Showing 255001 words to 258000 words out of 346625 words

Chapter 86 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

@โ‚ฆ1800*
*10GB. @N3000*
*15GB. @N4500*
*20GB. @N6000*
*30GB. @N9000*
*(Valid for 30days)* Check your data
Balance through, *461*4#* OR
*131*4#*
*AKWAI DATA NA SAURAN NETWORK*

*CALL/SMS 09037037040 or WHATSAPP No 08183611133
๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
*MTN 1GB @ 300*

*biyan kudi taโœ”Bank ne*
*ACCOUNT NUMBER:*
*1500981702*
*ACCOUNT NAME: AISHA MUHAMMED HERITAGE BANK







Aneesah ce tsaye bakin kofa tana kallon bedroom din Abuturrab da mamaki, shi dai yana kishingide saman kujera a parlon yana danna wayarsa ko kallon inda take bai yi ba, can ta dawo cikin parlon da sauri tace "Captain ina kayan dakina??" Sai a sannan ya ajiye wayarsa ya kalleta yace "Among the four rooms out there, though na kulle guda daya, so u can chose from the other 3" Kallonsa ta dinga yi babu ko kiftawa, ganin ya ci gaba da danna wayarsa tace "Meye dalilin ta6a min kaya ka fitar daga nan bangarenka ba tare da izinina ba Captain?" Ya kalleta yace "Saboda bangarena ne nan ba na matana ba, here is my comfort zone alone, amma a duk sanda na bukaci ku xa ku xo nan din ai...." Aneesah tace "Walakancin naka har ya kai haka Captain?? Ni xaka yi ma wannan walakancin?" Sai kuma tayi wani murmushi ta fice fuuu, dakunan dake corridor din after staircase ta shiga budewa taga furnitures dinta a ajiye ko jerawa ba ayi ba a daya daga dakunan, duk sai da ta bi sauran dakunan ta bude, amma banda guda daya wanda shi bathroom da toilet din dake ciki ba shi da banbanci da na bangaren Abuturrab, sannan the room is a bit bigger than the rest kuma a wannan dakin Safara'u take xama, shi kadai ne a kulle cikin rooms din, Aneesah ta juya fuuuu ta koma side din Abuturrab, tana huci tace "Toh shi kuma wancan dakin da ka kulle fa??" Ya gyara xamansa yace "Na uwar gidana ne" Still tayi tana kallonsa, sai kuma tace "Uwar gidanka???" Yace "Yeaa because i married her before u, kuma tace wannan dakin take so.. rashin adalci kike son inyi?" Aneesah ta girgixa kai cike da bacin rai tace "Wllh baxan yarda ba wannan dakin da ka kulle shi nake so sai dai duk tsiyar da xa ayi ayi, ni xaka raina ma wayo kace uwar gidanka?? Wllh baxan yarda ba Captain, yaushe ka koma ka aureta din da ta xama uwar gida??" Ya mike yace "Kafin in aureki na koma na aureta, look idan any of the room except d close one basu maki ba Aneesah, xaki iya kwasan kayanki ki kai downstairs ai akwai daki sannan duk ya fi na sama girma" Daga haka ya fice daga parlon ya bar ta tsaye, Aneesah ta bude baki ta bi sa da kallo xuciyarta na bugawa, murmushi kawai Abuturrab yake yana sauka downstairs, he never thought Aneesah will calm down so quickly, bai ta6a tunanin xata amince da cewar Jiddah matarsa ce babu wani gagarumin tashin hankali ba, duk bata yi abinda yayi tunanin xata yi ba, kuma yayi mugun mamakin da har ta amince taje ta ba Jiddah hakuri domin ta dawo gidansa, this is something he never expect from her, although yasan tana sonsa amma bai yi tunanin to this extent da xata yarda su xauna da Jiddah a matsayin kishiyarta duk kiyayyar da take mata. Aneesah ta shige dakinsa ta xauna kasan carpet ta fashe da wani matsanancin kuka kamar ranta xai fita, yanxu a hakan ma duk hakurin da tayi Jiddah ce uwar gida ba ita na? Anya xuciyarta xai iya daukan wnn takaicin da bakin ciki kuwa, handbag dinta ta jawo tana kuka sosai ta shiga kiran line din Aunty dake can gidansu a Abuja yanxu haka, banda ma tausan da ita Auntyn da Safara'u da Uwarta suka dinga mata ai ita ba kwana kusa ta so dawowa ba, amma duk sun addabeta ta dawo kar ta ji komai, sai da wayar Aunty ya kusa katsewa snn ta daga, Aneesah ta kuma rushe mata da matsanancin kuka tace "Aunty wllh baxan iya ba xuciyata xata fashe, Aunty wai fa ce min yake ai ita Jiddar ce uwar gida sannan duk ya kwashe kayan dakina daga bangarensa ya kai wani dakin, ita kuma ya kulle mata wannan babban dakin da Aunty Safara'u take ciki, ni dai wllh Aunty xan iya mutuwa idan na ci gaba da sauke kaina kasa kamar yanda ku ka ce, wayyo na shiga uku wllh baxan iya sharing captain da wata shegiya ba, wllh Aunty na tsaneta ban ki in kasheta ba Allah ya sani" Aunty dake ta sauraronta tace "Wai me yasa ke ba a isa a gaya maki magana ba Aneesah, ance maki haka nan muka turaki ki koma dakin ki?? Ba dai ni nace ki kwantar da hankalinki ba to me xai dameki? Nace maki duk abinda yace kice masa toh kawai babu musu, xai ci kaza kazansa ne wllh, ai yau Uban nasa xai xo wajena a Abuja, bayan abinda muke yi ta karkashin kasa shi ma da abinda xan gaya masa idan mun hadu, kuma duk a kan batun nan, ki kwantar da hankalin ki kawai Aneesah, ubansa ma ya kasa nutsuwa tun da na bar masa gida duk da ya maida ni balle wani Aliyu karamin alhaki, in sha Allah yau Abban nasa xai shigo wajena a nan Abuja nace maki, kar ki ji komai ki kwantar da hankalin ki xan yi duk abinda ya kamata" Kuka kawai Aneesah take tana kara regretting irin downgrading kanta da tayi wai taje har gida ta ba Jiddah hakuri, sai taji da ma hatsari tayi a hanya bata karasa gidan ba da dai hakurin nan da taje ta bata, she felt so downgraded, wato yanxu Jiddah will now feel belong and important tunda anje an bata hakuri, Aunty ta katse mata tunaninta tace "Kina ji na kuwa Aneesah?" Cikin shessheka tace "Ina ji" Aunty tace "Toh kiyi hakuri, ba cutarki muke ba da muka ce ki kwantar da kanki ai komai na da dalili, yanxu dai ki samu wa enda za su jera maki kayan gadonki a dakin da ya baki, lkcn da xai kwashi kayan naki ya maida bangaren nasa da uban wa xai yi shawara, ke dai sai anjima kawai muna nan muna maki shiri yar nan" daga haka Aunty ta katse wayar, Aneesah ta dinga kwalla tana jin mugun tsanar Jiddah har ranta, she hate her uncontrollably, wllh ita fa xata iya bindigeta idan an bata bindiga take ji.... Umma ce parlon Ummi tana ta danna wayarta tana jiran fitan Hajja tayi ma yar uwartata maganar da ya kawota ta wuce gida don akwai inda xa ta, tun da Hajja ta kyallara ido taga shigowarta gidan ta biyo ta parlon Ummi, kuma taki fita gashi har anyi awa daya, Hajja ta gyara xama tace "To shi Usman din yace maki xai yi tafiya kuwa ko bai ce maki ba Hauwa? Ni dai ya shigo wai yana da wani meeting a Habuja" Ummi tace "Ehh haka ni ma yace min jiya" Hajja ta kyabe baki tace "Toh shi har wani saninsa aka yi a Habuja da xai je wani meeting? Da su wa xai yi meeting din, wllh baku ga yanda ya dinga bani hakuri yana rokona gafara ba da ya shigo, ni dai nayi shiru abuna, kun dai ga ya je yayi kulle kullensa ya sa Aliyu ya maida aurensa da Nanisa, to har da hakurin nan ya dinga bani wai an sasanta lamarin kuma ita Nanisar taje har gida ta ba Jiddah hakuri, snn mu ma nan ta xo ta bamu, ni dai kar a kirani da fitinanniyar uwa shi sa nayi shiru ba ruwana, amma Nanisa ai ba matar xama bace, duk da dai abinda yasa na hakura bai wuce Jiddah da take matsayin matarsa ba ita ma yanxu, tsaf xata dinga masa duk abinda yake so, xata tsaftace masa muhalli da abinda xai ci babu ganda, kinga kuwa daga nan ai ta kwace miji a hannunta, mu ma duk haka muka yi muka tsira, tsaftar mu ce ta kwace mu wllh...." Babu dai wanda ya tankata a cikinsu, Hajja tace "Toh ni dai ba ruwana da duk wannan, damuwata yanxu kawai Aliyu da baki yayi ma yawa wllh, kowa ya bude bakinsa me tsamin gaske sai yace Aliyu kamar dai ya kashe d'an mutum, wllh wnn abun na hanani bacci, shi kuma idan ka basa hayaki sai ya ki yi, ba wai fa hayakin tsafi bane, ko su wannan garin habbatus saudan ai ana turarawa domin miyagu... balle ma wanda xan basa ba boka bane ya bani, ina ga dai da kaina xan dinga xuwa ina turarasa da hayakin, kafin nan Jiddah ma ta tare ita ma duk in hadasu in masu, don wllh wllh duniya ba gaskiya yanxu miyagu sun yi yawa ta ko ina, Ko Nanisar nan ban yarda da ita ba Allah" Ta gefen ido Umma ta kalli Hajja amma bata ce komai ba, Hajja ta rike kai tace "Huhuhu... Abun na damuna wllh, wani sai kaga ya ci ado ya yafo katon gyale ya sa kwaba suu, ya kona fetur dinsa ya fito tun daga gida duk don kawai a raya dumi da gurmi, shi dai Aliyun nan komai yayi dai dai ne wllh tunda ba sata yayi ko kisan kai ba, aure fa kawai yaje aka daura masa babu shawara da ko wani shege, amma duk an sa shi a bakin duniya kamar wanda yayi wani axababben laifi, wllh daxu da ya xo gaisheni baku ga kyan da yayi ya d'an murmure ba, dubu biyar ya ajiye min a dinga saka min kati ga alkawarin turare da yayi min, to wa xai min haka banda shi din dama? Shi Bashir dama yana can yana lalatansa da mata a kasan turawa shi sa ku ka ji na ja bakina nayi shiru da xancensa da Jiddah, Atoh ba ruwana ni kaina nasan iskanci yake yi, ni kuma ai baxan so abinda xai cuci er yarinyar ba, balle ma figaggiyar uwarsa tana nan da girman kai kamar dawisu ba son yarinyar take ba wllh, kowa na murmurewa ya dawo d'an duma duma da shi yayi kyau kamar Ramlah, amma ita tana can kamar sandan agwai taki gaba taki baya duk da uban dukiya da aka tara sbda mugun halayen da take a masarautan, to ba ruwana da xancen da bai shafeni ba ta kaina nake, amma gaskiya kowa ya cire baki da idonsa a kan Aliyu, Jiddan nan dai matarsa ce ba farkarsa ba, to meye wnn fitina da bala'i fisabilillah, har ana kona man fetur a xo ayi da shi, To ba ruwana gulma dai ajalin me shi ce" daga haka ta mike ta fice daga parlon ta wangale masu kofa. Murmushi kawai Ummi tayi don sarai tasan da Umma take, Umma da ta hade rai ta mike ta kulle kofar ta dawo tace "So take in biyeta ni kuma ba da ni ba wllh" Ummi tace "Ai kam sai hakuri Hajja, da ma ina son xan kiraki sai gashi ma kin xo..." Umma tace "Ehh kuma ba dadewa xan yi ba da akwai inda xa ni, gashi duk Hajja ta 6ata min lkci wllh" Ummi tace "Ki saurareni Ramlah, ina son don Allah kiyi hakuri ki bari Jiddah ta tare a dakinta, tunda har ya gano kuskurensa ya kuma yi nadama, main point a nan da Aliyu baya sonta babu abinda xai maida shi sake aurenta, don haka nake son komai ya wuce ta koma dakinta don Allah, ba wai ina magana on Behalf of Aliyu bane, Aa kawai ina magana ne sbda naga ya dace, mu ba kananun yara bane" Umma dake ta kallonta tace "Ummi yanxu Abuturrab har kin ga alamar ya gano kuskurensa yayi nadama? Kina nufin kawai a basa ita a banxa yaje ya ci gaba da walakantata daga inda ya tsaya yaya? mutumin da har yau bai fito direct ya fadi dalilin da ya sa ya koma ya sake auranta ba sai kame kamen rainin hankali da yake, komawa fa yayi ya aureta don yana son xama da ita ba don yana sonta ba?? Kawai don bata da gata sai a mata haka yaya? Ni wllh sai duk banji dadin da wannan ya fito daga gareki ba, Yarinyar da ko waec din bata xana ba?" Ummi tace "Toh yanxu ina amfanin xuwa da yayi ya dauketa ya kai ta gidansa ta kwana sannan ya maido maki ita?? haka kike son a ci gaba da yi ko ya?" Umma tace "Toh ai haduwarmu nake jira da shi yaya, wllh haduwarmu baxai yi kyau ba, sai na masa rashin mutuncin da xai dade bai manta ba, wnn shawara taki kuma bata gamsheni ba kwata kwata yaya, don har yanxu ban yarda Abuturrab ya saduda ba, yana nan a d'an iskan da muka sansa wllh" Ummi dai sai kallonta take, Umma tace "Ita wancan mara tarbiyar an sa ya maidata, to ana nufin ma gida daya xa su xauna tare da Jiddar su kasheta a banxa yarinya ba wani bakin kirki ba?? To kuwa sai dai aki tarewan har abada wllh in dai gida daya xa su xauna da mahaukaciyar matar nan tasa" Ummi tace "Toh wani gidan garesa a Kaduna da xai raba su Ramlah?" Umma tace "Wllh shi ya sani, Jiddah dai baxata xauna gida daya tare da matarsa ba, idan ma haya ce yaje ya nema mata amma sam babu xancen xamansu gida daya da Aneesah, yarinyar da babu Allah a ranta?? Aa wllh baxai yiwu ba, Jiddah baxata iya xama da ita ba" Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh indai batun xama gida daya ne xan masa magana a san abun yi sai kar a hadasu din, amma batun wai Jiddah baxata tare ba yanxu ki janye wannan batun Ramlah, ai ana karatu a gidan miji, ke a ina kika yi karatun ki? Ni kaina a ina nayi furthering karatuna, don haka wnn ba hujja bace, tunda Hajja ma ta dage kan sai ta tare xuwa next week in sha Allah xa ayi ma Jiddah duk abinda ya kamata ta tare gidan mijinta, Allah ya basu xaman lafiya da xaman hakuri kuma, shkkn fatanmu" Umma ta bude baki tana kallon Ummi kafin tace komai Ummi ta girgixa kai tace "Bana son kina min musun nan Ramlah, ni xan cuci Jiddah ne, ko kuma xan yarda Aliyu ya cuceta? Yanda na fada haka xa ayi, batun xama gida daya ne kawai xai xo in shaida masa baxai yiwu ba... Idan ya so ko driver ne sai ya samar mata ya dinga ajiyeta a makaranta kullum, shkkn na gama maganata ni kam bana son wani maganan"
Aunty ta gama kada ma Abba shayi a hotel room din da ya sauka tana kallonsa tace "Amma sai jibi dai zaka koma ko Yallabai" Abba dake duba laptop dinsa yace "Allah ya kai mu" Tayi wani murmushin kissa tace "Ameen, amma akwai wata muhimmin magana da nake son yi maka Yallabai a kan Aliyu" Abba ya daina abinda yake a laptop yace "Ina jin ki" Tace "Kaga dai wannan yaro kawai xuwa yayi yace mana ai ya koma ya daura aurensa da Jiddah, ba a san ko shiryawa yayi duk domin kada a rabasa da yarinyar ba, snn wa ya kai ma sadakin in har da gaske ne an sake wani auren, don haka Yallabai kamata yayi a tisa keyarsa a tafi hayin gun wanda ya daura masa auren don a tabbatar, daga nan ai yace kishiyar uwar yarinyar na raye sai ya kai ku a gana da ita ma, ba wai ayi ta xama haka kamar bamu da ilimi ba, kasan dai yaran yanxu ba wani tsoron mahaliccinmu suka cika ba, to gwara dai a tsananta bincike kada suje su yi xama na haramun da yarinya, mu ma sai laifin hakan ya shafemu tunda bamu xurfafa bincike ba" Abba na gyada kai cike da gamsuwa yace "This is true, ina komawa kadunan in sha Allah xai kai ni da Alhaji Lawal wajen shi wanda ya daura masu auren, wannan gaskiya ne Hafsah" Aunty tace "Atoh, don Aliyu kam ya xama abun tsoro wllh, abunsa yake kai tsaye babu shakkan kowa, ko wa ya koya masa haka oho kamar dai wanda ake xugawa" Abba yace "Wannan ba damuwa bane gwara da kika tunatar da ni, tun farko ma abinda ya kamata ayi kenan" Abba ya ci gaba da danna laptop dinsa, Aunty tayi murmushi tana ci gaba da juya shayin da cokali a hankali. Abuturrab na xaune parlon Umminsa bayan ta gama fadin abinda xata fada ya dago kansa yace "To Ummi, xan ajiye daya a nan kaduna daya kuma ta xauna a gidana na Abuja in sha Allah..." Ummi tace "Toh hakan dai ya fi, idan Allah ya yarda xuwa next week din sai Jiddah ta tare..." Abuturrab yayi shiru bai ce komai ba, bai ta6a xaton haka da wuri ba, bai ta6a tunanin it will be this easy ba, sai kuma ya kalleta a hankali yace "Toh Ummi ai Umma ce...." Ummi tace "Aa Umma ba matsala bace na kirata nan munyi magana, ya rage naka kuma ka xama me tsoron Allah kayi adalci tsakaninsu Aliyu...." Farin cikinsa ya kasa boyuwa, cikin sanyi yace "Toh nagode Ummi, Allah ya saka da alkhairi Allah ya kara girma, nagode Ummi" Ummi tace "Ameen, sadakin nata fa??" Abuturrab ya sauke kansa yace "Mai anguwan ya bani in taho mata da shi tun a lkcn yana wajena, i bought her gold" Ummi tace "Toh maa sha Allah, hakan yayi kyau sosai, amma fa ga wata er shawara, ka rike Ahmad d'an uwanka da kyau, coz he made everything easy as it seems to u, he made sure he convince each and everyone... barin dai Hajja, a da na dau alwashin cire hannuna a lamarinka tunda kai baka shawara da mutane kanka tsaye kake aikata abinda ya xo maka, worst of


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login