Showing 243001 words to 246000 words out of 346625 words

Chapter 82 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

Ficewa Umma tayi daga dakin kamar xata tashi sama, Ahmad ya bi bayanta da sauri, amma Umma bata sauraresa ko na second daya ba ta kama hanyar Police station ita kadai, ta kuma yi warning dinsa kar ma ya bi ta. Dole Abuturrab ya tilasta likita yayi discharging dinsa daga asibitin, ya kira Ahmad yayi driving dinsu gaba daya xuwa gida, Hajja har suka isa gida bakinta bai yi shiru ba, ba irin la'antar Aneesah da bata yi ba, tana shiga parlor ta fara kwala ma Abba kira kamar xata tsaga gidan, Ummi dake kitchen ta fito da sauri tace "Ai bai dawo ba Hajja..." Hajja tace "Toh ai duk gidan uban da yaje xai dawo ya sameni yanxu yanxun nan kuwa, ba shi dai babban burinsa ayi saki ba, to ya dawo ya sa ayi wannan da wajewa, don wllh ni dai idan Aliyu bai saki yarinyar nan ba xan iya mutuwa..." Ummi da gabanta ya dinga faduwa don a tunaninta Jiddah Hajja ke fadi tayi shiru tana kallon Hajja, Hajja tace "Wllh Hauwa da kyar likitoci da Nas suka kwace ta a hannunta, tana can duk ta mata jina jina an kai ta wani asibitin..." Sai kuma ta rushe da kuka, Ummi tace "Me ke faruwa Hajja?" Hajja tace "Meye kuwa baxai faru ba Hauwa, tsinanniyar Nanisa matar Aliyu ce ta saka Jiddah a hammata ta dinga duka kamar an aikota, daga wai Ramlah ta sa tayi ma Aliyu awara tun da ta iya ta kawo masa asibiti, ni dai can kofar gida na fita na samo mana agajin gaggawa aka xo aka fitar da ita daga Asibitin anyi dawanan Kaduna da ita" Abuturrab ya wuce dakinsa kawai, Ummi ta dinga salati tace "Ina Jiddar yanxu Hajja?" Hajja tace "Ramlah ta dauketa ta kai ta wani asibitin nace maki, baki ganta ba abun ba a cewa komai duk ta ji mata rauni ta ko ina" Sosai hankalin Ummi ya tashi ta koma parlonta da sauri ta dau waya ta shiga kiran Umma har ya katse bata dauka ba, Ahmad dai ya ma rasa bakin cewa komai a parlon, Hajja tace "Ina jin saki kala biyu ma xa ayi a gidan nan yau, wato Hafsah Allah ya tsine mata albarka, tana tsaye duk aka gama wnn tashin hankalin bata yi yunkurin yin komai ba, wannan ne kuma ya tabbatar min cewar da hadin bakinta Aneesah ta xo tayi abinda tayi, ai ita ta fara shigowa dakin asibitin da minti biyar sai ga Aneesah, to duk xan nuna masu ni er banxa ce, xan kuma nuna masu ni na haifi uban Aliyu sannan ya haifi Aliyun" Ummi ta fito rike da makullin mota tace "Bari xanje can gidan Hajja" Hajja tace "Wani gida bayan nace maki a asibiti aka kwantar da su, mu kanmu bamu san asibitin ba, yanxu mijinki xaki kira min duk gidan uban da yake ya dawo yanxu yanxun nan" Ummi tayi shiru tana kallon Hajja, Sai kuma ta koma parlonta kawai, bin bayanta Ahmad yayi ya kulle kofar yace "Ummi plss ki kira Umma ta tafi police station i tried stopping her but she isn't listening, wannan family issue ne bai kamata a kai station ba" Ummi tace "Police station kuma? I called but she isn't responding" Ahmad ya nemi waje ya xauna yace "Ki kara kira Ummi, bana son hakan ya faru wllh, su Abba baxa su ji dadi ba" Ummi ta shiga kiran Umma har ya katse still bata dauka ba, Ummi ta xauna ita ma cike da damuwa tace "Toh wai ya aka yi wnn abun? Babu kowa wajen ne har aka bari Aneesar ta doki Jiddah?" Ahmad yace "Ni bana nan na bar wajen Umma ce ta kirani after the incident" Ummi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Bayan kusan minti ashirin Abuturrab ya fito daga dakinsa ya nufi kofa, Hajja dake ta xaune tana jiran Abba ta bi sa da harara tace "To banda ta dalilinka a gidan uban wa Jiddah xata san axxalumar matarka? Wllh Allah ya isar mata... Xan ga abinda ubanka xai ce a kan wnn lamarin kuma ai" Shi dai bai ko kalleta ba ya fita.... Aunty na can bedroom dinta ta kulle da makulli kafin kowa ya kira Abba dama ta kirasa ta giggilla masa karya tana kuka, yace ta kwantar da hankalinta gashi nan dawowa... Kiran Safara'u ne ya sake shigowa wayarta for the 5th time, bayan na Aneesah kusan takwas da ta ki dagawa, ta dake dai ta dauka don ta ji abinda xa su ce mata, bayan ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren cikin tashin hankali Safara'u tace "Hafsah to ga motar yan sanda guda sun shigo gidan Aliyu sun xo tafiya da Aneesah don ma Allah ya rufa asiri kamar mun sani muka garkame kofa.... Banda bubbuga kofa bbu abinda suke yi yanxu haka" Aunty tace "Yan sanda kuma??" Safara'u tace "Wllh, da muka leka ta window muka ga wnn matar Ramlah ce tayi masu jagora" Aunty tace "Ina xuwa" daga haka ta katse wayar, ta shiga kiran Abba, yana dagawa ta sanar masa abinda Umma tayi, yyi shiru sai kuma ya katse wayar, Ummi ya shiga kira, tana dagawa yace "Ki kira yar uwarki ta sallami yan sandan nan da ta kwaso idan ba haka ba xan dau mummunan mataki a kan ke da ita wllh" Rasa ma abinda xata ce masa Ummi tayi.... Bai kuma jira me xata ce din ba ya katse wayarsa, Ummi dai ta dinga kallon Ahmad. Cikin minti ashirin Abuturrab ya isa gidan Umma... Direct dakinsu Maimoon ya nufa, yana bude kofar Jiddah dake kwance ta juya da sauri ta mike xaune don duk a tsorace take tana ganin kamar Aneesah xata ce xata xo gidan, Ya shigo dakin yana kallonta, mikewa Maimoon dake dakin tayi ta fice don ta ji har shi tana jin haushinsa, Jiddah ta ki kallonsa tana gyara duvet din jikinta gabanta na faduwa.



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you





Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulu mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd guess what😍munyi upgrading kayanmu gbdy domin jindadinku🥰bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida
💯 Natural/organic

maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki komai da komai
Akwai soap 3k
Student package 7k
Beauty kit 11k
Bridal kit 18k

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏





Abuturrab ya xauna gefen gadon yana kallonta, still ta ki yarda ta kallesa, yayi kasa da murya yace "Look at me Jidderh..." Dauke kanta tayi ya kamo hannunta kamar jira take ta fashe masa da kuka ta rufe ido, a hankali ya daura kanta bisa shoulder dinsa cikin sanyin murya yana patting bayanta yace "Kiyi hakuri pls, i caused u all this... And ni nasan matakin da xan dauka a kanta" ita dai kuka kawai take, ya dago kanta yana kallonta a hankali ya kai hannu jikinta yace "Tell me where is hurting u now" Turasa tayi ta girgixa masa kai har sannan ta kasa daina hawaye, Bude kofar dakin aka yi Abuturrab ya juya da sauri tare da saketa, ita ma ta koma baya da sauri gabanta na faduwa, Umma ce ta shigo tana ganinsa a dakin ta wangale kofar tana nuna masa hanyar waje tace "Mu je ka bude masu gidanka a tafi da matsiyaciyar yarinyar nan yanxu...." ya mike amma ya rasa abinda xai ce mata, Cikin tsawa tace "Mu tafi nace ko baka ji na ne?" Yayi lowering voice dinsa yace "But Umma plss ba sai anje police station ba, i will personally deal with..." Wani tsawan Umma ta kuma yi masa tace "Ba sai anje police station ba?? Ohhh kana nufin ko bayan an kai ta police station din kenan kai babu wani hukuncin ma da kake da niyyar yi mata tunda kai ne dalilin da yasa ta kusa kashe yar mutane? Wait first who are u to question my order Aliyu?" Da sauri yace "Aa ba haka nake nufi ba Umma" Umma tace "Wato tun ba a kai ko ina ba kenan a titi wannan mummunan al'amarin ya faru babu kunya a kan idonmu, to in sha Allahu daga kai har matsiyaciyar nan bbu ajalin Jiddah a cikinku, babu inda xa ku ganta balle ku kasheta daga kai har matarka, police station kuwa ko uban da ya haifeka bai isa ya hanani kai ta ba balle kai..." Cikin tsawa tace "Fita mu je ka bude masu gida my frnd" kofa ya nufa ya fita Umma ta bi bayansa, a motarta suka koma station ta sake biya aka bata en sanda suka nufi gidan Abuturrab, a kofar gidan ta tsaya tare da en sandan tana kallonsa babu wasa tace "Go in and get her out" Ya d'an kalli yan sanda ya kasa ce mata komai, kawai dai ya nufi gate din cikin gidan ya shiga yana tafiya a hankali, mai gadi ya taso da sauri cike da damuwa yace "Yallabai ina fatan dai lafiya ko? Daxu ma sun xo suka dinga buga kofar shiga cikin gidan..." Abuturrab bai tsaya ba yace "Lafiya lau" har ya isa entrance din parlon yayi knocking, lkci daya kuma ya ciro wayarsa a aljihu ya kunna, dialing number din Aneesah yayi, kamar wayar na hannunta yana fara ringing ta daga da sauri, fashe masa da kuka tayi kafin ta ce komai yace "Zo ki bude min kofa" Tace "Honey yan sanda ne fa sun fi biyar suka shigo compound din nan daxu, suna ta knocking, kai kana ina yanxu don Allah?" Yace "Ina bakin kofa" kallon Safara'u tayi sai kuma ta mike da sauri ta sauka downstairs tana kallon kofar, tafiya tayi a hankali ta isa bakin kofar tayi kasa da murya tace "My captain?" Yace "Bude kofar" Wani ajiyar xuciya ta sauke ta bude kofar ya shigo parlon, ta rushe da wani sabon kukan tana kallonsa, Controlling temper dinsa kawai yake cause he felt like doing her exactly what she did to Jiddah at the hospital, wani haushinta yake ji har cikin ransa, ya dai dake yace "Tafi ki sako hijab din ki?" Ta dakatar da kukan da take tace "In je ina??" Yace "Inyi wucewata in bar ki ne?" Tace "Aa..." Da sauri ta wuce sama, ba a dau lkci ba ta sakko tare da Safara'u da ita ma ta xumbula Hijab din don xatonsu fitar da su xai yi daga gidan, yana ganinsu ya nufi kofa ya fita, Aneesah ta bi sa da sauri cike da wani farin ciki ashe Aliyu na sonta dama haka, wato dawowa yyi ya fitar da ita daga gidan tunda en sandan might likely come back, Safara'u dai sai bin su take da sauri ita ma, yana fitowa daga parlor ya ga en sanda biyu tsaye gefe da gefen balcony din, Umma kuma na tsaye daga kasa fuskar nan nata a murtuke, a hankali ya karasa sauka sai ga Aneesah ta fito, tana fitowa en sandan mata suka cafketa, daya dake rike da handcuff tace "U are under arrest" Xaro ido Aneesah ta dinga yi tana kallon Abuturrab tana bin en sandan da kallo cikinta ya duri ruwa sosai, Tuni Safara'u ta juya a guje ta koma cikin gidan, haka suka fitar da Aneesah daga gidan tana cewa "Captain da kai xa a hada baki a kai ni station?? Da kai captain??" Tsawa yar sandan tayi mata ta rufe ma mutane baki, sannan aka sa ta a mota aka wuce, Umma ko kallon Abuturrab bata yi ba ta shige motarta tayi reverse ta bi bayan motan en sanda Abuturrab ya bi ta da kallo kawai. Abba ne ya shigo parlor babu ko sallama yana kallon Ummi dake xaune tare da Hajja a parlon directly, yau kam Hajja ta bada labarin yanda incident din asibitin ya faru ya fi sau ashirin har da demonstration dinta, gashi ta ki yarda su tafi gidan Umma duba Jiddan wai ai dole Usman ake jira a je da shi ya gane ma idonsa abinda Hafsah ta sa Nanisa ta aikata ma Jiddah, don haka a hada hannu har shi a kwato ma Jiddah hakkinta tunda ba uwa ba uba, Shiru Ummi tayi ta sauke kanta tana sauraron Abba dake gaggaya mata magananganu ido rufe, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, Hajja ta mike ta daka masa wani axababben tsawa tace "Shet up malam... A gabana kake wannan tijara babu tsoron Allah balle ni??? A gabana kake mata wannan cin mutuncin Usman??" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tace "Ita Hauwar me ta maka kake jifanta da wa en nan axababben maganganun ba dadin ji?? Er banxa ka mayar da ita kenan Usman?? A gabana fa aka yi komai a asibitin nan ba wai labari na tsinta ba, ita Hafsar ce tayi maka duk wannan tsarin? to wllh wllh yau a gidan nan ko ni ko ita, Allah sai ka xaba ko ni ko Hafsah tunda babu wanda xai kiraka ya giggilla maka wannan karyan da ya sa ka dawo kake sababi sai ita, wllh idan baka xabi ko ni ko ita ba ka canxa uwa kawai kafin dare" Abba bai kuma kallon Hajja ba ya wuce bangarensa rai a bace, Hajja ta nemi waje tana kara rushewa da kuka ta ciro wayarta ta mika ma Nafisah dake xaune kasa gefenta tace "Kira min Kabiru" Nafisah ta amsa ta kira mata sannan ta mika ma Hajja, Yana dagawa ta sakar masa kuka tace "Duk abinda kake yi ka barosa don bai fi ni ba, ka biyo jirgi ka taho garin kaduna ta faru ta kare Usman babu xagi da cin mutuncin da bai min ba yau har korata yayi, ka taho kawai kabiru xuciyata xata fashe" daga haka ta katse wayar ta mika ma Nafisah tace "Kira min Umaru" Nafisah ta kira mata shi ma Hajja ta sanar masa, duk sai da ta bi ta kira 'ya yan mijinta gaba dayansu su bar duk abinda suke su taho kaduna Usman ya xageta ya koreta daga gidansa, Ummi dai na xaune tayi tagumi abun duniya ya dameta, banda radadi da xafi babu abinda xuciyarta yake mata and she is trying her best to hold back tears, duk wannan abun kuma Aunty na part dinta tare da er ta Aisha sun bama makulli.... Ko minti goma Abba bai yi da shigewa bangarensa ba Umma ta shigo gidan, tana shigowa ta kalli Nafisah tana huci tace "Abban naku ya dawo??" Nafisah ta gyada mata kai kawai, Umma tace "Toh ya fito gani nan na tako da kaina naxo ba sai yaje can gida ya sameni ba, ya fito ya sa a daureni har karshen igiya kamar yanda yace, gani gidansa ya fito" Hajja ta marairaice tace "Ya daure ki ko a dauresa??? Huhuhu ai da Masar ne yau xai san ya xagi mahaifiyar da ta tsugunna ta haifesa don wllh wllh baxai kwana kasar su ba ma, sai sun walakantasa sun masa dukan tsiya" Umma ta kalli Ummi tace "Ki tashi mu tafi Yaya, ya dade bai dau hukuncin da yace ba wllh, tashi muje babu shegen da ya isa ya sa maki hypertension, wllh dai dai nake da shi" Hajja ta mike tace "Babu inda xata je wllh, sai dai shi katon ya fito ya bar mata gidan, sannan in har ya kwana da auren Hafsah a kansa kowa xai girgixa da lamarina a gidan nan..." Tana huci ta kare maganar, sai kuma ta koma ta xauna tace "Kema koma ki xauna Ramlah yau kowa ya xuba ido akwai kallo" Nan Hajja ta kuma bi ta doddoka ma duk wa enda ta kira wani sabon kiran wai ga fa kayanta Usman ya watso bakin kofa.... Umma dai taki xama gidan tayi wucewarta ranta fess Aneesah xata yi kwanan cell, kuma ta ji dadin yanda Hajja ta tsaya ma Ummi, Ana idar da Magrib duk wa enda Hajja ta kira suka iso gidan, tana nan xaune ta hakikance a parlor taki motsawa ko nan da can, sallan ma a parlon tayi, duk suka xauna nan kasa suna gaisheta, ta amsa tana shessheka, babu yanda basu yi da ita a kan sun shiga parlon Abba ba ta ki, ta kalli Ummi da fitowarta daga part dinta kenan ta xo yi ma bakin sannu da xuwa tace "Kiyi kiran Aliyu da Ramlah su xo, a gabansu xa ayi komai" Ummi ta amsa mata da toh, sannan ta dau wayarta ta shiga kiran nasu, Abba ya fito daga bangarensa ya gaida brothers din nasa, shi dai Abban El-Basheer kallonsa kawai yake, Hajja ta wani dauke fuska kamar ta ga mugun abu, xaunawa yayi shi ma a parlon, Ummi bayan ta gama kiraye kirayenta ta taho ta xauna ita ma, Hajja ta kalli Kabiru tayi mici mici da ido tace "Dama ku gaya masa duk inda matarsa Hafsah take ta fito ta nemi waje ta xauna a nan ita ma" Abba dai bai ce komai ba, sai kuma ya mike ya tafi bangaren Aunty, ba a dau lkci ba suka fito tana biye da shi a baya, da hijab dinta me jan kasa, ta ki kallon kowa na parlon fuskar nan nata babu yabo babu fallasa ta nemi waje ta xauna ta gaida yan uwan mijin nata, duk suka amsa, ko kallon Hajja ita ma bata yi, ba a wani dau lkci ba Umma ta shigo gidan, ganin Aliyu bai iso ba, Alhaji Kabiru ya bude wajen da addu'a aka sake gaisawa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login