Showing 288001 words to 291000 words out of 346625 words
Chapter 97 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
yayi ta fama da na shi" Ummi tayi murmushi tace "Kowa fa da halinsa yake xaune Hajja, ni wllh bana mata bakin cikin dawowa dakinta, karya ce ke karewa ba dai gaskiya ba..." Kwafa Hajja tayi ta nufi dakinta, Umma kuma ta fice daga gidan gaba daya.... Abuturrab na xaune parlor tun bayan fitar su Umma, gaba daya good mood dinsa yau ya baci, hukuncin da xai ma Aneesah kawai yake tunani, ga shi Ummi ta hanasa hukunci me kankat wato saki, abubuwan da ta dinga masa tun farkon aurensu ne ke dawo masa da yanda ya sameta ba virgin ba, and he hate himself for everything, he hate himself for being silent for that long babu wani hukunci da ya dace da ita banda ya rabu da ita na har abada don ba canxa halinta xata yi ba, ba daina abubuwan da take yi xata yi ba, babu abinda yake basa mamaki irin yanda ya iya xama da ita for this long duk da mugun kazantarta, a yanda ya ba ma tsafta muhimmanci a rayuwarsa bai ci ace ya iya ci gaba da xama da Aneesah ba, kai bai ma ta6a xaton xai iya rayuwa a inda kazanta yake ba, duk wa ennan tunanin suka hadu suka sa yaji inaa baxai iya rayuwa da ita a matsayin mata ba, banda he was impatient tun xamansu na farko da Jiddah ya gano me tsafta ce sosai, bai ta6a dawowa ya tarar da gidan ko jikinta ba dai dai ba, komai ya gwada mata a rananta na farko a gidan yayi sinking a kanta, bude kofar parlon aka yi ya daga kai da sauri Umma ta shigo da Maimoon da wasu yan mata biyu, ko kallonsa bata yi ba ta wuce sama su Maimoon na biye da ita, Maimoon sai boye hannunta take cikin Hijab dinta, Abuturrab ya bi su da kallo har suka haura sama, next thing da ya fara ji shine fashe fashe da tarwatse tarwatse a sama, ya jinginar da kansa da kujera sai kuma yayi murmushi, shi dai ko motsawa bai yi ba har suka sauko kasa bayan minti talatin, Umma ta nufi kofa kamar boss su Maimoon na biye da ita a baya, ko da wasa Maimoon bata yarda ta kalli inda Abuturrab yake ba, ya bi su da ido har suka fita sannan ya mike ya haura sama, dakin Aneesah da ya gani a wangale ya nufa, ya tsaya bakin kofa yana kallon yanda suka yi kwatsa kwatsa da dakin don har ya fi na Jiddah muni, har akwatunanta sai da suka faffasa, ga show glass dinta me shegen tsada da aka kawo mata kwanan nan shima duk sun hallaka shi, ya fi minti biyar tsaye kafin ya juya a hankali ya bar bakin kofar, yana tunanin dama haka auren mata biyun yake? Shi ya xata a film kawai irin haka ke faruwa, so even in reality, reality din ma a gidansa, ya sauke wani ajiyar xuciya shi dai baxai ce ya ji haushin su Umma ba ko kadan that serves Aneesah right, downstairs ya koma ya ci gaba da xamansa a nan. Throughout ranan a dakin Ummi Aneesah ta yini, haka nan kawai taji hankalinta ya kwanta sosai, ko ba komai ta samu saukin abinda xuciyarta ke mata tun shekaranjiya, ganin idon Ummi ya sa duk aka kira sallah kafin a ajiye mic a masallaci xata tashi taje tayi alwala a bandaki, da yake kafin su dawo gidan sai da Ummi ta kai ta chemist aka duba mata yankewan da tayi aka yi mata alluran tetanus sannan aka bata drugs shi sa ta samu saukin xafin wajajen da ta yanke, rabon da ta ci abinci har ta manta sai yanxu a dakin Ummi da aka kawo mata tuwo me xafi da miyar kubewa, ramar da tayi was so obvious shi yasa Ummi ta sake tausaya mata don a hakikanin gaskiya kishiya ko ma wace iri ce babu dadi kai ko da kishiyar rana daya ce, balle wnn irin bambanci da Abuturrab ya nuna kiri kiri ai sai mutum ya hadiyi xuciya ya mutu, Aneesah ta gama cin tuwon ta ajiye plate da bowl din gefe ta tafi bandaki ta wanke bakinta ta fito ta xauna saman darduma, ita fa bata ji tayi regretting abinda ta aikata ma dakin Jiddah ba, da son samu ne har da motar ya kamata ta hada a lkcn, ta share hawayen da ya kawo idonta duk da xuciyarta ya rage xafin da yake mata amma har sannan bai dawo dai dai ba, duk son da take ma Abuturrab xai walakantata ya ci mata fuska haka dama... tana son kiran Aunty da yan uwanta amma bbu dama tunda bata taho da wayarta ba, bude kofar dakin aka yi ta daga kai, suna hada ido ya wani daure fuska ya juya ya fice daga dakin don bai san tana ciki ba da baxai shigo baz ta bi sa da kallo. Main parlor ya koma ya xauna sai ga Ummi ta fito daga bangaren Abba wanda ko minti talatin bai yi da dawowa gidan ba, ya gaisheta ta amsa tana kallonsa, mikewa yayi yace "Abba ya dawo ne?" Tace "Ehh" parlon ya nufa ya shiga ya gaida Abban nasa, yana xaune cikin parlon Hajja ta shigo, Abba ya gaisheta da ladabi yace "Dama yanxu xan shigo ai dakin naki Hajja" Hajja tace "Aa ba ruwana ni ba sai ka shigo ba, ni da abu ya tsaya min a rai ba gashi na taho da kaina ba" xaunawa tayi parlon tace "Toh abubuwan da suka faru dai yau Usman da a Masar ne kai da kake tushen komai xa a daure, abubuwan da suka faru yau kam sai godiyan Allah waiiii, Aa ban ta6a ganin haka ba ko a pim" Abba dai kallonta yake ta yi, Hajja tace "Toh ba dai komai bari Ramlah ta iso na sa yara sun kira min ita daxu so nake ayi komai gaban idonta, tun da na dawo Masar abubuwa ke ta faruwa a garin nan, wanda lkcn da nake bauchi babu haka wllh" Abba ya sauke ajiyar xuciya yana kallon Abuturrab yace "Do u have any idea of what happened?" Hajja tace "Aa ba sai ka juya masa yare ba, ni nan xan maka bayanin komai tunda a kan ido na aka yi, amma sai Ramlah ta iso, to amma kafin ta iso ina son kayi kiran Hafsah ta xo, nasan ai tana garin, kayi kiranta ta xo gidan nan" Kallonta kawai Abba yake, Hajja ta kalli Abuturrab tace "Ta shi mu je, idan kowa ya hallara sai a dawo ayi magana sinka sinka" Ya kalli Abbansa, Abba yayi masa alaman da su tafi, mikewa yayi ya bi bayanta suka fita, shi fa duk gaba daya tunaninsa na kan Jiddah amma shakkan xuwa gidan Umma yake, bai ta6a tunanin xai yini yau ba tare da ita a gefensa ba, is she even feeling much better now? Ta iya ta ci abinci kuwa, duk wa ennan tunanin suka taru suka damesa a dakin Hajja, wanda kawai Hajja surutunta take bai san me take cewa ba, Da karfi Hajja tace "Ko ba haka ba Aliyu?" Ya daga kai ya kalleta duk da bai san me take cewa ba a hankali yace "Haka ne" Tace "Atoh, kowa xai san ni er banxa ce wllh, shiru shiru na nacutata tun ba yau ba na sani" Yana kallonta yayi kasa da murya yace "Hajja don Allah idan an xauna kice masu su bar ni in tafi da matata, sai ta xauna bangarena kafin a canxa mata kayan daki, ita kuma Aneesah dama xance taje gida ta huta ne na kwana biyu don na gaji da halayyanta wllh" Hajja tace "Nima nan da ba gida daya muke ba na gaji da ita balle kai, ita kuma Jiddah uban wa ya isa ya hanaka tafiya da ita mutum da matarsa, ai dama tare nace Ramlah su taho, kafarta kafarka, babu shegen da xai shiga hakkin ka ina gidan nan" Sosai Abuturrab ya ji hankalinsa ya kwanta, sallama aka yi bakin kofar dakin, Hajja ta daga kai da sauri tayi mici mici da ido kamar me son gano muryar, Sai kuma ta amsa tace "Bismillah" Aka bude kofar Aunty ta shigo dakin kanta a kasa hannunta rike da karamin cooler, Hajja sai satan kallonta take, Aunty na murmushi ta xauna saman carpet bayan ta ajiye coolern hannunta tace "Sannu Hajja" Hajja tace "Yauwa sannu" Cike da ladabi kanta a kasa tace "Ina yini Hajja?" Hajja ta hade hannunta yanda manya ke gaisuwa tace "Lafiya lau Hafsah, lafiya lau wllh" Aunty tace "Fatan mun same ku lafiya, ya jiki jiki" Hajja tace "Aa wllh Alhmdlh, ashe kina dai kadunan" Aunty tayi d'an murmushi tace "To ya xa ayi Hajja, muna nan wllh, sai yanda hali yayi" Hajja tace "Allah sarki, to sannu da xuwa" Aunty tace "Yauwa Hajja, rayuwar ce sai hakuri wllh" Abuturrab da ya dauke kansa da farko don bai yi niyyar gaisheta ba sai kuma ya juya ya d'an kalleta babu yabo babu fallasa da nufin gaisheta, amma me?? buda ido yyi sosai ganin abu take kokarin cusawa karkashin gadon Hajja tana jan Hajja da xance, ya kalli Hajja dake ta wani murmushi tana cewa "Hakuri kam ai ya xama wajibi a wannan xamanin" Aunty ta gama tura abinda xata tura ta dauke hannunta da sauri, sai kuma ta mike tace "Toh Hajja bari in karasa parlon Yallabai shi yayi kirana dama" Hajja tace "Aihoo ai ni nace ya kiraki, ni na sa shi wllh" Aunty tace "Allah sarki Hajja, bari in je in dawo" Xata fita suka kusa cin karo da Umma, Aunty ta koma gefe, Umma ta shigo Aunty na wani murmushi tace "Ina yini Hajiya Ramlah" Umma bata tsaya ba tana tafiyarta tace "Lafiya lau" Kujera ta nema ta xauna, Aunty ta amsa gaisuwar Jiddah da wani irin fara'a tace "Sannunku da xuwa" Jiddah ta sunkuyar da kanta ta karasa parlon ta xauna saman carpet daga kusa da Hajja, Abuturrab sai kallonta yake babu ko kiftawa, Aunty dai ta fita parlon ta nufi bangaren Abba tana murmushi. Hajja ta yi wani murmushi tace "Shegiya matsiyaciya wai ni xata yi ma siyasa kamar warce bata yi xaman Masar ba, to xata ci kaza kazanta yau wllh" Tana fadin haka ta bude warmer din da Aunty ta ajiye taga farfesun kayan ciki sai turiri da xuba kamshi yake, Hajja ta kalli Jiddah da ta sa hijab har kasa tace "Maxa Dauki d'an iskan naman nan ki boye a hijabinki ki tafi can kwararo ki juye ki dauraye mata kulanta ki kawo, maxa maxa" Jiddah ta mike ta amshi warmer din ta nufi kofa a hankali Abuturrab ya bi ta da kallo, yana son tashi ya bi bayanta but he have to bring out abinda Aunty ta tura karkashin gado kuma yana son yin hakan ne ba tare da kowa ya lura ba, a hankali ya gaida Umma ta amsa tana danna wayarta, Hajja tace "Bari Jiddar ta dawo duk mu baxama parlon Usman" Umma dai bata ce komai ba, ba a wani dau lkci ba Jiddah ta shigo ta ajiye warmer din sannan ta xauna Hajja tace "Allah ya maki albarka, tashi parlon Usman xa mu tafi" mikewa Jiddah ta kara yi, Hajja ta mike Umma ma ta tashi suka nufi kofa gaba daya Abuturrab ya bi su da kallo, bayan fitansu ya tashi ya tafi karkashin gadon dai dai ta inda Aunty ta xauna ya tura hannunsa a hankali yana laluban kasan, bai ga komai ba alamar ta wuntsular da shi can ciki, hakan yasa shi dage katifar dakin, can ya hango wani katon abu kamar laya an garkame da wani irin kwado ya dinga kallon abun snn ya ciro handkerchief dinsa ya durkusa ya dauka yana kallo da wani irin mamaki, nannadesa yayi da handkerchief dinsa ya saka a aljihu snn ya mayar da gadon yanda yake ya fita dakin xuwa parlon Abbansa. Abba ne xaune parlon sai Aunty, Ummi da Aneesah dake xaune kasa daga gefen Ummi, Jiddah kuma ta xauna kasa kusa da Umma, Hajja ta shimfida darduma tayi xamanta a kai ta mimmike kafa tana kallon Aunty da Aneesah kasa kasa, xaunawa Abuturrab yayi shi ma a kasa, Abba ya bude taron da addu'a sannan yana kallon Hajja yace "Kin yi kirana kwanaki kadan da suka wuce ban samu tahowa ba sai yau, ina fatan lafiya Hajja" Hajja ta gyara xama tace "Toh ni dai kafin ince komai a nan so nake in ji ko kauron Mama nayi maka ya sa kaji gwara ka mayar she ni gantallaliya kawai Usman" Abba dai yayi shiru yana kallonta, Hajja ta kalli Aunty da kyau tace "Maimaita abubuwan da kika gaya min a parlon Aliyu ranan" Sosai gaban Aunty ya fadi ta dinga kallon Hajja.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_
Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*
If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp
A fusace Hajja tace "Ba kallona xaki tsaya yi da idanuwa kamar bakwainin kwarkwata ba Hafsah, cewa nayi ki maimaita abubuwan da kika gaya min gidan Aliyu yanxun nan" Aunty ta gyara xama ta d'an daure fuska babu ya6o babu fallasa tace "Kamar me kenan? Dama mun hadu a gidan Aliyu ne Hajja?" Hajja ta saki salati tana tafe hannu tace "Huhuhu duniya ta tara sheggu, wato bamu hada gidan Aliyu ba?" Aunty ta ki cewa komai, Hajja ta kalli Abuturrab da karfi tace "kai Aliyu wani rana ne muka hadu da Hafsah a gidanka?" Abuturrab ya daga kai a hankali ya kalli Aunty, wani shegen kallo take masa fuskarta a daure, Ya kalli Hajja yace "Ranan Juma'ahn da ya wuce" Hajja ta gyara xama tace "Aa kai kuma ba haka xaka ce ba, labari xaka dauko tiryan tiryan na dalilin xuwa na gidan naka sannan da naje me ya faru a can din, kana yin abu kamar dai kana tsoronta" Abuturrab ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Ranan Juma'ah na dawo daga wajen aiki na biyo nan na daukeki xuwa can gidan nawa..." A fusace Hajja tace "Toh ai sai ka fadi dalilin kai ni gidan naka" Abuturrab ya sunkuyar da kai, Hajja ta bude baki tace "Kun ga algungumi ko? Da gasken dai tsoron Hafsah kake... Wasu narka narkan zawarawa yan uwan Nanisa su biyar da wannan mata Hafsah ne fa suka tafi suka ta re masa a gida na kusan wata daya suna xuba tsiyarsu kamar ya yan tasha, to uwarsa Hauwa ba tsayayya ba balle ta kwatar masa gida ta fatattakesu, kanwar uwarsa kuma abu kadan ta kwaso hukuma tana gaba suna biye da ita, to yabawa da yayi da hankalina da natsuwa da iya magana ya sa shi xuwa ya daukeni domin in je in masu nasiha akan cewar bai dace su tare a gidan yaro ba, su kama gabansu su tafi, don wllh sun mayar masa gida gidan xawarawa shi kuma bashi da bakin magana, ai ko na shirya naje gidan, in gaya maku suna xaune sun yi washarere dasu a parlon babu kunya babu tsoron Allah, nayi masu sallama na gaishesu nace A'a Hafsah dama kina kaduna ashe? Ai a tunanina kina Benue?" Hajja na demonstrating tana jujjuya ido da hannu tace "Ba sai mata ta dinga jujjuya min ido cike da axababben rashin kunya da fitsara take ce min ehh kwarai ina nan ban je ko ina ba, babu kuma wanda ya isa ya sani in je wani gurin, ko baki da labari ni da Usman mutu ka raba, sannan ko ke da kika durkusa kika yi nakudarsa kika haifesa kinyi kadan ki raba ni da shi wllh ki ji in gaya maki kinyi kadan, wato ke a xaton ki ya sakeni ko?? To kin yaudari kanki tsohuwa, don kuwa babu abinda ya canxa a kan matsayina a wajen Usman, ina nan a matsayin matarsa lokaci kawai ake jira ki ga ikon Allah, ai ba sabon abu bane rabo ya kashe mutum...." Hajja ta rike kai tace "Huhuhu.... in gaya maku ta wani ja min tsoki da na ji sa har tsakiyar kai na, ni dai nayi shiru duk jikina yayi sanyi" sai kuma ta fashe da kuka ta kwance ha6ar xaninta tana shessheka, Abba dai kansa na kasa duk yana sauraronta, Aunty tayi karfin halin cewa "Ni? Ni muka yi haka dake Hajja?? A ina muka hadu muka yi haka? ki ji tsoron Allah...." Tsawa Abba yayi mata yace "In my present??" Aunty ta wani ta6e baki tana jijjiga kafa tana hararan Hajja kasa kasa, Hajja ta share hawayenta cikin rawar murya tace "Usman ai ko da ace gallaza maka nayi kafin ka kai matsayin da kake yau ya kamata in ci darajar haihuwar ka da nayi, ballantana ba daya kanwar biyu, gata dai wannan ka samu kamar xan kashe kaina a kanka, ko Kabiru bai samu kulawa da son da na nuna maka ba tunda shi ubansa ya ha'ince ni na dai bar komai sai gobe kiyama kawai, kai kuwa ubanka mutuwa ce ta rabani da shi bawan Allah, to Usman duk sadaukarwan da nayi a kanka yau sai ka rufe ido ka xabi mace a kaina? Dubi fa wahalan da nayi tayi a kanka amma sakayyar da xaka min kenan? Har xagina matar nan ta ta6a yi a gabanka shekaru ashirin da suka wuce ta ci min mutunci ta walakanta ni, kafin xuwana Masar na farko, amma wai sai kayi mata saki daya a wancan lkcn ma, ko awa biyu kuma ba ayi ba ka maidata ba da sanina ba sbda lalacewa ta sameka Usman..." Sai kuma ta fashe da kuka, Aunty dai ta kasa xaune waje daya jin abubuwan dake fitowa daga bakin Hajja, Cikin kuka sosai Hajja tace "Na xata ko bare yace xai walakanta ni sai inda karfinka ya kare balle a cikin gidanka, shkkn na xama er banxa kenan bani da gata, matarka