Showing 3001 words to 6000 words out of 346625 words
Chapter 2 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
baka san wayayyun sun fi tsafta ba, ni fa I don't care.... As far as xata yi tsafta 100%, wllh ko haduwa da mace kazama ban son yi a rayuwata, sae inji gaba daya hankali na ya tashi, u know how sensitive I am...." Dariya Ahmad yyi yace "Ita Aneesar tana da irin tsaftar da kake so kenan" Abuturrab yace "Kai ma kasan da ba don haka ba da tuni ae na rabu da ita, kawai sae kaga mace ta ci kwalliya iya kwalliya ta fito amma just check inside, ni in dai mace na da tsafta ko kyanta bai fi 80% ba i will manage her..." Girgixa kai Ahmad yyi yana kallon titin gabansa, Abuturrab yace "Ba ga wajen danwaken can mun wuce ba" Ahmad bai san lkcn da yyi dariya ba yace "Aa D'an gyero ne ba danwake ba" Abuturrab dai bai ce masa komai ba da ya lura u turn yake son yi, dai dai gun awaran Ahmad yyi parking, wata yarinya ce da baxata wuce shekara sha daya ba xaune a wajen tana juya awaran cikin kasko, Ahmad na kallonta yace "Ina me awaran?" Yarinyar tace "Ta je dauko canji a gida shine tace in tsare mata, ae sunanta Aunty Jiddah, a gidansu Bibalo take..." Ahmad ya koma jikin motarsa yace "Gidan ba nisa?" Yarinya ta nuna masa wani rubabben layi dake gefensu tace "Can karshen layi ne, gidansu daya da Bibalo" Shi dai Abuturrab na xaune kujera me xaman banxa yana kallonsu, Yarinyar tace "Lah ga ta can xuwa" Duk suka kalli direction din da ta nuna, Tafe take fuskarta daure hannunta rike da yar karamin bokiti dake a rufe, wanda ke dauke da dafaffen awara, sanye take da hijab ruwan kasa da iyakarsa gwiwa duk man awaran da take tuya yayi staining Hijab din, Abuturrab ya d'an yi tsaki ya hade girar sama da ta kasa yana kallon titin gabansa, tana isowa yarinyar ta tashi tace "Aunty Jiddah gashi xa a siya a awara, da motarsu ma suka xo" Ahmad ya wara ido yace "Aunty Jiddah a bamu kalan na jiya" Ta daga kai ta kallesa tace "Na nawa?" Yyi murmushi yace "Yanda kika sa jiya" Bata ce komai ba ta durkusa ta sa masa awaran sannan ta mika masa ledan, dubu daya ya ciro ya mika mata, tana kallon kudin tace "Yanxu na kai kudi gida na amso canji, ka d'an yi hakuri sai in koma in dauko..." Ya juya ya kalli Abuturrab yace "Ko a siya maka kai ma Captain?" Kallon Abuturrab din tayi ita ma suka hada ido, yyi saurin dauke idonsa yaki cewa komai, Ahmad ya kalleta yace "Toh kinsan abinda xai faru me awara? ki ajiye canjin...." Da sauri tace "Aa ka jira in tafi in dawo ynxu" yace "To tsaya ki saurareni mana, ajiyewa xa ki yi gobe idan Allah ya kai mu na xo sai a bani awara na canjin" tace "Toh" murmushi yyi ya nufi mota rike da ledan awaran, sae da ya shiga motar ta ga ledan yajinsa bata sa masa ba ta mike da sauri tace "Kayi mantuwa" motar ta nufa tana mika ma Abuturrab ledan yajin, da mamaki yake kallonta kamar dai mugun abu take mika masa, yace "Kai!! kinga na siya abu a wajen ki ne?" wani kallon cikin ido tayi masa snn ta xaga ta mika ma Ahmad ta koma gun xamanta tana juya awaran kan wuta, Ahmad ya tada motar suka bar wajen yana hararan Abuturrab da ko a jikinsa. Jiddah na xaune a d'an dakalin kofar gidansu bayan isha, dawowarta kenan daga bakin titi ta gama tuyan dankali da take yi, ta ta takure waje daya cikin hijab din jikinta, wani matashi ne da baxae wuce shekara ashirin da tara ba xaune d'an nesa da ita, yace "Kin yi shiru Jiddah" Ta d'an kallesa tace "Nace babu wata matsala" yace "Kin tabbatar?" Ta gyada masa kai, yace "To ki ci gaba da hakuri kin ji.... In sha Allah idan....." Kamar daga sama suka ji muryar Hansai, ta rike kugu tana kallonsa da kyau tace "Ta ci gaba da hakurin gyatuminka?" Ya kalleta ya duka har kasa yace "Ina yini Baaba" Ta wani sha kunu tace "Da ban yini ba xaka gan ni algungumi?? Ta ci gaba da hakuri a saboda ana cutarta ko? Sannan ban rabaka da kofar gidan nan ba? Dama tun da naga yara sun shigo da kayan tallanta ita bata shigo ba nasan da walakin goro a miya, shine nace bari dai in leko in ga ikon Allah" shi dai bai ce komai ba ya sunkuyar da kansa, tuni Jiddah ta mike ta makale da bango gabanta na faduwa, Hansai ta cire takalmin kafarta ta jefa mata a mugun fusace tace "Wuce ciki munafuka kawai, dama ban rabaki da wnn yaron mara tarbiya ba, ni xa ki ja ma abun kunya a unguwar nan?" Da sauri Jiddah ta shige ciki Hansai ta kai mata dundu da karfi, sannan ta maida dubanta kansa tana huci tace "Wllh na sake ganin ka tare da yarinyata gidan gayun garin nan yyi mana kadan da ni da kai, idan kuma karya ne mu xuba da kai" Tana kai wa nan ta shige ciki ya mike a hankali ya bi ta da ido....
💖 Jiddatul~khair 💖✍🏻*Ina me mika sakon ta'axiya xuwa ga Chamo bisa rashin mahaifinta da tayi, Allah ubangiji ya ji k'an sa ya gafarta masa, ya sa aljanna makoma, ya bada hakurin rashi, mu kuma Allah ubangiji ya kyautata namu Ameeeen*👏🏻
💖💖 *Jiddatul~khair*💖💖
_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻
2.....
Abuturrab na kwance saman gadon dakinsa yana rike da wayarsa, kunnensa sakale da earpiece, video call yake da wani matashin da baxai wuce sa ba, matashin na xaune cikin wani ubansun parlor yana cin apple, Abuturrab ya girgixa kai yana kallonsa yace "Look... I don't want to say anything about that.... idan Mummy na kusa ka bata mu gaisa" Matashin na taunar apple yace "It's already late, tayi bacci..." Abuturrab yace "It's late tunda baka son fita, so when are u coming to kd?" El-Basheer yace "Xa mu shigo kano tare da Mai martaba next week in sha Allah, probably ni xan karaso, amma sai kana nan" Abuturrab yace "In dai Friday ne ina nan in sha Allah" El-Basheer ya daga kafada yace "Ohk then" Abuturrab yace "Let me pick a call, sai da safe" El-Basheer ya gyara xamansa yana murmushi yace "The lady u don't want to talk about?" Katse call din Abuturrab yyi ya dau daya wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne hade da cewa "How u babe?"
Abuturrab ne xaune parlonsa a gidansa dake Abuja shigowarsa gidan kenan ko awa daya bai yi ba, kasancewar weather babu kyau yasa suka yi landing flight da suka yi piloting daga Lagos a Abuja a maimakon kano.... Grapes ne gabansa yana ci a hankali yana kallon wani action movie da ake yi a tv, bude kofar parlon aka yi, lkci daya ya daga kai, he was expecting no one other than Ahmad da ya sanar ma yana Abuja... Tsayinta matsakaici ne.... ita ba siririya ba ita ba mai jiki ba, ta karasa shigowa parlon ta kulle kofan tana kallonsa ta cire Nikab din fuskarta, fara ce sosai, kallonta shi ma yake, she looks so orderly from head to toe, tuni kamshinta ya baxa parlon, shi dai kallonta kawai yake ta nufesa da damuwa ta xauna gefensa tace "Why ain't you picking my call Captain?" Ya gyara xamansa yace "It wasn't long da muka sauka ai, na sa wayar a caji a can daki, how are you doing?" A hankali tace "I'm fine, ya gajiya?" Yace "Alhmdllh, where are u coming from?" Ta buda manyan idanuwanta tace "Home... kace min xaka sauka Abuja shi sa na samu na fito" ya shafa beard dinsa yace "Ahmad na hanya, bana son ya xo ya sameki nan, u know how he thinks" Ta langwabar da kai tace "Ohk, amma nace maka ina son muyi magana, ina ta bin ka yau kusan sati biyu kenan sai kace min you will be piloting today, u will be piloting tomorrow...." Da damuwa ta kare maganar, Ya kalli agogo yace "To ina jin ki yanxu, I'm sorry i forgot about that" Shiru tayi, ya kafeta da idanuwansa, sai kuma yyi murmushi ya kamo hannunta yace "Ina jin ki Aneesah" Tayi kasa da murya tace "Aliyu a gidanmu an takurani in fito da miji, kwanaki kuma na gaya maka baka ce komai ba, idan har da gaske kake kana sona what is hindering you pls?" Ya dauke idonsa daga kallonta, bayan few seconds yace "To a jira ki gama karatun mana ko? Ina ce saura kadan" Ta girgixa kai tace "Aa last week Abbana ya kara min magana, and he is very serious about it this time, don't u love me ne Aliyu?" Abuturrab ya xaro ido yace "Not at all Aneesah, kema kinsan ina sonki.... kar ki damu xa mu yi magana, yanxu ki tashi ki tafi kafin Ahmad ya xo..." Ta gyada masa kai sannan ta mike, mikewa yyi shi ma ya wuce daki ya dauko kudi ya mika mata kafin yace komai tace "Aa ni da motana na fito don't worry" Bai ce komai ba ya rakata har balcony snn ya amshi jakarta ya sa mata kudin yace "I know da mota kika xo, Chocolate din da ban kai maki ba last week sai ki siya, ba kudi ne me wani yawa ba" Murmushinta me kyau tayi, tayi kasa da muryarta tace "Thank you my Captain" ya kashe mata ido yace "C'mon babe.... Nikab din kuma na meye yau kika sa?" Tace "I just felt like" ya daga kafada yace "Alright sai mun yi waya" ta gyada masa kai ta nufi gate ya juya ya koma parlor, her neatness melt his heart always nd make him fall for her deeply. Wata dattijuwa ce xaune dakinta tare da yan mata biyu, aka bude kofar dakin duk suka daga kai, Dattijuwar na murmushi tace "Aa Abuturrab sannu da xuwa" ya karasa ciki yana murmushi shi ma, ya xauna sannan ya gaisheta da ladabi, tace "Ka dawo weekend kenan" yace "Ehh daxu muka sauka, ya karfin jikin Umma?" Tace "Alhmdllh na ji sauki yanxu" yace "Allah ya kara lfya" tace "Ameen" ledan hannunsa ya ajiye yace "Ahmad yace in taho maki da wannan" Tace "Kun hadu a Abujan kenan" Yace "Ehh kwana na biyu a can, weather babu kyau sai yau na samu muka bar Abujan xuwa kano, daga kano na biyo private jet" Umma tace "Toh Allah ubangiji ya tsare mana ku dai, Allah ya rabaka da sharrin kayan bature, haka kai kuma Allah yayi hanyar cin abincin ka" Amira tayi 'yar dariya tace "Kabu kabun jirgi Ya Abuturrab yake fa" Ta gefen ido ya kalleta bai ce komai ba, amma ya hade rai sosai, Umma tace "Ni dai Allah ya tsare min shi" a hankali yana kallon kanwar mahaifiyar tasa yace "Ameen Umma" Tace "Mun yi waya da Ahmad daxu nace masa wani awara da yake kawo min nake son ci wllh, gaba daya bani da appetite, yace kuma a hayi ake yi ko" Abuturrab ya d'an buda ido, sae kuma da sauri yace "Allah sarki, baxa a iya maki a gida ba Umma? Ae kamar yafi tsafta ayi a gida kawai" Tace "Aa da wahala, beside babu ma waken suyan a kasa, Hurairan da xata yi ma ta tafi garinsu daxu, kanninka kuma babu abinda suka iya gasu nan dai xaune, gwara kawai a siya a wajen ya fi, naga me kyau ne sosai ran da ya siyo ae" Abuturrab dai bai sake cewa komai ba, tace "Kuma yace ka san wajen, tare ma ku ke xuwa" Da sauri Abuturrab ya kalleta, lkci daya ya kirkiri murmushi yace "Anya xan gane kuwa Umma, a wani layi ne can cikin hayi fah, the place is very complicated" tace "Aa Aliyu na fa sanka sarai, ko baka sob xuwa ne, idan ma da gaske ne baka gane wajen ba ai kiran Ahmad din xaka yi ya sake maka kwatance" Bai ce komai ba amma lkci daya mood dinsa ya canxa har hakan ya kasa boyuwa a fuskarsa, sai dai bai bari ta lura ba, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna karfe biyar da few minutes, Umma tace "Ko kana da inda xaka je ne?" Ya d'an shafa kansa a hankali yace "Aa, bari in je in dawo" tace "To Allah yyi maka albarka" da kyar ya amsa da "Ameeen" snn ya mike ya fita, sosai ya hade rai bayan ya shiga motarsa, why will Ahmad tell her ya san wajen, ynxu kawai sai ya fara driving xuwa hayi wai yaje siyan awara why??? wani tsaki yyi ya tada motarsa ya bar compound din. Driving kawai Abuturrab ke yi har ya shigo hayi, he was very observant kar ya wuce inda ake suyan awaran, haka nan yake jin ransa na baci, wani ma ya gansa ya xata shi xai ci, U turn yyi ya samu waje yyi parking yana kallon yarinyar da ta mike xata shiga karamin layin nasu bayan ta sauke kaskon awaran kasa, almajirai uku ne tsaye gun da wasu yan mata biyu, Abuturrab ya dake yace "Kee" bata juyo ba don tafiyarta kawai take kuma da alama ma bata ji ba, Daya daga yan matan wajen tace "Bata ji ba, yanxu xata dawo, xata amso canji ne" Bai ce komai ba ya jinginar da kansa jikin kujeran motar, bayan kusan minti biyar sai ga ta tana dawowa, kallonta yake har ta iso bakin titi, ta kalli motar sannan ta durkusa gun sana'arta, Yarinyar daxu tace "Ke jiddah jiranki ake xa a siyi awara" Sai snn ta daga kai suka hada ido da Abuturrab, ya hade giran sama da ta kasa yace "Nawa kike siyar da kayan siyarwar taki?" Tace "Wanda ya rage a nan bashi da yawa, amma ynxu xa a kawo daga gida...." Bai ce komai ba ya dauke kai, ta sallami mutanen dake tsaye a wajen, bata son komawa gida dauko danyen awaran Gwaggo Hansai ta sake koranta tace bata gama ba, kuma ta bar mata dukiyarta a titi almajirai su sace, Abuturrab ya jinginar da kansa da kujeran motar yana kallon agogon wrist dinsa, wata yar tsohuwa ce ta xo wucewa da kullin icce a kanta, hannunta daya rike da yar leda, ta rike ha6a tana kallon jiddah tace "Har yanxu kaddararren awaran nan bai kare ba har na je inda xa ni na dawo? Ke dai kin yaye islamiyya ko, Amma Hansai dai daga d'an iska sai ita, ko da yake ba ruwana, ba dangin iya balle na Baba ace na fiye sa ido, amma banda haka kullum ke kenan bakin titi kina tuyan awara babu arabi ba boko ubanki kuma ba bakin magana ya xama mijin ta ce, to ba dai ruwana da abinda bai shafeni ba...." daga haka tayi wucewarta, Jiddah ta bi ta da ido hade da daure fuska, Abuturrab ya bi tsohuwar da ido har ta isa wani d'an kuturun gate ta bude ta shiga, ya sake kallon Jiddah dake gyara wutan murhun kusa da ita, Bibalo ce ta iso wajen rike da bokitin awara ta ajiye nan kasa tana fari da ido, fuskarta kamar warce ta shafa boju tace "Hansai dai tace na dubu da dari uku da tamanin ne kafin anjima da daddare kice na dubu da dari uku da hamsin kika gani tunda dama kin saba...." Ko kallonta Jiddah bata yi ba tayi wucewarta tana taunar cingam... Jiddah na fara xuba awaran a mai Abuturrab ya sauke glass din motarsa gaba daya yace "Ke malama jiranki nake fa, kina bata min lkci, kinsan minti nawa nayi a nan yanxu" Sai a sannan ta kallesa tace "Toh ai sai an soya ko baka ganin danye ne? Idan kuma danyen kake so ai magana xaka yi" Dauke kanta tayi ta ci gaba da abinda take, ya rungume hannu daga xaunen da yake cikin mota yana kallonta da mamaki yana sake apprehending abinda ta fada masa, sai bayan minti goma ta kallesa bayan ta kwashe awaran da ya soyu tace "To na nawa kake so?" Ya mata wani kallo yace "Me kika ce min daxu? Sake fada in ji" Ta rufe awaran da ta kwashe a takaice tace "Toh baxan siyar ba, ka tafi gaba can akwai wata me awaran a gaba" muryar Hansai taji a bayanta tana cewa "Bai soyu bane Jiddah, ko ba awaran me motar xai siya ba? Baxa kiyi da jini ba kin xauna kamar wata rubabbiya ni Hansai" da sauri Hansai ta karaso tana kallon Abuturrab tace "Alhaji yi hakuri a kwashe maka yanxu, ta nawa kake so?" Abuturrab na tada motarsa yace "Ae tace ba na siyarwa bane, in tafi akwai a gaba" Da sauri Hansai ta bude roban awaran taga soyayyen awara da ta kwashe a jibge, ga wasu ta xuba a mai, wani lafiyayyen mari ta wanke ta da shi tace "Ubanki ne xai siya wannan da kika kunshe min a gwagwa? Yo ina ma yaga arxikin siyewa tukun, muguwa, axxaluma yar bakin ciki, to Allah ya isa cutata da kike...." Wani marin ta sake wanka mata a mugun fusace ta hankadata, Abuturrab ya xaro ido yana kallon ikon Allah, Hansai ta juya garesa da sauri tana dukawa tace "Don Allah kayi hakuri Alhaji, kayi hakuri Alhaji.... wllh akwai na nawa kake so?" Kasa ce mata komai yyi, ya kalli Jiddah da ta mike tsaye tana shessheka ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta, Yace "Toh har ya kai ki mareta haka??" Hansai ta kara hankade Jiddah da karfi tace "Toh idan ban mareta ba me xan mata, wannn da kake gani makira ce me mugun hali, kuma babu abinda na rageta da shi wllh tllh" cikin tsawa tace "Baxa ki bace min daga nan ba sai na watsa maki man kaskon nan a jiki gaba daya?" Matsawa tayi daga wajen tana kuka sosai, Hansai ta kara turata tace "Muguwa bar min awarata xan karasa suyan, ki je wannan tulin wankin na tsakar gida ban son in xo in ga ko hankici a