Showing 252001 words to 255000 words out of 346625 words
Chapter 85 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
tace "Xan dauko" daga haka ta juya ta wuce, ta tafi kasa ta dauko masa abincin ta kawo ta durkusa ta ajiye gabansa sannan ta koma ta dauko kayan shayin da bread su ma ta ajiye, yana kallonta yace "Why just a cup?" Ta girgixa kai tace "Ni baxan sha ba ai" ya mike yace "Jirani" daga haka ya fita parlon, tana dai durkushe har ya dawo da wani cup da ya wanke with plate da ledan gasasshiyar kaza, ya raba ruwan shayin into equal two ya xuba madara da milo with sugar cubes, ya juya da cokali ya ajiye mata daya a gabanta yana kallon eyeballs dinta, ta kalli agogo kamar xata yi kuka tace "Karfe tara ya wuce fa yanxu" yace "Kuma kike bata ma kanki lkci" bai jira me xata ce ba ya juye kazan a plate ya ajiye mata gabanta yace "You had better start eating and stop wasting ur time don idan baki ci ba baxan maida ki gida ba..." ko rufe baki bai yi ba ta dau tsoka daya na nama ta fara ci a hankali, idan ta ci sae ta dau shayin ta sha kadan, duk yanda yayi da ita ta ki cin bread din da kwai wai ta koshi, lkci lkci take kallon agogo don duk hankalinta baya tare da ita, har dai ta shanye shayin ta jingina da kujera tana jiransa ya gama, kamar bai son ci abincin yake ci, sae yayi minti biyu xuwa uku yana kallon Tv kafin ya ci gaba da ci, tayi narai narai da ido a hankali tace "Kai fa nake jira, ko in sauka kasa in jira ka?" Ya kalleta yace "Kike jirana ayi me?" Ta xaro ido tana kallonsa tace "Toh wa xai maida ni gida?" Yace "Oh that?" Tayi shiru tana kallonsa xuciyarta na bugawa, yace "Toh bari in gama inyi wanka" hade kai tayi da gwiwa wani hawaye ya taho mata, mikewa yayi ya isa kofar ya sa makulli ya cire snn ya shiga bedroom, tun Jiddah na ta zaune tana jiransa har ta gaji ta mike tana kallon agogo dake nuna karfe goma da minti talatin, ta fashe da kuka ta nufi dakin ta tsaya bakin kofa ta bude a hankali tana kallon ciki, kwance ta gansa yayi rub da ciki idonsa lumshe, goge hawayen dake xuba idonta tayi ta juya ta koma parlor, gajiya tayi da xama ta kwanta saman kujera ta takure waje daya ta rufe idonta nan da nan kuma bacci ya dauketa don da gida ne ita tuni tayi bacci ma.... Karfe sha biyu Abuturrab ya tashi ya fita dakin ya dawo parlor, kallo daya yayi mata ya dauke plates din abin da suka ci ya nufi kofa ya bude ya sauka downstairs ya kai kitchen, kayan shayin da bread kawai ya bari a parlonsa, ya dawo ya shiga daki ya bude press ya dau bedsheet dinsa da duvet ba na Aneesah ba, har ya fita ya dawo ya dau hijab din Aneesah dake a goge, sannan ya tafi wani dakin ya shimfida xanin gadon bayan yayi dusting din ko ina ya dawo clean, fita yyi ya koma part dinsa, ya nufi Jiddah dake bacci, dukawa yayi yana kallonta, doguwar riga ne jikinta me sharashara amma ba sosai ba don ba a ganin jikinta, What a sleeping beauty, ya fi minti daya yana kallonta bbu ko kiftawa, bayan few seconds ya lumshe ido ya dauketa kamar Baby ya nufi kofa, a gigice ta bude ido tace "Na shiga uku, mene haka?" Bai tankata ba har ya fita dakin, bakinta na rawa tace "Don Allah ka ajiyeni ba bacci nake ba, i will walk with my feet, pls ka ajiyeni" har suka shiga dakin da ya gyara bai ce mata komai ba ya tafi ya kwantar da ita saman gadon a hankali yana kallonta, ta kasa kallonsa balle su hada ido, yyi kasa da murya yace "Kina son xa kiyi wanka?" Da sauri tace "Aa na yi a gida" yace "Toh ban ga kinyi sllhn isha ba, and u didn't wash ur teeth after eating..." Gaba daya a rikice take, tace "Nayi fa" yace "A ina?" Ta rasa abun cewa yace "Je kiyi alwala yanxu" sauka tayi kan gadon ta wuce bandaki da sauri, ya bi ta da kallo kamar yasan abinda xata yi ya mike da sauri ya bi bayanta tana kokarin saka makulli ya tura kofar ya shiga bandakin, ta fashe da kuka ta marairaice masa tace "Alwalan fa xan yi ka shigo" yace "Yi ina kallonki" ta rasa ma abinda xata ce masa, gaba daya a tsorace take da shi sae xare ido take, cikin rawan murya tace "But i want to ease my self" yana kallonta da kyau yace "Ai ban hanaki ba" Alwalan ta fara yi, gaba daya a rude take, shi dai yana kallonta har ta gama ya bata hanya ta fita sannan ya fita shi ma, hijab din ya dauka ya mika mata ya shimfida mata darduman, ta amsa ta saka hijab din, ya koma gefen gado ya xauna yana kallonta, sai kuma ya mike ya kulle kofar dakin, da bathroom duk ya cire keys din ya ajiye karkashin pillow, yana ganin ta idar da sllh ya kashe wutan dakin ya kwanta hade da lumshe ido, hawaye ne ya shiga sauka idonta tana xaune kan darduman, daga karshe ta kwanta ta takure waje daya, cikin bacci taji ya dauketa ya kwantar saman gado ya cire mata Hijab din jikinta ya rufa mata duvet, ya manna mata soft kiss a cheek dinta, ita dae runtse ido kawai tayi xuciyarta kamar xai fito kirjinta don tsoro, tana jin sa ya kwanta close to her ya cire mata hulan kanta ya xare ribbon din gashinta, a haka dae bata san lkcn da bacci ya sake dauketa ba.... Hajja ce rakube jikin kofar dakin Umma dake waya da Ummi inda take shiga ba ta nan take fita ba bayan ta sanar ma Ummi abinda Abuturrab yayi jiya, lkci daya Hajja ta tura kofar da karfi ta shiga tace "Huhuhu ke dai daga baxawara a fitina sae ke Ramlah, Ramlah ya xaki sa yaron mutane a bakin duniya haka tun jiya, daga dai ya xo ya dau matarsa, kika san aikin da yake so ta masa da ya tafi da ita tunda ita wancan ballagazar kazama ya saketa har saki uku? Matarsa ce fa ta sunna wa enda suka shaida kuma sun shaida, kai wannan mata da a Masar ne da an je an duba kwakwalwarki, mata tun jiya kin ishemu da mita ko baccin kirki baki bar mu mun yi ba wai Aliyu ya dauki Jiddah kaman wanda ya sace ta, Haba Ramlah!! Kawai daga tashi yau kin kama waya kin doka ma Hauwa kira, to me Hauwar xata yi? Ku dai wllh bakwa tsoron Allah ke da er uwarki, yaro dai da matarsa ta sunna ku bi ku sa masa ido kamar wanda yayi karuwanci, tirrrr da halinku wllh" Umma ta katse wayar hannunta fuskarta a murtuke tace "Don ubansa ni nace na basa Jiddah ne da xai dauketa ya tafi, ina ruwana da komawarsa da yayi aka sake masa aure?? Sannan kin xo kina wasu maganganu...." Da sauri Hajja ta katse ta tace "A'a... Ba tashin hankali bane Ramlah, kawai tunasar maki nake cewa matarsa ce ta sunnar ma'aiki ba wani abu ba, kilan yan gyare gyare xai sa ta gidan yayi k'ura tunda kinsan gidan ba kowa shi kuma yau ya dawo daga tukin jirginsa..." Umma ta ki tankata tana danna wayarta fuska daure, juyawa Hajja tayi ta nufi kofa murya can kasa tace "Ke dai ki rage fitina ko wannan kiba taki xai sa6e ki dawo mutum, fitina kadae ya isa ya dinga hura mutum ba sai abinci ba, amma ke kuwa fitinarki yayi yawa wllh, wannan ma nasan don kina jin kunyan idona ne da a gidan yan sanda asuba xai maki, to ni dae ba ruwana na sa halira take ko wa, ta yi masu kumallo Sapiya ta kai masu, sae ta dau kayan jiddah kala biyu ko uku ta kai mata" Daga haka Hajja ta juya ta fice daga dakin. karfe bakwai Jiddah ta bude kofar dakin da suka kwana a hankali ta fita ta bar Abuturrab dake bacci, sae kusan karfe shidda suka yi sllhn asuba sbda sun makara, wanda shi dai Abuturrab da wayonsa ya mance rabon yyi missing jam'i , kofar parlor ta nufa tana waige waige bayan ta sauko kasa tana isa kofar xata bude taji sa a kulle, ta 6ata fuska kamar xata yi kuka, babu yanda ta iya haka ta koma parlon ta xauna, sae kuma ta mike ta shiga bandakin dake downstairs xata yi wanka, bata ga sabulu ba haka yasa ta koma sama ta bude dakin a hankali ta shiga ta dau sabulu a bandaki ta dau hijab din da tayi sallah ta fita, bayan tayi wanka ta hau gyaran gidan da yayi k'ura which is so obvious ba kamar jiya da daddare ba. A hankali Abuturrab ya bude ido ta dalilin wayarsa dake vibrate, jawo wayar yayi ya ga Aneesah ke kiransa, yayi silencing wayar ya mike xaune yana kallon agogo dake nuna karfe tara, kiransa aka sake yi ya dau wayar yana kallon screen din, lkci daya ya hade rai, sai kuma ya daga ya sa handsfree yyi shiru, cikin rawan murya tace "Captain don Allah ka saurareni ba don halina ba, plss listen to me for God sake captain...." Sae kuma ta fashe da kuka sosai har da shessheka, babu yabo babu fallasa yace "Ina saurarenki" Pleadingly tace "Kayi min rai Captain, kayi min rai kayi hakuri, wllh kai ma ka san ina sonka, sonka da kishin ka ne ya ja min abinda na aikata ba da son raina ba, sharrin shaidan ne wannan abinda ya faru wllh, don Allah kayi hakuri ka gafarceni ka maida ni dakina captain, hakan baxai sake faruwa ba nayi maka alkawari, ka dubi girman Allah ka yafe min pls" yace "Kin yarda xaki xauna da abokiyar xama yanxu kenan?" Cikin kuka tace "Wllh na amince Captain, na yarda wllh" yace "Good, idan har kina son dawowa dakin ki kamar yanda kika ce to sai kin ba ita warce kika doka hakuri, xaki je har gida ki sameta ki bata hakuri yanda ya kamata sannan ki ba Umma da Ummi hakuri, u are coming back only on that condition Aneesah...." Shiru tayi taki cewa komai tana jin xuciyarta na mata wani xafi, yayarta Falmata tayi mata alama da tace masa tohhh, Aneesah ta galla mata wani harara, Abuturrab yace "U are not ready to come back then, don haka kada ki sake kirana baxan dauka ba" Cikin tashin hankali tace "Wllh i am ready captain, xan bata hakurin..." Yace "We will talk later then" Bai jira cewarta ba ya katse wayarsa ya mike l ya fita dakin ya tafi bangarensa, fess ya ga parlon ko ina sae walkiya yake, ya fi minti daya yana bin parlon da kallo, sai kuma ya karasa bedroom dinsa, nan ne kawai bata shiga ta gyara ba, wanka yayi ya shirya cikin kananun kaya ya sauko downstairs, dai dai nan aka yi ring din bell, Jiddah dake kitchen tana goge goge babu warce ta fado mata sai Aneesah, ta kasa motsi a inda take tsaye gabanta ya dinga faduwa, Abuturrab ya karasa ya bude kofar, Safiyya ce tsaye rike da breakfast ta gaishesa sannan ta mika masa basket din, yana kallonta yace "In ji wa?" Tace "Hajja" murmushi yyi ya kalli karamin jakar hannunta yace "Wannan fa?" Tace "Hajja tace a kawo ma Jiddah" ya amsa yace "Kina da kudin mota?" Tace "Driver ne ya kawo ni" yace "Sae anjima" kulle kofar yayi ya juya ya koma parlor ya ajiye abincin da jakar kayan ya nufi kitchen, ja baya Jiddah tayi da sauri da ya bude kofar, bayan sun hada ido ta juya masa baya har sannan xuciyarta bai dawo dai dai ba, ya karasa kusa da ita ya jawota kusa da shi yayi kasa da murya yace "Good morning...." Ganin taki cewa komai ya juyo da ita a hankali, suna hada ido ta sunkuyar da kai, ya lumshe ido ya daura lips dinsa a forehead dinta underneath his breathe yace "Good morning... other half" Juya masa baya tayi, tayi kasa da murya tace "Ka nemeta" ya bude ido yana kallonta sosai yace "Wace?" Ta juyo tace "Ur Other half, ko ka mance wacece ni?" Da farko shiru yyi yana kallonta, sae kuma yace "Wacece ke?" Tayi wani murmushi ta nufi gas ta kashe tace "Jiddah me Awara ta hayin rigasa, warce ba class dinka ba, warce ka aura kawai domin taimako ba don wani abu ba, warce kace ta saka a ranta kai din ba mijinta bane, snn kuma baxa ka ta6a xama mijinta ba, the jiddah that u were ashame to show as ur wife, the Jiddah u divorced without second thought, and the same Jiddah....." Wani tsawa ya daka mata, lkci daya tayi tsit ta juya tana kallonsa, daure fuska yayi sosai yace "Ni kike gaya ma haka?" Tace "Yes i was only reminding u" ya nufeta fuskarsa a tamke, haka nan taji gabanta na faduwa tayi still tana kallonsa, ya fixgota yana mata wani kallo yace "Ce maki aka yi na manta?" Tayi shiru, a d'an tsawace yace "Do u think u need to remind me of all this?" Sunkuyar da kanta tayi, ya saketa ya juya ya fice daga kitchen din... Ta fi minti biyar a tsaye kafin ta samu courage din fitowa parlor, xaune ta samesa a parlon, tana karasowa parlon ta kasa kallonsa, shi ma bai kalleta ba, lkci daya ya mike yace "Dauko gyalenki" bata ce komai ba ta wuce sama, ba a dau lkci ba ta sauko da mayafin tana kallonsa taga ya wuce sama, sae gashi ya sauko da car key dinsa, ba tare da ya kalleta ba ya nuna mata jakan da Safiyya ta kawo yace "Dauki kayanki ki sameni a mota" ta bi sa da kallo kafin ta dau jakar ta bi bayansa.... Har suka isa gidan Umma bai ce mata komai ba yayi parking bakin gate ya bude lock din motar, bude motar tayi ta bude back seat ta dau jakarta ta kulle masa motarsa ba tare da ta kallesa ba ta nufi gate, ya bi ta da kallo har ta shiga gate din sannan ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido xuciyarsa na bugawa... Jiddah tana ta tsaye bakin kofa ta kasa shiga ciki, ta rasa me ke mata dadi, haka kawai taji duk nauyin kowa na gidan ma ita take, gajiya tayi da tsayuwa daga karshe ta bude kofa a hankali ta shiga, bbu kowa parlon hakan ya sa ta nufi dakinsu da sauri ta bude ta shiga, Maimoon na ganinta ta kwashe da wani dariya tace "Aunty Jiddah da sassafe haka?" Lkci daya Jiddah ta hade rai ta ajiye jakarta ta tafi can karshen gado ta xauna, Maimoon dae sae murmushi take, Jiddah ta mike daga karshe ta nufi kofa da nufin ta tafi can bayan gidan tayi xamanta, Maimoon dae sae kallonta take kamar me son gano abu har ta fita, sae ta kuma kyalkyalewa da dariya... Jiddah taji kamar ta nutse bayan sun yi clashing da Umma da ta fito dakinta, ta sunkuyar da kanta ta risina a hankali tace "Ina kwana Umma" Umma da ta ki kallonta ita ma tace "Ina Aliyun?" Jiddah ta kasa cewa komai Umma ta wuce parlor kawai, ji tayi kamar ta koma dakin nasu kawai, muryar Hajja ta ji tace "Aa har kin dawo da sassafe haka kamar ana koranki? Ina Aliyun?" Jiddah ta risina ta gaisheta, Hajja tace "Ga dai kaya na bada a kai maki xaki bugo wannan uban sammako haka, ni dai ba ruwana wllh" daga haka tayi wucewarta tace "Toh ko bakin Ramlah ma bai isheku ba, mata kawai katuwar banxa" Throughout ranan Jiddah ta kasa sakewa gidan, bayan tafiyar Hajja gidan Ummi tsarguwan nata yyi yawa don dama Hajja ce kawai ke jan ta kamar ba abinda ya faru, jiddah kuwa gani take kamar kowa tunanin da yake daban a kan kwanan da bata yi a gida ba jiya, Ahmad ma da ya xo gidan duk hiran da ya dinga janta da shi ta ki sakewa, gani take kamar shi ma an gaya masa, she wished all this never happened, wani haushin Abuturrab take ji har cikin ranta, da yamma tana kwance a daki Safiyya ta shigo wai ana kiranta a parlor, ta mike da kyar ta sa hijab dinta ta fito, sosai gabanta ya fadi ganin Aneesah da yayarta Falmata xaune a parlon, Umma ma na xaune ta sha kunu, Jiddah ta xauna ba tare da ta sake kallonsu ba tace "Umma ga ni?" Umma ta kyabe baki tana nuna mata su Aneesah tace "Wai ke suke nema" Jiddah ta kallesu babu yabo babu fallasa tace "Ohk" Aneesah ta d'an kalleta after gathering much courage tace "Dama na xo ne in baki hakuri a kan abinda ya faru, sharrin shaidan ne ba wani abu ba" Jiddah na kallon Tv tace "No ya wuce ae" Aneesah ta dake tace "Toh nagode..." Falmata na kallon Umma tace "Sae ayi hakuri Umma, hakan baxae sake faruwa ba tayi nadama wllh" Umma taki cewa komai, bayan few minutes Aneesah tace "Toh mun gode Umma xa mu tafi can gidan gun Ummi Allah ya kara girma" har suka fita parlon Umma hararansu take.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
**DATA! DATA!! DATA!!!*
**Assalamu Alaikum**
*A.M.J DATA SERVICE*
*Muna sayar da DATA bundle akan farashi mai sauki, tuntubemu domin yin subcription dinku*
*📶MTN DATA🌕*
*Ina kke customer's ganifa na garzayo muku da data Mai aminci*
*mtn data plan*👇🏼👇🏼👇🏼
*500MB @₦200*
*1GB @₦ 300*
*2GB @ ₦600*
*3GB @₦900*
*4GB. @N1200*
*5GB @₦1500*
*6GB