Showing 177001 words to 180000 words out of 346625 words
Chapter 60 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
da aka kaita chemist aka ta mata allurai, Iyah har ce mata tayi sumanta biyu. Ranan Friday da yamma Ahmad na xaune bedroom din Ummansa, ko minti talatin bai yi da shigowa ba Umma tace "Yauwa Ahmad ina son maka tambaya, Me ke janyo mace ta fara al'ada kuma ta daina sa ko ya dinga mata wasa?" Ahmad yyi shiru yana kallonta, can yace "Mace yar shekara nawa Umma?" Tace "Yarinya karama..." Ahmad yace "Irregular period kenan..." Umma tace "Oho nima ba tambayarka nake ba" Ya shafa kansa yace "Mai aure ce ko mara aure Umma?" Umma tace "Aa bata da aure" yace "That could be Hormonal Imbalance, too high or too low Thyroid hormone level, wannan shine dalilin in har mara aure ce... " Umma tace "To yana da medications ne? I mean is there anything that could be done about it?" Yace "Ehh ba xa a rasa ba Umma, amma akai ko ma wacece asibiti xai fi" Umma tace "Toh Shikenan" Bai kuma cewa komai ba amma can kasan xuciyarsa ya san Jiddah ce Umma ke magana a kai, Umma ta shigo da wata hiran, sun jima suna magana kafin ya mike yace mata xai je gidan Abuturrab don yana gari, Umma tace "Toh sai ka dawo" Yace "Daga can xan tafi gida Umma, sai gobe xan shigo in sha Allah" Tace "To ka gaida Ramlah" Yace "Xata ji in sha Allah" Ahmad na fita wajajen karfe biyar Umma ta sa Jiddah ta shirya suka wuce asibiti, Basu suka dawo gida ba sai bayan magrib, magunguna kawai aka dora Jiddah a kai, xata wuce daki rike da ledan maganin, Umma da ta xauna parlor bayan ta cire Hijab dinta tace "Baki dai manta dosage din ba ko? Duk da an ma rubuta a jiki ai" Jiddah ta juyo tace "Ban manta ba Umma" Umma tace "Toh kar dai kiyi wasa da shan su, Allah ya sa a dace" Jiddah tace "Nagode Umma" Daga haka ta wuce dakinsu, Umma ta kashe ya fi dubu talatin a magungunan da aka rubuta ma Jiddah a asibitin da suka je. Washegari asabar tare Ahmad ya shigo gidansu da Abuturrab, babu yanda Ahmad bai yi da Abuturrab su tafi dakin Umma ba don tana ciki amma yaki ya xauna parlor wai xa su gaisa idan ta fito, Ahmad ya wuce dakin Ummar tasa, Maimoon ce ta fito daga dakinsu da uniform din Islamiyyarta fuskarta kunshe cikin nikab, ganin Abuturrab xaune a parlor tace "Ina yini yaya" Kai kawai ya gyada mata, ta murguda baki daga cikin Nikab din ta nufi kofa, Safiyya ma na fitowa ta gaishesa tayi hanyar kofa, Kallon kofar dakin kawai yake, sai ga Jiddah ta fito tana kokarin daura nata nikab din, suna hada ido tayi turus a inda take, sai kuma ta dauke kanta ta nufi kofa ta fita parlon ta kulle kofar, mikewa Abuturrab yayi ya nufi dakin Umma ya kwankwasa sannan ya bude yayi sallama, bai shiga can cikin dakin ba ya gaisheta da ladabi daga bakin kofar, ta amsa masa tana tambayarsa aiki, yace "Alhmdlh" Umma na kallon Ahmad yace "Yaran nan basu tafi makarantar har yanxu ba ko?" Shi dai Abuturrab bai ce komai ba, ta mike ganin fita xata yi Abuturrab ya bata hanya ta fita, dubawa tayi ko sun tafi ganin sun tafi din ta dawo, Abuturrab yace "Dama na xo gaisheki ne Umma sai anjima" Tace "Toh nagode" Yana kallon Ahmad yace "Mu yi waya" Daga haka ya juya ya fita, har su Maimoon sun kai bakin titi da kafa tunda ba driver xai kai su ba, yayi parking a gefe yana kallon Safiyya yace "Ku shigo inyi dropping dinku" Sake baki Maimoon tayi cikin Nikab din, tunda take xata iya cewa bata ta6a shiga motarsa ba, ko a hanya ya ganka da ka hau motarsa gwara ya baka kudin mota ko kuma yayi kamar bai ta6a saninka ba, Ita kanta Safiyya mamaki ya cikata, ta dai bude gaban motar ta shiga, Jiddah dai bata ji dadin shiga motan da yace su yi ba, Maimoon ta fara shiga sannan ita ma ta shiga, jikin door din motar Jiddah ta makale ko da wasa bata kalli inda yake ba, Yayi breaking silence din motar bayan sunyi nisa yace "Yaushe Siyama xata dawo?" Safiyya tace "Tab, ta fara karatu fa a can yaya" Yace "To maa sha Allah" Maimoon ce tayi masa kwatancen inda makarantar tasu yake, yana isa makarantar yayi parking bakin gate, Safiyya ce ta fara sauka tana masa godiya, Jiddah ta bude side dinta ba tare da ta kallesa ba ta sauka motar ta wuce cikin makaranta ya bi ta da kallo, Maimoon dake masa godiya taga ya bi Jiddah da kallo ta d'an kikkifta ido tana kallonsa, can dai ta sauka motar ta kulle masa ta bi bayansu Jiddah da sauri, dafe Jiddah tayi bayan sun shiga gate tana xaro ido tace "Jiddoh ya naga Captain ya bi ki da kallo???" Jiddah ta kalleta da sauri tace "Waye haka?" Maimoon ta fashe da dariya tace "Ya Aliyu mana, wllh ina ta ce masa mun gode tsabar yanda ya bi ki da eyes bai ma san ina magana ba Jiddoh" Safiyya dake jin su tayi dariya tace "Kallon godiyan da bata masa ba yake mata, naga ko kallonsa bata yi ba ta sauka abunta ta wuce, kilan abinda ya basa mamaki kenan ya bi ta da kallo" Maimoon tayi shakaf da hannu tace "Habaa... no wonder, I for say, wllh kinga wani kallon da ya bi ki da shi, kuma da gaske ne baki masa godiya ba wllh, next time kar ma kiyi gigin sake shiga motarsa don disgaki xai yi wllh" Jiddah ta ta6e baki tace "Wannan ma banyi niyyar shiga ba" Ahmad yayi ma Umma sallama xai fita tace "Yauwa ina son magana da kai Ahmad, kuma kar kuyi missing train ko?" Ya kalli agogon wrist dinsa ya koma ya xauna yace "Da d'an sauran time, ina jin ki Umma" Ramlah dake xaune gefen gadon Umma rike da handbag dinta ta tashi xata fita Umma ta kalleta tace "Ina kuma xa ki, dawo kiyi xaman ki" Ramlah tace "Aa Umma xan shiga bandaki ne" Daga haka ta fita, Umma tace "Ji shashasha" Shi dai Ahmad murmushi kawai yayi, Umma tace "Makarantar boarding nake son da a sama ma Jiddah, Cause her capacity is now more than mere lesson, tana da kokari sosai Ahmad fiye da yanda kake tunani, Malamar ma ta bada shawaran kawai ta tafi boko da mates dinta she now have a standard root" Ahmad yace "Boarding kuma Umma? why not day, ai bata da wasa balle ace taje boarding, sannan gwara day din saboda koyon abubuwan yau da kullum, irinsu girki, da dai sauransu Umma, Jiddah bata da hayaniyar da xata iya xama a boarding school gaskiya" Umma tace "To ai ba sai me hayaniya ke xuwa boarding ba Ahmad" Umma tace "Yanxu dai shawarata kike nema Umma, kuma shawaran da xan baki shine a samar mata day ta fara daga ss1, she can do it" Umma ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Toh shkkn" yace "Yauwa Umma, kinga baxa ayi depriving dinta from full Islamic education ba in jeka ka dawo ne" Umma tace "Kuma haka ne, amma wacce makarantar kake ga xa a saka ta?" Yace "Tunda su Maimoon sun kusa gamawa kawai a nema mata wani daban ita ma, akwai wata makaranta not to far away daga gidana ko a samar mata a can?" Umma tace "Aa gidanka yayi nisa sosai gaskiya" Ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Toh sai ta xauna gidan nawa mana Umma" Wani kallo Umma tayi masa daga sama har kasa kafin tace "Toh baxata xauna ba" Dariya yayi yace "Kema kinsan Ramlah bata da matsala Umma and she can do so many cooking da Jiddah xata iya koya, don ma yanxu bata da lafiya sosai" Umma tace "To ubana nace Aa, daga nan xata dinga xuwa makarantar..." Yace "Toh shkkn Umma, sai driver ya dinga kai ta, idan xata dawo kuma ta samu abun hawa tunda kinga hanya ce" Umma tace "In dai am samu nan kusa kusa a samar mata admission kawai, don unguwar da kake yyi nisa" Ahmad bai kuma cewa komai ba, can ya mike yace "Toh shkkn Umma, xa mu yi waya kar muyi missing train" Umma tace "Toh Allah ya tsare hanya, ya kiyaye, kuma ku yi addu'a" Yace "In sha Allah" Daga haka ya fita dakin ya kulle mata kofa.....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
*Assalamu Alaikum Everyone ba dogon labari bane ba🤗*
*Sunana Ummu Nuwairah (Known as Mîkyããj Sããdy)*
*Shin kina fama da kuraje ne ko tabo🤔,shin kina son ki haske? Shin kina fama da matsalar fata ne? Ko ko so kike ki haske me aji ba wai kamfala ba, ki koma santsin madara yaukin zuma🥰*
*To matso kusa kiji 'yar mîkyããj Sããdy tazo miki da hadaddun kayan gyaran jiki, masu kamshi kaca kaca😍😍kuma a cikin kudi kalilan😃kayan mu ingantattu ne babu sight effects a ciki, kuma ina mai tabbatar miki in kika saya da izinin Allah sai kin dawo, kin kawo wasu, kema kuma ki fara sara💃🏻💃🏻*
_Domin ganin kayayyainmu ku bibiye mu ta Instagram @mik_yaaj_saady
WhatsApp no: 08061570778
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Em3E7rFyyhoGd7Upakosyk
Bayan kwanaki kadan da Umma tayi magana da Ahmad sai gashi ranan wata Asabar ya shigo gida rike da admission form na Jiddah da receipt na kudin makarantar, Umma ta gama duba takardan da ya mika mata tsaf sannan ta kallesa tace "Ba nace maka makarantar yayi nisa ba Ahmad?" Yace "Umma kece fa kike ganin da Nisa amma ba wani nisa, sannan kan hanya ne ai..." Umma tace "Toh yanxu biya mana kudin makarantar kayi?" Yayi dariya yace "Ehh tawa gudunmawar kenan" Umma tace "Toh Allah yayi albarka, mun gode" Yace "Ameeen" Tace "Ina Ramlah?" Yace "Na ajiyeta gidan Captain" Umma tace "Ohk, yana nan kenan" Ahmad yace "Ehh yana gari, jiya ya shigo" Tace "Toh madallah" Ahmad yace "Xuwa monday sai a kaita schl din for documentation, in sha Allah hopefully xa su saka ta ss1, kinga in dai ya kara maida hankali a ss2 kawai sai tayi waec dinta" Umma tace "Toh Allah ya kai mu, da kana gari ne sai ku je tare ai" Yace "Ina nan har Tuesday" Umma tace "Toh shkkn sai ku je tare din xai fi" Yace "Allah ya kai mu" Daga haka ya nufi kofa ya fita. Karfe biyu Maimoon da Jiddah suka shigo gidan daga saloon sun je kitso, Umma ce xaune parlor tare da Hajja da ta yafa uban mayafi ga jakarta a gefe, daga ganinta kasan bata jima da shigowa ba, A tare Jiddah da Maimoon suka gaisheta, Hajja tace "Har anyi kitson?" Maimoon tace "Ehh" Hajja ta kalli Umma tace "Toh kince sai yamma xa su dawo kuma gasu ko minti ashirin ba ayi da shigowata ba sun dawo" Maimoon da Jiddah dai suka wuce dakinsu, Umma ta ajiye wayarta da take dannawa tace "Dama ba ce maki nayi in dai da layi saloon din xa su iya kai wa har yamma ba? Idan kuma babu layi xa su dawo da wuri? Haka fa muka yi dake Hajja" Hajja tace "Atoh A masar dai magana daya ake, ko don baki son ta rakani ne kika fadi hakan wa ya sani, ni fa nan da kike gani na Allah ne ke daura min son mutum ba wani mahaluki ba, ga can gantalalliyar can Nafeesah me yasa bance ta rakani ba? kice saboda bata gaisheni, sannan wannan bakar yarinyar Aisha sace sace take min a daki, komai aka kawo ta wawura ta boye, shi yasa bata da fasali wllh, to ni ba ruwana ta kaina nake bana biye su, yau dai ina tashi da sassafe nace ma Usman tunda wannan yaro Aliyu yayi aure muka kai masa amarya ban sake komawa gidan ba, kuma ko yanka ni xa ayi idan na hadu da amaryar a hanya yanxu dai ba ganeta xanyi ba wllh, Usman ya fahimceni yace in shirya in je to, barin ma yau Asabar yana gari yana hutu, to ni a gaskiya bana son tafiya ni daya kamar mayya, shine nace kawai direba ya kawoni nan in samu wannan yarinya Jiddah ta rakani muje, ita dama yar ki Maimuna tun wani fada da nayi mata ta daina gaisheni sai yau da taga idonki, banda jiddar babu me mun biyayya yanxu wllh tllh" Umma dai ci gaba da danna wayarta tayi kawai, Jin Hajja tayi shiru tace "Banda abunki Hajja ai jiya juma'ah da babu Islamiyya ya kamata ki xo ba yau da xa su tafi Islamiyya ba" Hajja tace "Toh yau Allah ya bani ikon bude baki ince xan je gidan amarya, ke fa Ramlah wani lokacin Sai in rasa gane inda kika dosa, sannan ni Usman bai wani ce in xo in nemi izininki in tafi da yarinya ba, kawai cewa yayi direba ya kaini in dauketa mu tafi, ni fa ba tsohuwar banxa bace Ramlah, banda tsautsayi babu abinda xai dawo dani daga Masar wllh, a can banda ganin girmana da mutuntani babu abinda larabawa ke yi, don dai Nafisah ta tafi gun mijinta a Habuja ne da ta baki labari da kanta, amma ku banda raini babu abinda ke tsakaninku da babba a kasar nan" Umma tace "Yanxu dai Hajja ga ki ga Jiddah, ni bance kar ki tafi da ita ba, maganan Islamiyya nake, malaman basu yarda da fashi ba" Hajja ta kundumo wani xagi tace "Su malaman Allah ne su da sai ace lallai sai abinda suka gindaya xa a bi? Ni me iya xuwa makarantar ce yanxu ince masu Jiddah baxata je ba sbda wani uzuri da ya taso" Umma tace "Toh rana dai na yi, sai ku tashi ku tafi" Hajja tace "Xuwa xa kiyi ki sanar mata ni ba ruwana duk an ma bata min rai, kamar warce xanje in siyar da Jiddar, ni da na sani ma ban yadda na dawo kasar nan ba wllh, yaushe xa a ga haka a Masar" Umma tace "Wannan Masar din dai Allah ya kai mu muga yanda ake yi a can din Hajja" Da sauri Hajja tace "Aa, ba ko wani gantallale ake bari ya shiga kasar ba ma, nima da yaya suka yarje min na shiga, ke dai kawai a bar kaza cikin gashinta" Dariya Umma tayi ta mike ta wuce dakinsu Maimoon, har sun fara shirin Islamiyya, Umma na kallon Jiddah da har ta saka uniform tace "Jiddah xaki raka Hajja gidan amarya wai" Jiddah tayi shiru tana kallon Umma tana son sanin wace amaryar tukun, Maimoon tace "Wace Amaryar Umma?" Umma ta ta6e baki tace "Gidan Aliyu wai" Sosai gaban Jiddah ya fadi, lkci daya mood dinta ya canxa har hakan bai boyu a fuskarta ba, Umma duk ta lura da hakan kuma, Umma tace "Kina kai ta dama xan baki kudin mota ki lallaba ki dawo, ko minti ashirin kar kiyi a gidan" A sanyaye Jiddah tace "Umma Islamiyyar fa?" Umma tace "To na gaya mata ta hau ni da fada, kawai kiyi hakuri ki rakata din, kuna isa gidan ki juyo abun ki" Jiddah tace "Toh Umma mu je da Maimoon idan ya so kawai sai mu wuce makarantar daga can" Umma tace "Ehh kuma haka ne, ku shirya ku fito, hakan ma shine dai dai, bari in sanar mata" Daga haka Umma ta juya ta fita ta koma parlor, tana kallon Hajja tace "Hajja ita da Maimoon xa su rakaki, idan ya so kuna isa gidan bayan sun gaisa da amarya sai driver ya karasar da su makarantar, da uniform a jikinsu ma xa su tafi, ina ga hakan xai fi ko" Hajja tayi tagumi tace "O'o Allah ina ganin jarabawa ni Dije, yanxu Ramlah ko ke kika haifi er nan Jiddah kya dinga min wannan axababben walakancin da kike min, ina ruwana da wata Maimu? Maimu da bata daraja kowa xaki hadani da? Dama ba Jiddah kawai nace ta rakani ba, a gaskiya a xo a kira min Usman, ya xaki dinga min kamar wata bare Ramlah?? Sannan da Aliyu bai je ya jajubo mana Jiddar ba a ina xaki santa ki nuna iko? A fa ta dalilin jikana ma aka san da wata jiddah a duniyar nan, ni dai wllh ki ajiye son kai kiji tsoron Allah Ramlah, ace a Masar ne ai sai anji dalilin wannan abinda kike min yanxu" Juyawa Umma tayi tace "Ni da ma kira kawai kika yi a tura maki Jiddar da wannan dogon xancen ba sai kin xo ba Hajja" Hajja tace "Oho dai ba ruwana da tashin hankali dake, ni yarinya ce da xan biye maki, banda dai kina kanwar Hauwa a ina xan sanki" Umma na shiga dakinsu Maimoon ta bude kofa tana kallon Jiddah tace "Ki canxa kaya ki xo ku tafi Jiddah" Daga haka ta bar dakin ta wuce nata dakin, Babu yanda Jiddah ta iya haka ta shirya cikin atamfa ta dau hijab dinta ta saka, Abinda Maimoon bata ta6a ganin tayi ba take yi a lokacin wato kumbure kumbure, fuskar nan nata kamar bata ta6a dariya ba kana gani kasan ko kadan ranta bai so ba, jakarta ta dauka ta fice daga dakin, ta wuce dakin Umma, Umma na kallonta tace "To ya xa ayi kiyi hakuri, amma kuna isa ki ce xaki Islamiyya ki fito, ga kudi a gaban mirror ki dauka kiyi kudin mota da shi" Jiddah ta karasa a hankali ta dau kudin sannan tace "Nagode Umma" Fita tayi daga dakin, bata san Umma ta ma fita jin takaicin rakiyar ba, Hajja na ganin Jiddah ta mike tace "Mu je, ai ba ita taje ta nemo ki a duniya ba da xata dinga nuna isa da iko a kanki, mata ta wani narka kiba uwa fanken Masar tana ma mutane rashin kunya kawai" Ita dai Jiddah bata ce komai ba ta bi bayanta tana tafiya a hankali, Driver na ta xaune mota yana jiran ranan