Showing 285001 words to 288000 words out of 346625 words

Chapter 96 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

fara don kaf dukiyarsa basu kai su siya kayan dakin Jiddah ba..." Ko kallonta Aneesah bata yi ba ta ciro makullin dakinta da ta tusa a kirjinta ta bude kofar ta shige sannan ta kulle dakin da key, Mahaifiyar Ali da mamaki ya cikata tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, menene amfanin haka?? Me mata suke son mayar da rayuwarsu a wannan xamanin?" Hajja dake ta xufa tace "yan iska mana... to wllh karshenta ya xo a gidan nan, in har xata iya ma kayan dakin da basu ji ba basu gani ba wannan tijaran to wllh tsaf xata kashe mutum da ta6aryar hannunta, ga fa yar mitsitsiyar kishiyar tata can, warce a haihuwan kaji tayi jika da ita kai har tattaba kunne, da er cikinta fa take kishi don bala'i har da lalata mata daki haka, toh Allah ya tsine maki Nanisa" Ali ya kalli Jiddah da Hajja ta nuna, kallonta ya dinga yi da mamaki ko kiftawa babu, Mum dinsa ma kallon Jiddah take har sannan, Jiddah ta sunkuyar da kanta, Hajja ta kalli Ummi tace "Huhuhu.... da na san abinda xai faru gidan nan kenan yau wllh da Ramlah xan taho asirina a rufe ba ke ba, a kira min ita yanxun ma ta xo taga abinda aka yi ma kayan yar ta, maxa kira min ita Maimoon ba mu ga ta shiru ba ai" a hankali mahaifiyar Ali tace "Toh Allah ya kiyaye, Allah ya kyauta, but this is so bad wannan wani irin bakin kishi ne haka ni Amina?" Hajja ta karbi wayar da Maimoon ke mika mata bayan ta kira Umma, Umma na daga kiran Hajja ta fashe da kuka tace "Ramlah ki taho gidan Aliyu yanxun nan ba lafiya babu dalilinta, ki saka hijabinki ko ba kaya ki taho kawai Ramlah" tana gama fadin haka ta mika ma Maimoon wayarta, Hajja ta kalli su Ali tace "Ku kuma da ku ka saurareni har ku ka shigo ku ka gane ma idonku wannan abun al'ajabin Allah ya maku albarka, kun dai ga me rayuwa ke ciki yanxu, kishi ne ake yi irin na tsinannun bayi, gashi nan dai sbda kishi ta hallaka kayan dakin kishiyarta har lahira, to karshen aurenta ne kawai ya xo ba mu sani ba" Ummi ta sauka downstairs ta xauna tana al-ajabin wannan abun da ya faru, tare Hajja ta sauko da Ali da mum dinsa, sai a sannan suka gaisa da Ummi, Hajja na nuna Ummi tace "Ita ce uwar mai gidan fa, amma kun ga babu wani hukunci da ta dauka, gata dai da takarda a hannu kamar malamar makaranta bata ta6uka komai ba, ai samun uwa tsayayyiya ma wani abu ne a rayuwan nan wllh, tirrrr" Hajiya Amina na kallon Ummi tace "Can we talk outside pls" Mikewa Ummi tayi ta bi bayanta suka fita compound, Ali na kallon Hajja yace "Duk matansa ne kenan kaka?" Hajja tace "Ehh wllh, ita warcan yar farar yarinyar da ka gani a rakube kamar mage sai gwale ido take to kayan dakinta aka yi ma wannan cin mutuncin da tijara, kuma gobe satinta ke cika daya da tarewa a gidan, ita kuma me k'irar yan da6a warce tayi aika aikan ta kai wata shidda ko shekara daya ina ga a gidan yanxu, toh kai in kai ne Aliyu don Allah wani hukunci xaka dauka bawan Allah?" Ya sauke ajiyar xuciya yace "Sai kawai in sallami ita wannan me 6arnan don da alama baxa ta bari a xauna lafiya ba" Hajja tace "Allah ya maka albarka, don kuwa wataran kashe Jiddar xata yi har lahira ko??" Ali dai yayi shiru, Hajja tace "Xa ma ka san me gidan idan kana shige shigen jirgi sbda matukin jirgin Najeriya ne, kuma ance shi kadai ne bakin fata" Murmushi yyi yana shafa kansa yace "Allah sarki" Bayan wani lkci Ummi ta shigo parlon ta kalli Maimoon dake saukowa tace "Kira min Aliyu" Mikewa Hajja tayi tace "A kira maki shi kiyi masa me?? Idan kina da wani amfani wllh shegiya nake Hauwa, ke da xaki sa sai ya rabu da matsiyaciyar yarinyar yau amma kinyi shiru kin ja gefe kamar dai kin samu fim din hausa kina kallo" Ummi bata ko kalli Hajja ba tace "Maimoon daga nan ku sauko har da Jiddah driver ya kai ku can gida yanxu" Ali ya sauke ajiyar xuciya don fa gaba daya case din nan ya daure masa kai, yace "Allah ya rufa asiri, Allah ya tsare gaba Kaka" Hajja tace "Wllh sai Aliyu ya saketa baxai xauna da yar da6a ba a gaskiya da raina, don daga wnn abun da ta aikata xaka san tana hulda da rikakkun yan daba" Ba a dau lkci ba Abuturrab ya sauko downstairs, har sannan fuskarsa a daure yake xuciyarsa na tafarfasa, Hajja tace "Ba daure fuska xaka yi ba kamar wawa, mataki xaka dauka yanxun nan, ni abinda ya tsaida ni kenan don da na tafi tuntuni, da fa a Masar ne har ni xa a kwashe idan yan sanda suka xo gidan nn wllh, sbda kamata yayi tun farkon lamarin a kai masu rahotu, to wannan sai Ramlah kuma tace tana hanya" Abuturrab ya nufi Ali yana kallonsa ya mika masa hannu, Ali yace "You just have to be calm and take things easy, do not make conclusion while angry" A hankali Abuturrab yace "In sha Allah" Ali ya mike yace "Toh kaka Allah ya tsare gaba" Hajja tace "Toh ina xaka kuma? Uban wa xa mu nuna a matsayin shaidun mu idan ka tafi?" Yayi murmushi yace "Ai gidanmu na kusa da wannan Kaka" Hajja tace "Atoh shkkn, duk kai da mahaifiyarka xa ku yi shaida ko gidan uban wa xa aje da kess din nan" Ali yayi ma Ummi sallama ya fita parlon, mikewa Ummi tayi ta hade kan su Maimoon suka bar gidan tare da driver, bayan tafiyar su da mintuna kadan sai ga Umma ta shigo babu ko sallama fuskar nan nata bbu yabo bbu fallasa ta jefar da jakanta saman kujera tace "Me ke faruwa Hajja?" Hajja ta mike ta rushe da wani kuka tace "Hau sama ki gane ma idonki Ramlah, je ki sama Ramlah..." Umma ta haura sama da sauri, tana arba da dakin Jiddah ta sauko tayi wani irin dariya tace "Wllh wllh ban ga shegen da xai hanani daukan fansan abun nan ba, ban ga wanda ya isa hanani daukan matakin da ya kamata ba, kuturin uba..." Tana kai wa nan ta figi jakanta ta nufi kofa kamar xata yi tsuntsu tana huci, Hajja ta dau katon jakarta ta bi bayanta sum sum tace "Ni da nasan kan komai" Ummi ta sauke boyayyen ajiyar xuciya ta kalli Abuturrab da kansa ke kasa tace "Aliyu" Dagowa yayi ya kalleta da idanuwansa da suka koma kamar garwashi, shi dai ya san ba don mahaifiyarsa dake gidan nan yau ba babu abinda xai hana shi yi ma Aneesah dukan tsiya wanda har sai ta suma, bai yi farin cikin kasancewar Ummi a gidan ba wannan abun ya faru, Ummi tayi kasa da murya tace "Kayi hakuri Aliyu, kar ka yanke hukunci cikin fushi, kuma ina umartanka duk hukuncin da xaka dauka banda saki...." ya marairaice mata yace "Ummi me yasa xaki ce haka? To meye amfanin xama da ita Ummi? Wllh baxan iya ci gaba da xama da ita ba, ta fita raina gaba daya, ko na xauna da ita ni nasan baxan kwatanta adalci tsakaninsu ba" Ummi tace "Xaka yi Aliyu, now tell me meye amfanin sakin nata? Shkkn sbda saki abun banxa ne sai ku maida shi ado kai da mahaifinka? Haba Aliyu, ni ban hanaka daukan duk matakin da xaka dauka ba amma kar ka saketa, Alhmdlh abun ya tsaya iya kayan daki kuma ba komai ya ja tayi haka ba sai kishinka, da bata sonka kuma baxata yi kishinka ba, kowacce mace da kalan nata kishin a xuciya, abinda tayi kuma yana nuni da how frustrated she is, ba wai nace abu me kyau tayi ba Aliyu, dole dama xa a hukuntata, but plss do everything except divorcing her, ko kadan bana son kalman nan ta saki, ban hanaka nuna mata bacin ranka ba amma don Allah banda saki kayi hakuri ka ji, kaga ta dalilin wannan abinda ya faru kila Abban naka ya hakura ka raba masu gida, sannan ina son tambayarka motar da ka siya su biyu ka siya ma ko yaya?" Ya kalli Ummi yace "Kawai warce ta cancanci motar na siya ma Ummi" Ummi tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Toh kai ka tsokano bala'in kenan, wa yace maka ana haka? Idan Kyautatawa kake son yi ma daya a cikinsu sai dai kayi shi a boye ba a sarari ba ai" Shiru yayi ba don maganan Umminsa na masa dadi ba, gashi baxai ta6a iya cewa xai ce mata Aa ba, yanxu yana ji yana gani xata hanasa sakin Aneesah, jinginar da kansa yayi jikin kujera yana jin xuciyarsa na tafarfasa, Ummi ta mike ta haura sama kofar dakin Aneesah ta tsaya ta kwankwasa tace "Aneesah?" Sai da ta kwankwasa sau uku sannan Aneesah ta bude dakin, Ummi ta shiga bedroom din nata ta kulle kofar tana kallonta, Aneesah ta koma ta ci gaba da xamanta a kan carpet idanuwanta sunyi jajir ga yanyankewan da tayi a hannu bai fasa xuban jini ba, Ummi ta ja kujera ta xauna tace "Me yasa kika aikata abinda kika aikata Aneesah" Kamar jira take ta fashe da wani matsanancin kuka tace "Ummi tunda yayi auren nan yake walakanta ni yake ci min mutunci, ya fita harkata bai damu yayi magana da ni ba, bai damu da halin da nake ciki ba, all he is after is his new wife..." kuka sosai take, Ummi tace "Kuma a tunaninki fasa kayan dakin Jiddah da kika yi xae canxa komai ne?" Aneesah ta hade kai tana kuka sosai, Ummi tace "Baki kyauta ba Aneesah, ko mahaukaci baxae aikata wannan abun da kika aikata ba, yanxu meye amfanin hakan?" Aneesah dai kuka kawai take, Ummi tace "Yanxu baki tunanin abinda xae je ya dawo wannan barnan da kika yi? Ko shi Aliyun kina ganin kyaleki xai yi da ba don ina gidan nan ba yau? Balle warce Jiddah ke hannunta?" Shiru Aneesah tayi tana share idonta, Ummi tace "Tashi mu je parlor" Tashi tayi ta dau hijab dinta ta saka tana hawaye ta bi bayan Ummi, suna saukowa downstairs, suka shiga parlon, kafin Ummi tace komai ta durkusa gaban Abuturrab tana kuka sosai tace "Don Allah kayi hakuri Captain, wllh sharrin shaidan ne, I don't know what came over me, kayi hakuri ka yafe min..." Ji yayi kamar ya haureta yana jin wani mugun tsanarta a xuciyarsa, ko ganinta bai son yi a sight dinsa wllh, ganin kallon da Ummi ke masa ya dake yace "I have nothing to say in here, tunda ba kayana kika yi ma haka ba, u wait for the consequence from the owners" Aneesah ta kalli Ummi, Ummi tace "Tashi" mikewa tayi Ummi ta dau handbag dinta suka nufi kofa Aneesah na biye da ita, Abuturrab ya bi Aneesah da wani mugun kallo har suka fita, he just can't keep on staying with her as his wife, ya tsaneta har ransa. Ko minti sha biyar basu yi da fita ba sae ga Umma da yan sanda Hajja na biye da su sae cewa take "Da kafinta ya kamata a xo don shegiyar ta garkame kofa tun daxu, shi ae jijjige kofar baxata masa wahala ba tunda aikinsa ne" Umma ko kallon Abuturrab bata yi ba ta nufi sama yan sanda mata biyu na biye da ita, bayan wasu mintuna suka sauko Umma na masa wani kallo yace "Ina take?" Abuturrab yace "Ummi ta fita da ita" da mamaki Umma tace "Ummi??" Hajja ta saki wani salati ta rike kanta tace "Amma daga tambadadde sae Hauwa, ta fita da ita ta kai ta ina? Kun dai ga jaraba ko?? Wato yanda Hafsah ta dinga gallaza mata taki barin a dau mataki haka take so a dinga yi ma Jiddah sbda bakin hali da mugunta? To wllh baxata sabu ba, to wa ma ya sani ko ita ta saka Aneesar ta aikata abinda ta aikata tunda har xata iya fitar da ita daga gidan? Kai jama'a, wa Hauwa take so ta burge a nan? Ita a dole ta Allah wai ko? to Allah ya wadaran naka ya lalace dai.." Umma ta fice da yan sandan xuciyarta na tafarfasa, Hajja ta bi bayanta tana cewa "Na gaji da Hauwa wllh, na gaji da halinta, to wai uban wa xata burge ne ban gane ba, da kyar idan bbu hadin bakinta a wannan tsiyar da Aneesah ta tafka, wato gwara ta hade kai da Aneesah a cuci Jiddah, ai kuwa xan nuna mata ni er banxa ce wllh" Mikewa Abuturrab yayi ya wuce sama rai babu dadi, ko kadan bai son ya kwana da auren Aneesah a kansa yau, Umma ta sallami yan sandan ta nufi gidan yayarta tare da Hajja, har sannan xuciyarta na tafarfasa, ai wllh Aneesah bata ci bilis ba, sae dai idan canxa sunanta aka yi daga Ramlah.....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




FZ BEAUTY SUPPLEMENTS
Dealer in all kind of dietary supplements such for skin whitening, skin glowing, weight gain, slimming, flat tummy, infection killers, dark spots removers, fertility booster, Hips boosters, Breast firming and Enlarging, Teeth whitening, eye, joint, stretch marks, and for marital pleasure. All supplement are available for wholesale and retail. For more information contact FZ via wa.me/2348143821028

FZ Beauty Supplements
Dealer ce ta supplement masu qara fito da kyaun mace ko namiji, hadi da qarama garkuwar jiki kuzari. Muna sayarda Supplemnt kamar na qarin duwawu, akwai wanda zaya taimaka wurin dawoda martabar Nono, akwai na rage qiba da tumbi, akwai na rakwainuwa, akwai na tada komada, akwai masu saka hasken fata da qyalli, akwai na infection, akwai na saka hasken ido da hakori sannan akwai na gyaran turaka. Muna maraba da mai sayen daya ko sari. Wa.me/2348143821028







Ummi dake xaune parlor ta daga kai tana kallon Umma da Hajja da suka shigo parlon babu ko sallama kamar an jefo su, Umma tace "Yaya na je can gidan na samu labari kin tafi da yarinyar nan Aneesah" Ummi tace "Ehh ya aka yi?" Umma tace "Ban gane ya aka yi ba Yaya, kin kuwa je sama kin ga abinda ta aikata ma kayan Jiddah?" Ummi tace "Na je, Allah kuma ya tsayar a nan Ramlah" Umma tace "Ba xancen kinje bane yaya, dukiya ce ta walakanta haka fa?? Ba sato kudin wanda ya siya mata kayan yayi ba" Ummi tace "Toh ya kike son ince Ramlah tunda dai abinda ya faru ya riga da ya faru sai ayi addu'an Allah ya tsare na gaba, ko da abinda kike son ince da ya wuce wannan? shi mai gidan ne xai dau hukuncin da ya dace amma ba mu ba, iyaka idan mun ga baxai yi adalci ba sai muyi involving kanmu" Hajja da ta kankance ido tana ta kallon Ummi tace "Tabdii, ashe haka kike ban sani ba Hauwa? Ashe haka kike? Tun ranan alhamis nake ta baxa ido Usman ya dawo in yi masa kaca kaca akan maganaganun da Hafsah ta min ranan a gidan Aliyu, sannan in nuna iko na da isata ya rabu da ita na har abada don ta ci min mutunci ta xageni ta min rashin da'a, shine kiri kiri yanxu kike nuna ma Jiddah bakin ciki kin je kin dauko kishiyarta mahaukaciya da tayi mata axababben ta'adi kin xo kin boyeta, kawai muka kwashi kafa muka je da yan sanda kika kunyata mu a gabansu?" Ummi tace "Hajja shi fa duniyar nan da muke ciki d'an hakuri ne, wata rana sai labari, sai a ga kamar ba ayi ba wllh, meye riba don ka xuba ido an ci ma sa'ar er ka mace mutunci, 'ya yan nan fa muna da su ta ko ina, kishin nan kuma halitta ce a xuciya sai dai na wani ya fi na wani, ko ince wani yayi na jahilci, sannan abinda Aliyu yayi bai kyauta ba wllh in dai xancen gaskiya xa ayi, idan xai kyautata ma amaryarsa don wani dalili na daban sai yayi sa cikin sirri ba a sarari ba, to what was he expecting dama idan ba tashin hankali ba a gidan nasa yau, ke kuma Ramlah halan har yanxu yan sanda basu gaji da ganin fuskarki bane a yankin nan? Komai kice yan sanda abu da xa ayi solving cikin gida sai ki kwasa ki kai ma yan sanda? Who does that for God sake?" Hajja ta rike kai tace "Huhuhu Allah ya wadaran naka ya lalace, na kara tsoron Hauwa, na tsorata da lamarinta!! waiiiiii Allah" Umma dake ta kallon Ummi babu ko kiftawa tace "Fine and good, daga yanxu duk wani abu da ya shafi gidan Aliyu dama na cire hannuna in sha Allah" Ummi tace "Aa gwara ki cire wllh da wannan sintirin gidan yan sandan dai, don wannan ba yi bane... kullum ana ganin yan sanda na kai komo a gidansa, babu saiti ne abun?" Umma tace "Ai sai ki tsaya ki saurareni yaya, ban gama ba" Ko kallonta Ummi bata yi ba, Umma tace "Amma kinga a kan lamarin Jiddah? Wllh babi wanda ya isa ya sa in cire hannuna, sai inda karfina ya kare ba sani ba sabo, kuma wallahil azeem sai an biya aika aikan nan da yar iskar tayi mata a daki, babu ruwana da wanda xai biya, kawai abinda na sani a mayar ma yarinya da dakinta yanda yake, kuma wllh baxata koma gidan ba sai an canxa mata kayan dakinta dai dai da yanda nayi mata" Hajja tace "Lallai... Toh da fa, ai babu tantama Hauwa ta aiki Nanisa tayi aika aikan da tayi, ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba, sannan Usman na dawo xan basa shawaran ya dawo da matarsa Hafsah tun dai kishiyar abar dadi ce, kowa sai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login