Showing 312001 words to 315000 words out of 346625 words

Chapter 105 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

ma da ta siyar ance ko dubu hamsin bata tsira da shi ba sbda duk bashin lapo ta biya, kuma har yanxu da nake maki wannan magana mutane sun fi ashirin da take bi bashi a hayin nan, ta tsallake kawai ta bar garin, an dai ce hakkin er marigayin mijinta ke bibiyarta, mu ma haka muka ji, wllh babu wanda yasan inda take" Hajiya Fatima tace "Toh Allah ya kiyaye Allah ya kyauta" Suka amsa da "Ameen" Hajiya Fatima da su Aunty Rahama suka juya suka koma gun motarsu, Jiddah dake cikin motar sai kallon wasu mutane da suka fito daga gidansu a maimakon babarta da Bibalo take, nan da nan taji gabanta ya fadi, Hajiya Fatima ta bude bayan motar tana kallonta, sai kuma tayi kasa da murya tace "Babu wani naku a unguwar nan bayan stepmum din taki Jiddah?" A sanyaye Jiddah tace "Basa gidan kuma ko Mama?" Hajiya Fatima tayi shiru tana kallonta, sai kuma a hankali tace "Ta siyar da gidan, ta bar garin" Jiddah bata san lkcn da ta fashe da kuka ba, Hajiya Fatima ta hade rai tace "Meye haka kuma? Meye na kuka? Kukan naki ne xai dawo da ita" Jiddah ta girgixa mata kai tana share idonta wasu hawayen na xubo mata tana tausayin rayuwarta kuma, Hajiya Fatima da duk jikinta yayi sanyi tace "Wa kike tunanin a unguwar nan gaba daya xai iya sanin inda ta tafi ko inda ta koma?" Jiddah na share idonta da kyar tace "Kila Iyah, ga gidanta can" Hajiya Fatima ta sa ta sauko daga motar suka nufi gidan Iyah gaba dayansu, banda Aliyu dake jingine jikin motarsa, sosai shi ma yake tausayin Jiddah... her story is heartbreaking, no relatives, no siblings, no parent, nothing nothing, what a life, Jiddah ta rungume Iyah bayan sun shiga gidan, Iyah ta kasa boye farin cikinta ta rasa inda xata sa Jiddah tsabar murnan ganinta sai ta fara hawaye, Hajiya Fatima dai kallonsu kawai take tana tsaye daga gefe da Aunty Rahama, Iyah ta farga da su ta dauko tabarma da sauri bakinta har kunne ta shimfida masu tace "Sannunku da xuwa, kun xo bamu da wutan nepa, fitina kuma batur yayi sanyi, ku xauna don Allah" Hajiya Fatima ta xauna, Aunty Rahama ma ta xauna sannan suka kara gaisawa, Iyah na kallon Jiddah dake xaune ita ma tayi nisa tunanin da take tace "Jiddah Hansai dai ta siyar da gida ta bar garin..." Jiddah ta sauke idonta kasa wasu hawayen na taruwa idonta, A Hankali Hajiya Fatima tace "Haka muka samu labari kaka, domin can muka fara xuwa kafin nan, yanxu kaka baki da masaniyar inda ta koma" Iyah tace "Ai babu wanda yasan inda wannan mata dai ta koma, duniya tayi mata xafi, kowa ya juya mata baya, er ta kuma Bibalo ta dauko mata abun kunya, ko kafin su bar anguwan nan bibalo Haihuwa yau ko gobe, abun dai babu dadin fadi, Hansai na cikin gararin rayuwa yanxu..." Hajiya Fatima tace "Ya salam, Allah ubangiji ya bamu dacewa..." Iyah tace "Ameen, alhakin Jiddah kadai ya isa hanata xaman lafiya a duniya duk inda xata je kuwa, haba ai Allah ba axxalumin bawansa bane, ta xalunci yar nan da kike gani, ta xalunci uwarta... Duniya kam ta juya ma Hansai baya, ita kanta kawarta me xuxxugata tana can ciwon kafa ya sa ta gaba ana tunanin yanke kafar ma xa ayi, bata iya xuwa ko ina, Zulai ba" Jiddah dai sai kallon Iyah take hawaye na sauka idonta, Hajiya Fatima tace "Toh ita zulan yanxu bata san inda Hansatun take ba?" Iyah tace "To sai dai ko gobe in shirya inje in jiyo maku, amma babu tabbas ta sani, in sha Allah ni dai xan je" Hajiya Fatima tace "Mun ko gode kaka Allah ya kara girma" Dubu uku Hajiya Fatima ta ajiye ma Iyah daga haka suka yi mata sallama da xummar gobe xa su dawo su ji yanda suka yi da Zulai a kan whereabout din Hansai, har suka koma gida Jiddah jikinta a sanyaye yake sai goge hawaye take a idonta, Hajiya fatima ta sa yayar Khaleesat ta kawo mata dinner don bata ci ba kafin su fita. Karfe tara da yan mintuna that same day Abuturrab yayi horn bakin gate din gidansa, Mai gadi ya taso da sauri ya bude masa gate din ya shiga yayi parking sannan ya sauka, gaba daya a gajiye yake, kwanan nan stressing kansa yake sosai na kai wa da komowa da yake xuwa kaduna, ya shiga ciki yana jin shoulders dinsa na ciwo saboda driving da yayi, sama ya tafi ya bude kofar dakin Jiddah ya shiga ciki, ya dinga bin dakin da kallo kafin ya juya ya fita, dakin Aneesah ya nufa ya murda kofar ya ji sa a kulle, mamaki ne ya cikasa, ya tafi bangarensa ya xauna, bayan minti sha biyar ya mike ya sake komawa dakin Jiddah don a tunaninsa daxu tana bathroom ne, ganin har sannan bata cikin dakin ya karasa ya tura kofar bayin yaga wayam babu kowa ciki, juyawa yayi ya sauka kasa da mamaki, ya shiga kitchen yaga babu kowa ciki nan ma, ya fito yana bin parlon da kallo cike da surprise, Ya kalli agogo dake nuna goma saura ya nufi kofa ya fita, gun mai gadi ya tafi mai gadin ya taso da sauri ya sake gaishesa, bai damu ya amsa ba yace "Babu kowa gidan... Da yaushe suka fita?" Mai gadin yace "Toh ita dai Hajiya daxun nan bayan magriba ina sallah naga fitarta, ita Hajiya karama kuma gaskiya tun da safe naga fitowarta kamar da matsala don hankalinta ma baya jikinta ta fito, ina tambayarta lafiya ma bata saurareni ba ta fita gate, sai na tafi da sauri in ga meke faruwa, to ni dai ban ga kowa a parlon ba ma" Abuturrab ya rasa ma exactly tunanin da xai yi ya dinga kallon mai gadin xuciyarsa na bugawa, juyawa yayi da sauri ya koma ciki ya dau wayarsa ya shiga kiran Maimoon tana dagawa yace "Jiddah tana gidanku ne?" Maimoon tace "Jiddah kuma? Aa yaya bata nan, lafiya?" Strictly yace "I am not joking" Tace "Wllh Allah bata nan yaya" he was shock at that, yace "Look, bance kice da Umma komai ba" Daga haka ya katse wayarsa ya kira Nafisah ita ma tambayar da yayi mata kenan tace bata xo ba, lkci daya ya ji hankalinsa yayi mugun tashi, ya juya da sauri ya fita ya koma gun mai gadi yace "Ita warce ta fita da safen ina kaga ta nufa?" Mai gadin yace "Yallabai ai ina ganin yanda ta fito kamar da matsala cikin gidan sai na yi cikin gidan da sauri, wllh ban san inda tayi ba, kuma ko da na fito babu alamarta" Abuturrab ya ji wani xufa na keto masa duk da yanda garin yayi sanyi don da akwai hadari, he was shock, a xuciyarsa ya dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ya nufi gate ya fice daga gidan direct ya tafi gidan Hajiya Fatima....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp






Abuturrab na shiga compound din gidan ya tafi entrance din parlon yayi knocking, he is just trying his very best to be calm, mai aikin gidan ta bude kofar, ta gaishesa bai amsa ba yace "Mama na ciki?" Tace "Eh Bismillah" shiga parlon yayi ya xauna saman kujera, sosai ya ji kansa ya masa nauyi dama ga gajiyar da yake tare da shi, Mai aikin ta tafi dakin Hajiya Fatima, bayan kusan minti biyar Hajiya Fatima ta fito parlon ganinsa tace "Aa, ashe kai ne, welcome son" Ya daga kai ya kalleta ya kasa cewa komai, ta xauna saman kujera cikin sanyin murya yace "Ina yini Mama?" Tace "Lafiya lau, ya su Jiddah da abokiyar xamanta" Bai san lkcn da ya kara gyara xama ba xuciyarsa na bugawa yace "Mama Jiddah bata shigo nan ba?" Hajiya Fatima tace "Jiddah kuma? Tace maka xata shigo nan ne?" Rike kansa yayi ya kasa bata amsa, ita dai sai kallonsa take, can tace "Aliyu" ya dago da kyar ya kalleta tace "Ina Jiddar tace maka xata je?" Cike da confusion yace "Mama daga wajen aiki nake yanxu haka... I have to drive all the way from Abuja after piloting d whole day..." Rasa ma takamaiman abinda xai ce mata yayi, sai kuma ya dafe kansa yace "Ban san inda ta je ba, ban san me ya faru ba, i called home duk ance bata je can ba, bata da wajen xuwa kuma da ya wuce can..." Mikewa yayi ganin he is just sounding foolish, ba abinda ya ke fada da yake making sense, bata lkci kawai yake karawa gashi dare yayi, to shi a ina xai ga Jiddah? Ina Jiddah ta je? He felt like he is going to collapse, lamarin yayi ma xuciyarsa nauyi, ya rasa exactly tunanin inda Jiddah xata je da xai yi, is this really happening, gaba daya ya ma mance batun Aneesah ma bai ganta a gida ba, gathering much courage yace "Sai da safe Mama, dama na xata nan ta shigo" Juyawa yayi yana jin kafafuwansa sun masa nauyi ya nufi kofa, tace "Aliyu" ya juyo ya kalleta, tace "Me yasa xaka bar Jiddah da matarka kadai a gida bayan kasan halin wannan ita matar taka?" Dawowa yayi da sauri xuciyarsa na bugawa, tace "Why Aliyu?" Ya marairaice mata yace "Mama ta shigo nan ne? Wllh ban san abinda ya faru ba, daga Abuja nake few minutes ago ban tadda kowa a gidan ba" Hajiya Fatima tace "Tashin hankali Abokiyar xamanta ta nemeta da shi shine ya shigo nan, don ko takalmi balle mayafi babu a jikinta ta shigo gidan nan" Abuturrab ya buda ido sosai yana kallonta so speechless, Ta girgixa kai tace "Sakacin yayi yawa Aliyu, ganganci ne barinsu su biyu kadai a gidan nan, a da ni banyi niyyar nuna maka Jiddah tana nan ba sbda naga kamar u are not ready to take any action, it's not as if i am trying to intrude into ur privacy amma naga bai kamata in xuba ido ba a matsayina na babba, ba wai ina maku shisshigi bane amma lamarin abun dubawa ne kada wataran ayi kisan kai" Ya duka gabanta without knowing he did so yace "Don Allah yanxu tana cikin gidan nan Mama?" Hajiya Fatima tace "Tana nan" Mikewa tayi ya bi ta da kallo har ta wuce ciki, ya sauke wani irin ajiyar xuciya ya rufe idonsa sai dai har yanxu xuciyarsa bai dawo dai dai ba, bayan kusan minti hudu Hajiya Fatima ta shigo parlon tare da Jiddah dake biye da ita a baya, Jiddah na hada ido da Abuturrab dake kallonta ko kiftawa babu ta sunkuyar da kai fuskarta babu walwala, Sounding so grateful yace "Nagode Mama Allah ya kara girma..." Tace "Aa ba ka gode ba, so kake matarka ta kasheta ne ko kuwa kana da wata manufarka daban na barinsu a gida daya?" Ya marairaice mata yace "Not at all Mama..." Tace "Toh tashi ka dau matarka ku tafi, xa mu yi magana gobe" Godiya ya dinga yi mata kamar warce tayi masa albishir da aljanna, infact shi tunda yake bai ta6a yi ma mutum irin godiyan nan da yake mata ba, sai taji ya bata tausayi kana ganinsa kasan matan nan nasa suna basa tension, Hajiya Fatima tace "Ku tafi Jiddah sai da safe, xan shigo in sha Allah da safen" Mikewa Abuturrab yayi yana kallon Jiddah da taki yarda ta hada ido da shi, babu yanda ta iya haka ta bi bayansa tana jin kamar ta fashe da kuka har ranta taji bata son xaman gidan, duk da yayyafin da aka fara, haka suka fito compound din ya kama hannunta kamar xa a kwace masa ita suka fita gidan sannan suka shiga nasu, suna shiga parlor ya kulle kofar ya rungumota jikinsa gam, ya runtse ido da damuwa yace "Me yasa kike bani wahala haka Jiddah, me yasa kike sa min ciwon xuciya? Kince ban maki komai ba duk xaman mu na farko balle ko ince ramawa kike yanxu, why are u giving me heart attack jiddah, tell me pls wife, kin ki barin in nutsu in yi aikina, so kike a bani query Jiddah? Do u want me to lose my job?" Tayi shiru tana jin yanda xuciyarsa ke bugawa, ga kamshinsa da ya cikata, lumshe ido tayi ita ma xuciyarta na bugawa, ya dago kanta a hankali yace "Me ya faru kika fita gida just like that? tell me plss" Hawaye ya kawo idonta a hankali tace "Nemana take da fada a ko da yaushe" yace "Me ta maki? Tell me" Cikin sanyin murya tace "Daxu da safe na sakko xan shiga kitchen shine ta xageni ta xagi iyayena, kuma har da marina" Ta fashe masa da kuka, lkci daya mood dinsa ya koma na bacin rai karara, yace "Ta mareki?" Cikin kuka tace "Ehh shine ni kuma ta kwala mata wancan vase din na fita parlon" Ya rungumeta bai ce komai ba yana tunani iri iri a ransa, hannunta ya kama suka wuce sama, ya tafi bangarensa ya dau wayarsa ya shiga bedroom dinsa ya dau spare key sannan ya fita, Jiddah dai na tsaye parlonsa ta bi sa da kallo har ya fita, ta xauna a hankali gefen kujera, bude kofar dakin Aneesah yayi yana kokarin dialing numberta, har ya katse mata daga ba, ya sake kira yana bin dakin nata da kallo, dagawa aka yi daga daya bangaren, murya kasa kasa tace "Hello my Captain" Yace "How are you?" Tace "Lafiya lau My captain, are u missing me this much?" Yace "Ya jikin yanxu?" Tace "Yanxu na sha magunguna na na kwanta har na fara bacci kiranka ya tasheni" Yace "Ohk kina daki ne?" Tace "Ehh wllh, ina daki a kwance" yace "Ohk can u go give Jiddah the phone plss?" Tace "Why not my captain, Allah ya sa ta karba din, bari in kai mata" Shiru yayi bayan wani lkci yaji tana cewa "Assalamualaikum, Jiddah, Jiddah..." Sai kuma tace "Ohh kofar ma a bude take ashe, bari in Shiga" Shi dai yayi shiru yana sauraronta xuciyarsa na throbbing, ya ji tace "Captain bata ciki fa, na duba bathroom ma ban ganta ba, let me check downstairs" Ya dake yace "Ohk" again bayan wani lkci tace "Bata nan wllh captain, and I can't even see her shoes da ta bari bakin kofa daxu da ta shigo, probably taje siyo abu ne a waje" yace "Ohk, gobe da safe xan dawo in sha Allah" Tace "Toh Allah ya kai mu my captain" Katse wayar yayi ya xauna gefen gado yana jin wani mugun bugawa da xuciyarsa ke yi, is this for real? Wait ina ma ta tafi tukun? Bai san sanda ya bude baki ba mamaki kaff ya gama cikasa, sai yake ganin abun kamar film, Aneesah?? Ya kara bin dakin nata da kallo ya kalli xanuwan gadon da suke xube a kasa, mikewa yayi ganin sachet kusan hudu dake xube daga gefen xanin gadon ya karasa ya durkusa ya dauka yana dubawa, sai dai xuciyarsa ya daina aiki na kusan second biyar, ya dinga kallon sachet din babu ko kiftawa da wani expression da ya fi kama da na shock, juyasu ya dinga yi yana kallonsu kamar idanuwansa xa su fito, lkci daya ya runtse ido ya nufi kofa ya fice daga dakin ya tafi bangarensa, bai ga Jiddah a nan ba ya shige bedroom ya kwanta jin kamar sanyi yake ji, ya fi minti ashirin a haka duk jikinsa yayi wani irin sanyi, he is really shocked, ruwa ya sauka sosai, can yayi karfin halin tashi ya tafi bandaki ya hada ruwan dumi yayi wanka ya fito, yana ta xaune gefen gadonsa yayi wannan tunanin yayi wancan tunanin, can ya mike da kyar wearing just his short nd singlet ya fita dakin, dakin Jiddah ya tafi ya kunna wutan dakin ya ganta kwance ta rufa da duvet, idonta biyu kuma ba bacci take ba, ita duk tunaninta wajen Aneesah ya tafi ya bar ta xaune parlonsa kawai, ya kashe wutan a hankali ya tafi kusa da ita ya cire duvet din gently ya kwanta drawing her closer to him ya juyo da ita, underneath his breathe yace My Precious Gift... Ta ki bude idonta tana sauke numfashi a hankali....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you







_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp






Da asuba Abuturrab na dawowa masallaci ya xauna downstairs ya jinginar da kansa a hankali jikin kujera ya rufe ido, gaba daya ya rasa me ke masa dadi, upon how sweet the night was to him bai yi wani baccin kirki ba, he was disturb all through, and he is still finding it hard to believe Aneesah bata kwana cikin gidan nan ba, yana ta xaune parlor har bakwai saura sannan ya mike da kyar ya haura sama yana jin kansa na sara masa, bude kofar dakin Jiddah yayi ya sameta ta koma bacci bayan ta idar da sallah, ya nufeta ya lulluba mata duvet a hankali yana kallon innocent face dinta, ya daura lips dinsa a nata ya lumshe ido, sai kuma ya mike ya fita, gently ya kullo kofar don ya san she really need the sleep, ya tafi parlonsa ya xauna ya rike kansa yana jin damuwa a ransa, sai kuma ya jawo wayarsa ya shiga dialing number Aneesah, har ya katse bata daga ba, ya kuma kiranta sai ta daga cikin muryan bacci tace "Hello my Captain" Yace "How


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login