Showing 69001 words to 72000 words out of 346625 words

Chapter 24 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

labarinsa, bayan gashi kace har ya xo da mahaifinsa, to idan haka ne ba sai sanda na ga damar basa matar xai tafi da ita ba, to wllh ni na canxa ra'ayi kan auren ma, ya dawo ya fadi nawa ya kashe ko gidan da muke ciki ne sai in sayar in biyasa, ba ruwana wllh" Mai Anguwa dake ta kallonta, ya d'an yi murmushi yana kara jinjina hali irin nata, ya fiddo wayarsa bayan kusan minti biyar yace "Alhmdlh, na samo lambar" Yana fadin haka yayi dialing number Abuturrab ya sa handsfree, kallon Hansai yayi bayan an sanar wayar baxai je ba, Hansai ta rushe da wani matsanancin kuka tace "To ko dai lambar karya ya baka, ni sai yanxa nake jin ma ban yarda da mutumin nan ba wllh, wa ya sani ma ko d'an yankan kai ne yace mana matukin jirgi ne shi, jirgi abar wasa ce da xai iya tukata bayan an sanar mana turawa ne kadai suka iya daga jirgi sama su tuka, sannan idan ba d'an yankan kai ba mutumi babu dangin iya balle na baba kayi ta kashe mana kudi haka daga jin an mana mutuwa, daga haduwar mu xuwa fa ranan da ya bada sadakinta wllh mutumin nan ya kashe mana yayi kusan rabin miliyan, to akan me? Aa wllh ya xo in biyasa ya maido min da 'ya ta" Mai Anguwa dai tabe baki kawai yake bai bata amsa ba, Hansai ta fara kokarin mikewa tace "Ai dai wayar baxata dauwama a mace ba, don haka ko gobe ma xan dawo sai ka sake gwada kiran lambar don ni bani da waya, haka kawai yarinya ta bace batt kamar yar kaza" Mai Anguwa yace "Allah ya kai mu goben" daga haka ta bar wajen tare da kawarta, Zulai tace "Anya wannan mai anguwan na da gaskiya kuwa Hansai?" Hansai ta kalleta da sauri tace "Atoh, nima shi na gani, baki ji har ya fara cewa Uban yaron sananne ne a garin nan ba, kawai dai sun danna masa uban kudi shi ma shine yayi mukus, to wllh a maido min da 'ya ta babu wani xancen auren karya" Zulai tace "Kuma fa da gaskiyan ki, ko dai wannan yaron d'an yankan kai ne, idan ba haka ba a wnn xamanin ina xai samo rabin miliyan ya kashe maku" Hansai ta tsaya tana kallon Zulai, can ta marairaice tace "Toh kuwa in har haka ne ya kassara ni, wa gareni da muke sana'a tare banda jiddar, ke baki ga ko me nasa Bibalo kin yi take ba sai ta nemi ta xageni, ai jiddah ita ce rufin asiri na a duniyar nan, gashi duk jarin na fatattakar, kuma sana'ar ba wani ciniki nake yi ba yanxu, uwa dai an juya min baya a anguwan" tana fadin haka ta fara matsar kwalla, Zulai tace "Toh da da kike shirin aurar da ita Jiddar ga Iliya fa?" Hansai ta ci gaba da tafiya tace "Toh ai ko daga gidan mijin sana'ar xan dinga bata tana min nufi na" Zulai ta ta6e baki tace "In ko ba d'an yankan kai bane to tana gunsa Wlh, abinda kowa dai ya shaida matarsa ce" Hansai ta share xufar goshinta tace "Toh uban me xai yi da ita wai Zulai, sai kiyi ta wani cewa matarsa, wllh babban mutum ne ko da kudi aka hadasa da jiddah banjin xai amsa balle bbu ko sisi, don baki gansa bane shi yasa kike wannan xancen banxan, lafiyayyen namiji ne fa wanda da kyar ya amince ya auri yar kaduna sai dai yar Abuja" Zulai tace "Toh wai ke kinga tun bayan da aka daura masa aure da ita ya sake dawo maki kofar gida, ai da wllh bata wajensa da tuni ya dawo an kai xance gidan yan sanda, duk inda ta shiga kuma sai an nemota, ke dai kawai kin cuci kanki, kina ji kina gani sbda shegen son kudi kin ba babban mutum irinsa auren Jiddah ga Bibalo yashe a gida" Hansai ta fashe da kukan takaici tace "Ni anjima da daddare ma wllh xan dawo gun mai anguwa ya sake kiran lambar, don bani da waya ne da na amsa lambar ai, kuma wllh in har da gaske jiddah na wajensa to ni ba da amincewata ya aure min 'ya ba, wllh sai ya sakar min ita, ina jiddah ina babban mutum kamar shi idan ba yana da wata manufa na yanka min ita ya bunkasa arxikinsa a ransa ba" Zulai ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Ohh!!! wa yasan irin daulan da Jiddah ke ciki yanxu" Turata Hansai tayi a mugun fusace tace "Don Allah idan baxa ki dinga fadan alkhairi ba kiyi shiru, jiddah ita har tana da wani daula a duniya, wllh ko tana da shi kinji rantsuwar musulmi ko? To sai na rushe daulan nan, muna nan da ke kuma xa ki ga jiddah sai ta dawo gidan nan, ai ba mijin aurenta bane shi din sai in kasheta yake da niyyar yi ya kara arxikinsa, ba kuma sa'an aurenta bane ko da kuwa ita ma yar me kudi ce, sai dai in ban haifu cikin shafa ba wllh" Daga haka tayi gaba a mugun fusace tana jin xuciyarta na tafarfasa.... Washegari alhamis Jiddah ta tashi taji tana jin yunwa sosai sbda daren jiyan babu abinda ta ci ta kwanta, sai kusan karfe takwas na safe ta shiga kitchen bayan tayi wanka, rasa abinda xata dafa tayi a kitchen din, jingina tayi da bango ta 6ata fuska xata yi kuka tana kallon tulin kayan abincin, tuwo ne kawai a ranta, lkci daya hawayen ya kawo idonta ta juya ta fice daga kitchen din, dakinta ta koma ta fada kan gado tana shessheka a hankali, bayan wani d'an lkci ta daga kai a hankali tana kallon wayar dake gaban madubi yana vibrate, mikewa tayi tana share idonta cikin sanyin jiki ta nufi wayar ta dauka tana kallon screen din, throughout jiya basu yi magana da Abuturrab ba banda yanxu da yake kira, ta daga ta kai kunne, Abuturrab na driving xuwa airport kasancewar karfe sha daya yake da duty, Shiru Jiddah tayi kamar yanda shi ma yayi shirun, bayan few seconds yace "Ni kike jira inyi maki magana?" Ta sauke idonta kasa a hankali tace "Aa" yace "Ohk in gaishe ki?" Tace "Ina kwana" Yace "Me kika ci yanxu?" Ji tayi kamar ta fashe masa da kuka, yace "Ina jin ki" cikin rawar murya tace "Ban ci komai ba" Yace "Me kike jira?" Tace "Ni bana son taliyar" ya d'an yi shiru kafin yace "Me kike so?" A hankali tace "Tuwo nake son ci" Yace "Toh sai ki ci inda kika gansa, ga abinci kusan kala nawa a gida kice duk baki ga abinda kike so a ciki ba, Shinkafa, doya, macaroni, spaghetti, irish, wake, indomie, cous cous.... Wait.. Are you even okay?? Dama tuwo abinci ne?" Ita dai bata ce komai ba, lkci daya hawaye ya kawo idonta, yace "Samun waje kika yi" daga haka ya katse wayar, hawayen dake makale idonta ya silalo, ta ajiye wayar ta koma kan gado ta kwanta tayi lamo tana shessheka. Har kusan karfe sha daya na safe tana kwance, jin yunwa ya dameta sosai ta mike a hankali ta fita dakin, kitchen din ta koma, indomien kawai ta dafa daga karshe sai dai gwara na yanxu a kan wanda tayi shekaranjiya. Da yamma Jiddah ta ji kamar an bude gate ta mike da sauri ta isa window ta bude labulen tana lekan waje, shi ta gani ya shigo gidan ta xaro ido ta sake labulen ta koma can karshen gado ta xauna kamar mara gaskiya, bayan kusan minti goma sha biyar ya bude kofar dakin nata, sunkuyar da kai tayi, yana tsaye bakin kofar yace "Baki iya dafa shinkafa bane ko wani abincin?" Tace "Aa na iya" Yace "Toh me yasa baki dafawa?" Tayi shiru, yace "Ohk, daga yanxu... daga ranan lahadi xuwa asabar xan sanar maki abinda xaki dinga girkawa tunda baki da hankali ke" Ajiye ledan hannunsa yayi ya juya ya fita, ba a dau lkci ba taji alamar ya fita gidan gaba daya, mikewa tayi ta isa gaban ledan da ya ajiye ta leka ciki taga take away ne, fiddowa tayi ta bude taga tuwon shinkafa that looks so palatable, ta bude inda miyan ke ciki taga miyar kubewa danye lafiyayye da ya ji nama da kayan ciki da ganda, kallon miyan da tuwon ta dinga yi, bata san lkcn da tayi murmushi ba ta mike ta wuce bandaki da sauri ta wanke hannu sannan ta dawo ta xauna ta fara cin tuwon, she was eating happily, mulmula hudu ne tuwon, ta rage wanda xata ci da daddare, har bacci barawo ya saceta sbda tsoron dake damunta a rai bata ji alamar ya dawo gidan ba. Washegari Friday ana saukowa masallaci Abuturrab ya shigo gida daga garin kano, babu kowa parlon, yana tafiya a hankali ya nufi bangaren Aunty, da sallama ya shiga parlonta, daga uwar daka ta fito ya xauna saman kujera murya can kasa yace "Ina yini Aunty" tana kallonsa daga sama har kasa tace "Kiran nawa bashi da amfani a gareka sbda kasan abinda ka kullala shi yasa ka daina dauka ko??" Ya shafa kansa cikin sanyin murya yace "Aunty ae na maki text nace xan dawo weekend in sha Allah" ta nemi waje ta xauna fuska daure bbu yabo bbu fallasa tace "Toh gashi ka dawo weekend din yau ai, ya ake ciki kenan?" Ya daga kai ya kalleta a hankali yace "Aunty ni fa ba matata ce ita yanxu ba kuma, kawai gaya maku ne ban yi ba" Da mamaki Aunty tace "Ban gane ba" Ya gyada kai yace "Haka ne, babu aure tsakanina da ita tun ranan da muka tafi can gidan nawa, so nake sai na dawo ne in sanar maku" Aunty ta daga hannu biyu sama tace "To Alhamdulillah ya Allah, tun faruwan lamarin nan sae ynxu naji dama dama" cikin sanyin murya yace "Amma don Allah wannan ya xama sirri tsakaninmu Aunty, Abba won't take it likely with me if he finds out" Aunty ta hade rai tace "Haba dai wa xan gaya ma kamar wata yar yarinya, wllh baka ji sanyin da xuciyata tayi ba yanxu, to ina ka bar ta yanxu? Ka maida ta kauyen nasu ne?" Yace "Tana can gidana Aunty" Aunty ta hade girar sama da ta kasa tace "Wani gidan naka?" Yayi kasa da murya yace "Aunty ina sane da abinda nake wllh, ba lkci daya xan yi komai ba ai sbda kada a xargeni" Aunty tace "Amma xamanta gidan nan naka ai bai yi ba" yace "Na sani Aunty, give me few days to think of another solution" yana fadin haka ya mike yace "I will be coming back" daga haka ya fita, ta sauke wani ajiyar xuciya tana jin kamar an biya mata wani bukatarta na musamman. Part din Ummi ya nufa, ya xauna ya gaisheta da ladabi, ta amsa tana kallonsa tace "Ya ku ke?" Yace "Alhmdlh" Tace "Toh madallah" kallon Tv dake aiki a parlonta kawai yake, can ya kalleta yace "Abba xai dawo yau ne?" Ta girgixa masa kai tace "Sai gobe in sha Allah" Yace "Allah ya kai mu lfya" Ta amsa da "Ameen... Ina Amaryar taka take?" Lkci daya ya d'an 6ata rai, ita dai tunda ta fada haka bata kalli fuskarsa ba, ya dago yace "Ni daga wajen aiki nake yau" Da sauri ta kallesa tace "Wajen aiki kuma, dama ka koma ne?" Yace "Tun lahadi" Tace "Toh ita sai ka bar ta a ina, ko tare da ita ka koma" Yace "Aa, gida take" Ummi tace "Ita kadai?" Ya gyada kai, Ummi tace "Toh kada ka sake barin ta gida ita kadai, idan baxa ka tafi da ita ba ka kawo ta nan" Yace "Toh" Shiru ne ya biyo baya, bayan few minutes ya mike yace "Sai na shigo da yamma Ummi, xan je gaida Umma" Ummi tace "Toh Allah ya kai mu, a gaishe su" Yace "In sha Allah" Daga haka ya nufi kofa, ta bi sa da kallo har ya fita, motarsa ya shiga ya bar gidan xuwa gidansu Ahmad. Sama sama ya amsa gaisuwar Maman Abdallah dake tsakar gida yayi shigewarsa cikin gidan, Maimuna dake parlor tace "Sannu da xuwa yaya" Yace "Yauwa, Umma fa?" Tace "Umma ta fita wllh" Ya d'an yi jim kafin yace "Okay idan ta dawo kice na shigo" Tace "Toh amma yaya Ahmad na ciki ai" Kallon hanyar dakin Ahmad yyi can ya karasa ya shiga dakin, Ahmad na operating laptop ya daga kai ganin Abuturrab yace "Yanxu nake shirin kiranka ashe kana hanya" Abuturrab ya xauna yace "Ban jima da shigowa garin ba" Mikewa Ahmad yyi ya kashe laptop din yace "Dama gidanka nake son xuwa akwai maganan da xa mu yi a can" Wani kallo Abuturrab yyi masa yace "Kaje kayi me a gidana?" Ahmad yace "Kai me ka xo yi nan? ka sameni parlor plss ina jiranka, kasan fa na san hanyar gidan ba wai ban san hanyar ba" Daga haka ya dau makullin motarsa ya fita, Abuturrab ya d'an yi jim, har ransa bai son Ahmad yaje gidan nasa, can dai ya mike ya bi bayansa. Duk fararen shadda ne jikinsu su biyun, babu yanda Abuturrab ya iya da Ahmad dole haka suka bar gidan tare a motarsa, Driving kawai Abuturrab ke yi ba tare da yana ba ma Ahmad amsa ba, Ahmad yayi wani dariya yace "Kai dai yarinya ba matarka ba balle kace kana kishin wani ya ganta, ni ina ga i just have to sacrifice and marry her together with Ramlah since ba Haram bane kuma i have the money to do so, and i will mould her to exactly how i wish and want her to be, har yanxu her brain is fresh, kaga daukan abubuwa baxai yi mata wahala ba, idan kuma su Umma basu amince min ba which i am not praying for that, i have a frnd da muka yi karatu tare da shi a Uk, har yanxu ma yana can, and ya dameni yana son in hada sa da yarinyar da na sani mai hankali ko cikin siblings or cousins dina ya aura, to yanxu ina ga i will hook him up with Jiddah, yanda na lura yanda Yusuf baya son hayaniya ita ma haka, and they will make a perfect couple, balle ma nasan su Abba baxa su hanani aurenta ba ni...." Parking Abuturrab yayi yana kallon Ahmad fuska daure yace "Ni yanxu fa ba gida xan je ba Ahmad, xan fara xuwa can gida in gaida su Aunty da Ummi, sannan xan amshi sako from a frnd coming from Abuja at bypass, don haka ya xa mu yi da kai???" Ahmad ya gyara xama yace "Ohk then, tunda ban fito da mota ba bari in samu adaidaita kawai ya karasar da ni gidan naka, and i will wait for u there...." Abuturrab ya katse sa yace "Wani gidan??" Ahmad yace "Gidanka mana, idan ya so idan ka gama uxururrukan ka sai ka dawo ka sameni, i will go gist with jiddah kafin ka dawo...." Wani irin kallo Abuturrab ke yi masa xuciyarsa na tafarfasa, Ahmad ya fara kokarin bude motar yace "Sai ka karaso, but don't take too long" Bluntly Abuturrab yace "Toh wai dole ne sai kaje gidan nan nawa, meye hadinka da ita yarinyar??" Ahmad yace "Hadina da ita shine ta dalilina ka fara saninta don da ba don ni ba baxa ka santa ba, sannan a lkcn da muke xuwa siyan awara a wajenta ni kadai nake ganinta kai kuwa murhu kake gani, amma dai duk ba wannan ba ma, wai ba inace yarinyar nan ba matarka bace ba yanxu kuma balle kace ko kishin xanje in ga matarka kake, pls what's the color of ur problem Captain?" Abuturrab yace "Don ba matata bace sai nace maka gidana ya koma cinema na xuwa ganinta? I have all right to protect her by all possible means, sannan da kake min gorin ba matata bace mintina nawa ne na mayar da auren idan na so yin hakan? Infact idan ma na mayar din sani xaka yi ko ance maka sanar maka xanyi?" Ahmad ya kallesa da sauri yace "Don Allah in kai ka cika namiji ka mayar da auren yanxu ma" Abuturrab ya ja tsaki yace "Toh sai ka saka ni in mayar ai" Ahmad yace "Ahaf ai nasan baxa ka yin bane, plss bude min mota my frnd, idan ka gama yawo a garin ka dawo gidan ka sameni tare da jiddah" Tsaki Abuturrab yyi ya ja motar suka ci gaba da tafiya, Ahmad yayi wani dariya yana gyara xama yace "Ka fasa karban sakon kenan" Abuturrab bai tanka sa ba har suka isa gida, ya sauka motar ya bude gate sannan ya dawo ya shigar da motar, Ahmad na kallonsa yace "It's very risky leaving this little girl all by her self in this house captain, why don't you want to leave her with umma or Ummi, kasan fa baxa su ki riketa ba" Abuturrab yace "A nan din nake son ta xauna ba sai taje wani waje ba" Yana fadin haka ya sauka motar ya tafi ya kulle gate din Ahmad ya sauka motar ya nufi entrance din shiga gidan, Abuturrab ya bi bayansa da sauri, amma tunawa da yyi kofar ma a rufe yake dole sai ya bude yasa yayi slowing pace dinsa, tsaye Ahmad yyi yana jiransa a balcony jin kofar a rufe, Abuturrab ya isa wajen ya sa makulli ya bude kofar parlon ya shiga sannan Ahmad ya bi bayansa....




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you

_Albishirin ku jama’a ko kusan akwai wani company da ya shahara wajen siyar da kayan alatu da abubuwan more rayuwa??_

_Wato Unique & Luxury Stores yana da bangararori daban-daban kamar haka_
*@unique_home_store_ng wanda ya shahara wajen siyar da kayan ado da qawata gida, kayan kitchen, furniture, carpet na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login