Showing 42001 words to 45000 words out of 346625 words

Chapter 15 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

you are looking much much better and healthier now" Abuturrab yyi murmushin karfin hali bai dai ce komai ba, ta karasa ta mika masa Bowl daya na fruit salad din tace "I made this for u" Amsa yayi yace "Thank you Aunty" Kujeran dakin ta xauna tana shan fruit salad din daya bowl din hannunta tace "Abbanku ma ya kara kira yanxu nace da sauki, shi ma duk ya damu" Ahmad da ya d'an hade rai yace "Ina yini..." Ba tare da ta kallesa ba tace "Lafiya lau" magana ta ci gaba da yi da Abuturrab dake shan fruit din hannunsa, Ahmad ya mike yace "Alright Captain, sai ka xo can gidan namu, i will be leaving now" Abuturrab ya kallesa da sauri, ta gefen ido Aunty ta harari Ahmad tana ci gaba da shan fruits salad dinta, Abuturrab yace "Ai nace maka nima xan fita Ina son in sha iskan waje" Ahmad yace "Okay ka sameni mota idan ka gama, i will wait" daga haka yace ma Aunty "Sai anjima" ko tankasa bata yi ba har ya fita ya kulle kofar dakin, Aunty tace "Yaushe har ka farfado xaka wani fita Abuturrab? Shi Ahmad din bashi da hankali ne ko don ya xo lkcn da jikinka yayi kyau, kana fama da kanka ina wani fita idan ba neman magana ba?" Abuturrab ya shafa kansa yace "Aunty na gaji da xaman gidan ne, ni nace masa mu fita, ba shi ba" Ta tabe baki tace "Toh ai shkkn...." Bayan kusan minti ashirin Abuturrab ya fita xuwa gun Ahmad bayan ya sanar ma Ummi xai je gidansu Ahmad din, Sbda yanda idonsa ya fada yasa shi saka bak'in spec dinsa, kananun kaya ne jikinsa wani sanyayyen kamshi na tashi jikinsa, kana ganinsa kasan he is still recovering, he still looks weak, Kallonsa kawai Ahmad yake yi har ya karaso ya shiga front seat, Ahmad na kallonsa da d'an damuwa yace "Wai malaria ne ya kamaka haka Captain, ka rame fa, kamar wanda yayi sati a kwance" Captain bai ce masa komai ba, Ahmad ya tada motar suka bar layin. Karfe biyar da few minutes suka isa gidansu Ahmad, Abuturrab yace "Ka bar motar a waje ba dadewa xan yi ba xaka maida ni gida ynxu" Hakan yasa Ahmad yyi parking a waje, Abuturrab ya bude motar ya sauka ya nufi cikin compound din, Ahmad ma ya sauka ya rufe motarsa ya bi bayansa, sosai gaban Abuturrab ya fadi bayan ya shiga compound din sun yi ido hudu da Jiddah dake tsaye ta jingina da bango a bakin tap din dake cikin compound din ta tara bucket.....

Abuturrab ya dauke idonsa hade da daure fuska yana tafiya, murya can kasa Jiddah tace "Ina yini" Bai kara kallon inda take ba balle ya tanka ta, tafiyarsa kawai yake kamar bai ji ta ba, Ta kalli Ahmad da ya shigo compound din shi ma, ta sauke idonta tace "Ina yini?" Murmushi yayi yace "Lafiya lau, sannu da aiki" Juyawa tayi tana kallon ruwan da take jiran ya cika, Ahmad ya bi bayan Abuturrab da har ya kusa main entrance din gidan, babu kowa parlon da Ahmad ya shiga sai kamshin girki dake tashi alamar ana girki a kitchen, bedroom dinsa ya nufa ya tadda Abuturrab a kwance idonsa a lumshe, ya karasa ciki ya kulle kofar yana kallonsa yace "Are you alright?" A hankali Abuturrab ya bude idon sae dai bai ce komai ba, cike da karfin hali ya mike xaune looking so dumbfounded, Ahmad ya xauna yana facing dinsa with seriousness yace "Tell me what is happening Captain, you look disturbed" Abuturrab ya shafa kansa ya lumshe ido wishing all this nonsense would turn out to be a dream, kara bude ido yyi, gathering much courage yace "I am in trouble Ahmad" Tuni yanayin Ahmad ya sauya, ya kafe sa da ido, can yace "Tell me what is it, me ya faru??" Cikin sanyi Abuturrab yace "Yes i will, amma kuma mafita nake nema a wajenka don Allah, and this should be a secret between just i and you for now plsss" Shi dai Ahmad kallonsa kawai yake waiting to here what is this that's weighing down his frnd har haka, Abuturrab yayi kasa da murya da kyar ya fara magna yace "Yarinyar da kake siyan awara wajenta a hayi, u remember her right?" Bude ido Ahmad yyi sosai yana kallonsa yana jiran jin abinda ya sameta, A hankali Abuturrab ya shiga basa labarin tun daga xuwansa siya ma Umma awara sanda bata da lafiya, abinda ya faru a ranan, har ixuwa yanxu da suke xaune tare da Ahmad a daki, Abuturrab ya share xufan goshinsa yana kallon Ahmad da ya bude baki for almost five minutes now ya kasa rufewa, Abuturrab ya hade rai yace "Don Allah ka daina kallona haka Ahmad ka bani mafita, find a way out for me, i am stuck, ban ta6a shiga rudani iya rayuwata kamar na wannan lokacin ba, what have i done to my self daga taimako??" Sae a sannan Ahmad ya kulle bakin da sauri, wato kawai sae yake ganin labarin da Abuturrab ya basa kamar tatsuniya, or is he dreaming?? Ya kifta ido kusan sau hudu sannan ya kafe Abuturrab da ido, he is finding it hard to believe all what Abuturrab said now, as if counting his words yace "Wait Captain... Wllh kamar fa ban fahimce wannan gajeran labarin nan naka ba, i am confus...." Captain yyi tapping dinsa on a serious note yace "You just have to believe all what i said, duk abinda na gaya maka hakan yake stop confusing ur self" Ahmad na nunasa da yatsa cikin wani expression yace "Are you for real Aliyu??" Abuturrab ya kafe sa da ido regretting everything from the start, Ahmad ya buda ido sosai yana kara digesting din lamarin with shock, he knows Abuturrab have a soft heart, a very soft heart kuwa, yana damuwa sosai da matsalan da ba tasa ba, he prioritized damuwar wasu kan nasa, but he never thought ya kai wannan extent din, bai ta6a tunanin Abuturrab can go this deep ba, what is baffling him more is yanda this time around taimakon nasa yyi sa ga talaka sosai, don Ahmad bai ta6a ganin yayi stressing kan lamarin local people ba, tsakaninsa da su sadaka if the need arize, babu wani magana me tsayi dake hadasa da su, Abuturrab ya hade rai ganin irin kallon da Ahmad ke masa yace "Nayi kuskuren gaya maka damuwata ne da ya sa ka min shiru Ahmad? Don't u have anything to say to me pls?" Lkci daya yanayin Abuturrab ya kara sauyawa gaba daya, sai yake jin wani sabon xaxxabi xai rufesa, da kyar Ahmad na nunasa yace "You mean you are married now without our knowledge Captain??" Cakumosa Abuturrab yyi a fusace yana huci yace "Wannan kake kira da aure? Haka ake auren dama? Mahaukaci ne ni da xan amince nayi aure yanxu" Ahmad yyi iya kokarin ganin bai yi dariyar da ya taho masa ba ganin how furious Abuturrab was, Turasa Abuturrab yyi ya mike yana jin xufa na keto masa yace "Ka gaya min meye abun yi ynxu, i have never been this confused all my life, what have i done to my self, taimako fa kawai nayi kokarin yi...." Lkci daya idonsa ya kada ya dawo ya xauna ya rike kansa, Wani tausayinsa Ahmad ya ji har ransa, hakan yasa kawai ya kawar da dariyar dake cin sa gaba daya a xuciyarsa, ya kwantar da murya yace "let's talk brother" Abuturrab ya dago da idanuwansa da suka yi ja yana kallonsa, Ahmad yyi shiru yana tunanin yanda Abuturrab yayi making fool out of him, ko da wasa bai ta6a gaya masa abinda yake yi ba sai da abu ya 6aci, har da raina masa wayo wai shu murhu yake gani a hayi, wani boyayyen ajiyar xuciya ya sauke yyi kasa da murya yace "before i say anything just tell me what u have in mind now about this issue?" A hankali Abuturrab ya kai hannu aljihunsa ya fiddo farar takarda da biro yana kallon Ahmad, Ahmad ya buda ido sosai, lkci daya ya girgixa kai yace "Nooo.... This isn't a solution, idan ka rubuta takardan nan dole gida xata koma ga axxalumar step mum dinta, kaga anyi ba ayi ba kenan, and at the end wannan mahaukacin kilan yace sae ya aureta..." Abuturrab yace "But I can't sleep in peace again today in har ina tuna auren warce ke kaina, baxan ta6a samun nutsuwa ba matsawar ban aiwatar da haka ba, me of all people fa?? Where will i start from with that girl, me xanyi da ita a rayuwata?? Ko a mai aiki wllh wllh wllh baxan yi employ dinta ba, baxan bata aiki ba a gida na dai, western education zero, islamic education zero, wayewa zero, tsafta zero, mu'amalat zero, kyau zero.... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ahmad dake ta kallonsa bbu ko kiftawa ya girgixa kai yana d'an murmushi yace "A bangaren kyau kuma ka so kanka Captain...." a mugun fusace Abuturrab ya fixgosa yace "What the heck.... Kyau xan ci?? Tsaftar fa?? Ilimin fa?? Wait wai kai Ahmad kana tunanin no matter what xan iya xama da local yarinyar nan a matsayin matata? Noo plss... God forbid, this is more like an abomination to me, idan na sake kwana da auren yarinyar nan a kaina yau wllh nasan gobe xan iya xarewa a wuce dani psychiatry" Ahmad ya lumshe ido ya bude yace "Duk na fahimce ka, amma idan ka saketa ynxu Captain ka gaya min meye makomarta? Ina kake son taje? Kasan xamanta tare da maigadin gidan nan da matarsa ba abu bane da xai ja lkci coz daki daya ne da su" Abuturrab ya lumshe ido ya bude yace "I don't care anymore, saninta da tausayinta ne duk ya ja min plight da nake ciki ynxu..." Ahmad yace "Ohk Now tell me, after the divorce what next, ya xa kayi da lamarinta? Kaga tamkar ka lalata aikin ladan da kayi ne daga farko har karshe" Abuturrab na masa wani kallo yace "What are you insinuating now? Kar in saketa kake nufi ko me?" Ahmad ya daga hannu da sauri yace "Aa ni bance haka ba" Abuturrab ya ja wani tsaki yace "Xan saketa, kuma xan ci gaba da mata taimakon da nayi niyya" Ahmad yace "Good, ta yaya?" Abuturrab yace "Under my roof" Ahmad yace "Elaborate plss" Abuturrab yace "I'm thinking i will have no choice but to explain everything that transpired to my Dad, xan ma Abbana bayanin komai, xan kuma kai sa har gun me anguwan, i don't want to look foolish, you get? Then he can explain everything to Ummi coz ni baxan iya ba...." Ahmad ya katse sa yace "You are confusing me, kai da kake da intention sakinta yanxu me xai kai magana kuma kunnen Abba?" Abuturrab yace "Don nace xan saketa ba yana nufin ai baxan yi duk abinda nayi niyya a kanta ba, wllh xan saketa without anyone's knowledge, daga ni sai kai ne xa mu san babu aure tsakanina da ita, amma she will be under my care xan kula da ita har sanda xata samu me aurenta" Ahmad da ke ta kallonsa baki bude yace "Under ur care as how?? a gidanku xaka ajiyeta kenan?" Abuturrab ya girgixa kai yace "A gidana dai" Wani tsaki Ahmad ya ja yace "See the way u are talking like an illiterate plss, ba matarka ba ba komai ba xaka ajiye a gidanka kuna rayuwa tare Captain, ko dai nine ban fahimce abinda kake nufi ba, ka min bayani yanda xan gane" Abuturrab ya masa wani kallo yace "Toh me xamanta a gidana xai kara ko xai rage? Did i look like someone that have anything to do with that girl? Haba Ahmad, don dai ta kwana ta tashi tayi girki ta ci abinci ta tafi boko ko islamiyya, xamanta a gidan nan da rashin xamanta duk daya to me, Monday to Friday ina gun aiki, na dawo sunday and Saturday, wait tell me what u have in mind first" Ahmad yace "Gaskiya baxan yarda da wannan rashin tunanin ba, kana cikakken namiji ka xauna gida daya da mace...." Mikewa Abuturrab yyi looking super angry yace "Amma ka gama da ni Ahmad, mace me tsafta iya tsafta ina xulumi da tunanin yanda xanyi tarayya da ita balle wannan, haba.. haba wannan xagina kayi wllh, ta ina xan fara abinda kake tunani, did you know who i am kuwa Ahmad, me xanyi da warce tayi tsaftar yarinyar nan sau biyar ma balle ita" wani kallo kawai Ahmad ke yi masa Abuturrab yace "You just insulted me wllh, and i am seriously not happy about it" Ahmad ya tabe baki ya ki basa amsa, Abuturrab yace "Sabida wannan kaddaran da ya fada min ma dole nan da lkci ba mai tsayi ba in auri Aneesah" Ahmad yace "Sai ka ajiye su gida daya kenan?" Abuturrab yace "Yes, kaga Aneesah ta samu me taimakonta aikace aikace kenan" Ahmad yace "Gaskiya ne wannan, to yanxu abinda nake son sani shine, idan ka rubuta takardan ba yarinyar xaka yi kenan ko ko ya xaka yi?" Abuturrab yace "I will do the rightful thing, giving her or not giving her" Ahmad yace "To su kuma can iyayen nata xaka bari su san tana wajenka?" Abuturrab yace "There is no need, idan ta samu 'yan cin kanta xata je garesu watarana" Ahmad ya sauke ajiyar xuciya. Karasawa Abuturrab yyi jikin window yana kallon waje, Ahmad dai sae kallonsa yake, shi har sannan ganin lamarin yake kamar a film, abinda ya fi daure masa kai yanda Abuturrab ya boye masa komai from beginning sae ynxu da abu ya baci, murmushi yyi yana gyada kai yana tunanin irin dariya da tsokanar da xae fara yi ma Abuturrab idan hankalinsa ya kwanta, sae dae deep down him he is so Happy for this young girl don yasan Abuturrab baxae ta6a cutarta ba, with him her future is super bright, komai na rayuwa baxai ji kyashin yi mata ba, maganar sakin da Abuturrab yyi ne kadai bai ji dadi ba har cikin ransa. Ana kiran magrib suka fita tare xuwa masallaci bayan sun yi alwala, Jiddah ce kadai xaune tsakar gida da buta a gabanta, tunda ta hangosu daga nisa tayi kasa da kanta tana alwalanta,, Kallonta kawai Ahmad ke yi yana mamakin yanda ita da gogan suka iya pretending, ko da wasa bata ta6a nuna masa ta san sa ba, murmushi kawai yake yi yana kara jinjina wannan lamari me abun mamaki, Abuturrab dai ko kallon inda take bai yi ba har ya fita gate din, Ahmad yyi murmushi ya bi bayansa, shi dai ya san ko giyar wake Abuturrab ya sha baxai yi accepting yarinyar nan matsayin matarsa ba, bayan an idar da sallah sun fito masallaci Ahmad na kallon Abuturrab yace "She isn't comfortable staying with the gate man and his wife, may be because daki daya ne, kaga baxai yiwu suna ciki tana ciki ba shi yasa take yawan xaman waje, na lura da hakan" Abuturrab bai ce masa komai ba har suka shiga compound din, sae a sannan yace "Idan na gaida Umma xaka saukeni gida yanxu" Suna bude kofar parlon Abuturrab yyi ido hudu da jiddah tana tsaye daga kusa da kofan parlon, sunkuyar da kanta tayi ta koma gefe cikin sanyin murya tace "Ina yini" Bai ce komai ba ya karasa cikin parlon, Ahmad ya sakar mata murmushi yace "Ki karasa ciki mana, kin tsaya a bakin kofa" Tana jan yatsunta tace "Abinci xan amsa inji Maman Abdallah" Ahmad yace "Toh ki karasa ciki" Ta d'an karasa amma ba can cikin parlon ba tace "Na gaya ma Aunty Huraira tace toh" Umma ce ta fito kitchen ganin jiddah tace "Yau ma jikin kofar kika makale Jiddah?" Jiddah ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Ma su sunan ki kuwa suna da sakin jiki ke ban san ya haka ba" Ahmad yace "Bakuwa ku ka yi gidan Umma" Umma tace "Ehh bakuwar Amina ce, gashi har yau taki sakewa" Ahmad ya kalleta yana murmushi yace "Ya sunanki?" A hankali tace "Jiddah" tausayinta Ahmad ya ji har cikin ransa, without allowing that to show... ya buda ido yace "Lahh Ummin Captain ce ashe" Umma tayi murmushi tace "Kai ba Umminka bace kenan?" Ahmad ya shafa kansa yana murmushi ya kalli Abuturrab da ya hade rai kamar bai ta6a dariya ba yana kallon TV, yace "Captain ga mai sunan Ummin mu fa" Umma na kallon Jiddah tace "Karasa kitchen din ki ga ko ta gama xuba maki, kinji" Kitchen din Jiddah ta nufa ta shiga ciki, Abuturrab ya gaida Umma a hankali, amsawa tayi da murmushi tace "Alhmdlh jiki yayi sauki kenan, ai daxu da muka je kana bacci" D'an murmushin karfin hali yayi yace "Naji sauki Umma" Tace "Toh Allah ya kara lafiya Son, bari a kawo maku abinci yanxu" A nan parlon ta barsa shi da Ahmad, Jiddah ta fito rike da abinci, bata yadda ta kallesu ba ta nufi kofa kamar mara gaskiya ta fita... Washegari Thursday karfe tara da yan mintuna Abuturrab ya fito daga bedroom dinsa, Bangaren Abbansa ya nufa, sai da ya bude kofar parlon Abbansa yace "Alhmdlh.... Much better now" sisters dinsa ne xaune parlon suna masa ya jiki kamar baxai amsa ba kuma bayan ya isa bakin kofar parlon Abbansu ya amsa sannan ya shiga parlon da sallama, Aunty ce tare da Abba a parlon, tun da ya shigo Abbansa ke kallonsa, ya xauna kasan carpet yace "Sannu da dawowa Abba" Abba yace "How are you feeling now?" A hankali yace "Alhmdlh na ji sauki" Abba yace "Allah ya kara lafiya" Aunty tace "Jiki kam Alhmdlh, kamar ba shi ba shekaranjiya" Abba na kallonsa yace "Kana stressing kanka da yawa ko, you look stressed out" Abuturrab ya girgixa kai yace "Aa Abba" Aunty tace "Kamata yayi ka dau hutun ko da sati biyu ne ka huta har ka murmure gaba daya, you look so lean" Shi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login