Showing 207001 words to 210000 words out of 346625 words

Chapter 70 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

take heavy food now" Ummi tace "Toh tunda hanya ce ya ajiye ku a gida mana, ko lallai sae Ahmad din ya xo" Ramlah tace "Toh shkkn bari mu bi sa" Abuturrab yyi ma Umminsa da Aunty Nafisah sae da safe ya nufi kofa ya fita, Aunty Nafisah tace "Na gansa wani iri, what does that mean?" Ummi ta ta6e baki tace "Ae a haka yake kullum" Aunty Nafisah tace "Haka kuma?" Ummi tace "Dama shi bai da fara'a ae, sannan ba a sanin cikinsa balle kasan me ya damesa" Aunty Nafisah tace "Toh Allah ya kyauta" Ramlah ta dau jakarta da na jiddah tayi ma su Ummi sai da safe, Ummi tace "Jiddar fa?" Ramlah tace "Kilan tana dakin Hajja, can xan je in duba..." Daga haka ta fita, Jiddah na xaune tayi jigum tana ta kallon Hajja dake ta surutanta, amma kusan duk bata ma san abinda Hajja ke cewa ba, Ramlah ta shigo tana kallonta tace "Taso mu tafi Jiddah" Hajja tace "Toh xa ku tafi, Ahmad din ya xo ne?" Ramlah tace "Ehh" Hajja ta tabe baki tace "Shi dai baya ba mutane komai, bakar rowa kamar uwarsa wllh" Ramlah dai ta juya ta fita, Jiddah na kallon Hajja a hankali tace "Sai da safe" Hajja tace "To Allah ya kai mu, ai ni ban san gidan Ramlah kike ba da na dinga kai maku xiyara a kai a kai tunda babu wani babba a gidan, Shi kuma Bashir idan ya aiko wayar xan amsa in ajiye maki, kuma babu shegen da ya isa yace baxa kiyi amfani da shi ba da rai na dai" Murmushi Jiddah ta kirkira ta mike ta fita, sai da ta fara xuwa tayi ma su Ummi sallama sannan ta fito, parlor ta tarda Ramlah na jiranta, ta amshi jakarta a hannun Ramlah sannan suka fita, har suka fita kofar gida babu wanda yace komai cikinsu, Jiddah ta dinga kallon motar da Ramlah ta nufa, lkci daya jikinta yyi sanyi sosai ta bi bayanta walking slowly, back seat Ramlah ta bude ta shiga, a hankali ta kai hannu gaban motar ta bude ta shiga sannan ta kulle, Abuturrab na kallon Ramlah yace "Ke gidanki xa a ajiye ki ai?" Ramlah ta kalli Jiddah da d'an confusion, sai kuma tace "Ohk to shkkn" Jiddah ta xaro ido tana kallonsa sai kuma ta kalli Ramlah, ya tada motar suka bar layin.

*fear Allah and pay for Jiddatul Khair before reading*


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;

Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697
[7/2, 6:44 PM] +234 806 724 2889: Parking Abuturrab yyi a kofar gidan Ramlah, Ramlah ta bude motar xata sauka, Jiddah ma ta bude xata sauka, Hijab dinta taji ya rike gam daga kasa, ta kallesa da mamaki amma ta ma rasa abinda xata ce, Ramlah ta kulle motar bayan ta sauka tana jiran ganin ko saukowa Jiddah xata yi, Jiddah ta marairaice tana rike da handle din kofar motar murya can kasa tace "Meye haka wai, ka sakeni in sauka mana" Abuturrab ya hada ido da kanwarsa dake tsaye still waiting for Jiddah to come down, a hankali ya sake Hijab din Jiddah ta bude motar ta sauka da sauri, Ramlah ta masa murmushi tace "Sai da safe yaya" Nodding kawai yayi, tuni Jiddah har ta shige cikin gidan, Ramlah ta bi bayanta... Karfe sha daya da wani abu Ramlah na kwance kusa da Ahmad dake operating laptop dinsa, tace "Doctor" ya kalleta yace "Yess dear" Tace "Ina son in maka tambaya ne dama" Ya bar danna laptop din da yake yace "Ina jin ki" Tace "Nasan yaya baya boye maka komai da ya shafi rayuwarsa da dai sauransu..." Murmushi Ahmad yayi yana kallonta, tace "Ka gaya min gaskiya ko da akwai wani alaka tsakanin sa da Jiddah" Yace "Me yasa kika min wannan tambayar?" Ta d'an yi shiru sai kuma tace "Naga wasu abubuwa ne da suka yi confusing dina" Yace "Kamar me?" Ta gyara kwanciya tace "Daxu a can gida muna xaune tare da Jiddah ya shigo yace in je in debo masa abinci, bayan na dawo da abincin sai ban gansu a parlor ba, i dropped the food sai ga Jiddah ta fito daga bedroom din Ummi, she didn't say a word ta fita, i was so surprise bayan few minutes na karasa dakin na gansa shi ma a ciki, sai kuma still daxu ya ajiye mu a gida, xata sauka mota naga ya rike hijab dinta but duk basu san na gani ba" Kallonta kawai Ahmad yake babu ko kiftawa yana sake assimilating din abinda tace, can yace "Sai aka yi yaya?" Tace "I don't know what she told him kuma daga baya naga ya saketa ta sauka motar" Ahmad dae yyi shiru, Ramlah tace "Tun daxu abun ya tsaya min, cause I am confused" Ahmad ya jawo laptop dinsa ya ci gaba da abinda yake, Ramlah tace "Ko akwai wani abu da ake boye mana ne Doctor?" Ahmad yace "I am confused just as u now Ramlah" Ramlah bata kuma cewa komai ba, Bayan few minutes ta mike ta fita dakin, dakin da Jiddah take ta nufa ta bude a hankali tana kallon cikin dakin, kwance ta ganta idonta a lumshe ta lullube da hijab dinta maimakon blanket da ke ajiye gefe, ta fi minti biyu a tsaye har xata juya Jiddah ta bude ido, mikewa xaune Jiddah tayi tace "Kina son wani abu ne?" Ramlah ta sakar mata murmushi tace "Nothing naga baki kashe wuta bane" daga haka ta kashe fitilar dakin ta juya ta fita ta kulle kofar, Jiddah ta lullube har kanta da Hijab din jikinta ta lumshe ido... Karfe daya da rabi na dare Abuturrab na kwance Aneesah na gefensa kamar xata shige jikinsa tana bacci, lumshe ido yyi ya bude, ya mike xaune a hankali being very careful not to wake Aneesah ya sauka kan gadon ya nufi kofa ya fita parlor ya xauna saman kujera ya rike kansa, ya fi minti talatin a nan sai kuma ya mike ya tafi bandaki ya dauro alwala ya fito... Washegari da ciwon kai sosai Abuturrab ya tashi, hakan bai hanasa ya shirya ya fita gida karfe goma ba ya tafi can gidansu, sai da ya jira na kusan minti talatin sannan suka dau hanyar Hayin rigasa da Abbansa, Alhaji Umar, da wani aminin Abban nasa, shi yake driving so absentminded, har suka iso hayi yayi parking dai dai layin Mai anguwa, kasa ce masu komai yayi, shi dai Abba kallonsa kawai yake ganin yayi parking babu wata magana, ya saci kallon Abban nasa, suna hada ido ya bude motar yace "Abba xa mu karasa ciki da kafa babu nisa" Daga haka ya sauka sauran ma duk suka sauka, Xaunawa Abuturrab yyi saman tabarman dake kofar gidan Mai anguwa suka gaisa da mutane biyu dake nan, Abuturrab ya d'an shafa kansa yace "Gun Mai anguwa muka xo" wani matashi yace "Ayya ai bashi da lafiya yau kwanansa uku a shika" Kallonsa Abuturrab ya dinga yi babu ko kiftawa, sai kuma yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un... Allah ubangiji ya tashi kafadunsa" Suka amsa da Ameen, mikewa yayi yana kallonsu Abba dake tsaye suna jin duk abinda Abuturrab yyi da matasan, Abba da Alhaji Umar da abokinsa suka ma Mai anguwan fatan samun lafiya sannan suka koma gun mota, Abba yace "Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, idan ya samu laifi sai a dawo ayi magana" Shi dai Abuturrab bai ce komai ba ya tada mota tunani iri iri a ransa, gida ya maida su Abba sannan ya karasa bangaren Ummi ya gaisheta, Ko minti uku bai yi a parlon Ummi ba aka bude kofar, Aunty ta shigo tana kallonsa tace "Wato da ni kake gaba a gidan nan ko Aliyu, sai dai ka shigo ka yo bangaren uwarka idan ka gama abinda ya kawoka ka fice kayi tafiyarka, to kayi ta banxa in dai nice wllh, dama uban me kake tsinana ni da shi banda ma ni da nayi tsaye kan lamarinka tun baka kai haka ba, in dan ta ita uwar taka ce ka xata xaka kai matsayin da kake yau?? To wllh kayi da ni Aliyu, kuma ni nasan tsinanniyar da ta shiga tsakanina da kai, nasan musabbabin duk wannan abinda kake min, xa kuma tasan ni er halaq ce...." Tana gama fadin haka ta fita tana huci, Shi dai danna wayarsa kawai yake, Ummi dake dakinta duk tana jiyo Aunty ta ta6e baki ta gama abinda take ta fito, gaisheta yayi bayan ta xauna, ta amsa tace "Akwai wani abun da tayi maka ne wanda ban sani ba take maka gori yanxu?" Yana danna wayarsa yace "Ko daya Ummi, ni babu wani abu da ta ta6a min" Ummi tace "Ohk, to me ya hadaka da ita yanxu baka shiga ka gaisheta?" Yace "Ra'ayi" Tace "Kamar yanda for years kayi ra'ayin dena shigowa gaisheni sai ka ga dama" D'an murmushi yayi yace "Aa Ummi" Tace "Toh Allah ya kyauta" Shi dai bai ce komai ba, tace "Har yanxu kuna samun matsala da Aneesar ne?" Ya kalli Ummi yace "Me kika gani Ummi?" Ummi tace "Sai naga abu xan tambayeka?" Ya girgixa kai yace "Aa Ummi, tana gyarawa yanxu" Ummi tace "Toh gaya min meye damuwarka Aliyu" Ya daga kai yana kallon Umminsa, Ummi tace "Tell me" Yyi kasa da idonsa, sai kuma ya mike ya koma gefenta ya xauna yyi kasa da murya yace "Ummi addu'a kawai nake son ki taya ni da shi" Tace "Baxan yi ba sai ka gaya min me ke faruwa" Yyi shiru ya rasa abinda xai ce, bayan few seconds cikin sanyin murya yace "Ummi , I don't know how everyone is going to take this, but..." sai kuma yayi shiru yana jin xuciyarsa na bugawa, Ummi tace "Bother not... Go ahead tell me what's happening, i might take it softly" ya marairaice mata yace "Might kuma Ummi, you just have to take it softly" tana kallonsa tace "Ina sauraronka" Ya d'an kalli kofa, Ummi na ganin haka ta mike tace "Mu je daki to" Mikewa yayi ya bi bayanta xuwa dakin. Driving Abuturrab yake a hankali har ya isa gida, bayan yayi parking ya sauka motar, baka ta6a fadin wani kalan expression ne a fuskarsa a lkcn, yana shiga parlor Aneesah ta leko daga kitchen tace "Welcome back my Captain" Yace "Thank you" tace "Na gama hada maka kayan, kaje ka duba ko sun yi" yace "Sai nayi sallah" Bandaki dake parlon ya shiga ya dauro alwala ya tafi masallaci don lokaci yayi, Aneesah ta karasa ta dau wayarta dake ringing bayan ya fita, ganin Aunty ke kiranta ta daga ta kai kunne, daga daya bangaren Aunty tace "Kar ki kuskura yayi tafiyar nan baki amshi abin nan ba Aneesah" Aneesah na ci gaba da taunar cingam din bakinta tace "Sai kace ina hauka Aunty, na fa gaya maki yanxu lafiya muke xaune babu komai wllh, duk abinda nace yana yi, girki kuwa kan ya dawo weekend chef salmah ta xo ta min varieties in xuba a deep freezer, sai dai in ciro inyi warming, kuma wllh yana ci yanxu, gida kuma kafin ya dawo nake sa almajirai su shigo har sama da dakinsa su share tsaff, in basu batattun kwanuka ta can bayan gidan su wanke, iyaka in kunna burner in cika turaren wuta... " Aunty tace "Toh kun kara hada shimfida kuwa?" Aneesah tayi wani dariya tace "Na fa ce maki Aunty Safara'u ma ta yo min sako me yawa last week bayan wanda kika kawo min, lafiya lau komai ke tafiya yanxu" Aunty tace "Toh madallah haka nake son ji, ni kuwa kinsan har yau ko xuwa gaisheni a bangarena baya yi, to amma ni nasan tun bayan da ya rabu da tsinanniyar yarinyar nan da naji ana ce ma Jiddah hakan ya faru, duk gaba daya ya canxa min ke kyace ni makiyarsa ce" Aneesah tace "Ikon Allah, to ita Jiddar haka xaki xuba mata ido Aunty??" Aunty tace "Ahaf ashe wasa da ni kike... Anjima dai ina nan shigowa in amshi kudin nan na ranan..." Aneesah tace "Aa Aunty ki bari ko jibi don nasan kafin ya tafi dole xai ban kudi me yawa" Aunty tace "Toh shkkn Allah ya kai mu, xan je anguwa ne dama da yamma, so duk da haka xan biyo din dai" Aunty tace "To sai kin xo" Daga haka ta katse wayar.... Ramlah na kwance parlor da yamma taji sallaman Hajja, mikewa xaune tayi don kofar ma a bude yake tun bayan da Jiddah ta tafi Islamiyya, Hajja ta shigo tace "Sannu, a nan ana ta fama ko, ai uwarki ma lokacin da take da cikin Aliyu haka ta xabga uban laulayin nan dai kamar baxata yi ba, to ke gwara naki naga kina narkan abinci abun ki, kawai sai dai yawan kwanciya kamar ruwa, cikin na kwari duk xaki daina jin haka wllh" Ramlah dai sai murmushi take tace "Sannu da xuwa Hajja" Hajja ta karaso tace "Yauwa, sannu ina mijin naki?" Ramlah tace "Ya fita baya nan" Hajja tace "Toh gwara hakan, Jiddah fa? na samu labarin a nan take abunta yanxu" Ramlah tace "Ehh amma ta tafi Islamiyya" Hajja tace "O'o kullum dai ace taje Islamiyya, irin wannan xuwan Islamiyyan nata haka ai ya ci ace ta sauke, kullum fa tana hanyar Islamiyya kamar dai a Masar, to Allah ya bata ilimi me amfani, duk da dai tana da gaskiyarta" Hajja ta ajiye ledan hannunta a hankali kan center table tace "Har gida aka kawo min wannan ledan in gaya maki, ni dai sai riritasa nake kamar kwai abunka da kayan amana, to ynxu karfe nawa suke tashi daga wannan Islamiyyar dai?" Ramlah tace "Ta ma kusa shigowa, tun biyu ta tafi" Hajja tace "Atoh wannan kuma wani irin karatu ne kamar su suka fi kowa tsoron Allah" Ramlah dai ta tashi ta tafi kitchen, Ruwa ta kawo ma Hajja a kan tray da lemo da cup, ta dibar mata jollof din spaghetti da yaji hanta da beef wanda Jiddah tayi ta daura fork a kai da soyayyun kaji, duk ta daura kan tray sannan ta fito parlon ta ajiye kusa da Hajja tace "Ga abinci Hajja" Hajja tace "Kina wannan tofe tofen yawun xaki kawo min abinci Ramlah? Aa ni dai Alhmdlh sai da nayi nak kafin in fito daga gida" Ramlah ta tafi tayi kwanciyarta bata ce mata komai ba, Hajja ta sa hannu ta xare goran ruwan tace "Gwara gwara wannan din dai, dama har gidan Aliyu nake son xuwa saboda naji labarin safaran turarruka yake, sai ya bani ko guda uku ne, Nafisah ma naji wai ta rokesa turaren ai" Ita dai Ramlah kallo kawai take, Bude kofar aka yi Jiddah ta shigo da sallama, Hajja na ganinta tace "Toh Alhamdulillah, sannu da xuwa Jiddah" Jiddah na ganinta sai da gabanta ya fadi, ta karasa parlon ta xauna saman carpet a hankali tace "Ina yini Hajja?" Hajja tace "Lafiya lau, ga sakonki nan tun daga bauchi aka kawo, babu wanda yasan meye a ciki banda ni da aka gaya ma, nima din dai ba budewa nayi ba tunda ni ba yar boko bace" Jiddah ta dinga kallon fancy leda din, Hajja tace "Toh dauka ki duba mana" Dauka Jiddah tayi ta fiddo abinda ke cikin ledan, kwalin latest Iphone ta gani cikin ledan, Ramlah ta xaro ido ta mike xaune tace "Hajja wa ya siya mata wannan?" Hajja ta kalleta tace "Aa kuma ai wannan ba ruwanki Ramlah, ke dai kawai ki mata fatan alkhairi, da fatan kashewa lafiya" Ajiye wayar Jiddah tayi tace "Toh ai ni Umma basu ce xan rike waya ba yanxu" A fusace Hajja tace "Waye kuma Umma?? Yar bakin ciki ce fa matar nan fitowa fili ne bata yi ta nuna, ita ta isa tace baxa ayi abinda nace ba, banda Aliyun da ya tsinto mana ke a can hayi kina galantoyi, wanda ma da muka je gidan naku shekaranjiya gani muka yi an rushe d'an kuturun gidan da baldoza ba komai sai fili, ai ina ga babu wani da ya isa ya hanaki amfani da wayar nan a yanxu dai, don ko Usman yayi yunkurin yin hakan xan nuna masa bacin raina ainun balle wata mata can da ta narka uban kiba, da Masar ne ita wannan dama da tuni an kwantar da ita a asibiti baxa ayi shawara da yan uwanta ba ma, toh wacece kuma Umma a wajenki banda dai tana kanwar Uwar shi Aliyun da yayi sanadin kawo ki cikinmu, ni dai ba ruwana a dinga yin abu bisa tsari, ina ma laifin kice inje ince mata xaki fara amfani da waya" Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba, Ramlah sai kallon Hajja take daga kwancen da take, Hajja ta sharce xufar da ta hada don fitina tace "Balle ma jikana ne ya bada wayan nan a kawo maki, toh ina ruwanta kuma banda dai fitina take son ja ma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login