Showing 279001 words to 282000 words out of 346625 words
Chapter 94 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
na short da singlet dinsa, a bucket ya saka xanin gadon bayan ya gama wankewa ya fita da shi waje, can inda yayi wanke wanke ya tafi ya kunna tap din, yana dauraye xanin gadon Aneesah da ke xaune kasa har sannan jikin window din ta mike jin an kara kunna pampo, kallonsa ta dinga yi har ya gama daurayan xanin gadon sannan ya shanya a igiyan dake wajen, ta dauke kanta da sauri ta koma gefen gadonta ta xauna. Yana komawa sama ya shiga bedroom din Jiddah ya xauna gefenta yana ta kallonta memory din last night na dawo masa afresh, he couldn't help it but smile, ya manna mata kiss a lips dinta underneath his breathe yace "I know i have always love u from day 30... I am proud of u wife, and i have to replace ur precious gift with something amazing" duk da bacci take ya kira Ahmad yayi sau uku yana tambayar ya tabbatar xata tashi babu wani ciwo ko xaxxabi, a kiran karshe Ahmad yace "Hey captain ka bar ni inyi aikina plss, bayan ka cuci er mutane kuma kayi ta damuna da kira..." Abuturrab ya shafa kansa a hankali yace "I neva knew haka abun yake, i never knew there is something of such a duniya, i couldn't control my self, i loss control" dariya Ahmad yyi yace "Ga ka ga mata a gida for months kace u never knew.... U neva knew what?" Abuturrab ya ja tsaki yace "Ban ta6a sanin cutar kaina nake ba sae jiya da daddare, ban san duk wahala nake ba kaina ba sae jiya, sae jiya nasan meye aure, sannan sai jiya nasan wacece mace" Ahmad dae dariya kawai yake yace "Kaga sae anjima xancenka ya fara fin karfina" daga haka ya katse wayarsa, Abuturrab ya kai hannunsa goshin Jiddah a hankali ya ji temperature dinta ya fara sauka, yanxu bacci take cikin nutsuwa, lumshe ido yyi ya bude yayi murmushi, lkci daya ya ji hankalinsa ya kwanta he felt relieved at last, ya daura hannunsa a hankali kan flat tummy dinta yana shafawa, he just have to compensate her with a surprise kafin ta tashi bacci, a huge surprise....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
FZ BEAUTY SUPPLEMENTS
Dealer in all kind of dietary supplements such for skin whitening, skin glowing, weight gain, slimming, flat tummy, infection killers, dark spots removers, fertility booster, Hips boosters, Breast firming and Enlarging, Teeth whitening, eye, joint, stretch marks, and for marital pleasure. All supplement are available for wholesale and retail. For more information contact FZ via wa.me/2348143821028
FZ Beauty Supplements
Dealer ce ta supplement masu qara fito da kyaun mace ko namiji, hadi da qarama garkuwar jiki kuzari. Muna sayarda Supplemnt kamar na qarin duwawu, akwai wanda zaya taimaka wurin dawoda martabar Nono, akwai na rage qiba da tumbi, akwai na rakwainuwa, akwai na tada komada, akwai masu saka hasken fata da qyalli, akwai na infection, akwai na saka hasken ido da hakori sannan akwai na gyaran turaka. Muna maraba da mai sayen daya ko sari. Wa.me/2348143821028
Karfe sha biyu saura Jiddah ta bude idonta a hankali, bin dakin ta dinga yi da kallo ta mike xaune hoping she won't feel any pain anymore, gaba daya ta ji baccin ya isheta, ta gaji da baccin, ga wani yunwan da take ji sosai, xuwa yanxu kam bata jin ciwon da take ji a gabobinta, karfi ne kawai bata da shi a jikinta, a hankali ta sauke kafanta kasan dakin xata mike tsaye, babu shiri ta koma ta xauna ta rufe idonta, dai dai nan aka bude kofar dakin ta juya da sauri, Maimoon ce ta shigo dakin da sallama ya ci kwalliya tayi daurin ture kaga tsiya, rike ha6a tayi tana kallon Jiddah tace "Shine ko kira babu Jiddah, kika sa muka raka ki mota muna matsar kwalla, amma yau sati daya mun ji ki shiru a dakin ki" Jiddah tayi murmushi bata dai ce komai ba amma har ranta tayi farin cikin xuwan Maimoon, tayi missing dinta sosai sosai, Maimoon ta karaso cikin dakin tace "Ni da na damu dake ai gashi na biyoki, kuma kar ki ce min sai yanxu kika tashi bacci? Aa gaskiya wnn dai ba yi bane, ko irin er kwalliyan nan da amare ke yi da safe babu kin wani xumbula doguwar riga kina xaune gefen gado?" On a serious note Maimoon tayi maganan, cikin sanyin murya Jiddah tace "Umma fa??" Maimoon tace "Umma tana gida, ita ma ai kin manta da ita daga tarewa, gobe sati daya amma ko kira daga ke har yayan" a hankali Jiddah tace "Ban manta da ita ba, ai bani da waya ne" Maimoon tace "Toh baxa ki amshi wayarsa ki kirata ba" Jiddah dai tayi shiru tana kallon Maimoon, Maimoon tayi kasa da murya tace "Ke na ji gidan shiru, ina yar dabar gidan take, ko ta bar maki gidan ne ta kasa xama?" Jiddah ta wani harareta, Dariya Maimoon tayi tace "Ke Allah kuwa kamar ke kadai ce a gidan, naji shiru, shi dama yaya ban ga motarsa ba a parking space" Jiddah ta sunkuyar da kai tace "Kika san ko tare suka fita?" Maimoon ta hade rai tace "Tare suka fita xuwa ina? Har yanxu fa satin ki daya bai cika ba, sai gobe xai cika, to sai kika yi shiru kika barsu suka fita tare" Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba, amma haka kawai taji abinda Maimoon ta fada ya tsaya mata a rai, tunda gashi baya nan kenan assumption dinta dai dai ne, fita yayi tare da Aneesah ita kuma ya bar ta nan tana wahala, Maimoon ta mike da sauri tace "Auu tare fa muke da kawayena suna parlor, ki taso mu je ku gaisa yan Islamiyyan mu ne" Jiddah ta kasa ce mata komai amma tasan baxata iya tashin ba, kafin Maimoon ta sake cewa komai tace "Ki ce su shigo nan, kaina ciwo yake baxan iya fita ba..." Maimoon tace "Ciwon kai kuma? Toh kin sha magani?" A hankali Jiddah tace "Na sha" Maimoon tace "Kina ciwon kan suka sa kai suka yi fitarsu?? Lallai, dama Umma tace idan na xo in sa ido ko da akwai wata matsala" Shiru Jiddah tayi, gaba daya taji ranta babu dadi, kawai imagine take da gasken sun fita ne da Aneesah, Maimoon tace "Tabdi..." Daga haka ta fita daga dakin, Jiddah ta wani hade rai don ba karamin tasiri xancen Maimoon yayi a xuciyarta ba, Maimoon na fitowa daga dakin Jiddah ta hangi Aneesah tana sauka downstairs ita ma dai da doguwar rigar kamar sannan ta tashi bacci, wani kallo ta bi ta da shi, Aneesah na fitowa parlor ta dinga kallon yan mata biyun dake xaune saman kujera a parlon, maimakon ta tsaya amsa gaisuwarsu, a takaice tace "Daga ina?? Wa ku ke nema?" Muryar Maimoon taji daga sama tace "Wajen matar gidan muka xo" Aneesah ta juya da sauri tana kallonta, Maimoon ta karasa sauka kasa tace "Jamila ku taso ku hauro sama ku gaisa, tana daki" Nan da nan Aneesah ta ji ta nemi ciwon kai da xaxxabin da ya rufeta tun sanyin safiya ta rasa, wani kwari ya xo mata, tana kallon kawayen Maimoon da kyau cikin daga murya tace "Toh idan nan din gidan ubanku ne sai ku haura saman in gani!!!" Duk suka yi turus suka tsaya, Cike da tsiwa da fitsara Maimoon na kakkanne ido tace "Toh ai kema naga ba gidan ubanki bane da xa ki ce baxa a hau sama ba, kuma sannan ba wajenki muka xo ba" Aneesah ta wani xaro ido ta nufeta da sauri tana huci tace "Ubana kika xaga?? Uba na??" Maimoon ta jefar da jakan hannunta ta cire mayafinta ta daura a kugu tana gyara ture kaga tsiyan kanta tace "Ohh ashe babu dadi, ance maki uba ya fi uba ne??" Jamila ce tayi kan Maimoon da sauri ta janyeta daga wajen kafin Aneesah ta cakumota, Hankali tashe Jamila tace "Kinga ki xo mu wuce Maimoon mu ba abinda ya kawo mu ba kenan wllh, don Allah mu wuce kawai" Maimoon tayi wani shewa tace "Inje ina?? Wllh ina nan, ki bar ta ta ta6a ni idan ta sha codin ne, wllh xata ga yanda ake kasa kasa da d'an mutum yau, ko ance mata nan din gidan babanta ne da xata hanamu shigowa? Gidan yayana ne fa kuma wajen yar uwata na xo don haka gomanta basu isa su hanani xuwa gidan nan ba wllh wllh" Aneesah tayi wani kukan kura tayi kan Maimoon tana kunduma mata xagi ta uwa ta uba amma tuni Jamila da Farida suka shiga tsakaninsu suna ba Aneesar hakuri, Kamar mahaukaciya Aneesah ta nufi kitchen a guje, Jamila ta dinga jan Maimoon su fita Maimoon taki fita ita ma tana kunduma ma Aneesah xagi, amma me? tana ganin Aneesah da tabaryan karfe da wuka daga ita har su Jamila suka haura sama a guje hakan kuma bai hana Maimoon dinga xaginta ta uwa ta uba ba, suka shige dakin Jiddah da gudu suka sa makulli, Jiddah dai sai kallonsu take don tana jin hayaniyar amma ta kasa tashi, gashi duk hankalinta ya tashi, da damuwa tace "Me yasa xa ki kulata Maimoon? Me yasa don Allah" a fusace Maimoon tace "Na kulata din, ita uwa ta ce da xan ji tsoronta inki kulata, ni baki ganta ba ma wllh naga duk ta rame ta yamushe sai kwala kwalan ido da kashin wuya kamar xa a jera duwatsu, kinga da gaske dai ta fara samun sleepless night a gidan ba a sani ba, to wllh bari yaya ya dawo duk inda ya tafi yayi min iyaka da ita don bata isa ta hanani xuwa gidan nan ba, kai ko shi ma bai isa ba balle ita, kullum idan muka tashi Islamiyya idan na ga dama sai na leko na ganki Babu wanda ya isa ya hanani" Daga Jamila har Farida kallon Maimoon kawai suke dukkansu a tsorace suke da Aneesah, Jiddah ta sauke wani ajiyar xuciya tana kallonsu tace "Sannun ku da xuwa Farida" Jamila tace "Hmm sannu Jiddah, mu dai da mun san haka xai faru da bamu fara xuwa ba wllh, Allah ya gani ba tashin hankali ya kawo mu ba, Maimoon da baki biyeta ba wllh" Jiddah dai tayi shiru, Maimoon tace "Lallai tunda ina tsoronta ai dole in ki biyeta... Ai da nasan haka xai faru yau da Rumasa'u xa mu xo gidan nan ayi duk bala'in da xa ayi, ayi fashe fashen kai" Bude gate din gidan suka ji anyi, Maimoon ta nufi window da sauri, har sannan tana huci tana kallon motar da xai shigo, wata sabuwar mota dal ash color sai wani talli yake ne ya shigo compound din, Maimoon ta wara ido a hankali tace "Waooww motar waye wannan, yaya ya canxa mota ne?" Jiddah dai sai kallon Maimoon take amma babu daman ta tashi taga motar, Maimoon ta dinga kallon wanda xai sauka daga motar ta ga Abuturrab, ta rufe bakinta tace "Lahh wllh yaya ne, ya canxa mota, waow latest ride wllh, wannan shi ake kira da ride" Jamila da Farida dai suna xaune kan kujeran da suka xauna a dakin, Maimoon tace "Ta so ki gani Jiddah wllh sabuwar mota ce..." Jiddah na ganin Maimoon xata dagata ta ga motar da sauri tace "Noo Maimoon am not feeling fine ina jin jiri" Kyaleta Maimoon tayi sai yaba kyan motar da yayi mugun tafiya da ita take, haka ta sa sai da su Farida suka taso suka ga motar ta window su ma suka ya6a sosai, Lkci daya Maimoon ta dawo sense dinta ta kalli Jiddah tana xare ido da sauri tace "Yaya nan xai shigo?" Jiddah bata kai ga ce mata komai ba suka ji an murda kofar dakin, Maimoon ta nufi kofar da sauri ta shiga bude makullin, tana budewa tace "Yaya sannu da xuwa" Daga sama har kasa yake kallonta kafin yace komai ya ga su Farida a xaune, gaishesa suka yi gaba daya kansu a kasa, ya amsa masu da murmushi fuskarsa yace "Yauwa sannunku da xuwa" Maimoon ta marairaice tace "Yaya in gaya maka wllh Aunty Aneesah hana mu xama tayi a parlor..." Da mamaki yace "Saboda me?" Tace "Wai ba gidan ubanmu bane, sai kaga abinda ta mana yaya, gashi da bak'i yan makarantan mu na taho duk ta bani kunya, ta xageni ta xagesu, ni dai ban kulata ba yaya, muna dai xaune parlon still sai ga ta da ta6arya da adda daga kitchen shine fa muka hauro sama da gudu muka shigo nan muka kulle kofa, Banda haka da Allah kadai yasan abinda xata aikata mana yau, ni dai ban kulata ba" Kallonta kawai yake boiling from inside, can ya kalli su farida yace "Ku yi hakuri don Allah" Duk suka ce ba komai wllh, Ya ajiye ledan hannunsa gaban mirror, ya kalli Maimoon yace "Kun ci abinci??" Maimoon ta rufe bakinta tace "Ina fa yaya?? Ko ruwa bamu sha ba tana neman rotsa mana kai da tabarya da adda balle abinci" Yace "Mu je ki daura maku abinci" Tayi wani murmushi tace "Toh yaya" Tana biye da shi suka sauko downstairs, su Farida ma duk suka fito daga dakin wanda su basu ki su yi wucewarsu gida a lkcn ba, Aneesah na xaune parlor har lkcn, Maimoon ta fara wani cartwork tana jujjuya ido tana biye da Abuturrab, shi kam ko kallon Aneesah bai yi ba ya nufi kitchen Maimoon na wani smiling ta yi ma kawayenta alamar su biyota kitchen din, da yake duk sun sha jinin jikinsu da Aneesah haka suka nufi kitchen din gaba daya, Aneesah ta bi su da kallo xuciyarta na suya taji kamar ta kwala ihu ko xata samu saukin abinda take ji a xuciya, is this really happening to her?? Yau ita ce ke witnessing wannan abubuwan, ko a mafarki bata ta6a xaton haka ba, bata ta6a xaton akwai daren da xai xo ta gansa yanda ta ga rana ba, a da idan taji wani na cewa bai yi bacci ba throughout dare ta xata karya ne, sai gashi yau hakan ya faru a kanta, don ko rintsawa bata yi ba, bata yarda tayi kukan dake cinta ba xuciyarta na mata xugu, ta wani dake tana huci daga xaunen da take, Sai da Abuturrab ya nuna ma su Maimoon foodstuffs din kitchen din sannan ya juya ya fita, yana kallon Aneesah da kyau ya nufeta yace "I think i told u the other day, i think i warned u cewar only my relatives are allowed into this house, and i am giving u this last warning today Aneesah, ko kallon banxa kar ki sake yi ma wani jinina idan ya xo gidan nan, that is idan har kina son ci gaba da xama da ni..." Mikewa tayi tana iya kokarin ganin bata fashe da kuka ba tana wani vibrate tace "Do ur worst Aliyu!! Wannan sabon threat din da ka tsira yi min na miye? Abu kadan kace idan ina son xama da kai, ka fito ka gaya min abinda ke ranka game da ni mana, ka fito ka fada nace, na gaji da walakancin ka, na gaji da walakancin da kake min, don ban gane ma'anar idan ina son ci gaba da xama da kai ba, a kan wata yar iska can kanwar bayana xaka tsaya kana gaggaya min wannan magana Aliyu, duk ka sa kanninka sun raina ni, to wllh wllh hakurina ya kare, bayan kauda kai da nake ta yi ina tausan kai na akan auren cin amanar da kayi sai an kara min da wani xafin" Abuturrab ya mata wani kallo yace "Idan har a tunaninki ina threatening dinki to ki dau matakin da kika ga ya dace, find a way out for ur self idan kin gaji da walakanci na kuma hakurin ki ya kare da ni, ki dau action din da ya dace and stop barking" yana fadin haka ya nufi stairs ya bar ta nan tsaye, ta sulale saman kujera ta rike kanta tana dannar xuciyarta kar ta fashe da kuka sbda su Maimoon dake kitchen, wai yau ita Captain ke mata wannan abubuwan, yau ita Captain ke gasa ma magana anyhow har da ce mata she is barking?? mutumin da a baya ko ci kanki baya ce mata komai tayi masa sai dai yayi overlooking baya tanka ta, what is happening to her!! Abuturrab na haurawa sama ya bude kofar dakin Jiddah suna hada ido ta sunkuyar da kanta, ya isa gabanta ya durkusa yana kallonta, ita dai ta ki yarda su hada ido, ya kamo hannunta yace "How are feeling now?" Bata ce masa komai ba, yace "Kina jin yunwa ko?" Still tayi shiru, yace "Ohk u need to sit bath first before eating" Daga haka ya mike ya cire agogon wrist dinsa ya ajiye kan bedside drawer ya nufi bathroom ta bi sa da kallo, bayan ya hada ruwan xafi a bathing tub ya fito, ya bude ledan drugs dinta ya dau iodized salt ya koma bandakin, yana fitowa ya ajiye ledan sauran yana kallonta yace "Should i?" Sai a sannan ta kallesa kamar xata yi kuka tace "Ni wllh bana so, i am okay" Bai tsaya ya saurareta ba yayi leading dinta with his help xuwa bandakin. Abinda tayi masa da safe shi din dai ta kara maimaitawa yanxu ma, ga uban shagwaba da ita ma bata san tana yi ba, shi kam hakan narkar masa da xuciya yake, ya dinga lallabata yana bata hakuri, da kansa ya ciro mata atamfarta da aka yi ma dinkin doguwar riga, ta shirya bayan yayi mata duk abinda ya kamata.... har ta gaji da kunyan nasa ta hakura and she felt much relieved now don da kanta ta maida turarrukan da ya kwaso gaban mirror, sannan ta dawo a hankali ta xauna gefen gadon, ya durkusa gabanta yace "Tell me, me xaki ci? Nasan baxa ki jira Maimoon ta gama girki ba