Showing 303001 words to 306000 words out of 346625 words
Chapter 102 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
Aneesah ma na bacci ko sallah bata yi ba ya dau jakar laptop dinsa da komai, snn ya buga gefen gadon yace "Na tafi...." Ta mike xaune tana murxa ido duk da haushinsa da take ji tace "Da wuri haka?" Yace "Yea i will be driving to kano, plss and pls Aneesah i want nothing but peace, i am begging u, kinga kece babba i am expecting nothing sai kwanciyar hankali har in dawo" Tayi wani murmushi tace "In sha Allah Captain baxa ka samu akasin haka ba, Allah ya tsare" Juyawa yayi ya fita ta mike da sauri bayan ta ji fitarsa gaba daya daga parlonsa, lekawa tayi taga ko xai tsaya kofar dakin Jiddah amma sai ta ga otherwise don sauka kawai yayi downstairs bai ko kalli kofar dakin ba, tayi wani murmushi ta juya ta koma ta ci gaba da baccinta, Jiddah na xaune kan darduma ta ji ya kunna motarsa, mikewa tayi a hankali ta isa jikin window tana kallon compound din, booth taga ya rufe bayan ya saka jakarsa ya nufi driver seat ya shiga yana gama warming motar mai gadi ya bude masa gate ya fita, Jiddah ta sauke idonta sannan ta juya ta koma gefen gadonta ta kwanta a hankali.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
FZ BEAUTY SUPPLEMENTS
Dealer in all kind of dietary supplements such for skin whitening, skin glowing, weight gain, slimming, flat tummy, infection killers, dark spots removers, fertility booster, Hips boosters, Breast firming and Enlarging, Teeth whitening, eye, joint, stretch marks, and for marital pleasure. All supplement are available for wholesale and retail. For more information contact FZ via wa.me/2348143821028
FZ Beauty Supplements
Dealer ce ta supplement masu qara fito da kyaun mace ko namiji, hadi da qarama garkuwar jiki kuzari. Muna sayarda Supplemnt kamar na qarin duwawu, akwai wanda zaya taimaka wurin dawoda martabar Nono, akwai na rage qiba da tumbi, akwai na rakwainuwa, akwai na tada komada, akwai masu saka hasken fata da qyalli, akwai na infection, akwai na saka hasken ido da hakori sannan akwai na gyaran turaka. Muna maraba da mai sayen daya ko sari. Wa.me/2348143821028
Karfe goma saura Jiddah ta bude kofar dakinta a hankali ta dalilin yunwan da taji ya dameta, tun da taga fitan Abuturrab daxu da sassafe ta tsorata da gidan kuma, material ne a jikinta na doguwa riga sai hulan da ta rufe gashinta da shi, ta fito daga dakin ta kulle kofar without making any sound tana satan kallon kofar dakin Aneesah dake can karshe duk tunaninta tana ciki, ta fara sauka downstairs shi ma bata yarda tayi making any sound ba, sosai gabanta ya fadi ganin Aneesah xaune parlon tana sanye da rigar bacci har sannan, ta daura kafa daya kan daya tana cin cake tana danna wayarta, xuciyar Jiddah ya dinga bugawa ta karasa cikin parlon tana tafiya a hankali, duk da yanda ta dinga avoiding su hada ido sai da suka hada idon da ita, daburcewa tayi, bata san lkcn da tace "Ina kwana" Aneesah tayi mata wani kallon daga sama har kasa, ta ja wani tsaki ta ci gaba da cin cake din hannunta tana danna waya, Jiddah ta sauke idonta ta nufi kitchen duk jikinta yayi sanyi, kulle kitchen din tayi ta turo baki ta jingina da kofar, sai taji haushin kanta gaisheta da tayi, to amma ai bata ma san sanda ta gaisheta ba, bin kitchen din ta dinga yi da kallo, duk da babu wani plate da aka bata amma kitchen din na bukatar gyara, rabon da ayi masa komai tun jiya da safe da ta yi, ta ta6e baki ta shiga store ta dau indomie guda daya a kwalli sannan ta fito, sai da ta fara daura kwai a kan wuta, tana tsaye har ya dahu, sannan ta fara girka indomie din, bata jima a kitchen din ba ta gama, ta juye indomie din a plate sannan ta rufe da wani plate ta dau fork ta bude kofar kitchen din ta fito, sosai gabanta ya fadi ganin wasu manyan mata har hudu a parlon tare da Aneesah duk sun cika parlon da muryarsu kamar ganga, da yake ta rufe kofar kitchen din shi yasa bata jiyo su ba tun daxu, tana fitowa parlor duk suka yi shiru, duk da ba kallonsu take ba amma jikinta ya bata duk ita suke kallo, har wani hardewa take tana tafiya da sauri, Chef salmah ce da Rabi'ah sai Suhaila da Fauziyya, duk kawayen Aneesah ne kuma sa'aninta da suka yi karatu tare a Abuja kana ganinsu ka ga gogaggun yan matan Abuja, Aneesah kadai ce ta dace tayi aure cikinsu, sauran duk gantalinsu kawai suke, kuma yawanci duk babu warce iyayenta ke nan kaduna kawai xamansu suke a garin, Chef Salmah da Rabi'ah ma su biyu kadai ke xaune gidan iyayen Rabi'ah dake Unguwan sarki, dukkansu suka bi Jiddah da kallo, Rabi'ah ta kalli Aneesah da wani expression tace "Wait... wai wannan er yarinyar ce kishiyar taki?" Aneesah ta kyabe baki tace "Wai ba" Wani dariya suka yi gaba daya har da kyakyatawa, Chef salmah tace "Kuturin uba!!! Yo ai wannam karamar alhaki ce Aneesah, ni wllh duk tunanina sa'ar mu ce aka kawo maki xa ku gwabza, yanxu da wannan er cikin naki aka hada ki kishi? To kiyi kishi da ita kice kinyi kishi da wa Aneesah?? Wllh ni duk sai naji raina ya baci, me aka yi aka yi wnn yarinyar, dubeta fa duk a tsorace kamar zomo...." Jiddah dake jin su ta nufi stairs ko juyowa bata yi ba tana jin kamar xata fadi sbda hardewar da take, Suhaila ta rike ha6a tace "Ikon Allah, yo minti nawa xa a 6ata wajen gamawa da wnn er yarinyar? Ni har kin ban kunya wllh Aneesah, ni fa na xata wata uwar mata ce ashe wai wnn kwailar aka kawo maki gida kika bi kika daga hankali kika bi kika ishemu a group" wani tsaki ta ja, Fauziyya ma ta ja tsakin tace "Wllh kwana uku yayi kadan idan ban sa xaman gidana ya gagareta ba shegiya nake, look how meek she is, wannan ai kamar kin samu er wanke wanke ne da share share, ya wuce ma ki aiketa ta amso maki kati ko cingam a kofar gida??" Duk suka kyalkyale da dariya, Rabi'ah tace "Toh ke yanxu Aneesah fasa kayan daki shine iya abinda xaki iya yi ki burge kenan? Is that all u can do? Haba wannan ai karamar alhaki ce" Aneesah tayi wani dariya tana jinjina kai tace "You guys are only being faster than ur shadows" Jiddah dai tuni ta shiga dakinta ta saka key, gaba daya ta tsorata da su, on a serious note Chef salmah tace "Kinsan Allah Aneesah lamarinki ya kunyata ni wllh, na xata xan xo in ga er 35 ne, wai ashe a kan wnn da kilan bata wuce 18 ba kika daga hankalinki haka" Aneesah tayi kasa da murya tace "I think i told u all yanda abubuwa suka dinga faruwa tun ma kafin ta tare, da rashin mutuncin da na dinga yi, yanxu abu kadan captain yake jira inyi shi yasa ku ka gan ni a yanda ku ka gan ni, shi yasa ku ka ga nayi shiru, wllh ba don mahaifiyarsa fa ranan da nayi ma kayanta aika aikan nan saki na yayi niyyar yi don har ya dauko takardan ta hanasa, banda haka ni dai kunsan ba kanwar lasa bace, kawai ku bar ni in ci gaba da bin su da ido for the mean time, ko kun ta6a ganin mutumin da bai kama dahir ba yana iskanci? Ai yanxu sai dai kawai in bi komai a hankali, domin kuwa a wuyar captain nake yanxu, nasan kuma babu wanda yake jin haushi sama da ni a duniyar nan, sarai na sani" Rabi'ah tace "Toh Allah ya kyauta, idan an kawo kayan mun gama gyare gyaren da xa mu yi sai mu tafi inda xa mu je kawai since akwai lkci, ni fa shi sa har yau ku ka ga naki amsa ma Alhaji Salisu, so kawai nake sai na gama duk abinda ya kamata tun daga waje, ta yanda ina shiga gidan komai ya dawo hannuna baxan iya wahala ba gaskiya, don haka sai na shirya tsaf anyi duk abinda ya kamata sannan xan basa izini ya turo" Fauziyya tace "Kina da gaskiyar ki wllh, wa xai xauna? Yan iskan uwayen gidan nan da jira kawai suke Allah ya kawoka su nuna maka takama da isa, to wllh ba ayi matar nan ba, shi sa muke shiri sosai kafin mu shiga...." Aneesah dai sai wani murmushi take tana girgixa kafa, jin ringing din wayarta ta mike ta isa gun wayar dake caji da sauri ta dauka ganin me kiran ta daga ta kai kunne, a d'an fusace tace "Ni ban ga wani alert ba har yanxu wllh, haba abu tun jiya dae kamar xa a turo min miliyan goma, gashi sbda rashin cikon kudin ba a turo min kayan ba har yanxu" Ta kyabe baki tace "Toh ina jira ni dai..." daga haka ta katse wayar, Fauziyya tace "Yanxu da mun xo karfe takwas da rabi haka xa mu yi ta xama kaya basu iso ba" Aneesah tace "Toh ba sai an samu cikon kudin ba sannan xa su iso Fauziyya, kun san fa na canxa furnitures din daga wanda na tura maku a group, wannan ya fi shi tsada, daga baya company din suka turo min wannan naga ya fi kwanta min kawai na xa6e sa" Sai karfe sha biyu motar kayan Aneesah suka iso gidan, kamar dai yanda aka yi na Jiddah ita ma haka sai da suka sauke sababbin kayan snn suka dinga fitar da fasassun waje suna lodawa a babban motar, kafin karfe uku masu kawo kayan duk suka shirya mata furnitures din sannan suka wuce... Suna xaxxaune da kawayenta a dakin bayan an gyara ya dawo fess, sai ya6a furnitures din suke, ita kuwa sai murmushi take tana bin dakin da kallo don ya fi nata na da kyau, miliyan 1.5 tayi kayan dakin, Babu warce ke da alamar tashi tayi sallan axahar cikinsu, Aneesah ta fita tayi masu rechauffe din jollof din dake freezer ta kawo masu dakin da drinks da ruwan gora, ko wacce ta sauko kasa xa a ci abinci. Sai wajen karfe biyar da rabi suka shirya ta rakasu bakin motar Rabi'ah dake kofar gida, Chef salmah tayi wani dariyan yan da6a tace "Sha kuruminki aminiya, mota kamar Aliyu ya siya maki wanda ya take wancan na garage, ke dai Allah ya bamu nasara kawai.... Mu ne fa!!" Rabi'ah tace "Banda ma tana ta mana xurfin ciki ai da ba a kai ga haka ba wllh, ni duk a xatona don taga tayi aure ne ta wani fita harkanmu take shan kamshi shi sa nima na sakata a kwadon shara, kawai na sha iskanci ne tsabagensa take mana, ashe tana nan tana ta kunsar takaicin d'a namiji, ni da na maida maza kamar rigar sawa ta, in cire sanda na ga dama in mayar, ga dai su da yawa a gari kamar ledan pure water, wani lkcn sai in ji bana ma son auren, gwara kawai inyi ta duniyanci na wllh" Dariya su Salmah suka yi suna hailing dinta da karfi, Suhaila tace "Toh kar dai ki manta karfe takwas xa ki fito Aneesah, don wllh wajen da nisa sosai" Aneesah tace "In sha Allahu takwas din kuwa..." Da haka tayi sallama da su ta dawo cikin gida cike da farin cikin xuwansu, kawayenta ne na kut da kut tare suke watsewarsu a Abuja, lkcn da aurenta da Abuturrab ya tashi babu irin shawaran da Rabi'ah bata 6ata ba kan kar tayi aure yanxu tana yarinyarta da ita ta fara fuskantar matsalolin rayuwa amma Aneesah taki ji, wnn ne ma yasa Rabi'ah bata yi attending bikinta ba sae su Fauziyya da Suhaila kawai. Jiddah na kwance daki kana ganinta kasa she is very sad, tun indomie da ta ci shi ma ba sosai ba da safe bata sake cin komai ba har yanxu sbda tana tsoron fita parlor, yunwa take ji sosai amma ta rasa yanda xata yi, ta mike xaune a hankali tana share hawayen da ya kawo idonta ta mike ta isa jikin window ta tsaya wani hawayen na sauka idonta, sosai take jin kewar Abuturrab, and she wished he is around da baxata ji yunwa ba.... Aneesah na shiga dakinta ta shiga wanka da sauri, bayan wasu mintuna ta fito, cikin gaggawa ta mulke jikinta da turarruka iri iri snn ta fito da wani ubansun English wears ta saka ta dau babban handbag dinta ta saka brush da maclean, sai panties biyu, ta debi turarruka kala uku ta xuba su a jakar, Hijab dinta ta dauko har kasa ta saka sannan ta dau flat shoe dinta shi ma ta sa ta dau dubu hudu ta xuba a jaka ta dau jakar ta nufi kofa ta fita, kulle kofarta tayi da makulli a hankali snn ta fara sauka downstairs without making any sound, Jiddah na tsaye jikin window dinta har sannan taga Aneesah da hijab har kasa da handbag ta nufi gate da sauri, Jiddah ta dinga kallonta har ta fita gidan. Da sauri Jiddah ta nufi kofa ta bude ta sauka da nufin tayi duk abinda xata yi a kitchen kafin dai ta dawo, tana ta tsaye kitchen tana tunanin me xata dafa da baxai dau lkci ba, kawai tayi deciding ta dafa jollof din pasta, ba kifi ba nama don a tunaninta xai bata mata lkci, cikin minti ashirin ta gama don pasta din rabi tayi amfani da ta juye a warmer ta dau ruwan gora a fridge ta fita kitchen din ta koma sama da sauri tana sauke ajiyar xuciya.... Har aka kira magrib bata ga Aneesah ta dawo ba, aka yi isha still tana ta xuba kunnen ta ji an bude gate an shigo amma shiru, wanka Jiddah tayi ta sauya kayan jikinta xuwa na bacci sannan ta kwanta gefe, she is just missing everything about Abuturrab so much, sau da yawa sai taji kamar lips dinsa a nata har sai ta kai hannunta bakinta, ta lumshe ido ta takure waje daya tana ta kwance har karfe goman dare, ta mike xaune cike da mamaki don har yanxu bata ji Aneesah ta shigo ba, a haka har bacci ya dauketa wajajen 11. Da asuba tana farkawa ta fito ta sauka downstairs don haka kawai taji hankalinta ya tashi ganin har bacci ya dauketa jiya Aneesah bata dawo ba, ta kofar parlon kadai xata san ko ta dawo ko bata dawo ba don in har ta dawo to xata kulle kofar parlor, ga shock dinta a bude taga kofar da ta murda, alamar ba a shigo ba balle a kulle, ta dinga kallon kofar a tsorace sai kuma ta juya a hankali ta koma sama. Gari na wayewa karfe bakwai Jiddah ta sauko parlor don bata jin dadi taga gidan so dirty, tunda ita dai ba me kiwiya bace, ga shi Aneesah da bakinta na jiya sun yi kaca kaca da parlon kamar yan yara, duk cake ne kan tiles da goran drink da ruwa, tana cikin sharan parlon aka bude kofa, daga kai tayi da sauri, Aneesah na ganinta ta hade rai taki yarda ta sake kallon inda take har ta haura sama, Jiddah ta bi ta da kallo tana ci gaba da sharanta a hankali, bayan ta gama tayi mopping xata kai bokitin waje sai ga Aneesah ta sauko daga sama da saurin ta again, atamfa ne a jikinta da mayafi sai handbag dinta sai xuba kamshi take, nan ma ko kallon Jiddah bata yi ba ta fice daga parlon tana picking call dinta tace "Kai Rabi'ah gani na fito yanxu, wllh na makara ne" Jiddah dai ta bi ta da ido don a bude ta bar kofar.... Bayan la'asar Jiddah ta fito kitchen kenan bayan ta wanke plate din da ta ci abinci, har sannan Aneesah bata dawo gidan ba, xata tafi sama ta ji an bude kofa ta juyo da sauri, Hajja ce ta shigo parlon ba ko sallama, Jiddah da ta ji dadin ganinta ta dawo parlon da sauri tana murmushi tace "Sannu da xuwa Hajja" Hajja tace "Bari Jiddah ba wannan ne gabana ba, Ina mijin naki?" Jiddah ta girgixa kai tace "Ya tafi aiki ai" Hajja ta rike kai tace "Kashh, wai nan na shirya ne ya kai ni gidan kyauta ance min shi kadai ya san gidan a Barnawa tunda a lkcn da ya maida Hafsah uwarsa da ubansa kusan duk kwana biyu sai sun je gidan da shi da ita, yanda yake xuwa gidan ma ko gidan Ramlah bai xuwa... Amma wllh ban ji dadin wannan shegen aikin da ya tafi ba, wai fa daga na d'an kishingida in huta yanxu kawai sae nayi mafarki an kwama ma bakina katon kwado bana um bana um um, kuma ni kadai ke ganin kwadon babu me gani wllh, su Usman da Hauwa sun tsaya kai na suna ta hajja lafiya, Hajja lafiya, amma ina ba baki an garkame sae kallonsu kawai nake kamar bebiye, to shi yasa ban ga ta xama ba a xo a kaini gidan Kyauta ayi min iyaka da Hafsah, wllh da kyar idan baxan kai wannan xancen kotu gobe ba, don ya gigita ni shiga bandakina biyar kafin in xo gidan nan, yanxu haka xancen da nake maki sae na kara xagawa a gidan nan, ai ko dabba ba a kulle ma baki ba balle mutum" Jiddah dake ta kallonta tace "Hajja ai ana kulle na doki" Hajja ta saki baki tace "Toh ni doki ce? Ina ruwana da doki xaki ce min ana kulle na doki, ana maganar mutane me ya kawo na dabba kuma Jiddah? Kawai mata matsiyaciya ki nemi garkame min baki ban maki komai ba, wllh baki ga ba ko abincin kirki ban iya ci a kan wannan xancen yau kwana hudu kenan,