Showing 96001 words to 99000 words out of 346625 words
Chapter 33 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
har ta gama sakawa, Flight crew din tace "Toh saka naki haka" Ba musu jiddah tayi yanda taga tayi, matar tayi murmushi ta yi unfasten din nata ta mike tace "Toh ki cire, sai jirgi xai tashi xa ki saka, Allah ya sauke mu lafiya" Jiddah ta cire, matar ta kuma sakar mata murmushi ta juya ta wuce, jiddah ta bi ta da kallo don kayan jikinta yayi mata kyau sosai ba kadan ba, ba su fi ashirin a Business class din ba, kowa kuma harkan gabansa yake, tunda wani mutumi ya xauna gefenta ta xama so uncomfortable, ga kamshinsa da ya cika wajen, shi dai bai kalleta ba sai operating din wayarsa da yake yi attentively, bayan minti ashirin duk passengers din sauran class din suka gama boarding plane din, Nan aka fara announcing ayi fastening Seat belt, ganin kowa na saka nasa ita ma ta fara kokarin saka nata, amma sai ta kasa sakawa sai fama da belt din take, sai a sannan mutumin dake gefenta ya kalleta ta gefen ido, ganin ta rasa yanda xata saka, ya kai hannunsa ya saka mata, bata iya ta kallesa ba kuma bata ce komai ba, a haka jirgin ya fara tafiya, dukar da kanta da yaga tayi na kusan minti 5 yasa ya sake kallonta yace "Are you okay?" Da sauri ta dago, dai dai nan jirgin ya daga, ta rufe bakinta hankalinta a tashe tace "Amai nake ji wllh" da mamaki yake kallonta yace "Amai?? Ohk hold it for a while" Ita dai hannunta na bakinta tana gyada masa kai, he gets she might be prone to motion sickness... ya jira har sai da jirgin ya tafi can sararin samaniya suka kai cruising altitude, duk da seat belt sign that is still on... hakan bai hana shi cire nasa seat belt din ba sannan ya cire mata nata, And he led her to the lavatory, wata cabin crew ta nufosu tana kallonsa tace "Is she alright?" Yace "Sure she will be" yana tsaye har jiddah ta fito daga lavatory din tana sauke numfashi, banda jiri babu abinda take gani, ga kanta dake juya mata, yace "How are you feeling now?" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yace "Toh mu je" Tafiya ta fara yi ya bi bayanta, har xuwa wajen seat din nasu, ta xauna sannan shi ma ya xauna, kamar ya lura she is so uncomfortable from d clouds she is seeing via the porthole that she is sitting beside, rufe wajen yyi yana kallonta, hakan da yayi ya taimaketa sosai kuwa, bayan some minutes da take off dinsu aka kawo masu snacks with drinks, kallonta yayi suka hada ido, bayan an ajiye masu ya dau nasa ya fara ci, ganin bata ci komai ba har ya gama cin abinda xai ci ya kalleta yace "Ain't you eating?" Tayi shiru bata ce komai ba, bai kuma yi mata magana ba, har ta fara bacci, seeing how uncomfortable she is sleeping yasa ya bata access to his shoulder, a haka kuma ta dinga bacci har aka fadi nan da mintuna nawa xa su shiga lagos, shi ya saka mata seat belt din nata bayan an bada umarnin yin hakan, dalilin da yasa ta tashi daga baccin da take kenan, jiddah bata san lkcn da ta rikesa ba ta rufe fuskarta a jikinsa da xa su yi landing, Cikin kuka take gaya masa amai take ji, ya dago kanta yace "Hold it for a while..." ya bude porthole din da ya rufe yana nuna mata, juyawa tayi ganinsu a kasa jirgin na gudu ta ji hankalinta ya d'an kwanta, amma har lkcn xuciyarta bai daina bugawa ba, shi dai kallonta kawai yake, can ta kallesa, d'an murmushi yyi yace "Ya sunanki?" Ta sauke idonta tace "Jiddah" yace "Jiddah!!" Ta gyada masa kai, yace "Wannan ne farkon hawanki jirgi Jiddah?" Ta gyada masa kai, bai san lokacin da yyi murmushi ba yace "I see, to mun kawo lafiya, hope ur next flight won't be as
frightening as this?" Ita dai bata ce komai ba,
yace "Ke kadai kika xo lagos?" Ta girgixa masa kai tace "Aa ni da yayana" yace "Wow, yana ina?" Ta buda masa hannu alamar bata sani ba, yace "Ba tare ku ka
shigo jirgin ba?" Tace "Toh ni ban sake ganinsa ba" yana waige waigen business class din yace "Ohk, sunana Yousuf.... Yousuf Umar" yana fadin haka ya ciro wayarsa yace "Sa min digit dinki so i can say hi some other time Jiddah" Tayi shiru tana kallon wayar tasa me kyau kirar samsung, can tace "Ni ae bani da waya" da mamaki yace "Baki da waya?" Ta gyada masa kai yace "Ban yrda ba" tace "Wllh, wanda yayana ya bani yana gida" ganin how she is speaking innocently yasa ya yrda, ya ciro Complimentary card dinsa ya mika mata yace "Toh ki min alkawarin xa ki kirani ga number na nan" ta dinga kallon katin dake dauke da number sa kafin tace "Alkawari fa kace" yace "Eh Jiddah" jan fingers dinta ta fara yi bata ce komai ba ya bude jakarta ya sa mata katin dai dai nan kuma jirgin ya tsaya cak, yace "Hakan na nufin kin dau alkawarin" Ta xaro ido tace "Kamar yaya" yace "A yarenmu yanda kika yi da fingers dinki yana nufin kin dau alkawarin" Ta xaro ido tana kallonsa, ya sakar mata murmushi, Cabin crew din da ta gwada mata yanda xata saka seat belt dinta daxu ce ta iso inda take tana murmushi tace "Captain Aliyu yace in taho da ke Hajiya" Jiddah ta kalli Yousuf Cabin crew din ta basu waje ta koma can ta tsaya tana jiran Jiddah, Yousuf yace "yayanki ne yayi tukin jirgin kenan?" Da mamaki take kallonsa tace "Tukin jirgi fa kace? Aa baxai iya ba" yana murmushi yace "Toh tashi ki je... ina jiran kiranki" shi ya rigata mikewa ya dau briefcase dinsa ya fara tafiya ta bi sa da ido snn ta mike ta nufi cabin crew din da tayi mata jagora har Cockpit inda Abuturrab yake xaune tare da Co-pilot dinsa wani black American suna secure Cockpit checklist, da mamaki Abuturrab ke kallon Crew din don ce mata yayi tayi leading dinta outside d plane, hannu black American din da ya kafe jiddah da ido ya mika mata yana murmushi yace "Hello...." Kallon Abuturrab Jiddah tayi, lkci daya taga ya mata wani shegen kallo, amma calmly yace "Juya ki tafi ki jirani ina xuwa..." Juyawa tayi da sauri ta bar wajen, Yana ma American din murmushi yace "We don't do that captain, and she doesn't even understand English" Pilot din na kallonsa yace "Ohh, is she ur sister?" Abuturrab yace "My friend's wife...." Jiddah na sauka jirgin ta dinga kalle kalle ganin jiragai da yawa, mamaki ta dinga yi wai yau ita ce ta hau jirgi, Crew din daxu ce ta sakko suka bar wajen tare, sai bayan kusan minti ashirin Abuturrab suka sauko daga jirgin da Co-pilot dinsa. Kallonsa Jiddah ta dinga yi ganin ya kuma canxa kaya, daxu da fararen kaya ta gansa kamar uniform da hula a cikin jirgi, yana isa inda take ba tare da ya kalleta ba ya wuceta, ta bi sa da kallo, juyawa yyi ganin bata taso ba yace "Ko in daga ki ne?" Mikewa tayi a hankali ta bi bayansa, hotel din da ya ke sauka a lagos not too far from Murtala Muhammad Airport ya nufa tare da ita cikin taxi, Tana biye da shi bayan sun sauka taxi din sun shiga hotel din, bin sa take kamar xata shige jikinsa ganin mata
kusan tsirara suna yawo
hankali kwance, garin kallon wata da ta gani da wando iya cinya ta kusa fadawa kansa, ya juyo yana kallonta, kamar xata yi kuka tace "Ina ne nan ka kawo ni?" Ci gaba yyi da tafiyarsa ta bi bayansa, har ya amshi makullin daki a reception tana makale da, shi dai bai sake ce mata komai
ba suka shiga dakin da ya amsa, bayan ya kulle kofar kamar xata yi kuka tace "Su basa jin kunya ne?" Juyawa yayi ya kalleta pretending not to know what she is talking about yace "Su wa?" Ta sunkuyar da kanta, yace "Tambayarki nake su wa?" Still ta ki cewa komai, ya ajiye wayoyinsa yace "Ke me ya aike ki kallonsu?" Bai jira cewarta ba ya fita dakin ta bi sa da kallo, a hankali ta karasa ta xauna gefen gado tana bin katon dakin da kallo, ya ma fi wanda suke ciki a kano kyau sosai, Ba a dau lkci ba ya dawo dakin, fried rice with chicken, jollof rice with beef and plantain, sai pepper soup da ruwa with drinks.... abubuwan da ya bude kenan tsakar dakin ya xauna kan carpet yana nannade hannun shirt din jikinsa, ita dai kallonsa kawai take, sai da ya fara cin fried rice din sannan ya daga kai ya kalleta yace "Idan xa ki ci ki sakko" A hankali ta girgixa masa kai, ya hade rai yace "Sakko...." Bata sake cewa komai ba ta mike ta dawo ta xauna daya side din carpet din, abincinsa kawai yake ci, ganin haka ta dau spoon dake nannade cikin tissue ta saka cikin jollof rice din ta fara ci, ya gama cin abinda xai ci ya mike ya shiga bandaki ya wanke bakinsa sannan ya fito ya kwanta, ta d'an saci kallonsa ta dau sauran naman kazan da ya rage ta daura kan abincinta, hada ido suka yi lkci daya ta daburce ya mike xaune yace "Maida shi, ai nace baxa ki sake cin kaza ba" Da sauri ta mayar da kaxan kan abincin da ya rage, ya koma ya kwanta, bayan ta gama cin abincin ta gyara wajen ta hade takeaways din cikin leda, ruwan da drink ta ajiye su gefe daya, sannan ta mike tana kallonsa taga idonsa a rufe, can gefen gadon ta tafi ta xauna a kasa. Karfe biyu saura Abuturrab ya koma Airport tare da Jiddah, don he will be piloting to Abuja, hankalinta ya tashi ganin jirgi xa su kara shiga tana kallonsa kamar xata yi kuka tace "Don Allah mu hau mota, wllh bana son jirgin nan" Lkci daya hawaye ya kawo idonta, yace "Baki so saboda me?" Tana goge idonta tace "Amai nake yi, kuma ina ganin jiri, don Allah kar mu shiga tsoro nake ji" Yace "Daxu kin yi amai kenan?" Ta gyada masa kai yace "A ina kika yi aman?" Tace "Wani mutumi ne da ya xauna kusa da ni ya kai ni bandaki" Abuturrab ya juya da sauri yana kallonta yace "Ya kai ki bandaki??" Ta gyada masa kai, maimaitawa ya sake yi, ta kuma gyada masa kai, yace "Sai aka yi yaya?" Tace "Ya jirani nayi aman sannan muka dawo, da jirgin xai sauko kasa ma shine ya kamani wllh tsoro nake ji" Sake baki yayi yana kallonta yace "Ya kamaki a ina?" Tayi shiru bata ce komai ba, ya rungume hannunsa yace "Ya mutumin yake???" Tace "Yana jin hausa, kuma dogo ne kaman ka, sannan yace min sunansa Yousuf" Ya xare glass din idonsa yana kallonta, can yace "Ohk har hira ku ka yi kenan" Tace "Aa bamu yi hira ba" Bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da tafiya ta bi bayansa gabanta na faduwa, ticket din da Abuturrab ya yankar mata sai da ya tabbatar the person next to her is a female, exactly abinda tayi daxu daga kano xuwa Lagos shi tayi daga Lagos xuwa Abuja, Bayan jirgin ya sauka Abuja ta fita tana kare ma jirgin kallo tana fatan babu abinda xai kaddara mata sake shiga jirgi, har suka isa gidan Abuturrab wajajen la'asar jikinta a sanyaye yake, duk yana lura da ita bai ce komai ba, xaunawa tayi kan kujeran parlon tana bin parlon da kallo, yana kallonta yace "Yanxun ma kinyi aman a jirgi kenan?" Ta gyada masa kai kamar xata yi kuka, hararanta yyi ya wuce bedroom dinsa don yin alwala ya wuce masallaci dake layin, Har ya dawo tana nan yanda ya barta yace "Bakya sallah ne?" Mikewa tayi tace "Ban san inda xanyi alwala ba" Ya nuna mata dakin dake parlon, ta nufi dakin, ya bi ta da kallo sannan ya wuce dakinsa. Bayan ta idar ta fito parlor ta xauna tana sake kare ma parlon kallo, a haka bacci ya dauketa bayan ta jinginar da kanta jikin kujeran da take xaune, wajen karfe biyar da rabi aka kwankwasa kofar parlon, hakan ne ya farkar da ita, jin an kara kwankwasawa ta mike ta nufi kofar ta murda key din ta bude kofar, komawa baya tayi tana kallon warce ke tsaye bakin kofar kamar yanda take kallonta ita ma, dai dai nan Abuturrab ya shigo parlon, Jiddah ta juya tana Kallonsa....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems
Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada
Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
[6/11, 7:21 PM] +234 803 540 6041: Abuturrab yace "But you didn't tell me kina xuwa Aneesah" Aneesah tayi wani murmushi tace "How will i tell you ina xuwa Aliyu, dama dalilin da yasa kake walakanta ni kwana biyu kenan, dama wata ka samu? Dama wannan ce dalili" Daga sama har kasa take kare ma Jiddah kallo tana murmushin takaici tace "Ki bar murna kin samu pilot har yana kawo ki gidansa saboda tsagwaron so, nima haka ya dinga min, but...." Abuturrab ya katse ta yace "Come off it pls Aneesah, what's all this? I thought i explain better to you her position, she is the lady...." Aneesah ta sake kallon Jiddah da sauri, Jiddah dai banda kallonta ita ma babu abinda take, A hankali Aneesah tace "Which lady Aliyu?" Yayi kasa da muryar yace "Ba ke kika ce in kawota ta xauna gidanku ba" Sosai gaban Aneesah ya fadi don bata ta6a tunanin Jiddah ce wnn yarinya da Abuturrab ke fadi mata ba, ta dinga kallon Jiddah xuciyarta na bugawa, ta ma rasa abinda xata ce masa, Abuturrab yace "Tunda kin xo yanxu sai ku tafi tare, dama anjima nake son kai ta gidan naku, hopefully nasan Mumy ta yarda ta xauna with ur family..." Aneesah ta hadiye abu da kyar, har sannan ta kasa daina kallon Jiddah da tayi mata wani kwarjini, a xuciyarta ta shiga kokwanton anya ita ce me awaran da Aunty ta ce, or is Aliyu playing her?? Abuturrab ya juya ya kalli Jiddah bbu yabo bbu fallasa yace "Dauko mayafinki" Shiru tayi tana kallonsa, a d'an tsawace yace "Baki ji na ne?" Ta koma baya tace "Toh ina xanje idan na dauko?" Yace "Ban sani ba, wuce ki dauko" Juyawa tayi ta koma can tsakiyar parlon ta tsaya kamar xata yi kuka tace "Allah ni babu inda xanje, ba gidan Baabarmu nace ka maida ni ba, nasan ita wacece da xan bi ta" Daga maganarta Aneesah ta kara tabbatarwa ita ce me awaran, Abuturrab ya saki baki yana kallon Jiddah, Aneesah ta hade rai tace "Toh nan din gidan ubanki ne da baxa ki bari ba?" Jiddah ta kalleta, a hankali tace "Ubana fa kika ce?" Aneesah da xuciyarta ya dau tafarfasa tace "Shi din..." Lkci daya Jiddah ta fashe da kuka tace "Ba dai ubana dake kabari ba wllh sai dai naki" Aneesah ta saki jakar hannunta tace "Kika xagi ubana?" Jiddah ta goge idonta tace "Ehh an xaga, me nawa uban ya maki da kika xagesa ke?" Aneesah tayi kanta a mugun fusace, fixgota Abuturrab yyi yace "Hey are u okay, what are u trying to do?" Fixge hannunta tayi kamar wata zakanya ta nufeta, cikin tsawa Abuturrab yace "Don't try that Aneesah, u will definitely see the other side if me by touching her" Tuni Jiddah ta tsorata ta bar wajen da gudu ta yi hanyar kitchen hakan bai hana Aneesah bin ta ba, shakota Aneesah tayi tace "Uban wa kika xaga?" Tuni Abuturrab ya nufesu, Jiddah ta kwala kara ta gatsa mata cixo a hannu, Aneesah bata yi wata wata ba wajen sauke mata lafiyayyen mari a fuska sannan ta wuntsular da ita a kasa tana cewa "Don kaza kaxanki ubana sa'an kaf danginki ne aka ce maki?" wani ihu Jiddah ta fasa tana cewa wayyo bayanta, wayyo kafarta, Kamar daga sama Aneesah taji saukan tagwayen mari wanda sai da yasa taga duhu na few seconds, ya fixgota fiercely yace "How dare you? You bitch" with shock Aneesah ke kallonsa, ya nufi kofa ya wuntsular da ita waje kamar yanda ta ma Jiddah yyi banging kofar, Banda rusa kuka babu abinda Jiddah dake yashe a kasa take tana kiran Baabarmu, Bude kofar Aneesah tayi tana daga tsaye bakin kofa hawaye kaca kaca a fuskarta tace "You called me a bitch Aliyu?? Ni ka walakanta ka sauke yatsunka fuskata a kan wannan yar talakawan bagidajiya jaka? Ni ka ci ma mutunci haka in her present? U threw me out of ur house a kan yar talakawa me tallan awara?" Jiddah ta goge idonta ta mike cike da tsiwa tace "Idan ana tafiya lahira da arxiki sae ki daura naku a kai ki tafi da shi in ga, kuma Allah ya isana, ban yafe maki ba, axxaluma...." Fixgo hannunta Abuturrab yyi ya nufi daki, cikin kuka tana son kwace hannunta take