yace "Ohk" sai da suka hau saman titi ta d'an kallesa amma bata ce komai ba, ganin haka yace "Say what is in ur mind Jiddah, be free with me and take me as ur elder brother" Ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Ni yanxu baxan iya xuwa in ga Baabarmu in gaisheta ba?" Da d'an mamaki yace "Baabarku? Me xaki yi mata idan kinje, ko kuma me xata maki ita?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Babu amfanin xuwa wajenta a yanxu dai Jiddah, idan kinyi hakuri wataran babu wanda xai hanaki xuwa gareta, when the rightful time comes da kanki ma xaki je ba sai wani ya kai ki ba kin ji?" Cikin sanyin murya tace "Toh, amma kuma akwai wata tsohuwa a layinmu ana ce mata Iyah, tana da kirki sosai, ko ita ma baxan iya xuwa in gaisheta ba?" Yace "Baki tunanin xata gaya ma Baabarku kin je?" Ta girgixa kai da sauri tace "Aa baxata fada ba, ai ita ba haka take ba, ita ce fa ke taimakona lokacin da nake gun babarmu, har abinci tana bani idan tana da shi" Yace "Toh yanxu kina son a kai ki can kenan?" Ta gyada masa kai a hankali, ya d'an yi shiru yana ci gaba da driving dinsa, kallon agogon wrist dinsa dake nuna karfe hudu da wani abu yayi, sannan yace "Kinsan me Jiddah?" Jiddah na kallonsa ta girgixa masa kai, yace "Ki bari ko gobe da daddare in kai ki, tunda kina gidana, i think it will be more safer..." Jiddah tace "Toh nagode" Yayi mata murmushi kawai. Suna isa gidansa yayi parking a space din parking sannan ya sauka motar ita ma ta sauka, tana biye da shi suka shiga gidan, Xaunawa tayi a parlor shi kuma ya wuce bedroom dinsa sanin Ramlah na can tana bacci, xai shiga dakin sai gata ta fito, ya d'an buda ido yace "Ashe ba bacci kike ba" Ta turo baki tace "Ina ice cream din?" Yace "Ohh kinga na mance wllh, I'm sorry anjima xan fita sai in siyo maki, fito ku gaisa da Jiddah" Ramlah tace "Da gaske?" Yace "Ehh" a tare suka dawo cikin parlon, Ramlah ta xaro ido tace "Lallai sis Jiddah ce yau a gidanmu, ashe xa ayi ruwa da kankara" Jiddah tayi murmushi tace "To ai ina xuwa" Ramlah ta karaso ta xauna kusa da ita tace "Aa sau biyu ina ga kika taba xuwa, ina fa sane, to ya su Umma?" Jiddah na murmushi tace "Lafiya lau, ya jiki?" Ramlah tace "Naji sauki Alhmdlh" mikewa tayi ta dau jakar Jiddah tace "Mu je ciki to" Jiddah ta mike ta bi bayanta, Ramlah ta kai ta dakin visitors, sosai Ramlah taji dadin xuwa Jiddah gidanta, Ramlah tace "Gashi ni banyi girki ba wllh, ko in dafa maki indomie kafin a daura dinner?" Jiddah tace "Daga gida fa muke, ai na ci abinci" Ramlah tace "Toh bari in kawo maki ruwa" Bata jira cewar Jiddah ba ta fita dakin, sai da Ramlah ta daura ruwan shinkafa a gas snn ta dau tray ta daura Chivita drink da ruwan gora sai glass cup ta dawo daki ta ajiye tana kallon Jiddah tace "To ga ruwa ki sha sis Jiddah" Jiddah ta d'an yi murmushi tana kallon hancinta dake shige da na Abuturrab, har idanuwansu iri daya ne, dama kuma duk a cikinsu ita tafi kama da shi, Ramlah ta xauna tana ta jan ta da hira, tun Jiddah na shiru shiru har dai ta fara biye mata, lkci daya Ramlah tace "Ohh na manta na daura ruwan shinkafa a gas, bari in xuba shinkafar in dawo" Jiddah tace "Toh bari in wanke in xuba maki" Ramlah ta nufi kofa da sauri tace "Aa wllh... Ai ba wani aiki bane" Daga haka ta fita, xaune ta tadda Abuturrab a parlor da Ahmad, Ta d'an buda ido sai kuma ta washe baki tace "Yaushe ka xo yaya?" Karasawa tayi ta duka gefensa tace "Welcome Yaya, ina yini?" Ya kalleta yace "Lafiya lau, ya gida?" Tace "Alhmdlh, ya aiki?" Yace "Fine Alhmdlh" mikewa tayi ta wuce kitchen, Ahmad dake shafa beard dinsa yana kallon Abuturrab yace "ina jin ka great Captain" Abuturrab yace "Kana jina na me wai, kai fa idan kaga mutum na neman abu a wajen ka ka dingi walakantasa kenan" a takaice Ahmad yace "Toh ka tafi asibiti kawai" Abuturrab ya dinga kallonsa, Ahmad yace "Yes, nasan kana da mata baxan rubuta maka wannan maganin da kace ba, ko dai Hygiene din ne bai kai yanda kayi expecting ba? Abu d'an sauki tunda kana da wadata sai ka kara aure kawai" Da dariya Ahmad ya kare maganar, Abuturrab dai ya kasa ce masa komai, Jiddah ce ta fito parlon rike da tray din lemon da Ramlah ta kai mata don xuwa kitchen ta taimaka ma Ramlah da girkin da tace xata yi, Tsaye tayi bakin corridor din dakunan ganin Abuturrab a parlon kafin ya ganta ta juya da sauri har tana tuntube ta koma ciki ta shige daki ta kulle kofar gabanta na faduwa sosai, Abuturrab ya kalli direction din don rufe kofa kawai yaji, can ya kalli Ahmad yace "Who is there?" Ahmad yace "Bakuwa muka yi" Abuturrab yace "Ohk" Ramlah ta fito kitchen ta ajiye masa ruwa da drink tace "Amma yaya ba yau xaka koma kano ba ko, naga yamma yayi" yace "Gobe da safe in sha Allah" Yana fadin haka ya dau bottle water daya ya bude ya sha ya mayar ya ajiye sannan ya mike yace "Sai anjima...." Ahmad dai sai murmushi yake yana kallonsa, Ramlah tace "Yaya ka tsaya ka ci abinci mana pls..." Yace "What are u cooking?" Tace "Shinkafa da miya ae bai da wahala" Yace "Idan naje can gida xan ci, yanxu gida xan wuce" Daga haka yayi ma Ahmad sae da safe ba tare da ya kallesa ba ya nufi kofa ya fita. Gidansu ya tafi, direct ya tafi bangaren Umminsa, fitowa tayi daga bedroom jin an bude kofar parlor, ganin shi ne ta koma dakin, ya bi ta har can, xaunawa yyi gefen gado sannan ya gaisheta, ta amsa tana kallonsa, bai kuma ce mata komai ba tace "Me ya hadaka da matarka?" Ya kalleta yace "Ummi ita da Hajja ce, ni ban mata komai ba wllh" Tace "Why did u create room for that, me yasa baka dakatar da Hajjar ba?" Yace "Sanda suka yi ma ni bana gidan, and na bata hakuri but she didn't listen to me tayi tafiyarta kawai" Ummi dai tayi shiru tana kallonsa, can tace "Are you okay?" Daga kai yayi ya kalleta sai kuma yayi murmushi yace "Did u notice anything mum?" Tace "Are u answering my question with a question?" A hankali yace "Kawai ki taya ni da addu'a Ummi" tace "Me ke faruwa?" Ya girgixa mata kai yace "Ba komai addu'a kawai nake bukata" Tace "Saboda ni ai bani da matsayin da xaka gaya min matsalarka ko?" Ya kalleta a hankali yace "Ko daya Ummi, ni kaina ban san me ke damuna bane" Tace "Toh Allah ya yaye maka" Yace "Ameen" Yace "Ummi in a month time xamu fita waje fa..." Tace "Xuwa yin me?" Yace "Aa wani babban mutum xa mu yi piloting" Ummi tace "Toh Allah ya kai mu, sai ku dawo yaushe?" Yace "Ban sani ba dai, sai yanda suka ce" Ummi tace "To Allah ya tabbatar da alkhairi" Yace "Ameen" tace "Yanxu ka tashi kaje ka ba matarka hakuri ka dauketa ku tafi gida tare, ba sai an sake wani xaman ba" Shiru yyi, Ummi dai na lura da shi, can yyi kasa da murya yace "Ummi Aneesah bata son xaman lafiya tare da ni, I don't know why she changed all of a sudden from who I knew her to be, kamar ana xugata kullum, kinga bata mutunta ni bata kunyar gaya min ko wani magana ya xo bakinta, sannan i wish u can come one day ki ga yanda ta mayar min da gida, kawai fa sai dai tayi wanka ta fesa turare abinda ta iya kenan, tsaftace muhalli Zero, girki Zero, ibada Zero, kullum sai nayi fama da ita a kan sallah, I'm so tired and fed up Mum, ko wata biyu fa ba ayi ba, har xullumin dawowa weekend nake wllh Ummi" Ummi da tayi shiru tana kallonsa taji tausayin d'an nata amma taki nunawa, can tace "Toh me yasa baxa ka daukar mata mai aiki ba?" Da sauri ya kalli Ummi yace "House help kuma Ummi? Warce ta xauna kafin ita a gidan duk da karancin shekarunta da rashin wayewarta ai ban daukar mata mai aiki ba, kuma komai na gidan ita ke yi, sannan ni ban ta6a dawowa weekend naga ba dai dai ba" Ummi dake kallonsa kasa kasa tace "Wacece ta xauna kafin ita?" Shiru yayi bai ce komai ba, Ummi tace "Wai Jiddah kake nufi?" ya daga kai yana kallon Ummi amma bai ce komai ba, Ummi ta tabe baki tace "Ni a iya sanina warce ta xauna kafin ita ai ba matsayin mata ka dauketa ba a lokacin ko? Wannan kuma matarka ce ta sunna...." Shi dai bai ce komai ba, Ummi ta ci gaba tace "Don haka sai kayi hakuri da duk abinda ka gani, da yanda ka gani, na farko dai ba wani ya nemo maka yarinyar nan yace ka nemeta ka aura ba..." Ya marairaice mata yace "Ummi to ai ni da muka hadu da ita da farko ba wai soyayya muke ba, kuma ni ban ta6a tunanin xan ma aureta ba, kawai dai ta kan kirani mu gaisa ne time to time, sai kuma WhatsApp chat, a airport din Abuja muka hadu taje gun uncle dinta, ni kuma mun sauke jirgi, and she requested my digit na bata kawai don ban iya walakanci ba, sai kuma coincidentally na dawo wani weekend na ganta a gidan nan ta xo gun Aunty da aunt dinta ashe Mum dinta close frnd din Aunty ce" Ummi dake ta kallonsa tace "Sai aka yi yaya? Sai aka ce ka so ta dole har ka aureta?" Yace "Aa Ummi but Aunty ce ai..." Sai kuma yayi shiru, Ummi ta tabe baki tace "Kaga Aliyu rabani da wannan labarin da na sani, yanxu dai kawai kayi hakuri ka nema mata house help, da xata dinga tsaftace maka gidan ka, sai kuma ka ci gaba da hakuri da sauran halayen nata tunda dai auren soyayya ku ka yi ba auren kiyayya ba" Bai iya yace komai ba, Ummi dai sai kallonsa take, amma can kasan xuciyarta tausayinsa take, she understands what he is going through, barin shi da yayi detesting kazanta with passion, ita har ta mance rabon da ya shigo dakinta balle har ya dade haka yana xance da ita kai tsaye, Ya d'an ja tsaki underneath his breathe yace "Karamar yarinya ma da ta kusa doubling age dinta warce ta tashi a ghetto bata irin abinda take yi na kazanta wllh, tun daga balcony nake jiyo kamshi lkcn da yarinyar ke gidan idan na dawo gida, for once ban ta6a shiga kitchen naga dirty utensils ko daya ba, ni har kunyar wani nawa nake ya xo gidana yanxu, dama a garin nake sai in dinga gyarawa ni kullum, kawai ita abinda ta sani sai tayi wanka ta fesa turare ta xauna tana danna waya, sai tara kawaye a gida" Ummi tace "Toh wai ita kuma wannan karamar yarinyar da kake sa wa a baki kake comparing da matarka meye hadinka da ita ne, why don't u face ur life ka daina mentioning dinta a lamarin ka, did she have anything to do with u again xaka sa ta a bakin duniya" Ya kalli Ummi amma bai ce komai ba, Ummi tace "Ni ka tashi kaje ka same matarka ka bata hakuri ka dauketa ku tafi gida, Allah ya ci gaba da daidaita ku, ba ruwana da matsalar cikin gidanku, it's something u should have known before marrying her" Abuturrab yace "But how mum, kullum fa fes fes xaka ganta a titi, waye xai san xata yi haka?" Ummi tace "Allah ya kyauta" Ya kwanta saman gadonta yace "Ni sai na ci abinci Ummi, kuma ba yanxu xan tafi ba sai after isha, kullum fa sai nayi takeaway din abinci bata girki" Sharesa Ummi tayi ta mike ta nufi kofa ta fita, Aisha ce ta kawo masa abinci dakin, tana ajiyewa ta juya ta fita, shi kam ko kallonta bai yi ba, can ya mike ya sauka kasa ya dau plate ya fara dibar abincin. Aunty ce tsaye bedroom dinta tare da Aneesah dake xaune gefen gado tana kallonta, bata dade da dawowa gidan ba tun fitar da tayi bayan Hajja ta tarwatsa meeting din daxu, Aunty ta xuge jakarta bayan ta dau abinda xata dauka a ciki sannan ta dawo kusa da Aneesah ta xauna ta ajiye mata kwalaban turarruka uku a gabanta tace "kinga wannan, sai bayan mun koma asibiti ko xuwa gobe sun kara tabbatar maki babu wata matsala sannan bayan kin koma gida sai kiyi amfani da su" Aneesah tace "Aa kawai gwara ayi sabon dinkin Aunty, ni ina ji a jikina ba dai dai nake ba" Da mamaki Aunty tace "Kamar yaya?" Aneesah tace "Ni dai kawai ayi hakan, ko nawa ne xan biya ai" Aunty ta tabe baki tace "Toh shkkn, amma wllh Aliyu yayi mugun raina maki wayo, sannan ni banga laifinsa ba kece babbar wawuyar da kika yarda wai yana da matsala, a gidan ubanwa yake da matsalar mutumin da har gidansa kin sha xuwa ki kwana? Ko ke duk xuwan da kike gidansa a Abuja kin ga alamar yana da matsala?" Aneesah ta tabe baki tace "Ban ta6a ganin haka ba wllh, kawai shi dai baxai yi intercourse ba sbda gudun sa6on Allah amma ba don bashi da lafiya ba ko wani abu, amma babu abinda baya min ai, ce min yayi of recent ya samu matsalar" Aunty tace "Wllh ni ban yarda da kanwar uwar nan tasa ba don ita ma waye bai san tana shige shige ba kilan taje ta hango aikinmu ne tasa aka lalata, shine yake ta maki hanya hanya..." Aneesah tace "Toh ai da kin tambaya inda kika je daxu" Aunty tace "Wllh na manta shaff ban tambayi mutumin ba, amma akwai wani da xan kira anjima a benue, xai sanar da ni komai, yanxu kuma sai ki kirgo dubu talatin na turaren nan ki bada" Aneesah tace "Ina na gansu Aunty, har yau fa nace maki kudin nan da kika ce in tambayesa sai min yawo da hankali yake, yace yau yace gobe" Aunty tace "Rabu da shi don ubansa, xa muyi maganinsa nan ba da dadewa ba, muna nan dake sai account dinsa ya dawo hannunki gaba daya" Kwankwasa kofar dakin aka yi, Aunty ta jawo pillow ta ture kananun kwalaban turaren a karkashi da sauri, Aka bude kofar Abuturrab ya shigo da sallama kansa a kasa, Hade rai Aunty tayi ta mike ta dau Hijab dinta ta saka ta shimfida darduma ta hau sallahn isha, Aneesah dai sai wani cika take tana batsewa tana danna waya, ya ja stool ya xauna ya fiddo nasa wayar yana dannawa, yana ta xaune har Aunty ta idar da sallah, sannan ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login