Showing 15001 words to 18000 words out of 346625 words
Chapter 6 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
a rush Aneesah, ba dai ni nace xan aure ki ba, meye kike damun kanki haka? Do i look like a liar or do my words sounds deceptive?" Ta kai hannunta kan nasa cikin sanyin murya tace "I just can't imagine loosing u My Captain, i just can't...." Yace "Keep ur mind at rest Neesah, i am all urs and urs alone" Yana fadin haka ya sakar mata murmushinsa dake kara narkar da xuciyarta, dai dai nan kuma ya kai layinsu Jiddah, yau bata awara a bakin titin don babu alamar ma ta fito, sai dai mutane ne cike fal a d'an layin nasu, a hankali yake driving din yana kallon cikin layin, Aneesah dake kallon direction din ita ma tace "What's happening there, ko anyi rasuwa ne?" kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Ko in sauke journalist taje ta gano mana???" Dariya tayi tace "Oops a wnn local area din xanyi journalism dina Captain? Haba this is so disgusting..." Tana magana tana yamutse fuska, shi dai bai ce komai ba yana ci gaba da driving dinsa, can gidan Kanwar babanta ya ajiyeta a unguwar sarki, bayan ya yi mata few shopping na kayan ciye ciye, ta sauka motar bayan yyi parking tana kallonsa, shi ma ya sauko ya fiddo mata da trolley dinta ya kai bakin gate din ya ajiye, ta dau ledan shopping din da yyi mata tana kallonsa bayan ya dawo cikin sanyin muryarta tace "Thank you My Captain, plss ka daure ka xo anjima da daddare mu yi hira..." Ya kashe mata ido yace "Ohk babe...." Daga haka ya shiga motarsa yyi reverse ta bi sa da kallo har ya fita layin tana sake jin wutan sonsa na ruruwa a xuciyarta. Abuturrab na komawa gida yyi parking nan kofar gidansu ya shiga ciki yyi alwala snn ya fito ya shiga masallaci don ana ta kiran magrib, bayan an idar ya fito masallacin ya shiga motarsa ya xauna yana danna wayarsa, ajiye wayan yyi yana kallon flowers dake xagaye kofar gidan nasu trying to imagine the meaning of the crowd they saw earlier a layin yarinyar nan me awara, did someone die again, tunanin hakan ya sa ya tada motarsa ya bar layin, yana isa yyi parking bakin titi ya dau nose mask dinsa a motar ya saka snn ya bude motar ya sauka, ashe da daddare sana'a ake yi sosai bakin titin layin, just like sauran layukan anguwan gaba daya, daga me soya wancan sai me soya wannan, masu siyar da gyada, rake, abubuwan ci na gargajiya dai yawa... A hankali yake tafiya cikin layin yana yatsine fuska, he is even afraid kada allergy ya je ya kamasa cos he is so sensitive to anything Filth,... har dai ya kai dai dai kofar gidan da yaron nan ya ta6a kai sa a matsayin gidansu yarinyar, tsaye yyi yana bin duk wajen da kallo, ginin block ne sai dai ko plaster babu, sannan gidan karami ne sosai, duk gidajen layin haka suke, banda gida daya da ya d'an darasu girma shi ma da kadan wato gidan Iyah, wata yarinya ce ke tafe ko takalmi bbu a kafarta, ya bi ta da kallo yace "Baby...." Juyowa tayi tana kallonsa yace "Xo in aike ki cikin gidan nan" Yarinyar da baxata wuce shekara shidda ba ta dawo tace "Gidansu Bibalo?" Yace "Ehh, shiga kice ana kiran me awara a ciki" Da gudu yarinyar ta shiga, babu kowa tsakar gidan don Hansai ko minti biyar ba ayi da fitarta ba, ta shiga makota, Bibalo kuma tun la'asar rabonta da gidan, yarinyar ta kutsa kai cikin dakin su Bibalo tana kallon Jiddah dake kwance ta takure waje daya kan yakunannen katifarsu da Bibalo, tace "Wai ana sallama a waje" Da sauri Jiddah ta mike xaune da idanuwanta da suka yi jajir, duk da tasan Hansai ta fita gidan don sai da ta bar mata sallahun bakar magana ma kafin ta fita amma hakan bai hana xuciyarta dinga bugawa ba jin abinda yarinyar tace, A tunaninta saurayinta ne Usman ya xo, kilan ya ji abinda ke faruwa ne, da kyar dai ta lallaba ta mike ta cire Hijab din jikinta ta dau wankakke dake a linke ta saka, sanyi take ji sosai don xaxxabi ne jikinta, ta fito dakin ta sa takalminta tana tafiya kamar iska xai kadeta ta fito kofar gidan, babu haske sosai wajen hakan yasa ta dinga kallon mutumin dake tsaye da fararen kaya ya juya baya, gani tayi ba Usman bane don wnn yafi Usman tsayi, ta bi layin da kallo tana kara tsoron kada Hansai ta dawo ta tarda ita a waje bayan an yi mata iyaka da wajen daga daxu da yamma, da kyar tace "Wa kake nema?" Sai a snn ya juyo ya sauke mask din fuskarsa yana kallonta, ta xaro ido tsoronta ya tsananta, haka xaxxabinta ma taji yana neman fin na da, don sanyi sosai ya dinga shigarta, kallonta ya shiga yi daga sama har kasa, rasa abin cewa tayi daga karshe ta jingina da bangon gidan, still looking at her yace "Baki da lafiya ne?" Ta gyada masa kai, lkci daya hawaye ya kawo idonta, bin layin ya sake yi da kallo, can yace "Baki sha magani ba?" Hawayen dake makale idonta ya silalo kasa ta girgixa masa kai tace "Babu maganin" yace "Ke da waye a cikin gidan?" Tace "Ni kadai ce, Baabarmu ta fita yanxu" Shiru yyi kamar me naxari sai kuma ya kalli inda motarsa yake yace "Akwai asibiti a nan anguwar?" Ta gyada masa kai tana nuna masa tace "A layin can gaba" Yace "Mu je" Da mamaki take kallonsa tace "Ina?" Ya wani hade rai yace "Mu tafi can din nace" ta marairaice cikin rawar murya tace "Baabarmu tace idan na sake fitowa ko nan bakin kofa sai ta kasheni wllh" Shiru yyi na few seconds kafin yace "Saboda me?" Tana share hawayen da ya ki tsaya mata tace "An sa min rana" Daga sama har kasa ya sake kallonta snn yace "Da wa?" Ta fashe da kuka tace "Da iliya" tana fadin haka kamar an tunxurata ta dinga rera kuka, yace "Ohk, amma bai san baki da lafiya bane bai kawo maki magani ba" Bata basa amsa ba sai kukan da take yi sosai, yace "Mu je" ganin ta ki motsawa ya daure fuska sosai yace "Ke kinsan daga inda nake?" Ta shiga goge idonta bata ce komai ba, yace "Mu tafi nace" A hankali ta fara goge idonta, ganin ya fara tafiya ta bi bayansa gabanta na faduwa tana waige waige har suka kusa bakin titi ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta don duk maxaunin bakin titin nan babu wanda bai santa ba, ya bude mata back seat, xuciyarta ya dinga bugawa da karfi ta tsaya tana kallonsa, ya sauke nose mask dinsa yace "Kina 6ata min lkci" A hankali tace "Baabarmu xata....." Wani kallo yyi mata yace "Nace ki shiga malama" shiga motar tayi a tsorace, ya rufe sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar, sai da ya hau saman titi yace "Ina asibitin yake?" Layi uku dake gaba da nasu ta nuna masa ya shiga layin suna isa yaga irin asibitin yyi parking yana kare ma wajen kallo, kafin yace "Nan din ne asibitin?" Kai kawai ta gyada masa, ya ja tsaki ya tada motarsa yayi reverse ya bar wajen, ta dinga kallonsa gabanta na faduwa, wani asibiti a cikin gari ya kai ta, yana parking haraban asibitin ba tare da ya juya gareta ba yace "Sauka" kalle kallen motar ta dinga yi alamar bata ma san ta ina xata bude ba, ya sauka ya xagayo ya bude motar, sauka tayi ya rufe motarsa, ganin yanda ta tsaya ya dake yace "Mu je" he sounds so pissed off, Ba musu ta bi bayansa har cikin asibitin, nan take ya yankar mata kati, ba a dau lkci ba nurse din ta sanar masa xa su iya shiga gun likita, yana daga xaune ya nuna mata office din likitan yace ta shiga ta gaya masa duk abinda ke damunta, Jiddah ta mike gabanta na faduwa tana kallonsa a hankali tace "Ai tsoro nake ji" ya hade rai a d'an tsawace yace "Tsoron likitan sbda xai cinye ki?" Sunkuyar da kanta tayi, yace "Juya ki shiga" a hankali ta juya ta nufi office din likitan da ya nuna mata, kamar me tsoron kofar ta murda ta shiga, sai a sannan ya mike ya bi bayanta xuwa cikin office din, tana xaune ta takure waje daya likitan na cewa ta kwantar da hankalinta ta nutsu, ganin ya shigo sai taji hankalinta ya kwanta, ya ja kujera ya xauna suka gaisa da likitan, likitan na kallonta yace "Me ke damun ki?" Cikin sanyin murya tace "Kai na ke min ciwo, ina jin xaxxabi, kuma ina ganin jiri...." Mikewa yayi ya dawo kusa da ita yana duba idonta da wani d'an abu kamar fitila a hannunsa, Abuturrab dai na xaune yana dubansu har likitan ya gama gwaje gwajensa snn ya koma ya xauna yana kallon Abuturrab yace "Xa ayi mata test, though symptoms din na malaria ne, but it's good ayi test din sannan kuma .... Is she ur sister?" Abuturrab ya d'an kalleta sannan a hankali yace "Yea" Likitan yace "Me ke damunta haka, yar yarinya da ita na ga Bp dinta ya hau" sake kallonta Abuturrab yyi, likitan na kallonta yace "Kina da damuwa ne 'yan mata, idan ma baxa ki gaya ma d'an uwanki ba ni ki gaya min" Sunkuyar da kanta tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta, Abuturrab yace "Dont worry Dr i will talk to her about that, ynxu dai idan ba damuwa kawai a hada mata drugs if there is need for injection ayi mata ba sai an yi mata test din ba cos i guess it will take up to 40mins kafin result din ya fito mu kuma a kan hanya muke" Likitan yace "Toh shkkn babu damuwa" daga haka ya fara rubuce rubuce yana gamawa ya mika ma Abuturrab ya amsa snn ya mike yyi masa godiya, ganin har sannan bata mike ba yace "Mu je" Mikewa tayi yana gaba tana biye da shi har suka fita office din, wajen bada allura Abuturrab ya ga abinda bai ta6a gani ba, don kememe taki yarda ta dinga rusa masu kuka a asibitin tana rokansu, hakan yasa ya koma office din likitan yasa ya rubuta magunguna kawai gaba daya ya biya bill din sannan suka fita asibitin, har sannan shesshekan kuka take, ya bude front seat ya hade rai yana kallonta a hankali ta shiga ya kulle sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver, sai da suka fita asibitin yace "Kin ci abinci?" Girgixa masa kai tayi tace "Baabarmu ta ba almajiri nawa" Ya dinga nanata sunan da ta kira a ransa, wai Baabarta, girgixa kai yyi cikin ransa still yace ba dai baabarki ba, gidan wani cin abinci ya tsaya ya siya mata abinci sai malt guda biyu da bottle water, yana shigowa motar ya ajiye mata, kallon ledan ta dinga yi, can ta bude ta ciro malts din ta ajiye gefe tace "Ban iya sha ba" Yace "Sai me?" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Tambayarki nake" a hankali tace "Ban iya shan lemo ba ni" Bai kuma ce mata komai ba, sai da suka shigo titin hayi yace "Taron me naga aka yi a layinku daxu da yamma?" Shiru tayi sai kuma ta kallesa a hankali tace "Baabarmu ce take dukana" Da mamaki yace "Saboda me?" Ta share hawayen da ya kawo idonta tace "Dama Iyah ce tace xata sa ni a motar tirela in gudu legas don kar a min aure da Iliya, shine sai na gaya ma wata kawata da muke xuwa makarantar dare tare da ita da, don gobe Iyah tace xata kai ni tasha, sai kawata taje ta gaya ma baabarta shine baabarta ta xo ta gaya ma Baabarmu, shine Baabarmu ta dinga dukana wai xata kasheni, duk aka taru a layin...." Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Shi dai sauraronta kawai yake yi, bayan few seconds yace "Wacece Ita warce tace xata sa ki mota ki tafi lagos?" Cikin rawar murya tace "Wata tsohuwa ce a layinmu ana ce mata Iyah...." Ya kalleta yace "Har yanxu xa ki tafi lagos din kenan don kar a maki auren?" Ta girgixa masa kai hawaye na sauka idonta tace "Aa baxan je ba amma xan kashe kai na" Bai ta6a expecting jin hakan daga bakinta ba, yyi parking yana kallonta da mamaki yace "Xa ki kashe kanki?" Ta gyada masa kai, yace "Da me xaki kashe kan naki?" Cikin rawar murya tace "Piya piya xan siya in sha" Bai san lkcn da ya bude baki ba yana kallonta ganin she is so damn serious, da wani expression yake kallonta ganin she is truly depressed and frustrated, tana goge hawayen dake xuba idonta tace "Dama ae Abbana ma ya tafi ya bar ni, ba sai in bi sa ba" ya kwantar da murya yace "Amma kina xuwa islamiyya kuwa?" Ta girgixa masa kai a hankali tace "Na daina tun da dadewa, tun sanda muka fara sana'a" Yace "Toh saboda xa a maki aure kike son kashe kanki?" Ta gyada masa kai, sai kuma ta hade kanta da gwiwa ta fashe da matsanancin kuka tace "Shaye shaye fa iliya ke yi, kuma har kwaya yana sha shine Babarmu take son in auresa...." Kallonta kawai yake, can yace "To wa kika ta6a ganin ya kashe kansa sbda xa ayi masa aure da wanda baya so?" Tana shessheka tace "Akwai wata ma ai ta kashe kanta a nan hayi" yace "Shine ke ma xaki kashe kanki?" Ta gyada masa kai, yace "Toh duk sanda kika shirya ki min magana ni da kaina xan kawo maki piya piyan, kin ji ni?" Ta dago tana kallonsa tace "Toh ai ni na shirya" yace "Yaushe?" Da kyar tace "Yau da daddare nake son in sha" yace "Aa kinga ni sai yau na sani, ki bari ko xuwa jibi xan kawo maki" tana shessheka sae kuma ta sakar masa kuka tace "Yayi min nisa" Yace "Ya sunanki?" Tana kallonsa da hawaye idanuwanta tace "Jiddah" Ya d'an yi shiru, bayan few seconds yace "Jiddah.... shekaranki nawa??" Cikin sanyin murya tace "Babaarmu tace sha bakwai" yace "Toh ki jira sai na kawo maki da kaina, kar ki kuskura ki siya da kanki, kin ji me nace maki?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ki yi min alkawari xa ki jirani" Tace "Nayi" yace "Kina komawa gida ynxu ki ci abinci ki sha maganin ki ai nurse din ta nuna maki ynda xa ki sha" Ta gyada masa kai, tada motar yyi ya ci gaba da driving dinsa gaba daya yana kara naxarin xancenta.
07087865788✍🏻💖💖 *Jiddatul Khair*💖💖
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
6.....
Suna kusa layinsu cikin sanyin murya tace "Toh me xan ce ma Baabarmu idan ta dawo, wllh har dukana xata yi" Bai ce komai ba yyi parking d'an nesa da layin snn ya d'an kalleta yace "Amma ba Baabar da ta haife ki ba ko..." Ta girgixa masa kai a hankali tace "Abbana yace ita ta rasu tun ina yar karama" ganin hawaye idonta ya dauke kai bayan few seconds yace "Allah ya gafarta mata" Ta sunkuyar da kanta ta amsa da Ameen, yace "Sai kice mata saurayin da xaki aura ne ya xo kika fito" Ta marairaice tace "Ai yana legas bai dawo ba" Yace "Kwanaki da na baki kudi ki bata don kar ki sake fitowa bakin titi, kin sake fitowa?" Ta girgixa kai tace "Aa bamu sake yin awaran ba sai shekaranjiya ta fara" bai ce komai ba ya tada motarsa ganin ya fara tafiya ta kallesa da sauri tace "Ina kuma xaka kai ni?" Bai bata amsa ba ganin wani shago da ake cire kudi ta Pos ya tsaya sannan ya sauka motar, without taking much time ya dawo ya shiga motar.... Dai dai layin nasu ya sake parking ya ciro kudi a aljihu yace "Gashi ki kai mata yanxu ma" Kallon kudin ta dinga yi, sannan ta kallesa tace "Ince wa?" Yace "Kice wani ya bata" Amsan kudin tayi gabanta na faduwa, yace "Me nace kiyi idan kin koma gida yanxu?" tace "Kace in bata wai in ji wani" Yace "Kafin wannan" Ta d'an yi shiru sannan tace "Kace in ci abinci in sha magani" Ya d'an daure fuska yace "To sauka" yana fadin haka ya bude mata motar ba tare da ya yarda ya ta6a ta ba, ta sauka, yace "Kulle min mota" Ba musu tayi yanda yace sannan yayi wucewarsa without looking at her, sai a sannan bugun xuciyarta ya tsananta, ta fara tafiya a hankali xuwa cikin layinsu, ta fi minti biyu bakin xaurensu ta kasa shiga, daga karshe ta kutsa kai ciki, tuni hawaye ya fara sauka idonta tana jiran jin saukan duka, sai dai me... Har sannan Hansai bata dawo ba balle Bibalo, gidan babu kowa, dakinsu ta shiga duk da akwai wutan nepa amma kamar ko da yaushe wutan is very low, xaunawa tayi ta ajiye ledan hannunta sannan ta boye kudin cikin ghana must go dinta, a hankali ta bude take away din abincin ta ga shinkafa da katon kaza, ta xaro ido, ita yaushe rabon da ta ci shinkafa balle wata kaza, shinkafa sai suyi kusan sati uku ma basu ci ba daga tuwon masara sai taliya 'yar Hausa ko garin rogo, Kaza kuma dama ranan sllh ne kadai Hansai ke bata kai da kafafuwan ko kuma wuya, yau kuma ga kaza kato a gabanta har da shinkafa, kasa cin abincin tayi tana ta kallonsa, tunawa da tayi Hansai na iya dawowa yanxu ko Bibalo yasa ta xaro ido, a hankali ta fara cin abincin, sbda a tsorace take ta kasa nutsuwa ta ci abincin, ta dai ci wanda xata iya ci, jin almajiri na bara ta mike da sauri ta fita da abincin da ta kunshe a ledansa ta mika ma almajirin ta dawo ciki, ta fi minti daya tana kallon magungunan, kafin ta fito da su tana