Showing 297001 words to 300000 words out of 346625 words

Chapter 100 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

spoon ya deba ya kai baki, lumshe ido yayi yace "umm.... So Yummy" mikewa tayi ta durkusa kusa da abincin ta dau plate ta dibar masa, sannan ta fara hada masa shayi, shi dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa, komai tayi burgesa yake, ba kuma yau ya fara jin hakan ba, for long ya ke ji hakan... bayan ta hada shayin ta dauka ta ajiye masa a gabansa a hankali tana kallonsa, kissing lips dinta yayi ya lumshe ido yace "Thank you MPG💖" ita dai kallonsa kawai take da manyan idanuwanta, under neath his breathe yace "My Precious Gift 💖" Ta sauke idonta amma har ranta taji dadin words din nasa, yace "kiyi serving kanki sannan ki dibar ma Aneesah ma, i will be back soon" Daga haka ya mike ya wuce sama, ta bi sa da kallo. Yana shiga dakin Aneesah ya tar da ita xaune can karshen dakin ko tunanin me take oho, ta d'an kallesa yace "Taso mu yi breakfast" Shiru tayi yace "I am talking to you" a takaice tace "Aa ku dai ku ci, ai kune masu gidan yanxu" Ya karaso cikin dakin yace "U admitted kina son xama da ni as ur husband Aneesah, and for peace to continue reigning in our midst duk abinda na fada just adhere and obey that's all, nace ki taso mu yi breakfast, i wasn't expecting you to decline that" Bayan few seconds ta mike ta dau mayafinta ta yafa sannan ta nufosa ya bi ta da kallo har ta fita, fitowa yayi ya kulle kofar dakin sannan ya bi bayanta downstairs din, Can gefe jikin kujera ta samu ta xauna, ya dau dankali da kwan da Jiddah ta debar mata ya ajiye gabanta, sannan ya hada mata shayi ya ajiye mata, Jiddah dai ko kallonsu bata yi ba, a hankali take shan shayin hannunta, Ya dau fork din dake plate din potatoes da Jiddah ta debar masa yana kallonsu both yace "Kun gaisa yau?" Babu wanda yace komai cikinsu, ya kalli Jiddah sannan ya kalli Aneesar duk babu wanda ya kallesa, yace "I am talking" Jiddah ta ajiye shayin hannunta ta mike, ya daga kai ya kalleta yace "Ina xa ki?" Without looking at him tace "I want to ease ny self" daga haka tayi wucewarta sama, Aneesah ta dau fork ta fara cin abincin gabanta, shi dai Abuturrab bai ce komai ba, bayan mintuna kadan ya kalli Aneesah yace "You met her downstairs, sannan she made this meal and tidied the whole house, why not even tell her weldone" Aneesah ta kallesa tace "Ni ban taso a gidanmu naga Babba na gaida yaro ba, ai darajar girmanta da nayi ya ci ace ta gaisheni kafin ni kuma in ce mata sannu da aiki, but tana jira ni in gaisheta, na san kuma na bata at least 7 good years, autarmu ma ta girmeta" Abuturrab yace "Amma sai ki yi mata sannu da aiki ki ga ko xata gaisheki ko baxata gaisheki ba, balle u met her ba ita ta xo ta sameki ba" Aneesah tayi wani murmushi tace "I am not surprise u are always supporting her, to ta dawo ta xauna sai in gaisheta i know i won't loose" Abuturrab bai ce mata komai ba, bayan some minutes yace "U asked for something few weeks ago, do u still need it?" Ta ajiye fork din hannunta tace "Bana bukatarsa, kawai yanxu cikon kudi xaka bani a kawo min wasu furnitures din, kudin da xa a turo min baxa su isa ba...." Ya girgixa kai yace "Bani da kudin furnitures because i didn't budget for it this month... anjima xan saka maki abinda kika tambaya 2 weeks ago" Bata dai ce masa komai ba, yace "And ki shirya before 12 xa mu shiga gidan neighbors dinmu a gaisa, so we can know each other more" Tace "Aa ni baxan je ba, ku je dai da matarka..." Calmly yace "Ni kuma nace ki shirya mu je" Bata ce masa komai ba, hakan ya sa ya mike ya koma saman kujera ya dau wayarsa dake vibrate, kallonsa take har ya gama wayar sannan ta sunkuyar da kanta tace "Captain i think i have to go to do hospital don jikina baya min dadi, ina yawan jin jiri da kasala sannan i don't have appetite na cin abinci...." yace "Ohk, Allah ya sauwake" tace "Ameen, i need to see a doctor" kwashe duk kwanukan tayi da plate ta wuce kitchen da su ya bi ta da kallo. Mikewa yayi ya wuce sama, bangarensa ya tafi hoping to see Jiddah there, ganin bata nan ya dawo dakin baki, kwance ya ganta saman gado idonta rufe, ya xauna gefenta yayi kasa da murya yace "Jiddah" Kin bude idon tayi ya dagota ta 6ata fuska tace "Ni bacci nake ji" Yace "Me yasa kika ki cin abincin?" Ta bude ido tace "Saboda na koshi" Yace "Amma baki ci komai ba" shiru tayi masa, yace "Or are u angry at anything?" Tace "Not at all" Ya kamo hannunta yayi lowering voice dinsa yace "U know what?" A hankali ta daga ido ta kallesa, yace "For the sake of ta girmeki ku dinga gaisawa da safe pls idan kin ganta..." Ta xame hannunta daga nasa tace "It's not necessary" da mamaki yake kallonta, can dai yace "Why?" Tace "That's just my stand on it" yayi kasa da murya yace "No Jiddah ina son ku xauna lafiya kamar yaya da kanwa pls, nasan in sha Allah Aneesah ta canxa halinta xa ku xauna lafiya without any problem" Murmushi kawai Jiddah tayi tace "Ae da kai ya kamata ta xauna lafiya ba ni ba, ni ina ruwana da ita tunda ba xamana take ba" Mamakin furucin dake fitowa bakinta upon her age ya dinga yi, and he saw nothing other than sheer jealousy a idanuwanta, ta mike tayi shigewarta bandaki ta bar sa a xaune, shafa kansa yayi thinking of where to start from, can ya mike ya sauka downstairs yana ta xaune parlon har kusan 12 jin footstep a sama ya daga kai, Aneesah ce ta sauko cikin English dressing da veil dinta ta karaso parlon ta xauna ba tare da ta kallesa ba tace "Na shirya" kallon agogo yayi sai kuma yace "Ohkk" ya mike ya tafi sama, dakin Jiddah ya shiga, ya sameta xaune da wani littafi a hannunta, yace "Xa mu shiga gidan neighbors dinmu mu gaisa yanxu, are u ready?" Taki cewa komai, ya karasa ya xauna gefenta ya amshi takardan yayi kasa da murya yace "Shkkn babu wanda xai gaida wani cikinku tunda baki so, i am sorry plss ban san ranki xai baci ba" Rungumeta yayi jikinsa yace "I am so sorry for making u sad wife" Kuka ta sakar masa, lkci daya ya rikice mata yace "Na fa ce kiyi hakuri ni ban san ranki xai baci ba wllh, don Allah kiyi hakuri" Cikin rawan murya tace "Bayan ita ce ta sauko ta gan ni ko sannu da aiki bata ce min ba tun asuba na tashi nake gyara gidan da bata gyarawa, sannan...." Bai bari ta ci gaba ba ya fara kissing dinta. Har aka kira azahar Aneesah na xaune parlon bata ga saukowarsu ba, tana ta xura idon ta ga ya fito xai je masallaci nan ma har aka idar da sallah bai fito ba, ganin karfe daya da minti arba'in ta mike ta wuce sama ta shiga dakinta. Karfe biyu da minti biyar Abuturrab ya fito daga dakin Jiddah sai a sannan ya tuna Aneesah da ya bari a parlor, ya d'an buda ido ya sauka kasa da sauri bai ganta ba, dawowa yayi ya bude dakinta ya ganta kwance tana danna wayarta, ya kasa hada ido da ita, ya dai shiga dakin, kallo daya tayi masa taga wani kayan ya canxa ta dai ci gaba da danna wayarta, still not wanting to look at her yace "Sorry i kept u waiting, i was busy with my laptop, taso mu je" Bai jira me xata ce ba ya fita daga dakin, Jiddah ta fito daga dakinta ta ki yarda ta kallesa kana ganinta kasan ta sha kuka, ta nufi stairs tana sauka a hankali, shi dai da ido ya bi ta, sai ga Aneesah ma ta fito daga dakinta ya sauka downstairs tare da ita, Kallo daya Aneesah tayi ma Jiddah dake xaune kan kujera a parlor ta dauke idonta, abaya ne jikinta da veil dinsa, Abuturrab ya kalli Jiddah yace "Ta so mu je" Daga haka ya nufi kofa, Jiddah ta mike ta bi bayansu. Abuturrab ya xauna a wajen shan isa bayan sun shiga compound din gidan, Aneesah ta danna bell din parlon aka bude kofar wata warce da alamar mai aikin gidan ce ta gaishesu, Jiddah dai ko kusa da kofar bata je ba sbda Aneesah dake tsaye, mai aikin tayi masu Bismillah, Aneesah ta fara shiga parlon sannan Jiddah ta shiga, wata matashiya da baxata wuce shekara talatin da biyar ba dake xaune parlon ta shiga welcoming dinsu tana kallon Jiddah, mai aikin gidan ta tafi ta kawo masu ruwa da lemo, Matashiyar matar dai tana jiran su fadi daga inda suke, Aneesah na wasa da xobunan hannunta tace "Nan makota ne, gidan da yake kusa da naku" Matar tace "Ayya sannunku da xuwa, ai kam ba a ta6a gaisawa ba, bari in kira Hajiyar tana sama" Wata yarinya ce da baxata wuce 19 ba ta fito daga kitchen, Matar tace "Yauwa Khaleesat ce ma Mama tayi baki" Khaleesat tace "Toh" Sai da ta fara gaida su sannan ta wuce sama, Jiddah ta bi yarinyar da kallo, haka ma Aneesah... Matar na kallonsu tace "Yaya da kanwa ce amma" Aneesah ta kirkiri murmushi, Ita dai Jiddah ta sunkuyar da kanta, Aneesah tace "Haka ne" Khaleesat ta sauko mahaifiyarsu na biye da ita a baya, da fara'a ta shiga welcoming dinsu, duk suka gaisheta ta amsa tace "Maa sha Allah naji dadin shigowarku wllh, ina me gidan naku?" Aneesah tace "Yana waje" Tace "Au haba, ce masa ya shigo mana" Aneesah ta mike ta nufi kofa ta fita... Hajiya Fatima tace "Khaleesat xo ga me shige da ke" Matar dake xaune parlon tace "Auu, ashe kema kin lura Mama, wllh tun daxu nake ta kallonta dubi har dimple din" Khaleesat tayi dariya tana kallon Jiddah tace "Ya sunanki?" Jiddah tayi murmushi a hankali tace "Jiddah" Hajiya Fatima tace "Maa sha Allah, amma in ji dai babu wata matsala yanxu jiddah?" Jiddah ta sunkuyar da kanta, Hajiya fatima tace "Duk sanda kika samu lkci ki shigo xan yi magana da ke kin ji?" A hankali Jiddah tace "Toh" Matar dake xaune warce ita ce first daughter din Hajiya Fatima tace "Ashe kin sansu Mama, ni ban ma ta6a lura da su a anguwar ba" Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "Nima shekaranjiya na shiga gidansu, warce ta fita yanxu ai kishiyarta ce"




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp









Duk wannan xancen da Hajiya Fatima da er ta suke, Jiddah dai kanta na kasa sai dai tayi murmushi, Hajiya fatima na kallonta tace "Ko dai baki da lafiya ne Jiddah?" Jiddah ta daga kai da sauri ta girgixa mata kai tace "Lafiyana kalau" Hajiya fatima tace "A nan garin iyayenki suke?" Jiddah ta gyada mata kai tace "Ehh" Hajiya Fatima tace "Allah sarki, yaushe mijin naki ke komawa aiki, naji kakarsa tace pilot ne shi ko?" Jiddah ta sunkuyar da kanta tace "Wani lkcn yana komawa ranan litinin da safe, ko kuma yau da yamma" Hajiya Fatima tace "To idan ya koma sai ki tambayesa ki kara leko mana kin ji" a hankali Jiddah tace "Toh" haka kawai Hajiya Fatima taji Jiddah ta kwanta mata, gashi kana ganin alamarta kasan bata da hayaniya da ma yanda take magana cikin sanyi, a ranta kuwa ta riga ta saka cewar uwargidan ce mai matsalar don a tunaninta Jiddah ce amarya, ita kanta daughter din Hajiya Fatima kallon Jiddah kawai take, Jiddah kuwa ta kagu su koma gida ta kwanta don ta ji bata jin dadin jikinta, taji kamar gabobinta ciwo xa su mata, Hajiya Fatima tace "A kawo maki abinci Jiddah?" Jiddah ta girgixa kai da sauri tace "Aa mama na ci abinci" Aneesah ce ta shigo parlon Abuturrab na biye da ita a baya, Hajiya Fatima ta dinga kallonta sai ta ga ita din ma ba mummuna bace, kawai dai kana gani kasan ta girmi Jiddah sosai, kuma da gani kasan wayewarsu da Jiddah ba daya ba, Abuturrab ya xauna saman kujera ya gaida Hajiya Fatima da first daughter dinta Rahmah, Hajiya Fatima na murmushi tace "Ya gidan fatan komai lafiya" Yace "Alhmdlh" Tace "Toh maa sha Allah, sai ayi ta hakuri Ali, Allah ya ba ku xaman lafiya, ya kauda fitina" Yace "Ameen" Tace "Takwaran naka baya nan yana wajen aiki..." Abuturrab ya kalleta yace "Ohk toh, ina gaishesa idan ya dawo" Tace "Xa a gaya masa in sha Allah" Mikewa yayi yace "Mun gode Mama, just to say hi ne dama" Tace "Haba dai har xa ku tafi, ko ruwa baku sha ba fa" Ya d'an yi murmushi yace "Alhmdlh...." tace "Toh xauna ban gama magana ba" komawa yayi ya xauna, Nasihan few minutes Hajiya Fatima tayi ma Aneesah da Jiddah, sai dai kuma ta fi stressing nasihar tata a kan Aneesah, Aneesah dai ba ma direction dinta take kallo ba amma tana sauraron duk abinda take cewa, daga karshe Hajiya Fatima ta kalli Abuturrab tace "Kai kuma reminder daya xan maka Ali... kayi kokarin xamo me adalci tsakanin matanka in har kana son wanyewa da duniya lafiya" Abuturrab ya sunkuyar da kansa yace "In sha Allah" Tace "That's all i have to say, Allah ya hade kanku, ya kauda duk wata fitina a tsakaninku, idan ma kaga da wata matsalar i am always around kafin dae ayi involving close ones" Da haka suka yi sallama da Hajiya fatima yana kara yi mata godiya, Aneesah ta mike ta bi bayan Abuturrab, sannan Jiddah ma ta tashi tayi masu sai anjima ta nufi kofa, Hajiya Fatima ta bi ta da kallo... Abuturrab na tsaye compound Aneesah ta fito, ya dauke idonsa daga kanta ya mayar kan kofar yana jiran fitowar Jiddah sae ga ta ta fito, kallonta ya dinga yi ganin kamar she is finding it a bit difficult to walk, Aneesah dai ta nufi gate abunta ta fita, yayi lowering voice dinsa bayan Jiddah ta iso inda yake yace "Are you okay?" Bata ce masa komai ba, ya kama hannunta suka fita daga gidan. Jiddah ta xame hannunta daga nasa bayan sun shiga parlon su ganin Aneesah a xaune, ta wuce sama tana tafiya a hankali, Aneesah ta bi ta da kallon gefen ido, kwanciya Jiddah tayi ta rufa da bargo jin kamar xata yi xaxxabi, Abuturrab ya dau makullin motarsa dake parlon yana kallon Aneesah da ta kunna tv yace "Xan fita siyo abinci yanxu, hospital da kika ce kuma I think it will be better a bar shi anjima da daddare tunda gobe xan koma aiki" Ta kallesa tace "Baxan iya jira har dare ba saboda ni kadai nasan me nake ji a jikina" Ya dinga kallonta yana juya key din hannunsa, sai kuma yace "Nan da awa nawa ne daren xai yi idan Allah ya yarda?" Tace "Kaga Captain.... ni bance lallai sai ka kai ni asibiti ba, idan ka dawo daga siyo abincinku ka bani makullin mota kawai in kai kaina asibiti ba wani big deal bane, ko kaji na tilasta maka ka kai ni hospital?" ya mata wani kallo ya juya ya fice daga parlon, ta hararesa sannan ta ci gaba da kallonta, tana ji motarsa ya fita gidan, ta kalli hanyar stairs, ta fi minti biyu tana kallon saman deep in thought taji an kara bude gate din gidan, ta juya da sauri sai kuma ta mike ta isa window tana leka waje, kallon babbab motar da ya shigo na sababbin furnitures ta dinga yi babu ko kiftawa, ta koma da sauri ta xauna a parlor, knocking aka yi bakin kofa ta ki tashi balle ta bude, sun kusa minti biyar a tsaye suna kwankwasa kofar, ita dai ko motsawa bata yi ba daga inda take, ta kalli wayarta dake ringing bayan wani minti biyar din, ganin me kiranta tayi silencing wayar ta ajiye a gefe, ya sake kira ta ki dagawa daga karshe ta mike ta haura sama, kallon kofar dakin da Jiddah take tayi kafin ta shige nata dakin ta kulle, har sai da Abuturrab ya dawo daga wajen da yaje siyan abinci sannan ya bude ma masu kawo furnitures din gidan suka shiga, yana xaune parlor suka dinga fitar da fasassun kayan dakin Jiddah suna sakawa a motar bayan sun sauke sababbin, ya mike jin mota ta shigo compound din ya fita waje, motar Ahmad ya gani, and he couldn't help it but smile, yana tsaye har Ahmad ya sauko, Ramlah ma ta fito daga cikin motar, Ahmad yayi er dariya bayan sun hada ido ya nufosa yace "This is serious.... kaga wani fresh da kayi kuwa Captain?? Meye haka Jiddah ke baka?" Abuturrab ya shafa beard dinsa a hankali yace "Abinda ya kamata ta bani" Dariya kawai Ahmad yayi, giving him a hug yace "I guess yanxu kasan kayi aure right?" Abuturrab ya dage girarsa murya kasa kasa yace "I am telling u" dariya kawai Ahmad yake yana gathering tsokanar da xai yi ma Abuturrab a xuciyarsa amma ba yanxu ba, Ramlah ta karaso wajen ta gaishe da yayan nata da ladabi ya amsa mata, ta shiga parlon, Ahmad yace "Ina matan naka?" Murmushi Abuturrab yayi ya juya ya shiga ciki Ahmad na biye da shi, stairs Abuturrab ya haura ya fara bude dakin Jiddah ya ganta kwance tana bacci, ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login