Showing 336001 words to 339000 words out of 346625 words

Chapter 113 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

Hansai, yau kam bai yi mistake din xuwa anguwan ba nose mask ba, tunda yayi parking Umma ke kallon layin da gidan yake, suka sauka daga motar ya nuna mata gidan, Umma ta shiga ciki ya tsaya daga waje ya ki shiga, da ya tuna irin abubuwan da Hansai ta dinga ma Jiddah a hayi da irin axabar da ta dinga gana mata tana amfani da ita tana making kudi shi kansa dubi irin karyan da ta dinga lafta masa ya bata kudinsa yayi dubu dari biyar sai yaji wani bacin rai ya xo masa, and he believes the situation she is right now serves her right, don haka ko digon tausayinta baya ji wllh, Umma na shiga dakin ta rasa wajen xama ga wani doyi da dakin yake, Hansai dake xaune kan darduma da wani rubabben fitila da ya d'an haske dakin ta amsa sallamarta cikin sanyin murya sai kuma ta mike ta shimfida mata buhun cement a kasa tace "Sannu" Umma ta daure ta xauna tace "Yauwa nagode... ya gida?" A hankali tace "Lafiya lau" Umma ta kunna wayarta ta ajiye sai kallon Hansai take ganin yanda idanuwanta suka wani kumbura tace "Amma in ji dai lafiya baiwar Allah" Kamar jira take ta fashe da kuka tace "Yau kwana uku Allah yayi ma 'ya ta rasuwa..." Sai ta dinga rusa kuka, Umma tace "Hasbunallah, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya gafarta mata" cikin kuka Hansai tace "Ameen" Umma ta girgixa kai tace "Nasan baki san ni ba, ni ce uwar rikon Jiddah sannan kuma kanwar uwar mijinta" Hansai ta dinga kallon Umma sai kuma ta sunkuyar da kai, Umma tace "Na xo neman wata alfarma ne a wajenki" Cikin rawar murya Hansai tace "Ina jin ki Hajiya, Allah ya sa bai fi karfina ba, ni ma kuma ina son rokon wata alfarka a gareki" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "In sha Allah" a hankali Hansai tace "Toh wacce alfarman kike so wajena Hajiya?" Umma tace "Hoton mahaifin Jiddah xaki bamu idan har kina da shi don Allah" Hansai ta goge idonta tace "Baxa a rasa ba" Tana fadin haka ta mike ta bude Ghana must go da ta ciro hoton kakar Jiddah da mahaifiyarta, ta dubo hoton mahaifin Jiddah wajen kala shidda ta ajiye ma Umma har da wanda yake saurayi, Umma ta dau hotunan tace "Toh nagode kwarai da gaske, ki fadi ta ki alfarman..." Hansai ta xauna a sanyaye tace "Alfarma daya nake so Hajiya don Allah a bar ni inyi xumunci da Jiddah, ko da sau daya ne a shekara in dinga ganinta xanyi farin ciki wllh, nasan na xalunceta na ci amanarta da na mahaifanta amma na roketa yafiya kuma tace ta yafe min yau wata hudu kenan tun xuwansu gidan nan, in ci albarkacin ubanta kada a rabani da ita don girman Allah" Hawaye kawai take tana shessheka, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh in sha Allah, xa ku yi xumunci" Godiya Hansai ta dinga yi ma Umma kamar xata ari baki, Umma ta bude jakarta ta ciro dubu biyar tace "Kiyi hakuri da wannan sai mun sake dawowa, duk da gobe ko jibi xa mu xo din tare da Jiddah ta yi maki gaisuwar yar uwarta in sha Allah" Har bakin mota Hansai ta raka Umma duk jikinta a sanyaye, har ranta take son rayuwa tare da Jiddah gatan da bata gwada mata ba tun ubanta na da rai har ya rasu tana son ta gwada mata yanxu duk da bata da komai, so take kawai ta ja ta a jiki tamkar bibalonta, tana ganin Abuturrab ta duka tana gaishesa, ya amsa a takaice ya xaga ya shiga driver seat ta bi sa da ido, Umma ta bude gaba ta xauna tana daga ma Hansai hannu har suka bar anguwar, sosai taji tausayin matar, lallai kam ita taga kamun Allah tun a duniya. Suna komawa gida da hoton Abban Jiddah Hajja tace Inaaa ai hoton baxai kwana ba aje a nuna ma mijin Hajiya Fatima kawai, haka suka shirya da ita da Umma, da Jiddah da Abuturrab xuwa gidan Hajiya Fatima bayan isha.....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp







Tun da suka shiga compound din gidan Hajiya Fatima Hajja ke washe baki tace "Toh kun ga dai, ai basu wani nuna su masu kudi bane da suka je can gida duba Jiddah, to haka ake son mutum wanda bai da burga ko fafa, kuma da irinsu ya kamata ayi xumunci, naji dadin yanda suka tsaya kan jiddah har ta ji sauki, ji yanda babbar er nan tata me mota ta dinga kula da Jiddah a asibiti tana nan nan da ita, to kuwa idan ma ku baxa ku yi xumunci da su ba ni dai xan yi" Abuturrab dake ta kallonta yace "An ce maki suna xumunci da mutan Masar ne?" Hajja ta juya da sauri baki bude ta kallesa tace "Meye da Masar din?" Bai sake tanka ta ba har suka shiga parlon Hajiya Fatima, sosai Hajiya Fatima tayi welcoming dinsu ta kawo masu fruits iri iri a tray da bottle water ta ajiye masu, Hajja sai wani murmushi take tana kallonta tace "Kinga yanda kika yi din nan? Wllh haka suke yi a Masar.... Kya ga kayan marmari iri iri a tray an ajiye ma baki, ko jarkan madara da cinyoyin kaji" Hajiya Fatima tace "Ikon Allah..." Hajja tace "Wllh, kin san daga Masar nake, daga xuwa bikin jikana shine na rashe a Najeriya, suna can suna ta kewana kullum sai sun kirani kira me motsi ta waya mun gaisa" Hajiya Fatima tace "Allah sarki, da kawai kiyi xamanki tunda kin dawo Baaba" Hajja tace "Inaaa xan iya kirga maki sau nawa na ci kaza tun Dawowata kasar nan, can kuwa gasu nan baja baja har sai ka ture, ke dai kawai ayi harka er nan" Hajiya Fatima ta dinga murmushi, Umma ta kalli agogo tace "Hajiya sai kika gan mu da daddare ba notice" Hajja ta amshe tace "Wllh kuwa ni na takura a taho ko min dare don ba a wasa da lamari me muhimmanci irin wannan, na lura in dan ta su ne sai dai a shashantar da xancen a hau wata sabgar can, kinga kenan yarinya bata da makubuli, sannan idan aka samo danginta ai babu wanda xai ta gadara da ita babu gaira ba dalili, to in gaya maki shine na basu shawaran aje duk inda matar uban Jiddah take a amso hotunan uban nata sai mu taho mu nuna maki, amma dai ina shi mai gidan naki yake tukun?" Hajiya Fatima tace "Yana sama Hajiya" Hajja ta kalli Umma tace "Mika mata hotunan ta gani, idan mu bamu san fuskar mijinta ba ai ita ta sani" Umma ta xuge zip din jaka ta ciro hotunan Baban Jiddah, Hajiya Fatima ta taso ta amsa tana kallo with much interest, waje ta nema ta xauna ba tare da ta shirya yin hakan ba tana ta maimaita kallon hotunan guda hudu dake hannunta babu ko kiftawa, Hajja tace "Toh kinyi shiru, gaya mana ai xaki yi ko yana kama da mijin ki ko baya yi" Hajiya Fatima ta dago ta kalli Hajja, tayi shirun kusan 5 seconds sai kuma ta sauke ajiyar xuciya tace "Bari in kai masa Hajja...." Daga haka ta mike ta wuce sama, Hajja ta gyara xama tayi kasa da murya tace "Da kyar idan ba mijin ne baban Jiddan ba, kawai dai yayi guduwansa ya dawo cikin gari yayi aurensa sbda wahalan duniya ya ishesa, ita kuma ina jin mijinta ya mutu ya bar ta da narka narkan 'ya ya da uban dukiya" Abuturrab ya dakatar da ita so pissed off yace "Menene haka don Allah?" Hajja tace "Aa kar ka min tsawa daga na fadi gaskiya xaka hayayyako min, ko kai baka ga yanda jikinta yayi sanyi qlau ba? Ai taga mijin nata ne a hoton, nan kuma bata san ya ta6a aure har da ya ya ba..." Umma tace "Kin ga mu ba abinda ya kawo mu gidan nan ba kenan Hajja, ya xaki dinga irin wannan maganganun a gidan mutane?" Hajja tace "Toh ba sai in ji duka ba, daga fadan gaskiya sai ai min caaa, ko gabanta ance maku baxan fada hakan ba tunda ba tsoron wani d'an banxa nake ba" Ita dai Jiddah ta kasa dago kanta, Abuturrab yace "Umma wai wa yace ta biyo mu ne?" Hajja tace "Uwarka Ramlah tace in biyoku don bana xagi Hauwa ko Usman ba tunda basu min komai ba..." Saukowan Alhaji Ishaq da Hajiya Fatima ya sa Hajja tayi shiru, Ya karaso parlon ya gaida Hajja, Abuturrab ya gaishesa, sannan suka gaisa da Umma, ya xauna a one sitter yana kallon Jiddah da ta ki dago kanta gabanta na faduwa yace "Ya jikin naki?" Jiddah ta dago da kyar lokaci daya hawaye ya kawo idonta jin muryar tasa kamar Abbanta ne yayi magana, cikin sanyin murya tace "Na ji sauki" Yace "Allah ya kara afuwa" Hajja tace "Ameen dai, ka dai ga hotunan da aka kai maka, ince kai ne a jikin hoton ko?" Ya girgixa kai yace "Ba ni bane Hajiya, amma nasan ina da alaka da koma waye a hoton, nasan wanda ke jikin hoton nan jinina ne..." Hajja tace "Yo ai ya rasu aka ce tun tale tale, ga er tasa dai can a xaune...." Alhaji Ishaq ya kara kallon Jiddah yace "Ya sunan baban naki?" A hankali Jiddah tace "Yusuf" Alhaji Ishaq ya jinginar da kansa da kujera yayi shiru, sai kuma ya kalli Hajiya Fatima bayan few seconds yace "Ina khaleesat?" Mikewa Hajiya Fatima wanda kana ganinta kasan gaba daya a sanyaye take ta tafi dakin khaleesat, sai ga su sun dawo tare, Hajja na ganin Khaleesat ta bude baki tace "Lahhh kaga wllh suna yanayi da Jiddan er kace wannan din?" Yace "Ya ta ce, don a shekaranjiya da na shigo parlon ma nayi tunanin wannan ce a xaune" Hajja ta saki salati tace "Ikon Allah ya fi gaban haka, toh yanxu kai baka da wani d'an uwa da ya 6ata ko ya shiga duniya shekaru aru aru ba a gansa" Alhaji Ishaq ya d'an yi murmushi yace "Ina dai neman Alfarma a bamu ita wannan yarinya mu tafi can garinmu gun mahaifiyata da ita, xa aji komai daga bakin ita mahaifiyar tawa idan munje" Hajja tace "Yanxu mahaifiyarka na nan da ranta?" Yace "Tana nan Hajiya" Hajja tace "Huhuhu, to ko gobe kace mu tafi ba sai mu tafi ba d'an nan, idan ya so a bamu daki kawai mu kwana a nan gidan" Umma ta kalli Hajja haka ma Abuturrab, Hajiya Fatima tayi murmushi tace "An baku Baaba, Allah ya kai mu goben lfya" Umma ta d'an yi murmushi tace "Amma da dai a bari jikinta ya d'an kara kwari ko xuwa jibi ina ga xai fi ko..." Hajja ta kalleta da sauri, sai kuma tace "Toh ai ba wasan yara bane wannan da xa a bari har jibi Ramlah, yanxu dai ki tashi Aliyu ya maida ku gida ni da Jiddah mu kwana nan din kin ji dai an bamu daki, idan ya so idan kinga xa aje garin dake tunda ke ce uwar rikonta sai ki fito da sassafe ki riske mu sannan a kama hanya, amma ba batun da xa a bari har jibi bane wannan kinji Ramlah" Abuturrab ya dinga kallon Hajja kamar ya shaketa, Umma tace "Allah ya kai mu goben, Hajiya bari mu kama hanya dare na yi" Hajja na kallon Aliyu tace "Sai ka amshi makullin daki na wajen Hauwa ka debo min kayana kala biyar, ita ma Jiddah ka bamu makulli mu bude gidanka mu shiga ta debi kayanta" daga haka ta mike tana kallon Jiddah tace "Tashi mu tafi sama a nuna mana dakin, Allah ya kai mu goben lafiya" Hajiya Fatima ta mike tana murmushi tace "Mu je a kai ku dakin" Jiddah sai kallon Abuturrab da ya hade rai take, Hajja tace "Toh ki taso mana ina maki magana" Tashi tayi a hankali ta bi bayansu Hajja, Alhaji Ishaq dai murmushi kawai yake, Umma ta mike tace "Toh Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya Alhaji, sai da safe" Yace "Ameen, Allah ya tashe mu lafiya, mun gode kwarai" Abuturrab ma yayi masa sallama sannan suka fita da Umma. Bayan Hajja ta ci tayi nakk wajen karfe sha daya, tana xaune kan katon gadon dake dakin da aka basu daga kasa kuma shinkafa ne da miya da coslow ga soyayyen kaji sai farfesun kifi da aka masu sharp sharp, tana kallon Jiddah da duk bata da walwala tayi kasa da murya tace "Ke baki ga wani kankanban da Ramlah keyi a gaban shi me kama da baban nan naki ba, to ko sonsa ta ji ta fara yi wa ya sani, kinsan mijinta xai shekara goma sha daya da rasuwa kuma ta ki aure, to idan ba sonsa take ba meye na wani make murya tace a bari sai jibi aje garin, ina ruwanta?? Wllh ban ta6a ganin haka ba tunda aka haifeni, idan ma sonsa take matar gidan nan dai ta fi karfinta" Murmushi kawai Jiddah tayi Hajja ta gyara kwanciya tace "Atoh, ni ba ruwana wllh" Washegari karfe takwas Alhaji Ishaq suka dau hanyar garin gombe, Ali ne ke driving din Abban nasa na xaune kujera me xaman banxa, Hajja da Jiddah sai Hajiya Fatima na xaune back seat.... Da yamma suka iso cikin garin gombe, Ali yayi parking a kofar gidan kakarsa, shi da Abbansa suka shiga masallaci yin sallan La'asar Hajiya Fatima tayi leading din su Hajja xuwa cikin gidan har parlon Hajiya Dada warce ita ce mahaifiyar Alhaji Ishaq, Hajiya Dada ta dinga masu sannu da xuwa baxa ka ta6a cewa ta kusa dari ba don da sauran kwarinta, sauran yaran nata duk suna gidan suna jiran isowar Alhaji Ishaq, wanda shine babban yayansu, su ma dai suka dinga welcoming dinsu... Bayan kusan minti ashirin Alhaji Ishaq ya shigo ciki tare da Ali don sai da ya tsaya gaisawa da 'yan anguwan da suka dinga kawo masa gaisuwa wanda hakan kadai xai sa ka fahimci yana siyasa ne. Hajja na kallon Jiddah bayan ta idar da sallah ta rike ha6a tace "Ke kiga kantamemen gidan da suka gina ma tsohuwar nan kamar baxata mutu ba..." Jin Jiddah bata tanka ta ba ta kyabe baki ta jawo warmers da aka tula masu a dakin, Hajiya Fatima ce ta shigo duk tayi serving dinsu abincin sannan ta fita, Hajja ta kara rike ha6a tace "Lallai manyan mutane ne, sai kace ina gidan kabiru don ma dai wahala bai isheni ba ai da babu uban da xai sa in bar gidan Kabiru yanda kika ga haka fa haka ake min a fadar nan ta Bauchi, to amma ni din ce wahalalliya inyi ta rabe rabe a kaduna ana hantara ta" Wajen karfe biyar Hajiya Fatima ta yi ma Hajja da Jiddah iso xuwa babban parlon Hajiya Dada, yaranta biyar a duniya kuma duk suna xaune parlon, maxa biyu mata uku, ko wannensu kana gani kasan nera ta xauna ne kawai, Jiddah ta sunkuyar da kanta bayan ta gaishesu gaba daya, su kuma suka dinga gaida Hajja ana tambayarta ya gajiyan hanya, bayan an gama gaishe gaishe Alhaji Ishaq ya mike ya isa gun mahaifiyarsu ya durkusa ya mika mata hotunan hannunsa yace "Dada kin gane waye wannan a hoton nan?" Hajiya Dada ta dau gilashinta ta saka tana kallon hotunan da kyau, wani murmushin takaici tayi tace "Wannan ai Yusif dina ne, bana ce maku yana nan raye ba babu wanda yake yarda dani ana ganin kamar xaucewa nayi, nasan yusif bai mutu ba, to ina yake yanxu? A ina yake?" Hajja ta daga hannu tace "Aa mu dai ya rasu kusan shekaru biyar kenan, sai dai ga er cikinsa nan a kusa da ni..." Hajiya Dada tayi shiru tana kallon Jiddah, sai ta fashe da kuka tana girgixa kai, duk kowa yayi shiru a parlon, a hankali ta fara magana tace "A shekaru kusan hamsin da suka wuce a kasar nan ina jin babu wanda ya kai mu shiga tsananin rayuwa da rashi da muke ciki da ni da mai gidana da abokiyar xamana, mai gidan namu ba shi da komai sai gona daya tak shi ma gadon mahaifinsa ne da ya ci, Yusuf shine d'a na na uku, ita kuma kishiyata Kulu a lkcn tana da ya ya biyu ita ma duk maza, duk da rashi irin na mai gidanmu Malam Sunusi haka ya dau son duniya ya daura ma Yusif don duk cikin yaran nasa ma ya fi kama da shi, babu abinda ya raga ma Yusif komai yi masa yake toh ashe hakan na kona ma ita kishiyata kulu rai ni duk ban sani ba, mai gidanmu ya sha siyan karamin dabba idan ya d'an samu kudi ya kawo gida yace a kiwata ma yusif, komai na gidan nan yace yusif, kwatsam watarana muka wayi gari babu Yusif babu dalilinsa a cikin gida, neman duniya dai a garin nan na gombe anyi amma ba a ga yusif ba, a lkcn yana da shekaru 4 kacal a duniya, na shiga tashin hankali da baya faduwa yanxu haka, wato mahaifinsa ma ya fi ni shiga tashin hankalin, ita kanta kishiyar tawa kullum cikin tayani kuka take, amma ya muka iya da wannan kaddara? Bayan shekaru biyu babu wani labari na ganin yarona muka tabbatar baxa mu sake ganin Yusif ba ya 6ata ne na har abada, amma ni dai ban cire rai ba kullum addu'a nake Allah ya bayyana min shi, kusan duk dare sai nayi kukan 6atan yusif dina, bayan shekara 49 da 6atan Yusif wato ina maganan shekaru biyu da suka wuce kenan, bayan shi mahaifin Yusif ya ma rasu da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login