Showing 231001 words to 234000 words out of 346625 words
Chapter 78 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
gefensa giving him a hug tace "Oyoyo my husband nayi missing dinka sosai wllh, amma dai yanxu daga kano kake ko? Don da naji ka shiru kuma I can't reach u tun shekaranjiya nace to kilan kano kaje..." Bude idonsa da ya canxa kamanni yyi ya mike, lkci daya yace "I want to be left alone Aneesah" daga haka ya wuce sama ta bi sa da kallo ganin kamar xai tashi sama, sai kuma ta tashi ta bi bayansa da sauri, bangarensa ya nufa yana shiga dakinsa ya sa makulli duk da xanin gadon dakin a gyare yake haka ya yaye ya bude press ya dau wani xanin gadon ya shimfida sannan ya dau duvet ya kwanta ya rufe har kansa. Har kusan asuba Abuturrab bai yi bacci ba, gashi ya ji gaba daya bai da strength din tashi yayi sallah, har alwala sae da ya daure ya je yyi duk da he is cold amma daga karshe kwanciya yayi without praying, sallan asuban ma a daki ya samu yayi, he wished all this wasn't happening, he wish all this will turn out to be a dream, his heart is to weal for all this... Ya kalli wayarsa jin shigowan message, mikewa yyi ya dau wayar ya xauna gefen gado, ganin message din na Abbansa ne ya ki budewa ya ajiye wayar xuciyarsa na bugawa, yana nn xaune har rana ta fito, kwanciya yyi jin kansa yyi masa nauyi sosai yana kuma sara masa, lkci daya bacci me nauyi ya daukesa... Hannu ya ji a forehead dinsa ya bude ido da sauri, Aneesah ce xaune gefensa tana kallonsa da damuwa tace "Are u okay captain? U are restless even in sleep, and it seems u are developing fever, ko dai duk stress din tafiyar ne?" Yayi kokari ya mike xaune ya cire hannunta a kansa yace "Hey i am okay" ta daure fuska tace "How will u tell me u are okay ga temperature dinka is saying it all, dubi fa yanda jikinka ya fara xafi" Ya hade rai yace "I said i am okay Aneesah, me yasa ma zaki tasheni ina bacci tukun?" Tace "Aa wnn ba bacci kake ba, bacci babu nutsuwa duk ka wani firgice kamar wanda yyi ma sarki karya?" Sauka yyi daga kan gadon ya fita dakin ta bi sa da kallo baki bude. Ummi ce xaune bedroom din Umma tayi tagumi kana ganinta kasan abun duniya ya dameta, Umma na kallonta tace "Toh ke sae kika yi masu shiru Yaya?" A hankali Ummi tace "Toh me xance? I was speechless Ramlah... I was mute all through, har yana cewa i should provide him in less den 24hrs or we both face the consequence" Umma ta mike cikin daga murya tace "Toh aje a hakan, kin san komai din ko da yanda xa ayi da ke?? Tabbas da goyon bayanki Aliyu yake duk abinda yake yi, sai aka yi yaya? Da akwai yanda xa ayi da ke ne? Ko wani ya haifar maki Aliyun?? Kuma ina ce dae ba kashe mutum yaje yayi ba auren sunna yaje aka daura masa da shaidu ya dawo gida, to wanda bai fasa ce wa ke kike xugasa ba... tunda munafuka annamimiyar matarsa ta daga hankali ta rikice kamar ita aka yi ma kishiya ba dole shi ma ya birkice ba, ita kuma Hajja tunda babu abinda ta iya sai son kai da son abun duniya da rashin alkibla ba dole ta gigice ba ita ma, ae tun ba yau nake nuna maki irin bambancin da take nunawa kiri kiri a kan 'ya ya ba, to wllh a da ina jin babu wanda ya kai ni bakin ciki da takaicin abun nan da Aliyu ya koma ya aikata ba, amma yanxu kuwa sae in da karfina ya kare, ae auren sunna yaje aka daura masa, in dai a kan Hajja da makira shegiyar matar nan Hafsah ne sae iya inda karfina ya kare, aure kuma ya riga da ya je yyi babu yanda aka iya da shi, shi kansa Abban sae yayi hakuri tunda dae ba sata yaje yayi ba ko wani mugun abu" Ummi dae kallonta kawai take bata ce komai ba, Umma na huci tace "Ba kallona xaki yi haka ba Yaya, fitowa xaki yi kanki tsaye ki goyi bayan d'an ki tunda abun haka ne, ki nuna masu ae fa shirun da kike yi ba tsoro bane, kuma kina da iko a kan Aliyu ba Ubansa kadai ba" Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "I am not against him dama Ramlah, kawai dae nayi shiru ne don kada uban da baabarsa suce ae goyon bayansa nake, amma kinga a hakan ma ban fita ba sunce da sani na yake komai har auren farkon ma, kuma wllh for months now yana ta son yyi min magana duk ina lura da shi amma ya kasa sae yyi kamar xae yi sae kuma ya wayance, ke akwai ranan da har daki sae da na shiga da shi kamar xae fada kuma ya fasa, sae dai yace in taya sa da addu'a kuma no matter how everything will turn out kar inyi fushi da shi, kin kuma san sa da xurfin ciki, ni dae nasan duk sallolina biyar bana masa fashin addu'a kuma ina masa fatan alkhairi a duk lamarinsa, duk wani abu da xai cucesa ina addu'an Allah ya nisanta sa da shi, don haka ni i am not against him going back to marry Jiddah, bayan ya saketa da watanni ni kaina nayi masa takaicin hakan barin ma idan aka duba halin da yake ciki tun bayan auren nasa na biyu, kwata kwata bai yi dacen mace ba, tafiyar nan da yayi kusan duk bayan kwana biyu sai ta xo gidanmu amma ko sau daya bata shigowa bangarena da sunan gaisheni, duk sanda Allah yyi muka hadu a main parlor sai ta gaisheni a can bbu wani ladabi, ga uban kazanta da yake complain a gidan nasa...." Umma tayi wani dariya tace "Ai kadan ya gani, sannan ni abinda ya fi tsaya min a rai ita Hafsah da ta xakalkale har tana ikirarin ba dai ya kunyatata ba me take nufi? Ita ta isa ta hanasa karin aure ko yin abinda yake ra'ayi ne? To wllh tana ji tana gani xan wanke Jiddah tsaf in kai ta gidan Aliyu da kai na, sai in ga ko xuwa gidan xata yi ta fito da ita, duk da dai xai ci ubansa kafin hakan ma ya faru" Ummi dai tayi murmushi bata ce komai ba, Umma tace "Ina baki shawara da kakkausan murya yaya, kar ki raga ma duk wanda ya gaya maki babu dadi a kan case din nan, ko Hajja ban cire ba wllh, shi kuwa ki barbade toka a idonki ki wankesa wankin babban bargo shi Abban idan ya sake attacking dinki, ai shiru ba hauka bane, me yasa sai da aka bari na bar gidan aka maki ca?? Toh in sha Allah har su gama duk abinda xa su yi a kan case din nan a can xan dinga yini" Tana kai wa nan ta nufi kofa tana cewa "Bari in kawo maki abinci" Ummi tayi tagumi can kasan ranta tana jin tausayin d'an ta, karfin hali tayi ta gaya masa maganganun da ta gaya masa jiya a daki, ta rasa dalilin da yasa ko kadan bata ji haushinsa ba, ta dai yi mamaki ainun amma ba wai haushin sa ba, daukar wayarta tayi ta sake kiransa still ta ji a kashe, tun ma da suke tare da Jiddah bata ta6a xuwa gidansa ba balle yanxu, banda haka da sai ita taje can gidan nasa, Jiddah ce ta shigo dakin da sallama rike da Tray me dauke da cooler din abinci da spoon, Ummi tana ta kallonta har ta ajiye tray din ta daga kai ta kalli Ummi tana d'an murmushi tace "In debar maki Ummi?" Ummi ta girgixa kai tace "Aa sai anjima, nagode" Jiddah tace "Toh" Sannan ta mike ta nufi kofa Ummi ta bi ta da kallo. Aneesah ce xaune daki tare da Safara'u, Safara'u ta kyabe baki tace "Ni ban ma ta6a jin haka ba wllh, ae kamata yayi idan wani abun ne ke samunsa sai ya sanar maki a matsayin ki na matarsa, amma ba wai yayi ta abu kamar ke 6are ce, ni na ma rasa gane alkiblan mijin nan naki kamar me tambotsai, ni da sai ince ki fita harkansa kawai ki kama kanki tunda shi d'an iska ne, idan kuma don gidansa da na xo ne yake ta wannan halayyan na basarwa yana ciccin magani sai in tattara inyi tafiyata ni bai isa ya walakanta ni ba, ance masa mu fakirai ne? Ko bai je gidanmu ya gani bane?" Aneesah da ta d'an hade rai jin ta xagi Aliyu tace "Kai Aunty Safuu, wllh ke dai da fassara kike, to ina ruwansa da xamanki? Ae shi ba haka yake ba, snn fa shi haka halinsa yake na Basarwa suna fa da jimi da jinin sarauta Aunty, yayan Babansa fa shine sarkin Bauchi kin sani, kuma ina jin ma kamar bashi da lafiya don yanayinsa ma ya nuna karfin hali kawai yake, kawayena ma ba ruwansa da xuwansu gidana balle ke kanwar uwata, yanxu Ahmad xan kira, kilan stress ne daga dawowan da yayi tafiya" Safara'u ta kara kyabe baki tace "Atoh ai da sai ince ki ba banxa ajiyarsa kawai, kowa ma na da jinin sarautar ae, mutumi ba shi da aiki sae ji da kai da nuna shi wani ne, to ta ina? kawai ki fita harkansa kema ki koyi d'an jan ajin nan na mata mana" Aneesah ta rike ha6a tace "Ina xan iya haka Aunty? Uhum lallai baki san yanda nake son mijina bane, in ja masa aji fa kika ce? Aa baxan iya ba wllh, baki ga ba duk na ma kasa cin abinci saboda wannan yanayin da yake ciki, Aa wllh duk wani abu da xai dami mijina bana so gaskiya" Safara'u ta dau ayaba daya ta 6are tana ci tace "Tsoron da nake jiye maki shine kada ya kyallara ido ya hango wata a tafiye tafiyansa tunda suna yawon kasashe ma, duk da dai mu bama sakankancewa balle har a mana kishiyar, a tsaye muke ta ko ina, ba gashi ba har mijina ya mutu ni daya ce tal sai uban tarin dukiya da 'ya ya biyu da ya bar ni da shi" Aneesah tace "Ni baxai mutun ba in Allah ya yrda, amma dukiyarsa kam nawa ne da 'ya yan da xan haifa in sha Allah, Babu wata shegiyar mace da ta isa ta ra6ar min miji in dai ina numfashi, don ni na gwammace ma in kasheta wllh, kuma yarana uku sun isheni xaman duniya" Safara'u ta jefar da 6awon hannunta tace "Toh dai kiyi kokari ki gama amfani da maganin nan, idan ma baki sani ba duk danginsa sun xura maki ido ne a ga ciki amma shiru ake ji, barin wnn kanwar uwar nan tasa da na ga alamar bata da mutunci, dama ni duk na tsaneta tun encounter dinmu a lkcn bikinku" Aneesah ta yi tsaki tace "Umma suke ce mata ko wa, ae ina ga baki tsaneta irin ynda ni na tsaneta ba, ko hanyar gidanta ma ban sani ba har yau, na lura ta fiye shisshigi kan lamarin Aliyu, ko da yake ita wnn ae karamar alhaki ce" Safara'u tace "Atoh dae, duk ta karkashin kasa xa a bi masu bakinmu alekum" Aneesah ta marairaice tace "In sha Allahu nan ba da dadewa ba Allah xae bani ciki, kinga Mummy ma duk ta damu inyi ciki, ko daxu ta kirani ko na gama amfani da wanda aka kawo last week nace eh, wllh na kagu ace yau ga d'a na haifa ma Aliyu" Safara'u tace "In sha Allahu kuwa kamar anyi an gama, nan da wata tara xaki sullubo masa d'a ko 'ya" Aneesah ta washe baki tace "Allah ya tabbatar Small mum" Da daddare Aneesah na parlor suna kallon wani movie da small mum dinta wayarta ya fara ring, dauka tayi ganin Abuturrab ke kiranta, ta d'an buda ido tace "Ina xuwa Aunty yana kirana, ya tashi kenan" daga haka ta wuce sama da sauri.... Tana shiga bedroom din nasa ta samesa kwance har sannan da duvet a jikinsa, ta karasa kusa da shi ta xauna gefensa da damuwa tace "Ka tashi Captain? I still can't reach Ahmad ni kuma bani da number Ramlah" Tana magana ta kai hannu goshinsa, xaro ido tayi ta dauke hannun da sauri tace "Subhanallah, Ur temperature is very high Captain, plss ka samu ka tashi mu tafi hospital, this is getting out of hand" Sai kuma ta washe masa baki tace "U need not worry about the driving, ur wife can now drive expertly, na koya sanda baka nan, babu inda bana shiga da mota yanxu" Ya mike xaune da kyar yace "With whose car kika koya?" Ta fara kas kas da cingam tace "Whose car kuwa banda naka? D'an kurkurjewa ne kawai yayi kafin hannuna ya fada, har by pass naje da mota na xagayo har Mando, baka ga yanda na kware ba yanxu nake gudu" Shi dai kallonta kawai yake can yace "Sai kuma wa ya koya maki?" Tace "Ehh to da farko da Aunty Safara'u muka fara naga dai ba abun arxiki shine nayi ma wani frnd dina Auwal da muka yi makaranta tare magana, shi dai yake ta koya min muna yawo a gari har hannuna ya fada" Kallonta yake bbu ko kiftawa, ta mike tana cewa "Bari in fito maka da kaya mu tafi asibiti gaskiya, tun jiya kana kwance baka da lafiya ka ki yarda baka da lafiya, ai ba wai ance wani abu na damunka bane, kowa ya san stress ne from ur long journey, journey din nan kuma har da kai aka dinga piloting jirgin, body no be firewood ae..." komawa yayi ya kwanta don idan ya fiye magana yana jin xuciyarsa babu dadi, ganin tana kokarin dauko masa kaya ya ajiye mata wayarsa yace "Akwai layin Ahmad ki kirasa" Ta jefa masa wani kallo tace "Sau nawa xan ce maka na kirasa bai shiga ba" Abuturrab yyi kasa da murya yace "His other line, Dr Ahmad" Daukar wayar tayi ta shiga contact ta duba number sannan tayi dialing, yana fara ring ta kallesa tace "Ashe yana da wata number dama nake ta trying na cikin wayata" Shi dai bai ce mata komai ba, Ahmad na daga wayar ta marairaice tace "Hello Dr, it's Aneesah wllh i am telling u for the pass 2 days now Captain ba shi da lafiya sosai kuma ya ki xuwa asibiti, ko masallaci baya fita wllh balle a xo ga cin abinci...." Shiru tayi sai kuma tayi saurin cewa "Toh shkkn, sai ka xo, na gode" Daga haka ta katse wayar tana kallon Abuturrab tace "Kaji wai yana can gidanku ma, he is on his way coming right away" Shi dai bai ce mata komai ba tace "Let me make a cup of tea for u sai ka daure ka sha ko kadan ne kafin ya iso" Daga haka ta fice daga dakin....
*In kinsan kin samu full document na Jiddatul Khair, kar ki fitar min da shi i am begging in the name of God* 🥹
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;
Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697
Tun da Ahmad ya shigo yake kallon Abuturrab dake xaune with a cup of tea a hannunsa, can ya karasa jikin window ya tsaya ya rungume hannunsa still looking at him yace "So what's wrong with you now?" Abuturrab ya d'an hade rai jin tambayar da yake masa, ya ajiye cup din hannunsa yace "Kawai ka rubuta min magani xa a amso min a pharmacy" Ahmad ya d'an yi murmushi yace "Ana rubuta magani without knowing d cause of a sickness?" Abuturrab yyi kasa da murya yace "Headache, dizziness, loss of appetite, Nausea, and... yawan faduwan gaba" Ahmad ya kuma yin wani murmushin kamar baxai ce komai ba, sai kuma yana kallonsa yace "And all this while Jiddah matarka ce kake fooling each and everyone of us Aliyu...." Abuturrab ya dauke idonsa daga kallonsa as if the question came unexpected, Ahmad bai kuma cewa komai ba, ya ciro biro a aljihunsa ya nufi gaban mirror ya dau takardan da ya gani a ajiye, ya d'an yi rubuce rubucensa snn ya dawo ya mika ma Abuturrab yana kallonsa yace "I think this drugs will do, Allah ya kara lafiya" Daga haka ya juya ya nufi kofa Abuturrab ya bi sa da kallo kafin ya fita cike da karfin hali yace "Ahmad" Ahmad ya tsaya sannan ya juyo, Abuturrab ya sauke idonsa kasa yace "U are not saying anything about the topic u brought up just now?" Ahmad ya girgixa kai yace "Nahh!! I have nothing to say, and i am wishing u nothing but d best" Yana fadin haka