Showing 240001 words to 243000 words out of 346625 words

Chapter 81 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

"Sannu" Umma ta kawo ma Ummi kujera ta xauna tana kallon Hajja tace "Toh ayi hakuri Hajja, xa a gyara in sha Allah" Hajja tace "Aa gwara ki gyara kam, yanxu ni da nake dolensa ba gani xaune a gefensa ba tun daxu, kema banda kina uwarsa baxan bari ki xo kusa da shi ba ma wllh, likitocin sun ce yana bukatar hutu sosai" Ba a dade ba Ramlah ta shigo da bargon da pillow hade da tabarma, Hajja tace "Yauwa er albarka, ajiye min can gefe da daddare a shimfida min inyi kwanciyata" Ramlah ta tafi ta ajiye inda Hajja tace.... Tun lokacin da Hajja ke ma Aneesah ihu Abuturrab ya farka don har tsakiyar kansa dake masa ciwo sosai yake jin surutun Hajja, amma ya ki bude ido ko nuna ya tashi, jin muryan Umminsa yanxu yasa shi bude idonsa ya mike xaune... Hajja tace "Alhamdulillah sannu Aliyu, ya jikin yanxu, amma inji dai ba surutunsu ya tashe ka ba duk su fita kawai, don ance a bari ka huta" Ya girgixa mata kai kawai, ya kalli Ummi a hankali yace "Ina wuni" Ummi tace "Lafiya lau, how are u feeling now?" Yace "Alhmdlh" Aneesah dai na tsaye sai kallonsa take tana tsoron xuwa kusa da shi Hajja ta koreta kuma, Kallonta yayi ai suna hada ido bata san lkcn da ta nufesa da sauri ba tace "How are u feeling now?" Hajja ta dinga mata wani kallo daga sama har kasa tana yamutse fuska, Umma ta tafi gun abincin da Ummi ta kawo ta dau plate ta shiga xuba masa har ta gama Hajja ta amshe ta kai masa tace "Ka daure ka ci ko kadan ne ka ji Aliyu?" Ya dinga kallon white rice din kafin yace "Ba shi nake so ba" Hajja tace "Me kake so Aliyu, fada min ko meye shi kaji" Ya d'an yi shiru, Hajja ta shiga lallabasa tace "Daure ka fada ko meye shi kaji Aliyu" Yace "Awara xan ci" Daga sama har kasa Umma take kallonsa, Aneesah tace "Toh Baby bari in koma gida yanxu inyi, i know it wont take long" Da sauri Hajja ta kalleta tace "Ba fa indomie yace xai ci ba Nanisa, Awara yace..." Umma tace "Xan kira can gida xa a soya yanxu a kawo, muna da shi ajiye a freezer dama" Hajja tace "Yauwa to maza kirasu, ko Jiddah ce sai a sa tayi tunda naga ta iya duk abun gargajiyan nan, dubi dambun da tayi ranan nan me shegen dadi wllh, sannan uwa uba tsafta, a tsaftace xata yi masa ta kawo tunda shi sarkin son tsafta ne" Aneesah da lokaci da mood dinta ya canxa ta hade rai tace "Nima ina da shi a freezer din, kuma cikin minti kadan xanyi in kawo..." Hajja ta kalli Umma tace "Yi min kiran Jiddah" Umma ta shiga dialing number Maimoon tana dagawa tace "Ba Jiddah wayar" Maimoon na ba Jiddah Umma tace "Kina ji na Jiddah" Jiddah tace "Ina ji Umma" Umma tace "Ku soya awara yanxu kuyi sauce xa ku kawo asibiti, xan kira driver ya je ya dauko ku" Jiddah tace "Toh Umma" Umma ta katse wayar, Hajja tace "Allah ya maki albarka Ramlah, yanda kika tsaya kan Aliyu kamar d'an da kika haifa Allah ya tsaya maki haka ke ma, uwarsa kuma Allah ya shiryeta..." Ummi ta mike tace "Toh Allah ya kara lafiya, Xan dawo anjima Hajja" Hajja tace "Je ki, tunda dai ga mu, idan da kara ma bai kamata ki biyo mu rigirigi asibiti ba sai kace ba d'an ki na fari ba, ai kara ma wani abu ne, duk sai naji kunya da na ganki wllh" Ummi dai bata ce komai ba ta nufi kofa ta fita Ramlah ta bi bayanta don Ahmad na jiranta tun daxu a waje, Umma dai ta tabe baki tana girgixa kai tana jinjina lamarin Hajja. Aneesah kam abun duniya ya isheta gashi har ga Allah bata iya awaran ba, to ko dai ta koma gida tayi order kawai yanxu yanxu, kallon agogo dake nuna shidda saura tayi, sai kuma ta nufi kofa ta fice daga ward din, bayan ta sauka downstairs ta shiga kiran Chef Salma, tana dagawa tace "Salma don Allah ina xan samu Awara yanxun nan na order...."




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you






Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulu mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd guess what😍munyi upgrading kayanmu gbdy domin jindadinku🥰bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida
💯 Natural/organic

maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki komai da komai
Akwai soap 3k
Student package 7k
Beauty kit 11k
Bridal kit 18k

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏





Ko gida Aneesah bata koma ba bayan ta amshi awarar a bakin hanya ta hau adaidaita ta koma asibitin, tana isa bayan ta sauka tana kokarin ba mai adaidaitan kudi sai ga Jiddah tare da Maimoon driver ya ajiyesu sun sauka motar, Hijab har kasa ne jikin Jiddah, Aneesah na ganinta bata jira amsan canjinta ba ta shige gate din asibitin kamar ana tunkudata ciki, Maimoon ta kalli Jiddah da sauri, ta rike ha6a tace "Saurin me wancan matar kuma take daga ganinmu? Ko dai sleepless night din ne tun yanxu" Jiddah dai bata ce komai ba, suka shiga gate din asibitin tare. Suna kallon Aneesah na ta xabga uban sauri, Maimoon bata san lkcn da ta kyalkyale da dariya ba tana tafe hannu tace "Ke wllh kamar tsoron mu take, saurin da take fa hade yake da guduwa" Aneesah na shiga ward din bata bi ta kan kowa ba tana kallon Aliyu dake kwance ta nufesa da sauri tace "Baby gashi nan har na yi" Tana fadin haka ta tafi gun basket din da Ummi ta kawo ta duka ta dau plate da sauri tayi backing dinsu don kar su ga tambarin inda tayi order din awaran ta juyesa a plate har da katon part na naman kaza ta sa spoon snn ta mike tana murmushi xata nufi gadon da Abuturrab yake Hajja tayi saurin mikewa ta dakatar da ita tace "Aa Nanisa... Ba xancen baby gashi har nayi bane, bani in ga irin awaran, wa xai ci abinda xae cucesa?" Aunty da shigowarta kenan kafin Aneesah ita ma da d'an coolern farfesunta ta dinga hararan Hajja kamar ta shaketa, Dai dai nan Jiddah suka shigo ward din da Maimoon, kallonta Abuturrab ya dinga yi without blinking, ita ko tun da suka hada ido sau daya ta sunkuyar da kanta, ta karasa gun Hajja ta durkusa ta gaisheta, Hajja tace "Tashi tashi, maza xuba masa ya ci tun daxu yake jira" Jiddah ta gaida Umma, sannan Aunty da ta ki amsawa, bayan nan ta mike, daga sama har kasa Aneesah dake rike da plate din awaranta take kallon Jiddah haka nan kawai taji gabanta na bugawa, Jiddah ta dau plate din da suka xo da shi ta bude warmer din awaran, Aneesah na ganin haka ta karasa gadon da Abuturrab yake tana mika masa awaran fuskar nan nata a tamke tace "Gashi nan na maka awaran Baby, eat it now" Ya amshi plate din ya ajiye gefensa yace "Thank you" Hajja ta bude hannu tace "Atoh dai" Mikewa Jiddah tayi tana mika ma Hajja awaran da ta xuba Hajja tace "Ya kike abu sanyi sanyi kamar kina shakkan wani, ki tafi kanki tsaye ki mika masa awaran tun daxu yake ta jira wllh, ko ke baki ga ya gantalar da wanda ta mika masa a gefe ba tunda ya san me xai ci ma kansa, atoh wa xai ci gaibu, maxa karasa ki basa, ae shi sa ake son duk runtsi ka xamo mai tsafta, Maimoon fita ki amso masa ruwan gora me sanyi, naga wa ennan duk ba sanyi...." Maimoon bata so ba, amma haka ta dau kudi da sauri ta fita taje ta siyo ruwan, Umma dai sai kallon ikon Allah take a cikin ward din nan yau, Aunty kuwa lkci daya ta ji xufa na keto mata daga inda take tsaye, a hankali Jiddah ta daga kai ta kalli Abuturrab suka hada ido cause bin ta kawai yake da kallo as if his life depends on that, kawai ta sauke idonta ta nufesa ta tsaya opposite side din da Aneesah ke tsaye ta kafeta da ido xuciyarta na ci gaba da bugawa babu sassauci, Jiddah tayi kasa da murya tana mika masa awaran tace "Ya jikin?" And he felt he was melting, kallon cikin idonta kawai yake, wanda hakan ya sa ta dawo uncomfortable ta sauke idonta da sauri tace "Is this enough??" basu ankara ba sai gani suka yi Aneesah ta kai hannu ta kwa6ar da plate din hannun Jiddah da karfi, har sae da awaran ya kife gaba dayansa a kasa, Jiddah ta ja baya da sauri tana kallon Aneesah gabanta na faduwa, tsalle Hajja tayi ta mike tana rafka uban salati ta kankance ido, Abuturrab yayi mata wani tsawa bayan ya fixge drip din hannunsa yace "Are you stupid Aneesah?? Are u mad???" Cikin daga murya Aneesah tace "Yes i am Aliyu, a gabana wata banxa yar talakawa xata wani kawo maka abincin ka ci bayan ni ma na kawo maka, ita a su wa? ko uban me ka hada da ita da xata wani xubo maka abinci ta taho simi simi kamar munafuka tana kallonka kallon cikin ido tana mika maka awara bata ji tsoron matarka na kusa da kai ba???" Ae tuni Aunty ta nufi Aneesah tana kokarin jan ta su fice daga ward din tana tutturjewa lkci daya kuma tana kunduma ma Jiddah wasu mugayen xagi jikinta na rawa, Hajja ta karasa kusa da su bakinta alekum ta dau plate din awaran Aneesan dake gefen Abuturrab ta kifa mata shi a kai cikin daga murya tace "Xo ki fita Shegiya uwar kazamai, ita Jiddar kike tambaya hadinta da Aliyu? to yanxu kuwa xa kiji hadinta da shi, Don kaza kazanki yanda kike matarsa ta sunna ita ma matarsa ce halaq malaq babu d'an kwal uban da ya isa ya canxa hakan, ko ke baki da labarin ya koma ya sake aure abarsa bai yi shawara da ko wani shege ba?" Sai da Aneesah ta dafa bango jin abinda Hajja ke cewa tana kallon Hajjar, ga jikinta duk awara tun daga saman kanta har kafarta, Ita kanta Jiddah jingina tayi da bango ta daya side din tana kallon Hajja babu ko kiftawa jin abinda take fadi, sae kuma ta juya ta kalli Umma... Aneesah ta nufi Abuturrab da sauri hankali tashe bakinta na rawa tace "What is she talking about Aliyu? What is she talking about i don't understand" Jin ya ki bata amsa kuma ya ki kallonta ta nufi Aunty ta riko hijab dinta kamar mahaukaciya tace "Aunty da gaske ne abinda matar can take fadi?? Is she for real" Hajja tace "Uwarki ce matar can ba ni ba, tsoron ki nake da xan ki fada maki gaskiya idan kowa ya ki?? ashe kwalo kwalo ake ta maki ba a sanar maki ba dama, to Jiddah dai matar Aliyu ce yau ni dai na fada maki kai na tsaye, kuma duk mun yi farin ciki da wannan abun arxikin, ae kowa na son nasa ya auri me tsafta...." Kaman daga sama suka ga Aneesah tayi kan Jiddah da tayi stiff a jikin bangon da take ita ma tana jin xancen Hajja kamar a mafarki, kafin Jiddah ta kauce tuni Aneesah ta cafkota ta hadeta da bango ta shakota iya karfinta, Abuturrab ya sauka saman gadon da yake yayi kansu da sauri, amma Umma ta rigasa yin kan nasu tana salati tana kokarin fixge Aneesah da ta kanainaiye Jiddah kamar macijiya tana kai mata duka ta ko ina, Hajja ta fasa wani ihu da karfi ta fice ward din a rude, cikin daga murya ta dinga cewa "Likitoci kuna ina ku kawo dauki, nas nas kuna ina ku kawo dauki, marasu lafiya kuna ina ku kawo dauki, an bar mahaukaciya ta shigo mana daki bamu san daga gidan uban wa ba, wayyoo xata kashe mana ita ku kawo dauki" Da yake da xuciya Aneesah ta rike Jiddah, duk karfin Abuturrab ya kasa kwace Jiddah daga rikon da ta mata, hakan ya sa shi ma ya shaketa da karfi amma inaaa taki cika Jiddah, Umma sai salati take tana kai ma Aneesah duka ita ma amma ko dar bata yi ba, sai cewa take wllh sai na kasheta nima a kasheni, wllh sai na kasheta, Allah sai na kasheta, Aunty taki ko motsawa daga inda take tana ta kallonsu, dai dai nan Maimoon ta shigo ward din tare da likitoci da Nurses, wani ihu Maimoon tayi tana bin dakin da kallo ta tafi da gudu ta dau cokalin diban miya ta nufi Aneesah wata nurse na kokarin riketa har sai da ta samu ta kwala mata da karfinta sau uku, hakan ne yasa Aneesah ta sassauta rikon da ta ma Jiddan sbda jiri da ya fara dibanta, Abuturrab ya turata baya da karfi without mind inda xata fadi, yayi saurin riko Jiddah da ta sulale kasa ya dauketa ya kwantar saman gado, Gaba daya likitocin where speechless a ward din... Is this movie they where acting or something of such here??? wani likita ne yayi kan Jiddah da sauri checking if she is fine sauran colleagues dinsa suka rufa masa baya, nurses din kuma suka dinga jan Aneesah da ta mike tsaye bayan ta fadi tana neman komawa kan Jiddah, don banda kundume kundumen xagi babu abinda take har dai suka fitar da ita ward din tana cewa su kyaleta ta kasheta, Abuturrab gaba daya ya gama rikicewa ya kuma ki barin kan Jiddah duk da instruction din doctors din, banda kuka babu abinda Jiddah take tana jin ko ina na jikinta na mata ciwo, Hajja bata tsaya iya kiran likitoci da nurses ba har masu gadi duk taje ta kira da passers by, Ta dinga ihu bayan ta ga an fito da Aneesah haraban asibitin tana cewa "Ku fita da ita can bakin titi kar a bar ta a nan, a fita da ita mahaukaciya ce, babu dawanau ne a kaduna? A taimake mu a mika ta can..." sbda yanda Hajja ta dage sai da aka fitar da Aneesah outside gate din asibitin, Hajja ta nemi gossip chair ta xauna ta rushe da kuka tana cewa "Yanxu xa ayi saki da wajewa ai ba sakin shirme da Usman ke son ayi da farko ba" Tuni Umma ta kira Ahmad ya taho ya fitar da su daga Asibitin, bayan ta katse wayar tana huci tace "Wllh sai ta san ta ta6a Jiddah, she must surely regret this..." Hajja ta gaji da kuka a waje ta dawo ward din bayan ta ta66atar an fitar da Aneesah, ta kuma rushewa da kuka tana kallon Umma tace "Ashe dama yar daba Aliyu ya aura duk bamu sani ba muke xaune da ita? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wllh bata doki banxa ba sai na shiga duk inda xan shiga an bi ma Jiddah hakkinta daga kaduna har Masar, xan nuna mata ni na fi ta dabanci, ni da nayi nawa dabancin a Masar" Abuturrab dai na tsaye kan Jiddah dake xaune saman gado likitoci sun bata pain reliever ta sha duk sun fita, ya ma kasa kallon su Umma ya kuma rasa abinda xai ce a ward din, ita dai Jiddah lokaci lokaci take share hawayen dake xubo mata ga kanta dake mata ciwo sosai har lkcn kuma gabanta bai daina faduwa ba, Abuturrab ya rasa ta yanda xai lallasheta saboda Umma dake ward din, Aunty dama tun da aka fitar da Aneesah ita ma ta fice sum sum sum, Maimoon da ke ta xaga ward din tana takaicin me yasa sai da aka aiketa hakan ya faru, wani kwafa tayi tace "Ai wllh bashi ta ci, kuma idan ban rama ma Jiddah wannan abinda ta mata ba ace ba ni bace" Umma dake ta boiling from inside sai jiran Ahmad dai take, yana xuwa kuma bata ko tsaya ta saurari kowa ba ta kama Jiddah suka nufi kofa Abuturrab ya bi su da kallo har suka fita... Ahmad da ke tsaye ward din bayan fitar Umma was so speechless sai kallon Abuturrab yake, sai kuma ya juya ya bi bayan su Umma, magunguna Umma ta sa ya siya ma Jiddah a pharmacy har da drip da xai kara mata wai, suna komawa gidan bayan ta sa ya saka ma Jiddah drip din, ta kuma sha magani ta kwanta ta mike a dakin tana saka hijab dinta kamar boss lady tace "Kai ni station Ahmad" Ahmad ya dinga kallonta ganin har ta nufi kofa ya bi bayanta yayi kasa da murya yace "Umma u need to calm down plss, wannan ai family issue ne, albarkacin Abuturrab da su Ummi kada ki kai ta police station, it won't make sense Umma" Umma ta juya a fusace ta kunduma masa wani xagi tace "A gidan uban wa wannan ya xama family issue?? Uban me Jiddah ta hada da ita da xai xama family issue? Wato ta doki banxa kenan kake nufi ko me?? Toh bari kaji ko Alhaji Usman bai isa ya hanani kai karar matsiyaciyar yarinyar nan police station ba yau, wllh sai na kulleta...." Jiddah dai sai kallon Umma take daga kwancen da take, Ahmad yace "Noo Umma plss listen to me..."


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login