Showing 333001 words to 336000 words out of 346625 words

Chapter 112 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

da Jiddar kun koya mata karatun duniya ba ne ku ka kaita gidan miji, ai ba a yarda da mata yanxu barin irin wa ennan da idanuwansa ya yage har kunne" Umma dai bata ce da Hajja komai ba tana ta tafiyarta, Hajja ta ta6e baki tace "Ni dai bata min ba wllh, wa ya sani ma ko mayya ce ita ta lashe d'an a ciki? banda haka mu kaff xuri'armu babu wanda ya ta6a barin ciki yana karaminsa wllh, kana samun cikinka sai ka haifesa lafiya da izinin Allah, toh sai kuma a fara 6ari a kan matar Aliyu? Aa wllh ni dai na dasa ayar tambaya a kan wnn mata dake shisshige masu, to naga mata tun jiya tana ta sintiri cikinmu kamar wata er uwarmu, wa xai yarda da haka banda ku da baku san ciwon kanku ba, ni don dai kada ace ban kyauta bane na cika fitina, banda haka wllh da na koreta nace imu imu ya isa ta koma gida kawai" A haka har suka isa mota Umma uffan bata ce mata ba, Hajja na kallon Rahama da murmushi tace "Toh mun gode yarinya Allah ya saka da alkhairi, yanxu tafiya xaki yi daga nan dai ko? Don mu gidan ubansa muka nufa" Rahama tace "Ehh Kaka ga motata can, nima gida xan wuce" Hajja ta juya ta kalli motar da ta nuna mata tace "Au haba, toh Allah ya saka da alkhairi, dama don naga ba can anguwan naku xa mu bane shi sa nace bari dai in gaya maki inda xa mu... Naka ma ya samu me kula da shi idan bai da lafiya a wannan xamanin ai abun farin ciki ne, don gaskiya yanxu ba a ba ma makotaka hakkinsa kamar xamaninmu" Aunty Rahama dai murmushi kawai take, can ta kalli Jiddah tace "Toh Allah ya kara lafiya Jiddah, sai na kawo mama can gidan in sha Allah, Allah ya kara afuwa" Jiddah tayi murmushi tace "Ameen Nagode Aunty" Aunty Rahama ta kara masu sallama ta tafi gun motarta, shi dai Abuturrab na xaune driver seat ya kulle, Hajja ta bude bayan motar tana kallon Jiddah tace "Toh shiga" Jiddah ta shiga motar Hajja ma ta shiga, Umma ta xaga xata shiga ta daya side din murya can kasa Hajja tace "Yanxu xata shigo duk ta matsi mutane malam" Kamar kuwa Umma ta ji abinda Hajja ke cewa ta bude front seat kawai ta shiga, a hankali Hajja tace "Toh Alhamdulillahi" Bayan sun d'an yi nisa Hajja tace "Yanxu ina muka nufa naga kana ta wani xagaye xagaye Aliyu" Umma tace "Can gidana xa mu tafi" Hajja tace "Me?? Aje gidanki a kan me? Anya kina tsoron Allah kuwa Ramlah ga dai gidan uwarsa a kai mata yarinya ta kula da ita tana yi nima ina yi xaki wani ce a tafi gidanki? To ni nace gidan Usman xa mu kai ta, ai matar Aliyu ce ba matar wani ba, mata kawai neman fitina yayi maki katutu, me xaki yi ma Jiddan wanda mu bamu iya ba, ni dai wllh kin cika wahala, to gidan Usman xa a kai ta in ji ni, mata duk kin shanye yayarki sai yanda kika yi da ita kina ta mulkanta yanda ranki ya so? To ni dai ba ruwana" Shi dai Abuturrab driving yake a hankali, Umma tace "Idan kaje can bus stop din ka ajiye ni Aliyu" ya d'an kalleta yayi kasa da murya yace "No Umma u just have to ignore her, don't take this personal, as if u don't know who she is" cike da damuwa Hajja tace "Toh wai meye kake bata baki kamar warce aka yi ma laifi dai daga fadan gaskiya, ni fa ba wani abu nace ba, ko kaji na xageta ne?" Umma tace "I said drop me Aliyu" yace "Then let me drop u home kawai, bai kamata kiyi dropping a hanya ba" Ta kallesa tace "Ba ni nace maka haka ba" parking ya nemi waje yayi ganin how serious she was ya juya yana kallonta ta bude motar ta sauka, sai duk Jiddah bata ji dadi ba taji kamar ta sauka motar ta bi Umma, shi dai Abuturrab ya bi Umma da kallo har ta kulle motar tayi gaba, Hajja ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh ba shkkn ba... Yanxu da fada nayi mata ai baxata sauka ba, kaga yanxu da nayi mata bayani cikin nutsuwa tayi wucewarta gida abunta baki alekum" Abuturrab bai tanka ta ba ya ci gaba da driving dinsa, Hajja tace "Kai kuma sai wani cika kake kana batsewa kamar dai mu muka kashe maka jariri Aliyu, toh kai arnene da baxa ka dau tawakalli ba, ita kanta warce d'an ya lalace a cikinta ma ta hakura tana ta fara'a abunta tun a asibiti amma kai sai wani nukurci kake yi kana ba ma banxa ajiyar mu, a hakan kake so Allah ya baka wani? Ai ba a ma Allah haka, da kasan xai baka ne?" Wani harara Abuturrab ya watsa mata ta madubi, Jiddah ta d'an yi murmushi ta sunkuyar da kanta. Da daddare Jiddah na kwance kan gadon Hajja bayan tayi wanka tayi shirin kwanciya, bude kofar dakin aka yi ta daga kai Abuturrab ya shigo dakin ya kulle, ta mike xaune tana kallonsa har ya iso ya xauna gefenta ya kamo hannunta yace "How are you feeling now?" Tace "Alhmdlh naji sauki" Gyada mata kai kawai yayi, da damuwa tace "Are u still sad" ya kalleta amma bai ce komai ba, cikin lallashi tace "Kayi hakuri plss, Allah ya rubuta hakan xai faru... And there is a reason for everything..." Ya d'an yi murmushi slowly yace "Sure wife" Ta rungumesa tace "Cheer up pls dear" Ya marairaice mata yace "Xa ki samar mana wani da wuri plss???" Er dariya tayi tana shafa chest dinsa tace "Sai in ka bani da wuri ae, sai in samar mana da wuri" yayi kasa da murya yace "Yanxu fa??" Xaro ido tayi dai dai nan aka bude kofar dakin, ta dinga kokarin kwace kanta amma ya ki saketa, Hajja tace "Kun ga jaraba ko? Ni dama sai da na innata a raina kawai dai na bi son rai ne na laka ma matar mutane maita, amma can kasan xuciyata ina tunanin kilan takuranka ne ma ya sa cikin nan ya lalace, banda haka yarinya daga 6ari ko kwana biyu ba ayi ba ka xo ka sa ta gaba a daki ka makaleta, yanxu meye ma'anar haka Aliyu? Ke kuma kin wani sakar masa jiki kamar kyanwa, ai kya bari ki murmure yanda ya kamata tukunna dai ko" Tashi Abuturrab yayi daga kan gadon ya nufi kofa, Hajja ta bi sa da wani kallon takaici, can tace "Tirrr, wannan ai jaraba ce kawai ba wani abu ba..." Jiddah dai ta koma ta kwanta ta ki yarda su hada ido da Hajja, don sai ta ji kunya sosai... Washegari da safe Hajja na kada mata shayi me kauri Abuturrab ya shigo dakin, ya xauna saman kujera yana kallon Hajja yace "Ina kwana" tace "Lafiya lau, basu baka kumallon bane a can ka yo mana nan?" Yace "Aa, Abba ne ke kiranki" Tace "Usman din?" Yace "Ehh" ta mike da sauri tana cewa "Dama nayi wani mugun mafarki a kansa wllh, shi sa yau da sassafe na fita na ba mai gadi kudi yaje can anguwan da almajirai suke ayi min sadakan kosai na dubu daya" Abuturrab dake kallonta yace "Mafarkin me kika yi?" Tace "Aa sai kace wata jahila xan xauna ina gaya maka mafarkin da nayi bayan naji ance babu kyau, er benue fa nayi mafarki tana kokarin tura mun shi a teku ta basa apple yana ci dadin apple na dibansa yana kakkanne ido, ni kuma sai gani na taho a guje ta bayanta kafin ta turasa ni nayi maxa na turata cikin ruwan sai ruwa ya tafi da ita ta dinga kurma ihu da karfi, ni dai na kamo hannun yaro na muka dawo gida" murmushi kawai Abuturrab ke yi Hajja ta fice daga dakin, Abuturrab ya mike ya dau shayin Jiddah da warmer din masa da miya yace "Tashi mu je" Ta xaro ido tace "Ina?" Ya sha kunu yana kallonta, mikewa tayi ya fita ta bi bayansa, bedroom dinsa ya tafi da ita bayan sun shiga ya kulle kofar, ta marairaice masa tace "So kake in ji kunya don Allah?" Yace "Ehh shi nake so ki ji" Xaunawa tayi saman carpet din dakin ta rasa ma me xata ce masa, ya ajiye mata shayinta da waina yace "Eat now" Abincin ta fara ci yana kallonta, taji ya kira sunanta, ta kallesa, yace "Tell me how everything happen pls" Ta ajiye wainan hannunta tace "Me yasa baxa ka cire wannan abun a ranka ba and move on pls?" Yace "Na cire wife, just that i am still wondering what happened all of a sudden on that day, tunda lafiya muka rabu da ke ai, and i even escorted you to the gate" Sai kuma ya jinginar da kansa da gado a hankali yace "I wish na raka ki har cikin gidan may be hakan da bai faru ba" cikin sanyin murya tace "Ko da kai ko babu kai dole hakan xai faru tunda Allah ya rubuta hakan" Yace "But pls tell me how it happen" Tayi shiru kamar baxata ce komai ba, ganin yanda yake kallonta a hankali tace "I saw someone just like my father...." Abuturrab yace "Ur father?" Ta gyada masa kai, yace "Where?" Ta sauke idonta tace "Gidan mama" Da mamaki yake ta kallonta yace "U mean ur father?" lkci daya hawaye ya kawo idonta tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Yes, i saw someone just like him" Abuturrab yayi kasa da murya da damuwa yace "Amma ai baba ya rasu Jiddah, wani baban kuma kike nufi" Ta fashe da kuka a hankali tace "Eh na san ya rasu, but they look so much alike, ni nasan abinda nake fada ai, i saw my father's duplicate" Abuturrab yace "Ikon Allah, bak'o su maman suka yi ne?" Tace "Nima ban sani ba, ina xaune parlon ya shigo and i was shock sbda nayi tunanin Abbana ne a lkcn at first, kallon Abba na kawai nayi masa...." Abuturrab ya dinga kallonta a bit confuse, knocking din kofar dakin aka yi, ya mike ya bude kofar, Jiddah ta goge idonta da sauri, Umma ya gani tsaye bakin kofar ya gaisheta ta amsa ta shiga dakin tana kallon Jiddah tace "Ya jikin?" Jiddah ta gaisheta ita ma sannan tace "Na ji sauki Umma" Umma tace "Toh maa sha Allah, sannu" juyawa tayi ta fita Abuturrab ya bi bayanta cause he need to talk to her about this. Karfe sha biyu saura na safiyar Hajiya Fatima ta iso gidan da Rahama bayan sun kira Abuturrab ya tura masu address din gidan, a lkcn da suka iso gidan Jiddah na bacci a dakin Abuturrab, Hajja na kyalla ido taga Rahama da Hajiya Fatima ta bi su har parlon Ummi, Umma sai wani hararanta take, Hajja na washe baki tana kallon Rahama tace "Ashe uwarki ce wannan mata me kirki haka?" Rahama na murmushi tace "Ehh" Hajiya Fatima suka kara gaisawa da Hajja cikin fara'a, Hajja tace "Ai ni na haifi Uban Aliyun, da yake dai ni ba mai shige shigen gidan yara bace shi sa tun ranan da aka yi wannan yakin a gidan baki sake ganina ba, balle an saki fitinanniyar gidan, kinsan fa halin banxa aka kamata tana yi dumu dumu, toh dai ba ruwana gwara ka rufa ma wani asiri kai ma Allah ya rufa maka naka" Hajiya Fatima tace "Haka ne kam Baaba, kinga rashin xuwan da baki yi ne yasa bamu sake haduwa ba don kuwa ina yawan leka masu duk bayan sati" Hajja tace "Oh oh dama nace Jiddah na murmurewa idan ta koma gidan mijinta nima sai in tattara in koma can din in sa mata ido da kyau don kada aje a samu wani cikin ya lalace a banxa, ai ba abu bane mai kyau er yarinya karama kamar ta cikin fari ace ya lalace, kwata kwata ba kyau haka idan ba a saka ido a kanta ba tayi ta samun ciki yana xubewa kenan, amma dai ni nasan da akwai wani abu a kasa ba banxa ba, da kyar idan wannan kishiyar tata ta barta a haka, don kaf xuri'armu babu wanda ya ta6a 6ari mu dai" Hajiya Fatima na murmushi tace "Toh Allah dai yayi mana mai kyau, ita kuma Allah ya bata wanda xai tsaya" Hajja tace "Ameen dai, to a kawo masu abinci mana, me lemo da ruwa xai yi ma mutum???" Ganin su Mama xasu wuce bayan Azahar Umma ta tafi dakin Abuturrab ta taso Jiddah ta fito su gaisa, Jiddah ta shigo parlon Ummi ta gaida su da murmushi fuskarta, Hajiya Fatima tace "Ya jikin Jiddah?" Jiddah tace "Na ji sauki Mama" Hajiya Fatima tace "Alhmdlh, Allah ya kara maki lafiya" Ummi na kallon Jiddah da ta rakube waje daya tace "Shiga ciki ki kwanta to..." mikewa tayi ta shiga dakin Ummi, Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "Tsautsayi dai kawai, ni fa na shiga gidan nasu da safe yace tana bacci..." Da sauri Ummi ta dakatar da ita don kada ma Hajja ta ji kan xancen tace "Allah sarki, Allah shi yasan dai dai ai Hajiya" Hajiya Fatima tace "Wllh abun ya tsaya min har yanxu a rai, ji nayi ta kwala ihu kawai..." Hajja ta gyara xama tace "Ta kwala ihu a ina?" Hajiya Fatima tace "A parlor na" Hajja ta hangame baki tace "Wai a parlonki cikin ya lalace dama?" Hajiya Fatima tace "Ehh wllh Baaba shi yasa abun ya dameni" Umma tayi saurin cewa "Aa babu xancen saka damuwa a rai Hajiya, sai kace ba musulmai ba, Aa mu kam mun yarda da kaddara wllh, ai ko ba a parlon ki ba tunda Allah ya kaddara sai cikin nan ya xube dole xai xube ko ma a ina ne, in ma dakina, dakin Ummi, ko ma dakin Hajja" Hajja dai aka rasa abun cewa, sai kallon kowa take ta gefen ido, Hajiya Fatima tace "Haka ne kam, Allah yayi mana me kyau" Umma tace "Amma kun yi wani bako a ranan da ya sameta a parlon naki ko?" Hajiya Fatima tayi shiru, sai kuma ta kalli Umma tace "Mai gidana ne, dawowarsa kenan ma daga Abuja" Umma tace "Ikon Allah... To ce ma Aliyun tayi taga yana kama da babanta ne...." Hajiya Fatima ta gwalo ido tace "Babanta, amma ai tace min babanta ya rasu" Umma tace "Kwarai ya rasu, amma tace wai suna kama sosai" Hajiya Fatima ta kalli Rahama da ta saki baki ita ma, Hajja tace "Me kama da babanta kuma??" Hajiya Fatima tace "Toh ni kam na rasa ma me xance kuma" Ummi tayi murmushi tace "Ai kam abun da mamaki, kuma dama irin haka na faruwa ai sai ka ga wani wanda ke kama da wani naka da ka sani" Hajja tace "Aa to ko dai uban nata mutuwan karya yayi masu, wato ya gaji da wahalan su da talauci a hayi" Umma da ta bude baki ta kalli Hajja tace "Toh sai kuma aka yi yaya?" Hajja tace "Atoh, ya gudu mana, so nawa muke samun irin wannan labarin daga karshe ace ai ya gudu birni ya auri wata mai kudi sun hayayyafa, ku ka san ko haka yayi shi ma" Salati Ummi ta dinga yi a ranta, Umma kuma ta dinga ma Hajja wani irin kallo, ita kam Hajiya Fatima sai kirkiran murmushi take, Hajja tace "Xancen gaskiya fa, idan kuwa har sun tabbata ya mutu din to duk yanda aka yi wanda ta gani din d'an uwan ubanta ne, tunda ba daga sama ta fado ba... ayi mutum ace bai da dangi ko daya" Hajiya Fatima da kanta ya gama daurewa don ita dai a iya saninta duk familyn mijinta ta sansu na kauye na birni da ma wa enda suke wasu kasashen, ta dinga kallon Hajja ta ma rasa abun cewa, Hajja tace "Da xa a samu hoton shi uban nata da aka ce ya rasu sai a kai ma mijin ki ya gani kawai" Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Ina ga hakan xai fi, idan anyi hakan kilan Jiddan xata fi samun nutsuwa ta kara sakawa a ranta cewar ba mahaifinta bane kawai me kama da shi ne" Hajja tace "Toh ba shkkn ba, amma idan nayi magana a dinga min kallon ta6a66iya, kawai abinda xa ayi kenan yanxu a samo hoton ubanta mu kai ma mijinki shi kuma mu ji me xai ce, sannan idan kin lura er ki na da wannan nakasan na gefen kumatu ita ma jiddah na da shi, wannan lotsewan nan" Hajiya Fatima dai tayi shiru, Hajja tace "kawai abinda xa ayi kenan" Sai wajen karfe biyu da rabi Hajiya Fatima da er ta suka bar gidan, amma gaba daya a sanyaye take da wannan lamari har Allah Allah take ta tafi ta sanar ma mijinta dake gari har lkcn. Abuturrab na kallon Umma yace "Xan gane gidan, wancan lkcn ma ai da Hajiya Fatimar muka je" Umma tayi shiru, sai kuma tace "Toh Allah ya kyauta, xuwa bayan la'asar sai mu tafi can din, nasan ita matar uban ai baxata rasa hoton marigayin mijin nata ba" Abuturrab yace "Haka ne, amma fa tana fita bara sai dare ake samunta a gida" Umma ta rike ha6a tace "Bara kuma? Allah me hikima, bara take yi?" Yace "Ehh" Umma tayi shiru sai kuma tace "Kar a biye halinta Aliyu, idan da taimakon da muka ga xa mu iya rendering mata we should do so, ta ci albarkacin Jiddah" Abuturrab ya girgixa kai yace "Bani da wannan halin Umma" Umma bata kuma ce masa komai ba, ya mike yace "In kina nan har magrib din sai mu tafi can gidan, idan kin koma gida kuma sai in je in daukeki a can gidan mu tafi" Tace "Shkkn" Bayan magrib Abuturrab ya tafi can gidan Umma ya dauketa xuwa can gidan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login