Showing 147001 words to 150000 words out of 346625 words
Chapter 50 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
dukiyarka baxasu siya min flask din ba tunda a Masar aka siye sa ba a kasar nan ba, sannan me ya kai flask dina hannunka bayan wancan matar na ba ta juyo min ruwan xafi?" Yace "In dai kin tambayi nawa aka siya sai ki gaya min" Daga haka ya juya ya fice daga dakin, ta fashe da kuka tace "Allah ka dai ga wannan xaluncin da aka min, a ina xa a samo flask irin wannan yanxu a kasar nan" Komawa gefe Jiddah tayi da sauri bayan Abuturrab ya fito don tana labe bakin kofar, ta bi sa sa kallo har ya wuce sannan ta shiga dakin gabanta na faduwa, a fusace Hajja tace "Ke garin yaya flask dina yaje hannun wancan mutumin da ya tsaneni?" Jiddah ta sunkuyar da kanta tace "Dauka yayi Hajja" Hajja tace "Toh yaje shi, ni ba yafewa nayi ba, kuma bari Usman ya dawo tunda shi na haifa" Ita dai Jiddah bata ce komai ba. Bayan magrib Umma ta ajiye ma Ummi duk abinda Hajja ta ba su Jiddah da Maimoon na kayan lefe, Ummi tace "Ki bar masu kawai tunda ita ta basu" Umma tace "Aa maida masu da kayansu yaya, a ina aka ta6a haka" Ummi tace "Wai ba ni nace ki bar masu ba??" Umma tace "Toh Allah ya kyauta bari in je in ma Hajja sallama" Daga haka Umma ta fita bangarenta, a corridor suka hadu da Aunty xata sakko parlor, Aunty tace "Aa Hajiya Ramlah ashe kun shigo, mun wuni lafiya?" Umma tace "Alhmdlh" Aunty tace "Tun shekaranjiya nake ta ce ma Ummi ta kiraku an gama hada lefe wllh..." Umma tace "Ai kam kaya maa sha Allah, Allah ya sanya alkhairi" Aunty tace "Toh ai ni na xata kin xo kenan sai mun dawo daga kai lefen, kin san gobe ne xa a kai fa da safe" Umma tace "Aa sai kun dawo Hafsah, ni ba wani dadi nake ji ba, Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lfya" Aunty tace "Ehh tun da ma da ni xa aje shkkn kawai, Allah ya kara lafiya..." Umma dai ta wuce dakin Hajja, Aunty kuma ta sauka parlor, Ummi na kallon Jiddah dake parlonta ita kadai, su Maimoon kuma na daki wajen Ramlah tace "Kwashi kayan ki kai mota Jiddah" Jiddah ta mike ta dau ledojin kayan da Hajja ta basu ta fita, Aunty dake xaune parlor da wata bakuwa da tayi, Abuturrab ma na parlorn don kudi ta kirasa xai tura ma bakuwar wai na zoben gwal guda biyu da xa a sa ma Aneesah a lefen, ta bi Jiddah da kallo tana kare ma ledojin hannunta kallo, shi ma Abuturrab kallonta yake, Jiddah ta gaisheta ta nufi kofa ta fita, mikewa Aunty tayi tace ma bakuwarta tana xuwa sannan ta fita da sauri, shi dai Abuturrab bai ce mata komai ba, a compound ta tsayar da Jiddah ta amshi ledojin hannunta tana duba abubuwan ciki, kwace dayan ledan tayi da karfi tace "Ubanki ne ya siya kayayyakin da aka baki ki kai mota??" Jiddah dai tayi shiru tana kallonta, Aunty tace "Baxa ki daina kallona cikin ido ba sai na tsole idanuwan?" Sunkuyar da kai Jiddah tayi, Aunty ta juya kamar xata tashi sama ta koma cikin gida, Abuturrab na kallon Aunty bayan ta xauna a parlor ta ajiye ledojin da ta amso a gefenta yace "Aunty da baki amsa ba ai ni nace xan siya duk abinda babu a ciki" Aunty tace "Rufe min baki, kai xaka gaya min abinda xanyi da wanda baxan yi ba, duk wanda bai rike girmansa ba xai ga rashin girma a gidan nan wllh, a kan me xa a debe ma yarinya kaya wannan ai karanta ne wllh, wannan abun kunya har ina kawai a bude lefen yarinya a yashe mata kaya??" Umma da ta shigo parlon tare da Ummi ta kalli Aunty amma bata ce mata komai ba suka fita parlon tare da Ummi Aunty tace "A gaida gida" a compound suka ga Jiddah a tsaye, Umma tace "Ina kayan? Kin kai mota?" A hankali Jiddah tace "Aunty ta karba" Juyawa Umma tayi ta koma parlon, Ummi ta bi ta da kallo sai kuma ta bi bayanta, Umma na kallon Aunty tace "Kayan da kika amsa xa ki bani Hafsah" Aunty tace "Wllh baxan bada ba Hajiya Ramlah, wannan ai ba girmanku bane daukan kayan yarinya, wannan ai karanta ne, ku idan aka ma 'ya yanku haka xa ku ji dadi??" Ummi ta kalli Abuturrab tace "Aliyu" ya daga kai ya kalleta, tace "So nake ka kwashe akwatunan nan gaba daya ka kai su gidan Ramlah da daddaren nan" Aunty tayi wani shewa tana tafe hannu tace "Gidan Ramlah? To ai naga ba Ramlah bace ta hada lefen, don haka xan ga me kwasan akwatuna ya fita da su gidan nan yau...." Shi dai Abuturrab kallon Ummi ya dinga yi ya kasa cewa komai, Hajja ta fito rike da fasasshen flask dinta tace "Me ke faruwa na ganku cirko cirko a tsaye?" Aunty na kallon bakuwarta tace "Xa a tura maki kudin na biyun ki tafi gida kawai Salaha" Daga haka ta bar parlon kamar xata tashi sama, Salahan ta mike ta fita parlon, Ummi na kallon Abuturrab strictly tace "Kaji abinda na gaya maka?" Yayi kasa da murya yace "Ummi duk bai kai haka ba, don Allah..." Wani tsawa tayi masa tace "I said take away the boxes to Ramlah's home" Hajja tace "Naga ikon Allah, na tambayi me ke faruwa an min shiru" Ummi tace "Cewa nayi ya kwashe akwatunan ya mayar gidan Ramlah daga can xa a kai su" Hajja tace "Atohh a kira mai gadi ya fitar da su xuwa motar mana me ake jira" Kallonta Abuturrab yyi fuska daure, Ummi tace "Ya fita ya kira mai gadin da kansa, idan ba haka ba wllh wllh baxa a kai kayan nan ba, kuma kudin da aka kai sai dai a yafe shi...." mikewa Abuturrab yyi yana kallonta, Ummi ta juya ta bar parlon Umma na biye da ita. Hajja ta nufi kofa don kirawo mai gadi tana cewa "Aa bai kai haka ba Hauwa ni da kaina sai in je in kira mai gadin a fito da akwatunan" Abuturrab ya koma ya xauna ya rike kansa ya rasa tunanin da xai yi, mikewa yayi ya nufi bangaren Aunty....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗
Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali
Ina masu pimples
Tabo(spot)
Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance
Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba
Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki
Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu
Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself
100%tested nd trusted
Soap price:3k
Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free
Maiso kindly message 08062991549
07046881166
Call 08064532391
Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏
Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝
Mg's skincare
Waya Abuturrab ya tadda Aunty na yi a parlonta rai bace, ko ba a fada ba yasan da wanda take wayar, yana dai tsaye har ta gama ta jefar da wayar kan kujera tana huci, ya kwantar da murya yace "Aunty duk bai kai wannan extent din ba, pls i want u to calm down...." A fusace tace "Ya kai har ya wuce extent din da kake fada, kuma wllh xan ga uban da xai fitar da kayan nan a gidan ga yau, sun san da nuna ikon me ya hanasu wahalan hada lefen? Tun da na fara hada kayan nan kullum sai na fita kamar yar iska, kuma bani xan shigo gidan nan ba sai karfe takwas din dare, to a kan me ba a ce min Allah ya shi min albarka ba xa a dinga bata min rai ana sa ni a bakin duniya?? To wllh wllh Ramlatu ta fita harkata, ta fita idona in rufe idan kuwa ba haka ba xan kai kararta ba wani shege, ko kuma in kai ta gani ga ka ayi min iyaka da ita" Abuturrab dai kallonta kawai yake, wayarta ne ya fara ring ta dauka ta shige daki a fusace ta kulle kofar, Abuturrab ya shafa kansa sannan ya juya ya fita daga dakin, bangaren Umminsa ya shiga, ya kasa kallonta ya xauna saman kujera cikin sanyin murya yace "Ummi don Allah kiyi hakuri, duk bai kai haka ba" Ummi tace "Inyi hakuri da me??" Kasa cewa komai yayi, Ummi tace "Wllh in har akwatunan nan suka kwana gidan nan sai dai ka nemi wata yarinyar da xaka aura ba wannan ba Aliyu" Umma dai na xaune tana danna wayarta tana girgixa kafa, Abuturrab bai kuma cewa komai ba ya mike ya fita parlon, a main parlor ya tadda Hajja tsaye bakin kofar parlon da su Maimoon, sai ga mai gadi ya fito daga dakinta rike da akwatuna biyu a hannunsa, Hajja ta basa hanya tace "Yanxu saura nawa?" Mai gadin yace "Saura hudu" Hajja tace "To yi maxa..." Mai gadin yayi kofar gida da akwatunan ya saka au booth din mota da driver din Umma ya bude sannan ya koma ciki da sauri, Hajja ta kalli Jiddah dake tsaye wajen balcony din tace "Toh ke wa kike da suna, ki kwashi kananun da ya ajiye a nan ki kai mota da tsayuwar nan, ki daina lagwai lagwai kamar ba mace ba kinji??" Jiddah bata ce komai ba sbda bata son mata musu ta dau kit din biyu ta nufi gate, Banda hararan Hajja babu abinda Abuturrab yake daga inda yake tsaye, can ya nufi kofar kamar xai tashi sama, Hajja na ganin haka ta basa hanya da sauri, bayan ya fita ta kalli su Maimoon tace "Kun ga d'an banxan ko? Kunga irin dabancin nasa ko?? Da ban kauce ba bangajeni yayi niyyar yi fa, anya wannan Aliyun da na tafi Masar na bari kenan shekaru uku da suka wuce? o,o to baxan biyesa ba, ba ruwana ni ba yarinya bace, kuma sai dai ya bangaje Hauwa ko Usman, ko kuma yar Benuen can, amma ba ni ba tunda ban hada komai da shi ba ai" Jiddah na ajiye kits din bayan booth taki komawa cikin gidan tana tsaye jikin gate har ranta bata jin dadin abinda ke faruwa, Abuturrab ya fito compound din, kallon driver din Umma yayi yace "Wa yace ka saka akwatunan a bayan mota?" Drivern ya xagayo da sauri yace "Aa kawai ni bude booth nayi ake xubasu a ciki" Calmly Abuturrab yace "Toh sauko da su" Kallonsa Jiddah ta dinga yi da mamaki, Driver ya koma gun booth da sauri xai sauke kayan, kafin driver ya fara sauke kayan ta daure tana kallon Abuturrab tace "Ina son in maka wata tambaya don Allah..." Sai a sannan ya kalleta, tace "To ka d'an ce masa ya jira kafin ya sauke kayan, kaji?" Driver ya kalli Abuturrab din dake ta kallon Jiddah da mamaki, Ta koma gefensa tana kallonsa, kana ganinta kasan she is afraid of talking to him, gathering many courage ta fara magana tana wasa da fingers dinta "Dama ina son in san wacece Baabarka a cikin Aunty da Ummi, ni har yanxu ban sani ba" Daga sama har kasa ya kalleta, ta ci gaba da magana ba tare da ta yarda sun hada ido da shi ba tace "In dai Aunty ce Baabarka to kayi dai dai idan kace a sauke akwatunan nan, tunda ai ba a wasa da maganan uwa, idan kuma Ummi ce Baabarka...." Sai kuma tayi shiru, yana kallonta da kyau yace "Ina jin ki" Cikin sanyin murya tace "Kaga ni ban samu gatan sanin mahaifiyata ba, na taso cikin maraicinta, saboda maraici da rashinta yasa na taso cikin rashin gata da kula..." Hawaye ya kawo idonta tana gogewa tace "Da mahaifiyata na nan duk abubuwan da suka faru dani da nasan baxa su faru ba, ko yan uwanta ni ban samu daman sani ba, bansan ko tana da yayyi ko kanni ba, ban ma ta6a ganinta ba" Ta kasa ci gaba tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, shi dai kallonta kawai yake, cikin sanyin murya tace "Toh kaga duk wanda baya ba Baabarsa muhimmanci baxai ji dadin rayuwarsa ba, kuma xai hadu da fushin Allah" Sai kuma ta daga kai ta kallesa tace "Albarkacin haifanka da Ummi tayi kaji maganarta na yau kawai mana, tunda tace bata son a bar kaya a nan ka bari a tafi da su xai fi, ko kai baka son ka xauna lafiya da matar da xaka aura?" Hajja ce ta fito gate din gidan tana yafa gyalenta da yar jakarta a hannu tace "Ina matukin motar yake mu tafi" Drivern Umma ya xagayo da sauri yace "Gani Hajiya" Tace "A ina xan xauna a motar?" Bayan motar ya bude mata ta shige ba tare da ta kalli su Abuturrab ba tana cewa "Bari in fara yin gaba da kayan" tana shiga ta kulle motar, Drivern dake ta kallon Abuturrab yana jiran wani instruction din jin bai ce komai ba ya xaga ya shiga motar ya tada suka bar layin... Jiddah ta daga kai ta kallesa ganin kallonta yake ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, ya gyara tsayuwarsa yace "Ohk, shikenan kin gama?" Shiru tayi da farko, sai kuma ta girgixa masa kai a hankali tace "Aa, yanxu don Allah kaje ka ce Ummi tayi hakuri ta yafe maka, sai kace mata Hajja kuma ta riga ta tafi da kaya" Yace "Koh?" Ta d'an kallesa, sai kuma ta sauke kanta ta gyada masa kai, yace "Ohk, kalleni" Kin yarda ta kallesa tayi, yace "Kalleni nace" Ta dake ta dago kai ta kallesa yace "Toh daga yau... Kika sake sako min baki a abinda ya shafi rayuwata sai na mareki, ke har xaki gaya min abinda xanyi da wanda baxan yi ba? " Jiddah dai bata ce komai ba, kawai ta juya ta nufi gate ya bi ta da kallon mamaki yace "Kee" ko waigowa bata yi ba, yace "Ba magana nake maki ba" Tayi shigewarta gate, shafa kansa yayi sai kuma ya bi bayanta. Parlor ya tadda ta xaune tare da su Maimoon, bai kalleta ba ya wuce bangaren Ummi, har sannan Ummi na xaune da Umma dake ta bata hakuri, kansa a kasa ya xauna kan rug din parlon, da kyar yace "Ummi don Allah kiyi hakuri ki yafe min, in sha Allah duk yanda kika ce xa ayi hakan xa ayi, kaya kuma na sa Hajja ta tafi da su can gidan Umma" Dama bai sa ran Ummi xata basa amsa ba, hakan yasa ya kalli Umma ita ma yace "Ku yi hakuri Umma, in sha Allah hakan baxai sake faruwa ba, duk yanda ku ka ce haka xa ayi, kaya kuma duk ranan da ku kace a kai sai a kai, kuyi hakuri don Allah" Yana kai wa nan ya mike ya nufi kofa duk suka bi sa da kallo, ba Ummi ba har Umma tayi mamaki sosai ba kadan ba, abinda bai ta6a yi ba kenan duk rayuwarsa karkari ya je ya ba stepmom din tasa hakuri ya bar gidan sai kuma randa aka gansa, Ummi tace "Wannan ba xuwan kansa bane..." Umma tace "Aa nima nayi mamaki, ko Hajja ce dai..." Ummi ta kalleta da sauri tace "Wacce Hajjar? Shi dai ya san what he is up to shiyasa ya shigo bada hakuri, amma this is so unusual of him, ni bai ma ta6a bani hakuri ba" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh koma dai menene tunda ya shigo kuma yace ayi hakuri, sannan yace Hajja ta tafi da kaya kawai kiyi hakuri yaya" Ummi dai bata ce komai ba. Abuturrab na fita Bedroom dinsa ya shiga ya sa makulli, wayarsa dake hannunsa ya fara ring ganin Abba ke kiransa ya daga, Abba yace "Kana ji na Aliyu?" Abuturrab ya xauna gefen gado yace "Ina ji Abba" Abba yace "Plss ka lallaba iyayenka duk yanda xa ayi kar a fitar da kayan nan daga gidan nan... It should remain their gobe a kai su" Abuturrab ya shafa kansa yace "Abba Hajja ae ta tafi da su" Abba yace "Ta tafi da su?? Amma baka yi making ko wani effort na hana tafiya da su ba Aliyu??" Yyi kasa da murya yace "Abba Ummi ta dau lamarin da girma ne, tayi fushi sosai, and...." Abba ya katsesa yace "And what nonsense? Ita kuma Hafsah fa? Ni nasan yawancin abubuwan dake faruwa gidan nan duk Ramlah ke xuwa ta hada, a kan me su basu hada lefe ba kuma su 6ata ma warce ta hada rai kana kallo Aliyu??" Shi dai Abuturrab yyi shiru, Abba ya katse wayarsa, kallon wayar Abuturrab ya dinga yi sae kawai yaji bai ji dadin abinda Abba ya fada ba har ransa, can ya mike ya koma parlon Ummi..... Hauka ne kawai Aunty bata yi