Showing 246001 words to 249000 words out of 346625 words
Chapter 83 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
sannan yana kallon Hajja yace "Hajiya lafiya me ke faruwa, kin kiramu duk hankali a tashi mun taho babu shiri" Hajja ta fashe da kuka tace "Baxan kiraku ba Kabiru, babu xagi da cin mutuncin da Usman bai min yau ba a gidan nan ni da uwar gidansa uwar 'ya yansa a kan wannan mata dai da ku ke gani Hafsah, kai ni har kayana yace in debe in bar masa gidansa baya son ganina" Bude baki Aunty tayi tana kallon Hajja, Abba kuwa kansa na kasa yana sauraronta, Hajja ta fyace majina tace "Don haka na kiraku ku xama shaida, in har Usman ya kwana da auren matar nan Hafsah to shegiya iyayena suka haifeni, wllh wllh sai ya saketa a gaban kowa ko kuwa ya canxa wata uwar a kasuwa" Abba ya daga kai yana kallon Hajja da sauri don maganan nata came unexpected, Aunty da ta fara jin xufa na keto mata ta dinga kallon Hajja xuciyarta na bugawa, Hajja tace "Shkkn na gama wannan babin, yanxu sai in koma maku babin abinda ya haddasa komai" Nan Hajja ta kwashe duk abinda ya faru a asibiti tana daga tsaye tana demonstrating har karshe... Tana huci tace "Yanxu duk xan kwasheku mu tafi gidan Ramlah ku ga yanda yarinyar ta mayar da Jiddan, to kuwa tunda yar daba ce har shi Aliyun wataran sai tayi masa jina jina ai, ni ko ina xa mu jira wannan ranan, oh oh ba matar xama bace wllh" Hajja ta kalli Ummi tace "Kema don haka Aliyu ya xo ki tisa shi gaba ya sallami yarinyar ko ya canxa uwa, duk nuna masu xa mu yi mu en banxa ne" cike da isa Umma tace "Kuma kin manta baki kara masu da cewa na kai ita matar Aliyun police station ba, yanxu haka tana can a kulle" Hajja ta kalleta da sauri tace "Auuu, kun ji abun arxiki, kai amma Allah ya maki albarka Ramlah, ka ga mace me kamar maza, yo ai da dani kika tafi gidan yan sandan in basu bayanin komai da yanda komai ya faru xa su fi daukar abun da muhimmanci" Gaba daya brothers din Abba kallon Umma kawai suke amma sun ki cewa komai sbda Hajja, Hajja ta koma ta xauna ta sharce xufar goshinta tace "Ko ni ko Hafsah yau" Aunty dai idan hankalinta yayi dubu ya tashi a lokacin, Alhaji Lawal ya d'an yi gyaran murya yace "Kina ji na Hajja" Hajja ta jefa masa wani kallo tace "Kai saurara Malam, ba na kiraku don ku kawo taku shawaran bane, ni fa umarni kawai na bada a nan ba wani abu ba, nayi kiranku ne don ku taho ku ba d'an uwanku shawaran yayi duk yanda xai yi kada in sakar masa bakina ya tagayyara, wllh wllh...." Sai kuma ta fashe da kuka sosai tace "Na fi shekara hamsin ban xubda hawaye ba sai gashi yau wai Usman xai sani inyi ta xubarwa kamar er banxa" Abba ya kalleta a karo na farko yace "Hajja kiyi hakuri, wannan abun wllh duk bai kai..." Wani tsawa tayi tace "Ya kai, har ya wuce... Wllh sai ka saketa" Duk aka kasa cewa komai a parlon Umma dai sai kallon tv da aka rage magana har karshe take bbu ko digon tausayin Aunty a ranta, Aunty taga fa da gaske Hajja take, ta mike ta isa gabanta ta fashe da kuka ta durkusa ta rike kafarta tace "Don Allah kiyi hakuri Hajja, idan ma wani laifin na maki kiyi hakuri kar ki kashe min aure...." Hajja ta janye kafarta tace "Kun ga muguwa wai inyi hakuri kar in kashe mata aure, halinki ne xai kashe maki aure ba ni ba, kuma ai Hauwa ya kamata ki tafi ki kama kafarta ki bata hakuri kafin ki bar gidan idan kuwa ba haka ba sai hakkinta ya kama ki wllh, wato kin cuceta ainun, kin shiga tsakaninta da mijinta kin raba su, walakancin da take hadiya ko kurma da bata jin magana baxa ta iya hadiyewa ba, duk wanda ya kalleta ya san cikin damuwa take babu kwanciyar hankalin xaman aure, hakan kuma bai isheki ba sai da kika nemo ma d'anta er dabar Habuja kika aura masa neman kashe masa uwar gidansa Jiddah, don kuwa duk ke kika koya mata abinda xata yi idan ta xo asibitin" Kuka kawai Aunty take cikin tashin hankali tana cewa "Hajja idan wani abun nayi ayi min hakuri don Allah" Hajja ta mike tana kallon Abba da kyau tace "Tashi ka dauko takardan da ka adana kake sa wa ayi sake sake ba tsoron Allah" Abba ya kalleta cikin kwantar da murya yace "Hajja..." Ta dakatar da shi a fusace tace "Wllh kar ka bari xuciya ta kwasheni in fada maka ba dai dai ba Usmanu" Ummi na son cewa ayi hakuri amma ta rasa ta ya don bata san yanda Hajja xata dau hakurin nata ba, ita dai duk jikinta yayi sanyi kuma har ranta bata son Abba yayi wnn sakin, mikewa Abba yayi ya tafi parlonsa, Alhaji Kabir ya mike ya bi bayansa, bayan sun shiga parlon yace "Hajja baxa ta saurari kowa ba a wannan lokacin Usman gudun matsala da kuma fushin uwa, ka rubuta ma Hafsah saki daya hakan shine kadai mafita" Abba dai bai ce komai ba ya dau takardan da biro suka fito parlon, Aunty na ganin takardan da biro ta kara rudewa tace "Usman yanxu sai ka iya saki na?? Takarda fa ka dauko Usman, yanxu baxa ka bata hakuri ba Usman" Hajja ta mike sai safa da marwa take fuskar nan nata a murtuke take cewa "Wllh baxan hakura ba kar ma a bani" Abba babu yanda ya iya haka ya rubuta takardan yana kallon Aunty xai ajiye a gabanta Hajja ta fixge ta kai ma Umma tace "Karanta min Ramlah" Umma ta amsa tana kallon takardan tace "Na sake ki saki daya" Sai da gaban Ummi ya fadi sosai ta dinga kallon Abba, Hajja tace "Shkkn haka ya sa?? To uban wa ya saka?" Umma tace "Haka aka sa" Hajja ta mayar masa tace "Rubuta Hafsah a gaba" Abba ya amsa ya rubuta sannan ya mika mata, kin amsa tayi tace "Aa bata da hannunka ba ruwana kar ta kai ni gaba tace ai ni na mika mata takardan ma" Abba ya ajiye ma Aunty takardan yana kallonta, ta dauka tana dubawa, wani murmushi tayi tana gyada kai ta goge idonta ta kalli Ummi da Umma sannan ta mike fuuu ta wuce bangarenta sunan Jiddah na mata yawo a kai...., Hajja tace "Sai a tafi a fara harhada kaya kuma a koma benue, Allah ubangiji ya saka ma Hauwa duk cutarta da kika yi" Mikewa Abba yayi xai bar parlon Hajja tace "Dawo malam" ya dawo kuwa, tana tafe hannu tana kallonsa da kyau tace "Aliyu kuma da ka sa a baki sai ya saki baiwar Allah har da rantse rantse to ka cire ido a kansa, rantsuwan da kayi kuma daga gobe ka fara daukan axumi don Aliyu ba shi da matar kirki da ta wuce Jiddah ita din alkhairinsa ce, yo kayi axumi sittin ma ranan da ka hallaka wani bawan Allah da mota a hanyar Abuja balle uku kacal? To tun wuri ka fara axuminka bakin ka alekum, ita kuma wannan mata ta Aliyu Nanisa take ko wa?? ni da Ramlah kadai muka san yanda xa ayi da ita wllh, yanxu ma police station din xan bi ta mu tafi" tana kai wa nan Abba ya mike ya bar parlon ta bi sa da wani shegen kallo, snn ta kalli su Alhaji Lawal tace "Duk na sallameku, a nemi me rufe mana taro ku koma garin ku"
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Ina mata ma'abuta gyaran jiki kuzu ga supplement na gyaran jiki kala muna da supplement masu sa haske da laushin fata da gyaran jiki da maganin sanyi da masu kashe kuraje da tanbo ku Wani kalar supplement muna da cikin sauki da rahusa kadan Daga cikin su
Lady capsule
Royal jelly
Sugar wanita
Khusus
Vitamin e
Cantik ayyu
Puspa ayyu
Dara
Rapit wanita
Maca capsule
Reload
Papaya
Collagen snail
Flat tummy
Sliming capsule
Da sauran su domin neman Karin bayani atuntube wanna number 08066726866 mmn mujaheed
Umma bata kara ko minti daya a gidan ba ta yi wucewarta gidanta ranta fess, bata ta6a jin Hajja ta burgeta irin yau ba, tana xaune parlonta bayan ta idar da magrib kenan Ahmad ya shigo tare da Abuturrab, tayi masu kallo daya ta ci gaba da jan carbinta, Ahmad ya xauna saman carpet yana shafa kansa, Abuturrab ya xauna saman kujera yana kallonta, Jin duk sun ki cewa komai ta kallesu tace "Wai ya aka yi ku ka xauna min jigum jigum a gabana? Lafiya" Ahmad ya sauke kansa a hankali yace "Umma don Allah kiyi hakuri ayi abinda ya kamata, Umma all this...." Umma ta katse sa tace "Inyi hakuri ayi me?" Ahmad yayi shiru, Abuturrab dai sai kallonta yake, ta girgixa kai tace "Kun ga ku fita harkata wllh, ku fita harkata kar in maku rashin mutunci, ku kun isa ku gaya min abinda ya kamata inyi?" Sallama aka yi bakin kofa, Ahmad ya juya, Nafisah ta shigo parlon ta karaso ta xauna ta gaida Umma sannan tace "Umma wai kawu Lawal xa su yi magana da ke a waje" Umma ta ta6e baki kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Toh sai su shigo" Nafisah ta mike ta fita, Bayan few minutes Alhaji Lawal da Alhaji Umar suka shigo parlon, xaunawa suka yi saman kujera Ahmad ya gaishesu, Abuturrab ma ya gaida su ya mike ya tafi bedroom din Ahmad, Ahmad ya mike ya bi bayansa, Hakuri Alhaji Lawal suka dinga ba Umma tayi hakuri ta janye case din da ta kai police station na Aneesah, Umma ta saki baki tace "Wato dai ana nufin banxa kawai ta doka kenan?" Alhaji Umar yace "Aa bata doki banxa ba, amma ta ci darajan masu daraja, sannan shi Aliyun dole xai dau matakin da ya kamata a kanta, ba ido xa a xuba mata ba...." Umma ta kasa ce masu komai don tana jin nauyinsu ainun, ita dai ta san da Abba ne bai isa ya sa ta janye case din nan ba, ganin ita suke saurara ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh a gaskiya sai ta xo har gidan nan ta ba Jiddah hakuri, sannan sai ta rubuta statement a station cewar ko kallon banxa baxai kara hadata da Jiddah ba" Alhaji Umar yace "Ai wannan ko baki fada ba doka ce, dole yan sanda sai sun sa ta rubuta statement din" Mikewa Umma tayi ta wuce dakinta ta dauko jaka da wayarta, ta fito ta shiga dakin Ahmad tana kallonsu tace "Ka fito ka wuce da mu station Aliyu" Ahmad ya kalleta yace "Umma kin manta patient ne shi?" Umma tace "Eh ban manta ba amma ya taso ya kama gabansa, kai kuma ka xo kayi driving dina" Daga haka ta juya ta fita, Ahmad ya d'an yi murmushi ya mike ya nufi kofa, Abuturrab ya tashi shi ma ya fita, Su Alhaji Lawal suka fara fita parlon Umma ma ta fita, Abuturrab dai na tsaye, Ahmad ya gane dakinsu Maimoon yake son shiga, shi dai bai ce masa komai ba ya nufi kofa, Abuturrab ya shafa kansa yana bin sa da kallo, Har Ahmad ya fita ya juyo da sauri ya kalli Abuturrab yace "Umma.. she is coming back" Ko rufe baki bai yi ba Abuturrab ya bi sa shi ma... A motar Umma suka tafi police station din, su Alhaji Umar kuma na tasu motar. Abuturrab ya kulle kofar parlon bayan ya shigo yana kallon Aneesah da ta wuce sama fuuuu kamar xata tashi sama, Calmly yace "Hey you, listen to me!!!" Kamar jira take ta dawo da sauri ta nufesa ta cakumo kwalarsa tana xaro ido tace "Me xaka ce min Aliyu?? Gaya min me xaka ce min?? Nace me xaka ce min??" Sai kuma tayi wani murmushin takaici tace "Ni kayi ma kishiya, kishiyar ma me tallan awara a hayin rigasa? Ni Aliyu? Hakan kuma bai isheka ba kai da iyayenka ku ka kulleni a cell a kan matsiyaciyar yar talakawa??" Sai kuma tayi wani dariya ta sake sa ta koma baya tana tafe hannu tace "Toh ni kuwa xan ga ta yanda xa ku yi xaman aure da ita, xan ga ta yanda xaka xauna da ita a matsayin matarka, xan ga ta yanda hakan xai faru...." Safara'u ce ta sakko kasa da saurinta jin shigowarsu da hayaniyar Aneesah, tana huci ta nufesa ta sauke masa mari me kyau cikin daga murya tace "Da hadin bakinka har xa a je a kulle 'ya ta a cell don ta doki wata banxa can mara galihu? A kan wata banxa ka amince aka ci mutunci matarka har gidan yan sanda? To wllh wlllh sai ka san ka mika Aneesah hannun hukuma sun tafi da ita police station, xaka san ka kai er mu station, wnn case din yanxu aka fara shi Aliyu..." Abuturrab ya dinga kallonta babu ko kiftawa trying hard to control his rising Temper, tafiyar da ya ji a stairs ya sa shi daga kai, ya ga Aunty ce ke saukowa cike da isa da gadara tana masa wani kallo, ita ma ya dinga kallonta har ta shigo parlon, tayi wani murmushi tana nuna sa da hannu tace "Aliyu xaka san ni Hafsah ka munafurta, i will mercilessly deal with u, xan nuna maku ku kananun kwari ne daga kai har uwarka da tsinanniyar kanwar uwarka, yanda uwarka da kanwarta suka sa na fita dakina na kwana daya kacal, yess na kwana daya ne kacal don babu uban da ya isa yyi terminating xamana a gidan nan don xuwa gobe matsayina still dai dai yake da na uwarka a cikin gidan nan, to haka ita ma xan sa ta fita gidan na har abada, sai xaman gidan ubanka ya gagareta wlh, kai kuma xan ga abinda xai sa kayi rayuwar aure da Jiddah a duniyar nan...." Sai kuma ta kalli Aneesah tace "Ki kwantar da hankalin ki Aneesah, Aliyu ya shigo da Jiddah gidan nan su xauna a sunan mata da miji mu ga, ta tare mu ga ta yaya" Safara'u tayi wani dariya kamar mahaukaciya tace "Ashe bashi da labarin ba a mana kishiya ne, ba shi da labarin mu daya muke rayuwa gidan miji har mutuwa, to kai da xama da mata biyu sai a lahira idan ana yi" Abuturrab na kallon Aneesah strictly yace "First thing tomorrow morning ki kwashi kayanki ki kama hanyar gidanku na sake ki Aneesah" Daga haka ya juya ya fice daga gidan without closing d door, xaro ido Aneesah tayi, tayi still a wajen kamar me son fahimtar kalman da ya furta, lkci daya ta dafe kirji jikinta ya dau rawa tace "Aunty ban gane me yake nufi ba, me yace ne wai?? Ku min bayani don Allah Aunty" Daga Safara'u har Aunty dama bude baki suka yi suka bi sa da ido ko wannensu with shock, Safara'u ta kalli Aunty da idanuwanta kamar xa su yi magana tace "Hafsah ashe dama d'an ta'adda kika hada aure da yar mu?? Hafsah kin san su waye familyn mu kuwa??" Wani kara Aneesah ta saki ta cakumo Aunty ta runtsa ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Aunty ji nayi kamar yace ya sakeni, ko ba haka yace ba??Ji nayi yace ya sakeni...." Ta kuma rusa wani ihu tace "Na shiga uku na lalace..." sai kuma ta sulale nan kasa a sume.... Bayan kwana uku, Umma na xaune dakin Ummi dake gefen gado a xaune, xuwanta gidan kenan amma bata ji dadin yanayin da ta tarda yayartata ba, ko bata fada mata ba ta san tana tare da damuwa da rashin kwanciyan hankali ne sosai, don har ta fada, Umma tace "Yaya na baki shawara na baki shawara kin ki dauka, wllh wllh yaya ki ajiye batun wannan mutumin a gefe, ki ajiye batunsa yaya, kar ki je wani cutar ya kama ki a bar ki da wahala, to wai sai me in Alhaji Usman ya fita harkanki? Abinci ne babu ko sutura ne babu? Sai me don Allah, nace maki ki debi kayanki mu tafi can gidan nawa ki huta na kwana biyu kin ki, idan ma baki son xaman gidana ne ki wuce Adamawa kawai mana, ga ki da yan uwa birjik dake marhaba dake kin tsaya takaicin namiji xai kashe ki yaya??" Ummi tayi murmushi tace "Kenan banyi appreciating duk kokarin Hajja a kai na ba, ai baxata ji dadi ba idan nace xan tafi tunda nasan har yau a bayana take kuma tana kan bakanta, ni damuwata Ramlah abinda mutanen gari suke fada a kan batun nan, Hafsah ta wuce tunaninki wllh, barin yanda take da shige shigen mutane kaf anguwar nan babu inda ba a santa ba, babu inda bata shiga, shi Usman Hajja ta sa ya saki Hafsah wai duk a kai na kamar yanda ake cewa, sannan shi kuma Aliyu kinga aika aikan da ya tafka, ance kuma ni na sa shi ya aikata hakan, to duka duka yaushe ya auri yarinyar da har xai saketa Ramlah? I am really confuse, na kirasa sai yace min ai ya koma aiki baya kaduna, to ya xan yi, har nan kanwar uwarta ta xo ta mana tijara da rashin mutunci har tana ikirarin xa mu gani ta kuma ci sa'an Hajja taje gidanki ranan, ni dai har ta gama ina xaune parlor bance mata komai ba, wato yanda na fitar da kishiyata shine na sa d'a na ya saki er su sbda mugun hali, kinga Ramlah duk wani abu na damuwa bana sonsa wllh kasa bacci nake, ni bani da wata matsala da Usman a yanxu, don da can din ma ai kusan a hakan muke xaune da shi, ai wnn ba sabon abu bane na saba, kawai yanxu abinda Aliyu yayi ma Aneesan ne ya tsaya min yake damuna"