Showing 321001 words to 324000 words out of 346625 words

Chapter 108 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

d'an takawa abinta, Umma dai takaici ma yasa ta kasa kallon Aneesah, she just finish checking all what is on the phone few minutes ago, ita ta ma fi Ummi da Abuturrab shiga wayar deeply, abun yayi muni ainun, Kuka kawai Aneesah take yi tana cewa ta shiga uku a gaya mata me tayi Aliyu ya saketa, Ummi ta girgixa kai cike da takaici tace "Baki kyauta ma kanki ba Aneesah, baki kyauta ba, kin cuci kanki, kin xalunci kanki, kin cuci rayuwar ki, kuma kin ci amanar aurenki, gaya min menene amfanin fornication Aneesah? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Aneesah ta dakatar da kukan da take xuciyarta na wani irin bugawa tana xare ido, Umma ta jefa mata wayarta tace "Allah ya shiryeki, ya kuma shirye masu ire iren halinki ya sa su gane, Allah ya rabamu da son xuciya irin naki Aneesah, sai kije kuma kiyi ta istigifari Allah ya gafarta maki...." Sai da Aneesah ta dauke wuta na kusan second goma ta dinga kallon wayarta da Umma ta jefo mata, Hajja ta tafe hannu tace "Allah ya isar ma jikana, Allah ya isar masa wllh...." Sai kuma ta fashe da kuka ta nemi waje ta xauna tayi tagumi tace "Dama duk tsawon lkcn nan da mazinaciya fasika yake xaune a gidansa bai sani ba, bawan Allah yana can yana neman na abinci a sararin samaniya bai rageki da komai ba na bukatar yau da kullum amma kike cin amanarsa haka, ashe dama uwarki bata gasa maki matancinki yanda ya kamata ba Aneesah, mu dai Allah ya isa wllh, na kuma gode Allah da bai sa mun hada xuri'a da mazinaciya ba, wllh da a Masar ne dama katon rami xa a haka a jefa yar iska ciki a bar iya katon kanki a waje, ayi ta jifa har sai kin mutu" Tsam Aneesah ta mike ko ina na jikinta na rawa ta dau wayarta ta fice daga parlon, kamar xata tashi sama ta dinga tafiya har xuwa inda xata samu adaidaita sahu, ta tsayar ta sakar masa kuka tace "Don girman Allah ka taimaka ka ajiye ni nan nan ba nisa bawan Allah, wllh ina cikin tashin hankali babu ko sisi a jikina, ka rufa min asiri bawan Allah" Mai adaidaitan ya tausaya mata yace ta shiga, ya ajiyeta har kofar gidan Abuturrab, ta sauka bakinta na rawa tace "Nagode" a guje ta shiga gidan ta nufi entrance, mai gadi dai ya bi ta da kallo, murda kofar parlon tayi ta shiga kamar an cillota, Abuturrab na xaune parlor kasan carpet Jiddah kuma na xaune opposite dinsa tana yanka masa watermelon ya kafeta da ido ko kiftawa baya yi.... Duk suka daga kai suna kallon Aneesah.


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp








Mikewa Abuturrab yayi ganin ta nufo su yana mata wani kallo furiously ya nuna mata kofa yace "Fitar min daga gida Aneesah, don't make the mistake of coming closer, leave my house immediately Aneesah..." Cikin tsawa ya kare maganar, ta taho kamar mahaukaciya without minding his words ta cakumosa cikin daga murya tace "Ka gaya min abinda na maka ka sakeni Aliyu?" Bai jira ta rufe baki ba ya shaketa sannan ya wurgar da ita kasa da karfi, Jiddah ta mike da sauri ta nufesa ganin yayi kan Aneesah ta rikosa tace "What is this u are doing?" Ko sauraronta bai yi ba ya dago Aneesah da ta kasa motsi bayan ta fadi kasan tiles, wasu tagwayen mari ya kai mata yace "U still have the guts to question me, u still have d guts to walk into my house? who advice u to come after me? Who gave u this deadly advice" Ya sake lafta mata mari, ya jefar da ita kasa yana ball da ita towards d door kamar ya samu kwallo, fixgosa Jiddah tayi cikin tashin hankali tace "Wai don Allah meye haka kake yi? What is this u are doing" Sai kuma ta fashe da kuka still holding onto him tana jijjigasa ganin bai fasa ball da Aneesah ba, ta dinga cewa "Stop this plss Aliyu, me tayi maka haka, do u have the heart of beating a woman this way??? Are u this wicked? Did a lady deserve this from u?" Bai san sanda ya tura Jiddah saman kujera ba, ya tafi xai dau wayan wuta gun kayan kallon da ke parlon gaba daya ransa ya gama baci biyosa da Aneesah tayi, Da Aneesah ta samu ta mike ta xagaye kujeran a guje ta cafko Jiddah ta shaketa da karfi tana cewa "Ke kika rabani da mijina, ke ki sa ya sakeni, ke kika hada komai da ya faru, yau xan ga ko da gawarki xai kare rayuwarsa, wllh sai dai wata ba ke ba" Abuturrab ya nufeta with full speed yana kokarin freeing Jiddah daga rikonta, komawa tayi kamar mahaukaciyar gaske tana gwale ido tana ci gaba da shake Jiddah, duk da dukan da yake kai mata taki sakinta, gaba daya hankalinta da idonta na kan wukar da ke kasa kan tray, kamar dai wancan lkcn da ta rike Jiddah a asibiti yau ma hakan ne tayi, duk karfin Abuturrab he couldn't free jiddah, duka ba na wasa yake mata ba amma taki cika jiddah, idan kuma yace xai yi amfani da force he will definitely hurt Jiddah, wani kukan kura Aneesah tayi ta hankade Jiddah ta fada kanta tana kokarin jawo wukan da take ta kallo da hannunta tana cewa "Wllh sai na kasheta idan ya so nima a kasheni, gwara in kasheta nima a kasheni duk mu bar duniyar babu me xama da kai...." Abuturrab yayi hanxarin sa kafa yayi wani ball da wukan kafin hannunta ya kai kansa, ya duka kasa ferociously ya kama hannun da ta so daukan wukan da shi yayi masa wani mugun murda har sai da yaji hannun yayi wani kara sannan ya sake, lkci daya jikinta ya mutu tayi wani karan axaba ta kasa ci gaba da rike Jiddah, with full strength ya dagota sama daga kan jiddah, ya dinga kifa mata mari yana kai mata kulli, jefar da ita kasa yyi yana haurinta yana tattaketa, ihu kawai take yi ta kasa tashi sbda hannunta da taji kamar baya jikinta gashi ta kasa daga hannun, ya kara dagota da hannu biyu ya bugata da pillar din dinning area, jini ke xuba ta bakinta da hanci, mari kuwa har sai da yaga palm dinsa sun kwanta a fuskarta sannan ya dinga jan ta kamar rago ya nufi kofa da ita, bai tsaya ko ina ba sai bakin gate ya wani cillata waje yana kallon mai gadi da ya ja gefe a tsorace, cikin tsawa yace "Kada ka sake barin ta shigo gidan nan, ka ji me nace maka??" Mai gadin ya gyada kai da sauri yace "Na ji Yallabai..." Aneesah ta mike da kyar ta xube kan gwiwowinta tana son hade hannunta amma ta kasa daga daya hannun nata, gaba daya tayi weak, cikin kuka sosai tana maida numfashi tace "Don girman Allah kar ka min haka Aliyu, wllh ina sonka baxan iya rayuwa babu kai ba, don darajan annabin Rahama kar ka gujeni, wllh xan iya kashe kaina idan na rasaka, I can't continue leaving without you Aliyu, wayyoo na shiga uku na lalace, kar ka rabu da ni Aliyu" Tuni Abuturrab yayi banging gate din ya sa lock ya nufi entrance din gidan da sauri, Xubewa yayi gaban Jiddah dake kwance yanda ya bar ta, ya dagota yana jijjigata yana kiran sunanta a rikice.... karfe sha daya da few minutes Abuturrab ya rako Ahmad bakin motarsa, gaba daya he isn't himself, Ahmad ya juya yana kallonsa yayi patting shoulder dinsa yace "She will be fine in sha Allah, u need not to worry Bro..." Abuturrab ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya kawai bai ce masa komai ba, Ahmad yace "Xan shigo gobe da safe idan Allah ya kai mu" Cikin sanyin murya Abuturrab yace "Ohk... Thank you Ahmad" Yana tsaye har Ahmad yayi reverse ya bar anguwan, sannan ya juya ya koma cikin gate din gidan ya kulle, yana shiga parlor ya kulle gidan ya haura sama, dakinsa ya nufa ya xauna gefen gado yana kallon Jiddah dake bacci, ya kai hannu goshinta a hankali yana kallonta with pity, bayan kusan minti goma ya jinginar da kansa jikin gadon ya lumshe idonsa. Cikin dare ya bude ido da sauri jin tana motsi don har bacci ya daukesa, ya gyara xamansa yace Jiddah, ta bude ido da kyar ya kamo hannunta yace "How are you feeling now?" Kanta kawai ta nuna masa, ganin mikewa xaune take son yi ya dagota da damuwa yace "Xai daina in sha Allah, should i make u tea or anything?" Ta girgixa masa kai da kyar tace "I want to ease my sef" Ya mike ya dagota ya kai ta har bathroom din suka fito tare, kuka ta sakar masa sbda ko ina na jikinta ciwo yake mata sosai, ya dauketa ya kwantar gefen gado ya durkusa gabanta yana kallonta cike da tausayinta yace "Kiyi hakuri plss wife, i caused u all this..." Throughout daren haka ya dinga lallabata bai yi bacci ba yana mata tausa a hankali, a haka har ta koma bacci wajen karfe hudu.... Ana idar da sallan asuba ya kawo mata shayi ya lallabata ta sha sannan ya bata magungunan da Ahmad ya taho da shi jiya bayan alluran da yayi mata, tana shan maganin babu dadewa bacci me nauyi ya dauketa, sai a sannan Abuturrab ya samu ya kwanta gefenta shi ma yayi baccin da bai yi ba daren jiya. Da rana ya dawo daga gidan Umma bayan ta kirasa yaje ya amsar ma Jiddah abinci don Ahmad ya bata labarin abinda ya faru, har da ta shirya xata taho yace mata ai da sauki ba sai ta je ba kawai tsorata Jiddan tayi but she is getting better, yana isa kofar gidansa ya tuna fa bai sake shiga gidan Hajiya Fatima yace da ita komai a kan xuwansu hayi ba, and that's very bad, sauka yyi motar bayan yayi parking a waje ya shiga gidan nata, bayan sun gaisa ya sanar mata jiddah ce bata ji dadi ba amma idan taji dama ko xuwa la'asar ne sai su fito su je can din, Hajiya Fatima tace "Allah sarki, Allah ya bata lafiya, kun je asibiti kuwa?" Yace "Cousin dina ya xo ya dubata kuma ya bata magunguna" Tace "Toh Alhmdlh, duk sanda taji saukin sai muje babu damuwa, kila xuwa magrib ma in shigo in dubata, Allah ya bata lafiya" Yace "Ameen na gode Mama, Allah ya kai mu" da haka yayi mata sallama ya fita gidan, motarsa ya shiga mai gadi ya bude masa gate ya shiga ciki yayi parking sannan ya sauka ya dau warmers din abincin ya wuce ciki, mamaki ne ya cikasa jin kamshi me dadi na turaren wuta dake tashi a each and every angle of the parlor, ya dinga bin parlon da kallo don an goge ko ina, murmushi yayi ya karasa tsakar parlon ya ajiye warmer din abincin ya haura sama, dakinta ya fara shiga nan ma dai sai kamshi yake tayi tidying ko ina, ya kullo kofar a hankali ya tafi nasa bangaren, lumshe ido yayi ya bude don kamshi ne ya hadu da sanyin ac, daga bedroom din har parlor nasa, yaushe rabo? Murmushi yayi ya juya ya koma downstairs ya shiga kitchen, ta gama wanke wanke tana goge wajen gas ta juya tana kallonsa, English dressing tayi ta daure dogon gashinta da ribbon, ko hulan ma bata sa ba, wanda ko tayi irin dressing din a gidan Umma sai ta sa hijab duk da isu isu ne a gidan, yau kuma kam bata sa hijab din ba, sunkuyar da kanta tayi tace "Sannu da xuwa" Ya shiga kitchen din giving her a hug from d back ya lumshe ido fuskarsa a kan gashinta yayi kasa da murya yace "Duk ke da baki da lafiya kika gyara gidan nan haka Babyna??" Ta rufe idonta a hankali tace "Na ji sauki" Rasa abinda xai ce mata yayi, yana jin sonta a ko da yaushe na komawa sabo a xuciyarsa, anya Jiddah xata bari yayi concentrating a aikinsa kuwa? Anya xai iya tsayawa without her close to him for good 5 days kuwa, da kansa ya ba ma kansa amsa da No a xuciyarsa, juyowa yaga tayi a hankali ta shige jikinsa tana boye fuskarta a kirjinsa, daga nan kuma labari ya canxa ma Abuturrab... Bayan la'asar yana dawowa daga mosque ya tafi bedroom dinsa, xaunawa yayi gefen Jiddah dake bacci yana jan dogon hancinta a hankali yana kallonta yace "Sallah plss" Ta bude idonta, ya dagota xaune yace "Kiyi sallah mu ci abinci" ta daure gashinta sannan ta sauka kan gadon ta tafi bandaki, ya mike ya sauka kasa. Da kansa ya dinga bata abincin tana jikinsa, idan ya bata sai shi ma ya ci, ya lura bata son cin abinci da yawa don sai lallabata yake tana ci da kyar, hakan da take kuma narkar masa da xuciya yake, he just can't get enough of her love... Daga karshe ya rufe abincin don wannan abinda take ma ya sa yaji ya koshi kawai, ya manna mata kiss a forehead dinta underneath his breathe yace "Ina sonki matata" tashi tayi xaune daga jikinsa tayi kasa da murya a hankali tace "Ka gaya min sanda xan koma schl pls" Shiru yayi ya ki ce mata komai lkci daya kuma mood dinsa ya canxa, ya dau remote yana changing channel, kallonsa kawai Jiddah take jin ya ki cewa komai, yayi mata side hug yayi kasa da murya yace "What do u need apart from me again in this life Jiddah? Me xa ki yi da wani schl?" Ta gyara xama tana kallonsa da mamaki tace "You mean i won't go to schl again? Ko waec din ma fa ban yi ba" Ya rungumeta ya kai bakinsa kunnenta pleadingly yace "Pls ki cire wani schl a ranki, babu abinda xaki rasa a rayuwar nan ko bayan rai na my wife..." sai kuma yyi shiru, kankameta yayi yace "Gaskiya ina da kishi sosai, bana son a dinga kalle min mata anyhow, don haka baxa ki kara komawa wani schl ba..." Jiddah ta rasa ma me xata ce masa don she is a bit shock, ya girgixa kai yace "Ba ki ga ko farkon xamanki gidana ba naki sa ki schl duk da maganan su Umma, why because ina kishin matata... Ina da kishi sosai, fiye da yanda kike tunani Jiddah, ko me kike son koya ni xan koya maki a gida babu abinda xaki yi da wani kwali bayan mijinki na da rufin asirinsa, idan ma kince salary kike son in dinga baki wllh ni xan raba albashina biyu in dinga baki rabi duk wata, i think that's what we will do plss, idan kina son farin ciki na kada ki sake min maganan boko plss...." Hawaye ya gani a idonta, ya dinga kallonta, sai kuma ya jinginar da kansa da kujera yace "Shkkn ki shirya ki koma schl din" daga haka ya mike ya wuce sama ta bi sa da kallo hawaye na sauka idonta. Har aka kira magrib bai sauko ba ita ma bata je saman ba, mamaki kawai take wai baxata sake xuwa schl ba, da ta tuna wannan furucin nasa sai taji hawaye ya taho mata, saukowa yayi ya fita parlon without looking at her ta bi sa da kallo, da kyar ta iya tashi ta tafi dakinta ta je tayi alwala. Da kayan shayi Abuturrab ya dawo gidan duk da ba wai na gidan ya kare bane, ya kai su kitchen ya ajiye ya dawo parlor ya xauna, bai kai minti goma xaune ba aka danna bell, ya juya ya kalli kofar sannan ya mike ya karasa can, yana bude kofar ya ga Hajiya Fatima ce, murmushi yayi ya bata hanya yace "Sannu da xuwa mama" ta shigo parlon tace "Yauwa sannu Aliyu, ya mai jikin" yace "Alhmdlh, bari in kirata" Sama ya wuce, Hajiya Fatima ta xauna parlon tana yaba wannan turaren wuta me shegen dadin kamshi da aka sa a parlon a ranta, don ya kama ko ina and the scent is so heavenly, Abuturrab ya fara saukowa kasa sannan Jiddah, da murmushi ta xauna ta gaida Hajiya Fatima, Hajiya Fatima tace "Lafiya lau Jiddah, ya kika kara ji?" Ta sunkuyar da kanta tace "Na ji sauki Mama....." Hajiya Fatima tace "Toh Allah ya kara afuwa, dama daxu da ya shigo yace min baki ji dadi ba shine nace bari in leko in duba ki, kuma naga kam jiki Alhmdlh" Jiddah tace "Nagode mama Allah ya kara girma" Hajiya Fatima tace "Ameen, amma wannan turaren wutan naki a ina kika siya kuwa" Jiddah tayi murmushi tana jan fingers dinta tace "Umman mu ce tayi order wajen S.SQuare Collection" Hajiya Fatima tace "Ikon Allah a wani kasuwan?" Jiddah tace "Aa a Gombe matar take, amma tana turawa ko ina" Hajiya fatima tace "Toh bani number ta, na jima ina neman turare me kyau haka ban samu ba sai dai a cinye maka kudi kawai" Jiddah na murmushi tace "Xan tambayar maki Umma idan na amshi number sai in kawo maki gida, ni wayata ta fashe" Hajiya Fatima tace "Toh shkkn, ina saurare" Sallama tayi masu Abuturrab yace "In sha Allah gobe xa mu je can hayin Mama" Tace "Allah ya kai mu lfya" Har balcony suka rakata ta wuce, Abuturrab ya haura sama Jiddah ta bi sa da kallo. Washegari da yamma suka wajajen karfe biyar dau hanyar hayin rigasa a motar Abuturrab, Hajiya Fatima na xaune bayan motar, Jiddah kuma na xaune gaban motar, tunda suka kamo hanya take bacci heavily, lkci lkci Abuturrab dake hira da Hajiya Fatima yake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login