Showing 105001 words to 108000 words out of 346625 words

Chapter 36 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

Jiddah xata bukata a kitchen ya siya, tare da Ramlah suka tafi siyayyen, duk ita ke fada masa abinda xa su siya na foodstuffs, har da filling din gas sun yi, kitchen din ya dawo well stocked up with foodstuffs, few pots, and some kitchen utensils, Jiddah dai na xaune parlon tun bayan dawowarsa da Ramlah, shi ma ya aika Ramlan taje ta kirata ne, yana tsaye kitchen din Ramlah ta jera komai, yana kallonta yace "Ahmad ya koma Abuja ne?" Ta gyada masa kai, ko ranan ma Ahmad ya kirasa amma yaki dagawa kamar dai shi ya aura masa jiddah, Ramlah na gamawa Abuturrab ya bata 2k transport ta fito daga kitchen din tana kallon Jiddah dake ta xaune, da murmushi fuskarta tace "Aunty amarya xan koma" ko lura da kallon da Abuturrab ke mata bata yi ba don jiddah kawai take kallo, Jiddah kam ta ga kallon da yake ma kanwartasa, cikin sanyi tace "To sai anjima" Ramlah ta nufi kofa.... bayan ta fita, Jiddah ta d'an kallesa suka hada ido, daure fuska yayi yace "In rokeki ki taso?" A hankali ta mike ta nufesa, komai na kitchen din ya shiga nuna mata da inda suke ajiye, ya koya mata kunna gas ya tabbatar ta iya kashewa ta iya kunnawa, yana kallonta da kyau yace "Anjima kafin in tafi xaki kunna min in gani" Tace "Toh" fita yyi daga kitchen din ya bar ta tsaye, ta bi sa da ido sannan ta bi bayansa. Abuturrab na komawa bangarensa ya ga calls din Umma har biyu, kiranta ya shiga yi bayan ta daga ya gaisheta, ta amsa tana tambayarsa ya gida, ya amsa mata, tace "Jiya naji ka je kun yi siyayya da Jiddah ko?" Yace "Ehh" Tace "Toh Allah ya saka da alkhairi" Ya amsa da "Ameen" tace "Yanxu meye babu cikin kayan, don xan taho anjima ne, sai in ga ko xa a iya tahowa da su" Ya d'an shafa kansa yace "Kawai Hijabs, bayan shi babu wani abu" Tace "Toh xuwa wani satin sai a dinka mata su" Yace "To Allah ya kai mu" Tace "Shi kenan dai ko?" Yace "Ehh" Tace "Toh sai na iso" Yace "Kamar yaushe xa ki taho Umma?" Tace "Xaku fita ne?" Ya girgixa kai yace "Xan koma aiki ne yau" Da mamaki tace "Xaka koma aiki kuma? ni na xata tunda ansan baka ji dadi ba xaka dau wani satin off?" Yace "Aa ni naji sauki, yau xan koma" Sake baki tayi, can tace "To ita Jiddar fa? Ko tare xa ku tafi?" Ya xaro ido kamar warce ta fado masa wani mugun abu yace "Aa" Tace "To ina xaka barta?" Yace "Nan gidan" Umma tace "Ita kadai?" Yace "Ehh babu komai" ta xaro ido tace "Aa gaskiya ka kawota nan kawai" Abuturrab yace "Aa xata xauna nan Umma" Umma tace "A kan me xaka bar yar mutane ita kadai a wannan gidan, ae baxai yiwu ba Abuturrab" Ya d'an shafa kansa a hankali yace "Umma tace fa xata iya xama, kuma ma xa a kawo mata mai aiki, ni nafi son ta xauna nan din kawai, and ranan laraba da safe xan dawo ai" Umma tace "Yaushe xa a kawo me aikin??" Da sauri yace "Ermm yau, in sha Allah" Umma ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Ni dai na fi gane ka kawota nan gida Abuturrab, ina ga xai fi wllh, it's not advisable to leave her all alone a gidan nan, she is too young for that, beside bata saba xama ita kadai ba" Trying all he xan to convince her yace "Umma xafa ta iya xama wllh, u shouldn't worry pls..." Umma tace "Toh amma is there anything wrong idan ka dawo da ita nan din, idan ka dawo weekend ba sai ka xo ka dauketa ba" Yace "Umma makaranta fa xata fara soon, plss u need not to worry" A hankali Umma tace "Toh shkkn wai dama don in dinga nuna mata wasu abubuwan ne, yasa nayi insisting" Ya girgixa kai yace "Ai bata da wani lkcn Umma, xata fara boko sannan islamiyya" Umma tace "Toh shkkn" ya d'an sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yace "Toh sai kin xo Umma" Tace "Kai xan ba Maimuna sakon kawai ta kawo, next week din xan shigo in sha Allah" Yace "Umma me yasa kika fasa kuma, ko fushi kika yi" Tace "Not at all, let me leave it next week kawai" A hankali yace "Toh shkkn Umma" Sallama tayi masa ta katse wayar tana mamakin irin taurin kan Abuturrab, wanda tasan da Aunty ce tayi masa wannan maganan baxai mata musu ba xai yi yanda tace, girgixa kai kawai tayi don kwata kwata bata ji dadin haka ba, Abuturrab ya sauke wani ajiyar xuciyar ya ajiye wayar. Bayan la'asar ya gama shirinsa don driving xai yi xuwa kanon, komai da yasan ya kamata jiddah ta sani ko ta iya amfani da shi a gidan sai da ya tabbatar ya nuna mata a gidan nan, abinda ya kara bata masa lkci kenan, xaune yake parlor waiting for Maimuna don baya son sai ya tafi ta xo, tana ring din bell ya mike ya bude kofar, gaishesa tayi da fara'a, ya amsa yace "Ya gida" Tace "Alhmdlh yaya, ina Aunty Amarya" Babu yabo bbu fallasa ya amshi ledan hannunta, sannan ya ciro dubu daya ya mika mata yace "Ki yi transport" tace "Tare da driver muke" Yace "Ohk" dubu daya ya kara xarowa aljihunsa ya hada ya mika mata yace "Ki saka kati" Tana murmushi tace "Aa ka bari nagode yaya" Ya hade rai yace "Amsa ki tafi" Amsa tayi yace "Sai anjima" Tayi masa godiya sannan ta juya a hankali, amma duk jikinta yyi sanyi don bai bari ta ga Jiddah ba, ya kulle kofar, kujera ya koma ya xauna yana duba abinda ta kawo, turarrukan wuta ne a kwalbansu kusan kala hudu sai burner, da wasu turarrukan na jiki, tabe baki yyi ya mike ya wuce sama, dakin jiddah ya bude ya ganta xaune duk ta dawo wani iri, tana ganinsa ta sauke kanta kasa, ya ajiye ledan yace "Umma ta bada a kawo maki" ta bi sa da kallo har ya jona burner din a socket, sannan ya bude turaren wutan guda daya ya diba ya xuba yana kallonta, bayan d'an lkci kamshi ya fara tashi, yace "Safe da yamma xaki tabbatar kin ma dakinki da parlor haka" Ta gyada masa kai kawai, waya karama ya ciro aljihunsa yana kallonta ya mika mata, ta mike ta isa inda yake ta risina ta amsa, yana kallonta yace "Number da xaki dinga samuna ne kadai a ciki, sai ki koyi yanda xaki yi amfani da shi ke kadai" cikin sanyin murya tace "Toh" Yace "Sannan ba ace ki xauna ke daya kiyi wani shiru kamar me xaman makoki ba, ga kayan kallo duk na koya maki yanda xaki kunna" Ta sunkuyar da kanta, kofa ya nufa yace "Na tafi" Ta kallesa da sauri tace "Ina xaka je" Yace "Garin da nake aiki" bude kofar yyi ta bi sa da ido, sai da taga ya fita kafin ya kulle kofar cikin sanyin murya tace "Allah ya tsare" Ya amsa da Ameen a takaice, da sauri tace "Yaushe xaka dawo?" Yana kallonta yace "Wannan bai shafeki ba, ko da wani abu da xaki bukata bayan duk wanda na maki??" Daga haka ya kulle kofar hawayen dake makale idonta ya silalo a hankali, ta fi minti goma tsaye yanda ya bar ta, jin an tada mota ta kalli window da sauri sannan ta karasa window din ta d'an bude labule tana lekan waje, tana ganinsa ya fita da motar, a hankali ta fara kuka ta xauna nan kasa, sai kuma ta fashe da kuka kamar ana dada tunxurata, Abuturrab ya sauka motar yana kallon gate din gidan, he just dont have any option then to close the gate from outside, don bai ma son ya gwada mata yanda ake kullewa daga ciki balle ya sa ta kulle ta ciki, yasan probably kafin ya dawo weekend an samar masa mai gadi kamar yanda yayi requesting ayi, ya kulle gidan ya koma ya shiga motarsa yana karasa addu'o'in da yake yi tun daga compound a ransa ya bar layin.....




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Do justice to ur self by subscribing before reading
Thank you
[6/11, 9:05 PM] +234 803 540 6041: Jiddah ta langwabar da kanta tace "Ai ban sani ba, in dai mata na xuwa sai mu dinga tafiya tare" That wasn't were Abuturrab wanted the conversation to end, but because of how cautious he was with time sbda sllhn juma'ah, ya kalleta kawai yace "Kafin in dawo masallaci ki tabbatar kin sake wanka kin shirya cikin atamfa, sannan ki karya..." Sae kuma ya hade rai, Ta sauke idonta kasa tace "Ni na karya da asuba ai" Daga sama har kasa ya kalleta sannan ya juya ya fita ta bi sa da kallo.... Ko da ya dawo juma'ah har ta shirya kamar yanda yace mata, Hijab ya sa ta daura kan atamfar, bayan ta sauko ta tsaya tana kallonsa, sau daya ya kalleta ya dauke kai yace "Fita ki jirani a waje" Ba musu ta nufi kofa ta fita daga parlon, sae a sannan ya tashi ya kashe appliances din gidan ya dau makullin motarsa da hulansa ya fita, the ride was silent har suka iso gidansu, gaba daya he was absentminded, yau da safe ma kiran Aunty ne ya tashe sa, har sannan kuma ya ki daukan kiranta, then is he even suppose to go home now? bai yi parking a kofar gidansu ba in case of necessity, ya juya yana kallon Jiddah yace "Ki jirani" Bai jira tace komai ba ya bude motar ya sauka.... Da murmushi Abuturrab ya amsa gaisuwan mai gadinsu ya shiga cikin gidan, sosai ya ji hankalinsa ya kwanta da kanninsa suka ce Aunty ta fita, Yana kallon Ramlah yace "Ina ta tafi?" Ramlah tace "She left for Abuja this morning" Shiru yyi yana kallonta, can ya nufi parlon Umminsa, ganin bata parlon ya fito, ganin ya nufi kofar fita Ramlah tace "Ummi na bedroom fa" Bai tanka ta ba har ya fita, tare ya dawo cikin gidan da Jiddah, murmushi kawai tayi ma su Ramlah da suka gaisheta, ta bi bayansa xuwa parlon Mahaifiyarsa, kafin yace mata komai ta xauna a kasa, ya karasa cikin bedroom din Ummi da sallama, gaisheta yayi da ladabi, ya shafa kansa yace "Ummi xa ku gaisa da ita a parlor" Ummi tace "Ohkk" Mikewa yayi ya fito parlon, ya xauna kan kujera, ba a dau lkci ba Ummi ta fito, jiddah ta sunkuyar da kanta ta gaisheta, Ummi ta amsa da murmushi fuskarta tace "Ya ku ke?" jiddahh tace "Lafiya lau" Ummi tace "To madallah, sannun ku da xuwa" Ummi dake kallonta kasa kasa ta ga ta canxa mata sosai, haskenta na ainahi ya fito ga wani glowing da take yi, Shi dai Abuturrab danna wayarsa kawai yake, jin Umminsa bata kuma cewa komai ba ya daga kai ya kalleta yace "Ummi wai Aunty ta tafi Abuja?" Ba tare da ta kallesa ba "Ai na xata xaka fi kowa sani tunda kun fi kusa" Ya sunkuyar da kansa yace "Aa bamu yi magana ba" Ummi tace "Ayyo" yace "Yaushe tace xata dawo?" Ummi tace "Baka da lambarta ne?" bai kuma cewa komai ba kuma bai dago ba, Jiddah dai sai kallon Ummi take, Bayan few seconds Abuturrab ya dago yace "An kawo lefen Ramlah ne?" Ummi tace "Bakwa magana da Ahmad din ne?" Yace "Shekaranjiya mun hadu a Abuja da na sauke jirgi a airport din can" Da sauri Jiddah ta kallesa, suka hada ido ya hade girar sama da ta kasa yana kallonta, turo baki tayi, Ummi dai tv kawai take kallo, Ya dauke kai yace "Amma yace min xai shigo kadunan yau, kilan xanje daukosa a tashan jirgi anjima" Ummi tace "Allah ya kawosa lafiya" yace "Ameen" Ummi tace "Idan kaga xaka iya sai ka bar ta nan har bayan bikin, tunda ranan talata xa su fara shagalgulansu" Abuturrab ya d'an yi shiru, can ya daga kai ya kalli Ummi yaga kallonsa take, suna hada ido tace "Ranan bikin sae ka kawota" Da sauri yace "Aa Ummi gobe xan kawota tunda bata xo da kaya ba" Ummi tace "Aa a bari ranan bikin dai" Yace "Uhn xan kawota goben in sha Allah" Ummi tace "Baxa ka siya mata ankon bikin ba?" Ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Nawa ne?" Ummi tace "Kala uku ne, daya na family, sai general one da xa a saka ranan yini, sai kuma na dinner, although naji yan matan sun fidda wani da xa su saka ranan talata" Yace "Nawa ne duka" Ummi ta hada masa kudin gaba daya tace "Gaba daya 40k ne" Yace "A dinke xa a siyo kayan?" Ummi tace "Ehh, da yake kayan dama a kyauta aka samosu daga kasuwa, iyakar kudin dinkin ne dubu arba'in" Abuturrab ya bude ido ya fara dariya yace "Ummi tambaya fa kawai nayi" A takaice tace "Nima amsa na baka" Ya shafa kansa yana murmushi bai ce komai ba" Ummi na kallon Jiddah tace "Su Ramlah na can daki kije ki samesu tunda naga baki son magana" Tayi murmushin karfin hali ta mike ta nufi kofa, Abuturrab ya mike yace "Ai bata san dakin ba, i will back Ummi" Da ido kawai Ummi ta bisa da kallon mamaki har suka fita. Dakinsu Ramlah ya kai ta, Ramlah na xaune da Siyama sai wata kawarta da Aisha step sis dinta, tana ganin Jiddah ta mike tana welcoming dinta da fara'a, bai amsa gaisuwan yan dakin ba banda na kawar Ramlah da bai sani ba, sannan ya juya ya fita ya koma bangaren Umminsa....

Karfe hudu saura yace da Ummi xai je dauko Ahmad a train station, Ummi tace "Toh Allah ya tsare" Yace "Ameen" Daga haka ya fita daga parlon, dakin su Ramlah ya nufa, Jiddah na xaune tana ma Siyama tsifa, su Ramlah suna ta labari a dakin ganinsa duk suka yi shiru, yana kallon Siyama yace "Ke tsifan sai an maki??" Tayi dariya tace "Ita tace ta xata min Yaya" Yana kallon Jiddah yace "Kinci abincin ko baki ci ba?" Ramlah tace "Yanxu muka gama cin abincin fa yaya" Wani kallo ya jefa mata yace "Nayi da ke?" Bata kuma cewa komai ba, yana kallon Jiddah fuska daure yace "Tambayar ki nake" Tace "Mun ci" juyawa yayi ya fita, Sai da Ramlah ta tabbatar ya tafi don har sai da taje ta d'an bude kofar taga babu kowa wajen sannan ta dawo tana kallon jiddah da murmushi tace "Yaya yana ji dake kamar yanda yake ji da profession dinsa..." Jiddah dai bata ce komai ba ta ci gaba da tsifar da take.... Bayan kusan awa daya da tafiyar Abuturrab Aunty ta dawo gidan, alamar dai ita ma train din ta biyo daga Abuja ta dawo, tun da ta kyallara ido taga Jiddah taji kamar taga mugun abu a gidan, ko gaisuwar Jiddah bata amsa ba, bata sake shiga damuwa ba sai ganin wani haske da kyan da Jiddah tayi alamar kwanciyar hankali, ita Abuturrab xai raina ma wayo?? Ta kusa minti ashirin xaune gefen gado a dakinta, ta saka wannan ta kunce wnn, ita Abuturrab ke son kunyatawa gun aminiyarta? Takanas ta shirya yau ta tafi Abuja ba mahaifiyar Aneesah hakuri bayan sun sanar mata abinda Abuturrab din yyi ma Aneesah a airport kamar yanda Aneesan ta gaya ma uwarta... Wani murmushi Aunty tayi tana gyada kai. Jiddah na ta xaune parlorn Ummi ita kadai don su Ramlah da yan matan gidan sun fita xuwa gun tailor, Ummi kuma ta hanata bin su tace mijinta bai sani ba, Jiddah na ta juya furucin Ummi a kanta, wai mijinta, ai ba mijinta bane Aliyu, tunanin hakan kawai sai taji jikinta yayi sanyi sosai, Ummi ce ta fito daga dakintaz ganinta xaune ita kadai tace "Ki shiga kitchen kiga ko aunty na ciki ki tambayeta abinda xa ki kama mata Jiddah" Jiddah ta kalli Ummi a hankali tace "Toh" Mikewa tayi ta fita bangaren Ummi, tayi hanyar kitchen din, jikin kofa ta tsaya tana lekan kitchen din don ita har taji tana tsoron matar nan da ake ce ma Aunty, ganin Auntyn a ciki, cikin sanyin murya tace "Aunty me xan kama maki wai?" Juyawa Aunty dake yankan cabbage tayi tana mata wani irin kallo tace "Me xa ki kama min?" Jiddah ta gyada mata kai gabanta na faduwa, Aunty ta ajiye wukan hannunta ta kunduma mata xagi tace "Ke a wa xaki kama min aiki?? Yanda kika samu wajen xaman yin iskanci gidan Aliyu kin xata nan ma haka ne, toh bari kiji... Wllh ki saka a ranki cewar xamanki ya xo karshe a gidan Aliyu, sai dai ya dinga bin ki can kauyen naku yana iskancin da yake dake, yau xai san ni mahaukaciya ce wllh" Jiddah dai kallonta kawai take a ranta tana kara nanata kalmar da ta jefa mata wai iskanci, tana nufin iskanci suke yi da Aliyun kenan? Muryar Aunty ya sake dawowa da ita, ciki tsawa tace "Baxa ki fita ki bar min kitchen ba mayya...." Cikin sanyin murya Jiddah tace "Ni ba iskanci muke yi ba wllh...." Aunty ta fixgi roban cabbage din gaba daya ta watsa mata ranta bace ta kunduma mata xagi tace "Kina shige da karuwar xaki ce min ba iskanci ku ke ba, dama mace da namiji na xama gida daya tare babu aure? Fita ki ban waje kada in fasa maki ido algunguma" Jiddah da ta rufe idonta da hannunta taji kuka ya taho mata ta juya da sauri ta bar kitchen din jikinta duk cabbage da suka makale, dai dai nan Abuturrab ya shigo parlon, durkusawa tayi nan parlor ta fara kuka kamar an aikota, kallon hanyar kitchen din yayi yaji muryar Aunty tana cewa "Sai yanxu na ke sake yarda cewar da gangan yayi komai da ya faru, har sabida


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login