Showing 261001 words to 264000 words out of 346625 words

Chapter 88 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

ita kuwa tuni tayi shigewarta mota ko kallonsa bata yi ba, a haka har suka bar gidan. Bayan magrib su Maimoon suka shigo gida da Umma, a nan parlor duk suka yi sallah, Huraira ta kawo masu abinci ganin Jiddah bata fito ba Umma ta kalli Maimoon tace "Jiddah bata ji shigowar mu bane?" Mikewa Maimoon tayi tace "Bari in duba ta" Dakinsu ta nufa ta bude kofar, kwance ta tadda Jiddah cikin blanket ta rufe har kanta, ta karasa kusa da ita tace "Bacci kike Jiddah, an fa yi sallah.." Xaunawa tayi kusa da ita jin bata amsa ba ta cire blanket din jikinta tana kallonta, Jiddah ta ki bude idonta amma kana ganinta kasan ba bacci take ba, Maimoon tace "Toh meye haka, kukan me kike haka?" Rufe fuskarta tayi da pillow ta ki cewa komai, Maimoon ta dinga kallonta, tun jiya da Umma ta sanar mata xata tare gidan Abuturrab taki bacci da daddare, yanda taga safiya haka taga daren, yau kuma ta tashi da ciwon kai tun safe, ga abinci ta kasa ci, sae take jin kamar xata yi xaxxabi, da ta tuna wai gidan Umma xata bari ta sake komawa gidan Abuturrab da xama this time around ba su biyu kadai xa su xauna ba har da Aneesah sai taji hawaye ya taho mata, duk wannan damuwan da take ciki bata bari kowa ya lura ba, duk da tun safe Umma ta shiga kasuwa da Maimoon, ko da suka dawo kasuwan kuma frnds dinta kawai ta jira suka iso suka kama hanyar gidan Abuturrab gaba dayansu, tun kuma da suka tafi take kuka har shigowar su yanxu, Mikewa Maimoon tayi ta nufi kofa, Jiddah na ganin haka ta mike xaune tana goge kwallar dake makale idonta kafin tace mata komai har ta fita, Komawa tayi ta kwanta wasu hawayen masu xafi na xuba idonta, kawai tausayin rayuwarta take kuma yanxu, shi kansa Abuturrab din taji tana tsoronsa ta rasa dalili, ko don sbda abubuwan da ya tsiri yi mata yanxu wanda baya mata a lkcn da suke su biyu kadai a gidansa ne oho, yanxu kam ko ganinsa ta ji bata son yi, yana bata tsoro ba na wasa ba, ko sunansa taji an kira sae gabanta ya fadi, sannan kuma ga Aneesah, ai bata san lkcn da ta fashe da kuka ta kife kanta da pillow ba tana shessheka tana tausayin kanta, Maimoon na komawa parlor ta duka kusa da Umma dake xaune kan darduma tace "Umma kuka fa take ta yi a daki" Umma ta kalleta tace "Kuka kuma? To kukan uban me?" Maimoon dai tayi shiru don ita ma har ta fara jin tausayin Jiddah, yanxu gobe haka xa a kai ta gidan Abuturrab a barota ita kadai ga Aneesah da yan uwanta a gidan, mikewa Umma tayi ta tafi dakin nasu, kulle kofa tayi bayan ta shiga ta nufi kan gadon ta xauna kusa da ita tace "Jiddah" Jiddah ta mike xaune amma bata yarda ta kalleta ba tana share hawayen da ya ki tsaya mata, Umma ta kamo hannunta cikin sigar lallashi tace "Gaya min kukan me kike Jiddah, tell me what it is my daughter" Jiddah ta girgixa mata kai wasu sabbin hawayen na kai komo a fuskarta, Umma tace "Kina da warce xa ki gaya ma damuwarki bayan ni Jiddah?" Jiddah ta fada jikinta cikin rawan murya tace "Umma me yasa baxa a bar ni a gidan nan ba" Umma tayi shiru ta ma rasa abinda xata ce mata, can tayi kasa da murya tace "Ke matar aure ce yanxu Jiddah, ba don kuma bama sonki ba xa ki tafi gidan mijinki" Tana kuka sosai tace "Umma wllh na fi son nan, don Allah a bar ni in xauna a nan" Umma tace "Da nan din da can duk daya ne Jiddah, kuma duk sanda kike son xuwa nan Aliyu baxai hanaki ba" Ta girgixa kai da sauri tace "Aa Umma ni bana son in xauna a gidansa wllh" Umma tace "Saboda me?" A hankali tace "Ni tsoronsa nake ji" Dariya ta ba Umma amma bata yi ba tace "Tsoronsa kamar wani dodo Jiddah" Cikin kuka tace "Allah Umma ina tsoronsa" Umma tace "Watanninku kusan hudu tare a gida daya Jiddah duk baki ji tsoronsa ba sae yanxu?" Jiddah tayi shiru tana tuna lkcn da suke tare gida dayan, to amma a lkcn bata ta6a tsoronsa ba sai yanxu, Umma ta dago kanta tana share mata idonta tace "Don't worry my dear... Da gidan Aliyu da nan duk daya ne kin ji" Jiddah tayi shiru tana kallonta, Umma tace "Kin yi sallah?" Sunkuyar da kanta tayi a hankali tace "Aa" Umma tace "Tashi ki je kiyi" Mikewa tayi a sanyaye ta nufi bathroom, Umma ta bi ta da kallo cike da tausayinta.... Babu wani abu da Umma ta ba Jiddah ta sha na mata don tana ganin at this her age bata bukatansa, iyaka dai turaren tsugunno da ta sa take yi, yanda Jiddah ta ga daren jiya haka taga na yau ma, da ta tuna xata bar gidan Umma ta koma gidan Aliyu sai taji gabanta ya fadi, hawaye ya taho mata, da safe shayi kawai ta iya sha bayan tayi wanka ta kwanta, nan da nan kuma bacci ya dauketa amma ba me dadi ba, karfe tara Umma ta fita xuwa gidan Ummi da frnds dinta don kwasan kayan kitchen din Jiddah a kai can gidan Abuturrab, A hanya Hajiya Rukayya tace "Toh yanxu ya xa ayi da jeran kayan Kitchen din tunda dai ita warcan naga kayanta ne ko ina na cikin kitchen din, jiya na shiga da naje daukan ruwa" Umma na gyara xama a motar tace "Ki sa ido ki gani ke dai, don ma ba yanda Hajja tace ayi xanyi ba, Hajjan fa cewa tayi duk a fitar da kayan kitchen din sun kaxance a ajiye ma me su a backyard a jera sababbi na Jiddah, to amma baxa mu yi haka ba ai, ni nasan yanda xan yi"




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp






Karfe goma Maimoon ta tashi Jiddah daga baccin da take, Jiddah ta mike xaune tana kallonta da kyar saboda kanta da yayi mata nauyi, Maimoon tace "Driver din ya xo yana jiranmu a waje" Jiddah ta marairaice tace "Gashina fa a gyara yake Maimoon, last week fa mun je saloon" Maimoon ta buda hannu tace "Oho go ai nima bani nace mu je ba, kina dai ji Umma ta fada da asuba ai da kince mata a gyara gashin ki yake" Jiddah bata ce mata komai ba ta mike tsaye ba don ranta ya so ba ta fara shiryawa, Maimoon tace "Ina jiranki a parlor" Daga haka ta dau hijab dinta ta fita, Jiddah ta gama shiryawa ita ma ta saka hijab din ta fito sannan suka wuce saloon din, har suka isa jikinta a sanyaye yake tayi nisa tunanin da take, Lkci lkci Maimoon ke kallonta amma dai bata ce mata komai ba. Bayan an gana gyara mata gashin da kyar da lallami Maimoon tayi convincing dinta aka yi zanzara mata henna a hannu, sosai lallin yayi kyau don expert ce tayi mata, Maimoon sai kallonta take tana murmushi, karfe biyu da yan mintuna suka koma gida, Umma dake parlor da frnds dinta sun dawo daga jeran kayan kitchen ta bi su da kallo har suka wuce daki, Jiddah ta xauna can karshen gado ta jinginar da kanta, she looks so sad, Maimoon ta je ta debo masu abincin don sun yi sallah a saloon din, da farko kin cin abincin Jiddah tayi sai da ta ga da gaske Maimoon xata je ta gaya ma Umma sannan ta sauko ta debi abincin ta kai baki, daurewa kawai take wajen cin abincin don jin sa take kamar magani... Throughout ranan Abuturrab a bedroom din Umminsa ya yini sai dai ya fita masallaci, Ummi dai na lura da shi kamar he isn't happy amma kuma bai ce mata komai ba, bayan la'asar tace "Wai baxa ka ci abincin bane, abincin tun karfe daya a ajiye? Ko a fita kitchen da shi ne?" Yayi pausing movie din da yake kallo a wayarsa yace "Xan ci Ummi" kallon abincin nasa dake ajiye kawai yake, Ummi tace "Tell me what is wrong Aliyu!!" Ya kalleta sai kuma yayi shiru ya sauke kansa ya ki ce mata komai, jin Ummi bata sake ce masa komai ba ita ma, ya daga kai ya kalleta yace "Ummi ni kawai na rasa gane amfanin aurena da Aneesah, can u imagine all 2 of her family members suna gidana yanxu haka... sannan Aunty ma na gidan tun jiya" Da mamaki Ummi tace "Wacce Auntyn?" Ya shafa kansa bai ce komai ba yana jin xuciyarsa na tafarfasa tuna abinda Aunty tayi masa da safe har da xagin Umminsa, Ummi tace "Wai Hafsah kake nufi ko wa?" Yace "Ita... Ummi gaba daya fa suna gidan yanxu haka" Ummi ta kasa ce masa komai sai kallonsa take da mamaki, Ya dafe kansa sounding so fed up yace "I'm really fed up with this Ummi, shkkn mutum ba shi da kwanciyar hankali a rayuwa, i regret marrying Aneesah, i regret ever making this mistake" Ummi ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya tace "Toh Allah ya kyauta, amma ban san me xance ba gaskiya, i think it's better kaje yanxu ka sanar ma Hajja, ita xata fi daukan Action, ko kace xaka gaya ma Abbanka ba wai sauraranka xai yi ba yanxu" Shi dai bai ce komai ba, Ummi tace "Haka Allah ya kaddaro maka sai kayi hakuri, kowa ma hakurin yake, kuma babu hakurin da yake tashi in vain, there is always a reward for that, Allah yayi mana maganin duk abinda ya dame mu" shirun dai Abuturrab yayi but he looks so worried, Ummi tace "Yanxu jiran tarewan Jiddah suke kenan da suka rigata tarewa a gidan? Toh me yayi xafi sai ka bari next week idan sun gama xaman nasu koh" Ya kalli Ummi da sauri, sai kuma ya sunkuyar da kansa yace "Aa nothing is going to change because of them Ummi" Ummi tace "Amma gaskiya kaje ka sanar ma Hajja, amma kar ka gaya ma Ramlah don bana son tashin hankali" Ya amsa mata da toh kawai. Ana kiran isha Abuturrab ya isa gidan Umma, sai da ya gama waya da Ahmad da ya kirasa for almost 10min sannan ya shiga masallacin dake layin yayi sallah ya fito, ya fi minti daya tsaye bakin kofar parlon Umma don shi ko kadan bai son matsalan Umma, a hankali ya bude kofar daga karshe ya shiga ciki da sallama, su Safiyya ne a parlon ya karasa ya xauna duk suka gaishesa, ya amsa without looking at them yana danna wayarsa, Umma na bedroom dinta tare da Jiddah dake xaune saman darduma a gabanta ta sunkuyar da kanta, lafiyayyen lace me tsada ne jikinta wanda yayi mugun amsan fatar jikinta, ko ba a fada maka ba xaka san kuka take duk da mayafin da ya rufe har fuskarta, nasiha sosai Umma ke mata kamar yanda uwa xata ma 'yar ta, Maimoon ta shigo dakin da sallama ta duka kusa da gadon jin Umma na magana bata ce komai ba, Umma ta kalleta tace "Ya aka yi?" Tace "Yaya ne ya xo yana parlor" Umma ta ci gaba da yi ma Jiddah maganar da take har ta kai aya sannan tace "Toh shkkn abinda xance maki kenan daughter, and i hope u won't disappoint me by taking all my words for granted, Allah ubangiji ya bada xaman lafiya... Sai da safe" Jiddah ta kasa tashi ta fara rera mata kuka, Umma da taji tausayin har ranta ta kalli Maimoon a hankali tace "Kama hannunta ku tafi" Maimoon taji kamar ta fara kukan ita ma, ta mike a sanyaye ta daga Jiddah suka nufi kofa, Umma ta bi Jiddah da kallo cike da tausayinta, babu yanda ta iya da yayarta ne amma banda haka in dai ta Hajja ne ko yakin duniya xa ayi baxata bar Jiddah ta koma gidan Aliyu ynxu ba, kawai duk abinda xai faru ya faru, but babu yanda ta iya da Ummi.... Tun da Maimoon suka fito parlor Abuturrab ke kallon Jiddah babu ko kiftawa, sosai kayan jikinta da mayafin suka mata kyau, ya mike yana kallon Maimoon yace "Umma fa?" Maimoon tace "Tana daki" Bai ce komai ba ya tafi dakin Umma, kasa shiga yayi yana ta tsaye kamar mara gaskiya can dai yayi shahada daga karshe ya tura kofar da sallama kasa kasa ya shiga ciki, Umma dake linkin Hijab dinta tayi kamar bata gansa ba ta hade rai, ya xauna saman carpet murya can kasa yace "Ina yini Umma" Ba tare da ta kallesa ba tace "Lafiya lau" Shiru yayi bayan few minutes ya mike yace "Toh sai da safe Umma nagode, Allah ya kara girma" Umma ta juyo tace "Ba ka gode ba Aliyu, wllh ko k'uda ka bari ya cuci wannan er marainiyar Allahn, Allah ya isa ban yafe ba, ba wai an ce sai ka ajiyesu gida daya ba dole.. Wllh duk abinda ya samu Jiddah ina me tabbatar maka xan mance relationship din meye tsakaninmu in ma rashin mutunci in dau matakin da ya dace, matarka kuwa ka ja mata kunne kar tace xata yi crossing part din 'ya ta, ta tsaya iya lane dinta, she should take her eyes off my daughter don wllh bani da mutunci, a al'adanmu na fulani kusan abun kunya ne ace uwa na sintirin xuwa gidan 'ya babu dalili to kuwa sai dai a kirani da mara kunya in this case" Shi dai Abuturrab bai ce komai ba yana sauraronta kansa a kasa, Umma tayi kwafa ta ci gaba da abinda take tace "Allah dai ya ba kowa sa'a..." Jin bata sake cewa komai ba, a hankali yace "Toh in sha Allah Umma, sai da safe" Fita yayi dakin, Maimoon dake xaune kusa da Jiddah kan kujera ta mike ta kama hannun Jiddah suka fita parlon safiyya da Huraira suka rakasu har bakin motarsa, shi dai yana biye da su a baya, Maimoon ta bude ma Jiddah front seat taki shiga sai kuka take tana rike da hannun Maimoon gam, Abuturrab na kallonsu gaba daya yace "Sai da safe" Babu wanda yace komai duk suka juya, Maimoon ta kwace hannunta cikin na jiddah ta nufi gate tana goge guntun hawayen idonta, yana kallon Jiddah calmly yace "Shiga" taki shiga taji kamar ta bi su Maimoon ciki da gudu, bin kofar gidan yayi da kallo tana ganin xae dagata tayi saurin shiga motar tana kuka sosai, ya kulle motar sannan ya xaga ya bude driver seat ya shiga... Har suka isa gida kuka Jiddah take, shi dai bai ce mata komai ba yayi horn driver ya bude gate ya shiga yyi parking ya kashe motar, sae a sannan ya jinginar da kansa jikin kujeran motar yana jin yanda take shessheka, juyawa yyi ya kalleta, Lowering his voice yace "Jidderh..." Kukanta kawai take, ya kamo hannunta a hankali yace "Gaya min kukan me kike" Ta xame hannunta taki cewa komai wani sabon kukan na taho mata, bude motar yayi ya sauka ya xaga ya bude side dinta ya sauko da ita, ya kulle motar yana rike da hannunta ya nufi cikin gidan da ita, sosai take jin gabanta na faduwa tana fatan ace mafarki take yau, tsaye yayi balcony yana kallonta ganin kamar ana dada tunxurata da kukan, ya dage mayafin kanta yana kallon kyakkyawan face dinta da ya baci da hawaye, side hug yyi mata murya can kasa yace "Ohk then! Next week in sha Allah xan maida ki gidan Umma amma sai kin daina kukan nan, stop the cry now..." cikin kuka sosai tace "Next week is too far, don girman Allah kayi hakuri ka maida ni yau, wllh bana son gidan nan, don Allah nace maka...." rungumeta yayi ta dinga rera masa kuka kamar ranta xai fita tana shessheka, ya lumshe ido yana jin yanda xuciyarta ke bugawa, ga kamshinta da ya cika hancinsa, bayan few seconds ya bude idonsa a hankali yace "Gobe xan maida ki, but sae kin daina kukan..." Cikin rawar murya tace "Kace wllh" yayi kasa da murya ya daura goshinsa a nata yace "Na ce" ta dauke kanta da sauri tace "Aa wllh xaka ce" ya juyo da ita yayi kissing lips dinta lightly, underneath his breathe yace "Ga shi nace" bai jira me xata ce ba ya manna mata wani kiss din a cheeks dinta yana rike da hannunta ya bude kofar parlon suka shiga, ba ita ba har shi sae da gabansa ya fadi ganin Aunty, Safara'u, Falmata da Aneesah duk xaxxaune a parlon, lkci daya ya dauke kansa yana ci gaba da tafiyarsa fuskarsa a daure, Jiddah kuwa tunda ta hada ido da Aunty da Aneesah ta dinga bobboyewa gefensa kamar xata shige jikinsa, hakan da tayi ya sa shi rungumeta ta side dinsa har suka wuce sama su Aunty duk suka bi su da kallo, A hankali Aneesah ta fara kuka tana jin xuciyarta na mata xafi, Safara'u tace "Meye haka? Kun ga wani shashanci ko, ke kam wllh dole ma miji ya rainaki... Haka aka koya maki kiyi? To kukan uban me kike masu yanxu don uwarki??" Falmata dake hararanta ita ma tace "Wlh ke kam baki yo halinmu ba Aneesah, ga dai yanda aka shirya abu da ke, kawai ki kama yi ma mutane kuka kamar wata mara class" Aunty dau takaicin yanda Abuturrab ya wuce bai ce mata kala ba ya cikata, tun dai da wnn yarinya Jiddah ta shigo rayuwarsa ya daina mata biyayya, ya daina ganinta da girma, sai kuma ga raini yanxu, to kuwa ai babu wanda ya kamata yaji haushin Jiddah fiye da ita tunda ita ce


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login