Showing 30001 words to 33000 words out of 346625 words
Chapter 11 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
masallaci, Jiddah na xaune compound din kan karamin kujera kusa da dakin mai gadin da ruwa cikin buta a gabanta tayi nisa tunanin da take, Har suka kusa isowa wajen Abuturrab kallonta yake haka ma Ahmad, kamar ance ta daga kai tayi ido hudu da su, sosai gabanta ya fadi ta sunkuyar da kanta da sauri ta fara alwala da ruwan butan gabanta har suka fita compound din, sai a sannan Ahmad ya kalli Abuturrab yace "Don Allah wa yarinyar nan tayi maka kama da???" Abuturrab yace "Wacce yarinya?" Ahmad yace "Yarinyar da ke xaune a compound" Da mamaki Abuturrab yace "Ohh dama akwai yarinya xaune a compound din?" Wani kallo Ahmad ya jefa masa, Abuturrab ya daga shoulders dinsa yace "Banyi noticing ba" Ahmad yace Karya kake "Wllh" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba, Ahmad yace "Joke apart captain, bata yi maka kama da wannan yarinyar da muke siyan awara a wajenta a hayi ba" Abuturrab ya ta6e baki yace "Kai da kake kallonta kenan idan kaje siyan awaran, ni kam banda murhu babu abinda nake gani a wajen" yana fadin haka ya shige Masallaci kafin Ahmad ya sake ce masa komai, Ahmad ya bi bayansa kawai. Ko da suka fito masallacin Ahmad ya tsaya gaisawa da abokansa na layin, Abuturrab ya shiga compound din kawai, Jiddah na ta sauri tana kwashe kayan shanyan da Maman Abdallah ta shanya don garin akwai hadari, tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai sai da ya iso dai dai inda take tace "Ina yini?" Bai amsa ba yace "Kina da wani matsala?" Ta girgixa masa kai, ganin haka ya ci gaba da tafiyarsa, dai dai nan Ahmad ya shigo compound din bata yadda ta kallesa ba har xai wuceta sai ya tsaya yace "Bakuwa muka yi yau a gidan ashe?" Taki yarda ta kallesa still, tayi kasa da murya tace "Ina yini" yayi murmushi yace "Lafiya lau, sannu da xuwa" Maman Abdallah ta leko tace "Dakta Abdallah fa boyewa yake idan yaji muryar ka" Ahmad yayi murmushi yace "Ae kice masa alluran ya kare" Ta kwashe da dariya tace "Lallai kam, shi dai ya tsorata da kai kawai Dakta" Ahmad yace "Ashe bakuwa muka yi gidan" Tace "Ehh wllh yar uwata ce daga kauyenmu ta xo jiya da yamma" Yace "Allah sarki, toh barkan ta da xuwa" Maman Abdallah tace "Ae ko dai Dakta, mun gode" Murmushi yayi ya ci gaba da tafiya a xuciyarsa ya kara gaskata cewa lallai kamanni ne kawai suka yi da me Awara a hayi, but the resemblance is so obvious even the dimples and large eyes, can balcony Abuturrab ya tsaya duk yana jin abinda suke fada, sai da ya iso Abuturrab yace "Kai dai baka abu da class Ahmad, meye na tsayawa hira da matar mai gadi pls?" Bai jira me xai ce ba yayi wucewarsa ciki, Ahmad ya girgixa kai kawai ya bi bayansa. Da yamma Mamam Abdallah ta ba jiddah kwanukansu ta kai can cikin gida sbda a ciki xa a sa masu abincin dare, Jiddah tace "Ta cikin parlon ake bi xuwa wajen girkin?" Maman Abdallah tace "Ehh inda muka je daxu ba, ynxu ma babu kowa gidan yaran duk sun tafi islamiyya, Hajiya nasan tana bangarenta yanxu haka, ai kinga dakin girkin da mai girki ta fito ta miko mana kumallo daxu da safe, nan xaki shiga, dakin ma ya kusa biyun wannan da muke ciki ae wllh" Jiddah ta mike ta dau babban samiran ta fita ta bar Maman Abdallah na linkin kaya, Babu kowa babban parlon kamar yanda Maman Abdallah tace, ko ina tsaf sae kamshin turaren wuta da ya kama parlon, Kasa karasawa can cikin parlon Jiddah tayi, tun da ta xo duniya bata ta6a ganin irin wannan parlon ba da ma komai na cikinsa, duk sai tsoro ya kamata, hanyar da taga Maman Abdallah ta bi daxu da safe ta bi ta d'an leka kofar da ta gani a bude ganin wasu mata biyu kuma har sun hada ido ta risina a hankali tace "Sannun ku da aiki" Duk suka amsa mata dayar tace "Shigo ki ajiye kwanon" Jiddah ta karasa kitchen din, ta kara masu sannu da aiki sannan ta ajiye kwanon, kanta a kasa tace "Me xa a kama maku?" Dayar matar tace "Aa babu komai 'yan mata, mun gode" Doguwar tace "Sae dai kawai wanke wanken dake cikin bahon wanke wanke, ba shi da yawa" Jiddah ta juya tana kallon sink da matar ke nuna mata, karasawa tayi wajen ta tsaya tana tunanin ta ya xata yi wanke wanke a takurarren waje haka sannan ta ina xa ta dinga xubar da ruwan wanke wanken, a hankali ta juya tana kallonsu tace "Ruwa da omo fa" Matar tace "Ga pampo a gabanki ki kunna, wannan roban kuma sabulun wanke wanke ne a ciki xaki matso ya fito"
Bayan magrib Abuturrab yyi parking inda ya sa6a parking ya sauka motarsa ya kulle da kafa ya karasa kofar gidansu Jiddah. Yaro ya aika ciki yayi masa sallama da mutanen cikin gidan, Hansai ce xaune tsakar gida da kawayenta biyu, Hansai ta sharbe majina tana matse hawayen kumburarren idonta tace "Wllh xai aika, waye bai san cewar shaye shaye Iliya yake ba, ni dai baxan kwana gidan nan ba yau gaskiya gwara in tafi wani wajen in kwana" Zulai tace "Aa nima dama ban bada shawaran ki kwana ba tunda ya furta sai ya kona gidan da kyar baxai aika ba" Ladi tace "Toh yanxu ina yarinyar nan ku ke tunanin xata tafi haka, wa gareta a duniyar ma gaba daya?" Hansai tace "Ai wannan magana ma bai taso ba, dolenta ta dawo duk inda ta tafi ta xo ta rabani da wannan mahaukacin mutumi, idan ya kona min gida gidan ubanwa xan koma kowa na ta kansa a rayuwar nan, dama gidan iyah nake ta tunanin ta shige amma duk dubawan da yan sanda suka yi a gidan babu ita babu alamarta" Kallon yaron da ya shigo suka yi gaba daya, yaron yace "Wai ana sallama a waje" Abuturrab ya daga kai bayan Hansai ta fito cikin gidan, ganinsa ta makale kofar xaure ta kasa karasowa, Ya karasa shi, yana dubanta yace "Ina yini?" Da kyar cikin rawar murya tace "Lafiya lau Alhaji, sannu da xuwa" kafin yace mata komai ta fashe da kuka tace "Muna cikin tashin hankali da alhini Alhaji" yana kallonta yace "Me ya faru?" Tana matsar kwalla tace "Tun jiya ake neman yarinyata har xuwa yanxu babu labarinta, ban san inda xan sa kaina ba xuciyata kamar ta fashe" Yayi shiru yana kallonta, ta sharbe majina tace "Shi kansa wanda ke da niyyar auren nata nan ya xo daxu da yamma ba irin tijaran da bai min ba har da ikirarin xai kona mana d'an gidan nan idan ba a fito masa da matarsa ba, wllh wllh bamu da masaniyar inda take, babban tashin hankalina ban san halin da take ciki ba yanxu" Yace "Yanxu ya ake ciki da shi wanda xai aureta din, baki basa kudin nasa bane?" Tace "Wllh yace baxai amsa ba, yanxu haka ma da kudin na tafi gun yan sanda na kai rahotu kasan sai an basu wani abu me d'an tsoka kafin su kula ka, sannan gidan radio da gidan talabijin duk na bi na rarraba masu kudin don su yi ta sanarwa har Allah ya bayyanata, yanxu maganar da nake maka ko dubu talatin ina jin kudin bai kai ba a ajiye a daki, 'ya ta bata fiye min komai ba a duniya?" Kallonta kawai Abuturrab yake bai ce komai ba, ta sake sharbe majina cikin rawar murya tace "In dai da wani taimakon da xaka mana yarinyar nan ta bayyana da wuri ka taimaka domin girman Allah Alhaji" Abuturrab yace "Ina shi madaurin auren nata?" Tace "Kawuna ne, tare da shi ma muke ta sintirin gidan radio da police station tun safe" Abuturrab yace "Ina son ki hadani da shi" Sosai gabanta ya fadi, yace "Yana da waya?" Da sauri tace "Aa bashi da shi, sai dai gobe in je in sanar masa, idan ka xo sai Bibalo ta kai ka" Abuturrab yace "Toh shkkn, nagode, sai goben" Daga haka ya juya ya bar wajen, ta bi sa da kallo gabanta na faduwa, da sauri ta koma ciki, Zulai tace "Waye hala?" Hansai ta share wani xufa da ya keto mata tace "Aa yan xuwa jaje ne, yanxu dai gidan Kawu Jibril xan tafi tare da Bibalo idan ya so sai mu kwana can kawai kada Iliya ya far mana cikin dare mu mutu" Ladi tace "Gaskiya kam, ku tafi can din kawai ku kwana, don kwana gidan nan ba karamin hatsari bane" Sai kusan karfe tara Hansai ta isa gidan kawun nata da Bibalo, Suna shiga d'an tsakar gidan yace "Me kuma kika xo yi nan kina neman ki ja min fitina Hansatu, ni nasan Iliya d'an daba ne amma bansan dabancin nasa ya kai haka ba, babu irin tijaran da iliya bai xo nan da tawagarsa sun min ba, in don dai shegiyar dubu ukun da kika bani ne cikin kudin sadakin yarinyar Allah ya kai mu gobe da safe in tafi in siyar da kaji na in baki kudinki, wannan tashin hankali har ina a kan dubu uku, wllh ban san tantirancin iliya ya kai har haka ba, to gaskiya baxai yiwu ba kuma ki fitar min daga gida kada ma yasan kina nan in shiga uku" Hansai ta fashe da kuka tace "Amma dai duk hatsin da yake kawo min ina dibar maka har rabin kwano wataran in kawo maka, har gawayi na sha cika maka leda me kayau kayau in kawo maka, kuma matsala ta samu sai ka rufe ido kace xaka koreni, cewa yayi fa xai kona gidanmu, idan na shashantar da batun ya babbake mu cikin dare fa?" Kawu Jibril yace "Toh ni cewa yayi xai ruguje gidan, ganinki ciki ai sai ya kara tunxurasa ya aikata hakan" Hansai na matsar kwalla tace "Yanxu duk ba wannan ba, dama wani Alhaji ne ya xo xai taimake mu kan lamarin da ganinsa babban mutum ne me fada aji, kuma tun mutuwar isuhu yake xuwa siyan awara ya mana ihisani, yanxu dai so yake ku hadu gobe a kan lamarin nan, don Allah ka sanar masa duk mun je gidan radio da gidajen talabijin din kaduna kai rahotu, dubu biyar xan baka kar kaji komai" Yace "Ina dubu biyar din?" Tace "Ba ni nace xan baka ba, fatanmu kawai ya taimakemu Allah ya bayyano mana da shegiyar yarinyar nan mu mika ma Iliya tsiyarsa ko ma sarara, don idan ba nemota aka yi ba aka damka ma Iliya bamu da sauran kwanciyar hankali wllh" Bata jira cewarsa ba ta shige dakin matarsa tana cewa "Lantana duk garin nan babu wanda bai xo min jajen abinda ke faruwa ba amma banda ke, ko ba komai ai sai ki ajiye duk wani tsiya dake tsakaninmu a matsayinki na musulma kixo ki jajanta min wannan musiba da ta sameni..."
07087865788....βπ» Start ur payment for the book because i am almost and almost done with free pages kar ku ji dippp an dakataπππ *Jiddatul Khair**ππ
_By khaleesat Haiydar_πβπ»
10....
Washegari da asuba bayan an idar da sllh Ahmad ya fito rike da karamar jakarsa, dakin Ummansa ya shiga ya gaisheta tace "Da asuba xaka tafi Ahmad?" Yace "Ehh kar nayi missing train din ne" Umma tace "To kun yi da drivern ya xo da asuba ne ko wa xai kai ka train station din??" Yace "Aa Abuturrab xai kai ni" Umma tace "Abuturrab kuma? yana garin ne? Lafiya bai koma aiki ba" Ahmad yace "Ehh satin nan yana nan yace min" Umma tace "Toh Allah ya tsare, kayi addu'a dai" Yace "Ameen Umma, in sha Allah" Har ya kai kofa tace "Har xaka tafi gashi ka mance da drugs din nawa" Juyowa yayi da sauri yace "Oops, kiyi hakuri Umma Abuturrab xai kawo maki anjima in sha Allah" Tace "Toh Allah ya kai mu, Allah ya kiyaye hanya" sallama ya kara mata ya fita dakin, yana fita compound ya dau wayarsa ya shiga kiran Abuturrab, Abuturrab ya daga yace "Gani na shigo layin yanxu" Ahmad yace "Alright" Sai da suka yi nisa Abuturrab ya d'an kalli Ahmad yace "Medical report din da nace xaka min din fa?" Ahmad yace "Idan aka yi how will it reach you?" Abuturrab yace "The plane coming from Abuja to kano, xan yi ma pilot din magana abokina ne, sai ku hadu ka basa" Ahmad yace "Flight din karfe nawa ne?" Abuturrab yace "karfe uku" Ahmad ya tabe baki, Can ya kalli Abuturrab yace "Toh wai ma me ya hanaka komawa gun aiki kake neman medical report din karya Captain?" Abuturrab yace "That is none of ur interest, kai dai kawai kayi min medical report" Ahmad yace "Toh baxa ayi ba" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba har suka iso Station din, Ahmad yace "Yauwa pls captain i will text some drugs now to you, na umma ne, xaka siya ka kai mata, i forgot to do so yesterday" Abuturrab yace "A hakan xan siya magani in kai mata? Kana ganin babu kaya jikina" Ahmad ya kallesa, Jallabiya ce milk color jikinsa, Ahmad yace "Shi kuma wannan bargo ne a jikinka kenan, beside ni bance da safe ba, wani pharmacy xaka samu a bude this early, kaga dole dai sai anjima" bude motar Ahmad yyi ya sauka yace "Thank you" Daga haka ya rufe motar ya shiga cikin tashan, Abuturrab ya bi sa da wani irin kallo, bayan few minutes ya ja motarsa ya bar wajen, Abuturrab ya na isa gida text din Ahmad na drugs din ya shigo, lkci daya alert din kudin drugs din ma ya shigo, tsaki Abuturrab yayi ya cire jallabiyan jikinsa ya shiga bathroom. Karfe goma saura Abuturrab ya fito dakinsa, bangaren step mum dinsa ya fara shiga ya gaisheta, tana gyara press dinta tace "Ina xuwa da sassafen nan haka, kai da nake tunanin ka dau hutu ne don ka huta" Yace "Xan je siya ma Umma drugs dinta ne" tace "Tohhh, Ahmad din fa?" Yace "Ya koma gun aiki" Tace "Toh nima ka siyo min Panadol night..." Yyi murmushi yace "Toh in sha Allah" Ya juya xai fita tace "Captain shiru shiru kuma baka turo abun ba, kada a siye wajen ne fa" Yace "Ehh ina son in sanar ma Ummi ne...." Da sauri tace "Sai ka sanar mata captain? Ina ce yanda ka dauketa haka ka daukeni?" Ya d'an yi shiru, sai kuma yyi murmushi yace "Toh nawa ne kika ce?" Tace "1.7m" yace "Toh xan tura in sha Allah" Tace "Yauwa ko kai fa, idan ka dawo anjima ka shigo da akwai wata maganan kuma" Yace "In sha Allah" daga haka ya fita, bangaren Ummi ya shiga, waya ne kare kunnenta, hakan yasa ya jingina da kofa ya jira har ta gama sannan ya risina ya gaisheta, tace "Lafiya lau..." yace "Jiya na shigo kin yi bacci" Tace "Ehh da wuri na kwanta" Yace "Ohk, sai na dawo" Daga haka ya fita dakin ta bi sa da ido. Abuturrab na shiga mota yayi ma Ahmad transfer din kudin da ya turo masa, sannan ya nufi wani babban pharmacy, ya siya duk drugs din, bai mance na Stepmum dinsa ba, ita ma ya siya mata pack har uku na drug din da tace sannan ya dau hanyar gidansu Ahmad, Sallama yyi bakin kofar parlon aka amsa masa sannan ya shiga, Umma na xaune parlon da Maman Abdallah dake xaune kasa Jiddah na gefenta alamar gaisheta suka shigo yi, daga kai Jiddah tayi suka hada ido da shi ta sunkuyar da kanta, karasowa cikin parlon yyi ya xauna yace "Ina kwana Umma" tace "Lafiya lau Aliyu, ashe kana garin" Kallonsa Jiddah tayi jin sunansa a karo na farko, ya shafa kai yace "Ehh ina nan Umma, ya karfin jiki?" Tace "Ah Alhmdlh sauki ya samu" Mikewa yayi ya karasa kusa da ita ya ajiye mata ledan maganin hannunsa yace "Ga drugs din naki Umma" tace "Toh nagode son, Allah yayi albarka" komawa yayi ya xauna yace "Ameen" tace "Ya su yaya?" Yace "Suna lafiya..." Tace "Toh a kawo maka breakfast?" Tana fadin haka ta mike, yace "Aa umma nayi breakfast a gida" Umma tace "Toh ga awara da Maman Abdallah da mai sunan yaya suka yi da safe, u will like it" Ya d'an kalli Jiddah da kanta ke kasa, Umma ta mike ta nufi kitchen, Abuturrab ya girgixa kai da sauri xai yi magana sai kuma yyi shiru ya sauke boyayyen ajiyar xuciya, Maman Abdallah na kallonsa da fara'a tace "Ina kwama abokin Dakta" Babu yabo babu fallasa yace "Lfya lau" Jiddah bata dago ba ita ma tace "Ina kwana" yace "Lafiya lau" Umma ta fito kitchen, sai ga mai aiki rike da karamin tray me dauke da awara da sauce da pepper soup din naman rago a rufe a wani warmer din, dinning ta kai ta ajiye, Umma na kallon Abuturrab tace "Gashi can a dining area son" Ya d'an yi murmushi yace "Nagode Umma" Tace "Ko a kawo maka nan?" Ya bi dining area din da kallo sannan yace "Ohk" Nan kusa da shi mai aikin ta kawo ta ajiye sannan ta wuce, Maman Abdallah ta mike cike da ladabi tace "To Hajiya xata maki gyaran ne yanxu??" Umma tace "Eh to, ko kuma ta bari gobe ai tana nan, ko ba kwana biyu ta xo yi maki ba?" Maman Abdallah tace "Tana nan tukun wllh Hajiya, don bata ma sa ranan tafiya ba" Umma tace "Toh shkkn gobe sai tayi min gyaran" Maman Abdallah tace "Toh shkkn Allah ya kai mu Hajiya" Mikewa tayi tana kallon Jiddah tace "Toh mu je gobe sai kiyi aikin ko" Umma tace "To ki bar ta tayi kallo mana, tunda ke ba kallo kike ba" Maman Abdallah tayi dariya tace "Ehh kuma haka ne, tunda xan je maki kasuwa yanxu, ina fita hijabi kawai xan sa in tafi dama" Umma tace "Toh ki bar mata Abdallah ko baxai xauna ba"