Showing 213001 words to 216000 words out of 346625 words

Chapter 72 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

yayi parking kofar gidan Iyah, sauka tayi daga motar da sauri ta shige gidan a guje, ya sauka ya jingina da motar tasa ya bi ta da kallo, Iyah na xaune tsakar gida da rediyonta a hannu, tana ma jikokinta dake kwance saman tabarma fifita sun yi bacci, Jiddah ta wara ido cike da murna tace "Iyah!!!" Fadawa jikinta tayi ta rungumeta, Iyah ta matsar da ita tana mata wani kallo daga sama har kasa, sai kuma tace "Jiddah????" Rungumeta Jiddahh ta kara yi lokaci daya hawaye ya kawo idonta tace "Nice Iyah, nayi kewarku wllh" Iyah ma ta fashe da kuka tace "Ashe rai kan ga rai Jiddah, ashe xan sake ganin ki a rayuwar nan?" Jiddah ta share idonta tana murmushi tace "Gashi kin gan ni Iyah" Iyah ta mike tsaye tana sake kare mata kallo don tabbatar da ita din ce kuwa, sai ta saki salati tace "Daga ina kike haka Jiddah?? Kece kika dawo haka kamar balarabiya Jiddah??" Jiddah tayi murmushi ta kasa ce mata komai tana kallonta, Iyah tace "Ke da waye yanxu haka? Daga ina kike?" Jiddah tace "Yana kofar gida, ince ya shigo?" Bata jira me Iyah xata ce ba ta tafi da sauri kofar gidan, har sannan Abuturrab na tsaye ya rungume hannunsa, tace "Wai tace ka shigo" kallonta ya dinga yi ta juya ta koma ciki da sauri, shafa kansa yyi ya bi bayanta... Har kasa Iyah ta durkusa tana gaishesa bayan ya shigo gidan, hakan yasa ya xauna saman darduma yana d'an murmushi calmly yace "Ina yini??" Iyah ta rushe da kuka tace "Wllh da kasan irin taimakon da Allah ya baka ikon yi da ladan da Allah xai baka da ba haka ba bawan Allah, ka taimaki rayuwar Jiddah a sanda take tsananin bukatar taimakon, ka cece Jiddah a dai dai lkcn da take bukatar ceto, Allah ubangiji ya sa ka samu me maka abinda kayi ma marainiyar Allahn nan duniya da lahira, Allah ya biyaka da aljanna, ya yalwata maka arxikin ka, Allah ya baka ikon ci gaba da riketa da amana, Allah kuma ya baku xaman lafiya tare na har abada ya bada xuri'a dayyaba" Kuka kawai Iyah take kamar jininta ce Jiddah, Jiddah dai duk jikinta yyi sanyi ta sunkuyar da kanta jin maganganun Iyah, shi ma kawai murmushin karfin hali yake yana kallon tsohuwar a hankali ya ce "Ameen nagode Mama" Iyah na kwalla tace "Wllh ki rikesa Jiddah, kaf duniya a yanxu dai baki da kamarsa, shine uwarki shine ubanki, ya maki abinda a cikin kashi dari na mutane baxa ki samu kashi biyu da xa su iya maki ba, ya fidda rayuwarki cikin kunci, maraici, tsanani, da bakar wahala, yayi maki duk wannan abun a lokacin da kike tsananin bukatarsu, to me xai janyo maki butulce masa a rayuwar nan, kiyi masa halacci yanda ya maki Jiddah, ga shi wai yau kece sai da na maki kallo kusan uku sannan na gane ki, ba don muryarki ba wlh baxan yarda ke din ce ba" Sosai jikin Jiddah yayi sanyi wanda bata san lkcn da hawaye ya dinga sauka idonta ba tana kallon Iyah, kallonta kawai Abuturrab yake babu ko kiftawa, Iyah tace "Ki rikesa, kiyi masa biyayya, ki rike yan uwansa da duk wani nasa Jiddah, da abinda xaki iya biyansa kadai kenan ki ji in gaya maki, nace kiyi masa biyayya, wllh kiyi masa biyayya, Allah kadai yasan sadaukarwan da yayi sabida ke, Allah kuma ya baku xaman lafiya na har abada, nasan baku ma kai ga shiga gidan Hansai ba, amma idan xa ku ji ta nawa ba sai kun shiga ba kuyi tafiyarku kawai, Hansai bata canxa ba dai daga yanda kika santa... Sai ma dai abinda ya faru" Jiddah sai goge hawayen da yaki tsaya mata take, Abuturrab ya ciro kudi aljihunsa ya ajiye ma Iyah yace "Kiyi hakuri Mama babu yawa wannan, in sha Allah xan sake dawowa gaisheki, sannan xan daukeki in kai ki inda mu ke" Iyah tace "Wllh gaisuwan da kuka xo min ma ya isa ya wadatar ba sai ka bani kudi ba Yarona" mikewa yayi yana kallon jiddah da ta kasa daina kuka, a haka dai Iyah ta rakasu kofar gida tana cewa "Ba sai kun je gun Hansai ba, kuyi tafiyarku Allah yayi maku albarka ya baku xuri'a dayyaba..." Cikin sanyi Jiddah tace "Iyah baxan iya tafiya ban shiga na gaisheta ba" Iyah tace "Toh shkkn Jiddah, Allah ubangiji ya kareki daga duk sharrinta ku shiga kawai, akwai Allah" Abuturrab ma bai hana Jiddah ba suka karasa kofar gidan nasu da kafa, gabanta na faduwa ta shiga gidan ta ma kasa ko sallama saboda fargaba, Hansai na xaune tsakar gida tana fiffita ga kwanon abinci a gabanta tana cewa "Yo ba gwara ma ya mutun ba ko xa a rage mugun iri, duk fa da hadin bakinsa da uban kudi da aka dinga lafta masa aka siyar min da 'ya ban ji ba ban gani ba, yau wata dai dai kusan biyar kenan, kuma wllh gaya maki ne kawai banyi ba amma so nake na hada yan kudaden wankauna, na kai gidan malam Hamisu a sake danne tsinanne kada Allah ya mikar da shi, kaf bani da makiyi irinsa a duniya yanxu kam..." Zulai dake kwance tsakar gidan da daurin kirji tace "Ai ko dai ance yana can shika rai a hannun Allah baya gane duk wa enda ke kansa, aiki ma xa a masa sai kuma jikin ya dada sususcewa kinga bbu xancen aikin ai sai ya farfado kuma" Jiddah ta kasa shiga gidan gabanta sai faduwa yake ta dinga karanto addu'o'i a ranta, Zulai ce ta hango shadow tace "Waye tsaye nan, ko Bibalo ce" Hansai tace "Bibalo ai sai karfe sha biyu kila, wani shegen ne ya tsaya min bakin kofa yana min la6e?" Jiddah ta runtse ido ta karasa shiga tsakar gidan, duk suka tsaya kallonta don akwai hasken wata sosai tsakar gidan, Hansai ta ajiye maficin hannunta tana kallonta daga sama har kasa tace "Waye wannan?" Da kyar Jiddah tace "Ni ce Baabarmu" Zulai ta mike a gigice tana sake gyara daurin zanin kirjinta tace "Ke wa??" Hansai dai hangame baki tayi tana kallon Jiddah daga sama har kasa, can ita ma ta mike ta nufeta tana sake kare mata kallo kamar taga aljanna, Hawaye ya shiga sauka idon Jiddah ta durkusa kasa cikin sanyin murya tace "Baabarmu" Hansai ta fashe da wani matsanancin kuka tace "Toh Alhamdulillahi, yanxu saura in kai ma Badalan kan dutse cikon kudinsa, aiki kam ya ci Alhmdlh... Allah ya maido min ita gida da kafafuwanta" wani shewa Zulai ta saki da karfi tana gode ma Allah ita ma, Jiddah dai sai kallonsu take, Hansai na sharban majina tace "Tashi mu shiga ciki, tashi" Jiddah tayi karfin halin cewa "Ba ni kadai ba ce Baabarmu" Hansai ta kalli soro da sauri tace "Ke da uban waye??" Jiddah ta sunkuyar da kanta tace "Ni da shi ne" Dai dai nan Abuturrab ya shigo cikin compound din don gaba daya hankalinsa ya ki nutsuwa shigan Jiddah gidan ita kadai, Hansai taji mugun faduwan gaba ganinsa tace "Ya xaka afko ma mutane gida haka kanka tsaye, kai waye??" Yana kallon Jiddah yace "Idan kun gama gaisawan taso mu tafi... It's getting late" Hansai ta gwalo ido tace "Ku tafi ina?? To wllh wllh karyarka ya sha karya Malam, babu inda 'ya ta xata daga tsakar gidan nan, ko taku daya baxata yi daga nan ba wllh, ku je ina?? Lallai sannunka...." tana huci ta kare maganar ta dago Jiddah da xumar shigar da ita daki tana cewa "Tashi don ubanki, idan kin sake fita ko nan da kofar gida Allah ya tsine min albarkan da yayi min...." Daga kasa har sama Abuturrab ke kallon Hansai da wani expression, can yace "Kin manta ita din matar aure ce?" Hansai ta mulmulo wani uban xagi tace "Fadi duk uban da ka kashe ni me iya siyar da gidan nan ne in biyaka, a gidan ubanwa ta xama matar aure?? Ka dau min ya ka tafi ka lalatata kace min matar aure ce??" Abuturrab na kallon Jiddah yace "Zo mu tafi" Jiddah hawaye na sauka idonta ta kallesa sannan ta kalli Hansai dake kokarin janta xuwa cikin daki, cikin kuka tace "Baabarmu...." Hansai bata saurari me xata ce ba ta wanka mata wani mummunan mari da yasa taji diff, ta kuma kai mata wani tana huci tace "Rufe min baki don ubanki" bai san lkcn da ya karasa compound din ya fincike Jiddah a hannunta ba yace "Kinyi na farko kinyi na karshe, kin kuma ci albarkacin ki na matar babanta da wllh sai na rama mata" Daga haka ya nufi soro da Jiddah, Hansai ta lafta wani uban ihu ta bi bayansu tana kunduma xagi tace "Idan Jiddah ta sake barin gidan nan shegiya aka haifeni, wllh babu inda xata je kuma ka cika min 'ya ta" Ganin ta yo kansu Abuturrab ya kwasheta da kafa sai gata wanwas a kasa, ya bude front seat ya saka Jiddah dake ta kuka a ciki sannan ya kulle ya xaga ya shiga driver seat, Xulai ce ta fito da katon tabarya tana ihu wai jama'a su kawo masu dauki, Hansai ta mike a rikice ta amshe tabaryan, da duk karfinta ta buga glass din bangaren da Jiddah take, ihu Jiddan ta fasa a tsorace ya fixgota jikinsa tayi lamo, don sai da glass din yyi tsawa, Hansai ta shige gaban motar kamar mahaukaciya tana cewa "Da dai ka tafi da Jiddah gwara ka kasheni, ka kasheni nace d'an banxa... xan ga ta inda xaka bi ai, sai dai ka takeni, babu inda xaka kai min ya ta d'an yankan kai..." Abuturrab yyi reverse sosai sannan ya taho a guje, wani uban tsalle Hansai tayi ta kauce sai gata da Zulai kwance a kasa, ya ja motarsa a guje ya bar layin, kuka kawai Jiddah take kamar ranta xai fita, har suka fita titin hayi bai ce mata komai ba....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you


It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;

Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697


Kofar gidan Ramlah Abuturrab yyi parking, tun barin su Hayi sai a lokacin ya juya ya kalleta, a hankali ta kai hannu a sanyaye xata bude motar taji a kulle, duk da haka ta ki kallonsa har sannan hawaye na idonta, yace "To kukan me kike, bayan abinda kika ce kina so nayi maki, gun Baabarki fa kika ce in kai ki kuma na kai ki" Hade rai tayi taki ce masa komai, hakan da tayi ya basa dariya amma bai yi ba ya jinginar da kansa da kujeran da yake xaune yace "Laifi na ne kenan?" Kamar jira take ta fashe masa da matsanancin kuka har da shessheka, kallonta ya tsaya yi, bude motar yyi ya sauka, ta hade kanta da gwiwa tana rera kuka tana jin xuciyarta na mata xafi, Booth ya tafi ya fito da duk kayan shopping din, ya nufi gate din gidan, dai dai mai gadi xai fito, ya mika masa yace "Ka ajiye su a bakin kofa" komawa yayi booth din motar, a haka duk ya kwashe kayan yana ajiye su cikin compound din mai gadi kuma na kai wa bakin kofar entrance din shiga gidan yana ajiyewa, Bayan kayan sun kare Abuturrab ya koma cikin motar ya kulle yana kallonta, jin shigowarsa ta dago kanta ta kai hannu xata bude side dinta taji ya kulle motar gaba daya, calmly yace "I'm asking u whose fault it is now? Mine?" Tana goge idonta a hankali tace "Nima ban sani ba ka bude min mota in fita dare yayi" ya dinga kallonta, sai a sannan ta kallesa tace "Ka bude min xan sauka" yace "Yeah!! You did good by wanting to go meet ur stepmom after so many months, that clearly shows u missed her no matter her maltreatment toward u... u had good intentions but, stepmum dinki bata canxa daga yanda kika santa ba, she is still the stepmom u knew her to be, don haka idan ma tana ranki ne har yanxu ki cireta na har abada, take her off ur mind totally and face reality, ki mance kin ta6a rayuwa da ita, ki kulle babinta a rayuwarki, face ur new life, bata sonki kuma baxata ta6a sonki ba...." Jiddah ta fashe da kuka cikin sanyin murya tace "Shikenan ni kuma bani da kowa kenan?" Kallonta ya dinga yi, a hankali yace "Baki da kowa??" Kuka kawai take ta ki ce masa komai, ya kamo hannunta yace "Baki da kowa kika ce?" Still bata basa amsa ba amma yanda take kuka kasan she is hurt, bude motar yayi ya sauka, ya xaga ta inda take ya bude side din, saukowa tayi xata wuce gate ya riko hannunta ya bude back seat yace "Shiga ki goge idonki da kyau before going.." ta kalli motar, sai kuma ta fara goge idon nata, ya d'an hade rai yace "Shiga nace, u can't go in with those eyes" a hankali tace "Ni na goge ai" Calmly yace "Get inside" Wani hawayen ya taru idonta ta shiga bayan motar, ya dau handkerchief dinsa ya mika mata, amsa tayi tana goge idonta amma da ta tuna abinda Baabarsu tayi mata sai wasu hawayen su xubo mata, shikenan ita ba warce xata nuna tace baabarta ce kenan, a wajenta ta taso fa ta ga kanta, kowa yana da wanda xai nuna yace yau ga d'an uwansa na jini amma ita banda ita, bata san kowa nata na jini ba, hade kai tayi da gwiwa crying sadly, shi dai kallonta kawai yake, can ya bi layin da kallo, babu kowa a layin don goma ma yayi, mai gadi ma tuni ya koma cikin compound din, shiga cikin motar yayi ya kulle, ta daga kai tana kallonsa tana kuka, yace "Kika ce ke baki da kowa??" a hankali ta fara matsawa taki ce masa komai, ya kamo hannunta yace "Tell me?" Ta girgixa masa kai kawai, yace "Kin manta kina da Umma, kina da Ummi, kina da Ahmad? Maimoon, Ramlah... Ain't they all there for u always?" Sunkuyar da kai tayi wasu hawayen na xubo mata bata iya ta basa amsa ba, yyi kasa da murya yace "Answer me" ta gyada masa kai a hankali tace "They are...." yace "Idan ni ban ta6a maki komai ba ae su sun maki kuma suna kan maki ko?" Ganin kamar tunxurata yake dada yi, ya lumshe ido ya jawota jikinsa, lkci daya ta hadiye kukan da take ta fara turasa a hankali tana komawa baya, ya rungumeta sosai murya can kasa yace "I know i am gonna..." Bai karasa ba kawai ya shiga kissing dinta passionately, tun tana kokarin kwace kanta a rikice har dai ta kasa kwakkwaran motsi ta tsaya cak kamar warce ruwa ya cinye, Tun dai ana kiss har abu ya fara wuce level din kiss, iyakar tsorata ta tsorata a lkcn, bata kuma san sanda ta fara rokansa cikin rawar murya tana cewa ya rufa mata asiri, sae da ya dawo mata kamar ba shi din da ta sani ba, bakinta na rawa tace "Don Allah Aliyu kayi hakuri ka rufa min asiri, don Allah ka bari, don girman Allah nace maka...." Gaba daya ya gigitata, Ya kai bakinsa kunnenta cikin muryar da bata san sa da shi ba yace "Me ya sa baki saka brassiere ba?" Cikin rawar murya bakinta na rawa tace "Bacci xan yi dama" bai kuma ce mata komai ba, ta kankamesa tana kara basa hakuri da sauran strength dinta, Sae da Abuturrab ya ga he is getting out of the little control he is trying to maintain sannan ya saketa ba shiri, da ta samu ta figi hijab dinta ko gama sawa bata yi ba ta bude motar ta fice fittt, ko kulle masa motar bata yi ba cikin sakwanni kadan ta shige cikin gate din gida, gaba daya ya hargitsa ta iyakar hargitsawa, Ramlah na xaune parlor ta xabga uban tagumi bayan ta gaji da tsayuwa Jiddah ta shigo parlon, Ramlah ta mike tace "Haba Jiddah ina kika je haka bayan kin san karfe nawa, kin fa san halin da nake ciki kuma kika sa na shiga damuwa sosai haka?" Jiddah ta kasa tsayawa parlon, bakinta har rawa yake tace "Wllh siyayya yayi yace a kawo maki gasu can a balcony, i.. i want to go ease my self now" Daga haka ta shige daki ta kulle tana sauke numfashi, fadawa tayi kan gado ta shige cikin bargo ta rufe har kanta.. Ramlah dai na ta tsaye parlon deep in her thought, tunda Jiddah ta shigo taji kamshin turaren Abuturrab... komawa tayi ta xauna ta kuma rafka tagumi tunani iri iri a ranta... Abuturrab ya fi minti talatin a mota bayan ya isa gida idonsa a kulle ya jingina da kujeran motar, he is just hoping Allah yasa Aneesah tayi bacci, wajen karfe sha daya ya sauka motar ya shiga ciki, ga mamakinsa sai ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login