Showing 45001 words to 48000 words out of 323952 words
suka samu wani Mai adaidaita suka hau Amanda ta fad'a mashi inda zai kaisu da turanci, rashida b'ata taba zuwa gidan Amanda ba Sannan kou kadan basu da closeness da Amanda, iyaka in tazo da safe sai su gaisa kowa yayi abinda ke gabanshi amma yau jin tace zata taimaka mata yasa zata bita har gidanta. In silence suka isa wata estate inda duk yawanci hayan gida ake amma ba kowa yake iya zama wajen ba sai Mai hali, sauka sukayi daga adaidaita ta biya suka shiga ciki,
"wannan wurin yana da kyau sosai... " inji rashida,
"yes... Wani alhaji ya bani in zauna kafin in gama service... " ta amsa mata,
"alhaji kuma..."
"yes... Alhaji... " ta amsa mata atakaice, rashida b'ata k'ara Jan maganar da tsawo ba suka Taka har inda nata Bangaren yake ta bude masu suka shiga, the parlour look OK And cool,
"relax... Bari inje watsa ruwa in fito... " Amanda ta fadawa rashida Tana zipping wandonta, zama rashida tayi Tana kalle kalle, bayan kaman minti ashirin amanda ta fito sanye da bump short looking sexy, rashida da tayi tsuru tsuru ta kalla before saying
"Bari in hado mana indomie..." ta fad'a cikin turanci, b'ata k'arasa ba rashida tace
"aa pls... Gida zani... Very soon mum dina zata fara kira taji why ban dawo ba... Dan Allah tell me how you want to help me... " ta fad'a jikinta na rawa, murmushi Amanda ta saki sannan ta zauna tare da cewa
"first question is kina da daman haduwa da shi?.. As in ganin shi at your own will?.. Can you give him something to eat? "ta tambayeta, da sauri tace
"aa... Sau daya kawai na ganshi... Dan sarki ne fa... " killer smile Amanda ta saki Tana cewa
"wow he's a huge fish in pond... So at all baki iya ganinshi balle ki bashi wani abu ya ci?.. " ta tanbayeta,
"kanin mijin sister ne... Nasa ta kirashi amma bai zuwa... He's very reserved... " ta fad'awa Amanda, shuru Amanda tayi for a moment sannna tace
"it's going to be tough than I expect... amma if Kinyi hakuri zakici riba... kin taba jin snatching?.. " ta tanbayeta,
"yes... " ta amsa mata wondering what she's talking about,
"then ki sawa Ranki zakiyi snatching dinshi daga hannun kowa ma wacece yake tare daita... " idanuwa rashida ta zaro Tana cewa
"how is it possible... ta yaya hakan zai taba yuwa?.. " ta fad'a sounding so confused, dariya Amanda tayi sannan tace
"ya kike ganin mutane suke iya snatching kudi a bank... All it takes is planning...in har akayi planning komai is possible... So Kiyi relaxing... " ta fad'a mata,
"how zanyi relaxing... Dan Allah help me... " rashida ta fad'a kaman zatayi kuka, matsawa Amanda tayi kusa daita sanann ta saka bakinta kusa da kunnenta Tana mata magana cikin kunnenta Wanda babu Mai ji at all sai rashida, Tana mata maganar rashida ta Zora manya idanuwa tayi saurin kallonta sannan tace
"sister how is it possible... How zata aminta Dani?... " ta fad'a sounding so surprised
"eh mana is possible... Wanann is the most simple thing... " Amanda tafad'a mata, kai rashida ta girgiza tace
"nidai gani nake kaman it's not possible... ya zaayi ta aminta Dani?.."hannu Amanda ta dora mata a baki Tana cewa
"Bakisan Mai son abinka yafika dabara ba?.. Ai dui Mai son abinka yasan yanda zaiyi ya kusanci wannan abun har ya kwanshe makashi...ni a wajena is most simple thing... "
"what if ta gane ina da wani intention?.. " dariya Amanda ta sakeyi Tana cewa
"Ke zaki Bari ta gane ne?.. "
"OK naji amma nifa ban ma san gidansu ba... "
"address dinta zaki nema.. ki tuna you're on a mission... so get yourself activated... " ta fad'a mata, shuru rashida tayi for sannan tace
"if alll worked as planned then what?.. "inji rashida
"kedai kiyi abinda nace maki... Then leave the rest to me... " ta fad'a mata, haka dai ta dinga fad'a mata it's nothing serious and she should try and follow her advice. Daga baya ta rashida tayo mata bankwana ta tafi. Kou da ta bar gidan b'ata wuce koina ba sai gidan sister dinta wato ummy, dukda ta rame and her face is swollen she look happy, saida ummy tayi mamakin how comes
"dear naga yau kaman kina cikin farin ciki... Kou dai kin samu Kinyi magana da yarima..." ummy ta fad'a Tana kallon face din rashida dake dauke da murmushi,
"Ant waye haka kuma...." kallon mamaki tayi mata tace
"ba gane waye haka ba... Are you OK?.. " ta fad'a mata, dariya rashida tayi tace
"anty Yazanyi tunda aurenshi zaiyi?...allah ya rufa min asiri...naji ya fita raina... Haka nan inzo in mutu a banza.. Anty na dauki kaddara... " tafad'a hankalinta kwance in a tune da ke kaman she's serious
"alhamdulillah... naji dadi wallahi.... am so happy to finally hear you're over him... " ummy tq fad'a sounding so happy,
"anty Allah dai yasa ya dinga son yarinyar dake sonshi..." inji rashida
"ai sister dinshi ce... Dole kou ba soyayya da akwai yanuwantaka... Ballema in bai sonta ai bazai aureta ba... "ummy ta fad'a mata Tana breastfeeding baby dake hannunta,
"tou Allah ya basu zaman lafiya.... Naji kince dan gidan Dan iya kou... "
"yes... " ta amsa mata,
"oh rayuwa kenan... Aliyu na aisha... " inji rashida praying her sister zata sake maganar sunan yarinyar da yarima zata aura,
"wacece aisha kuma?.. " inji ummy,
"I thought kince sunanta aisha... " rashida ta amsa mata
"aa tasleem dai... her name is tasleem.. karatu ma take yanzu... "
"Allah sarki... Allah yasa ayi a saa... Nan garin take karatu kou abroad... "
"nan take mana... Wannan popular uni take.. " ta amsa mata
"wai anty wata nawa aka saka bikinsu?.. "
"baa kaiga sakawa ba... Sai ranar Wednesday zaa saka rana" , sai kuma ummy tayi mata kallon tuhuma tana cewa
"wai why are you interested in the girl?. " ta tambayeta,
"anty ban gane am interested in her ba... kawai inason sanin the lucky girl ne... kawai ma a bar maganar... Bari in shiga kitchen in Dan ci abinci...pls ki kira mummy kice mata ina gidanki... Kar tajini shuru... " tafad'a Tana tafiya mean while cikin ranta tas, ta mance rabon da tajita cikin such happiness, ta samu abinda take so, wato sunan wacce Aliyu zai aura.
Shi kam yarima babu abinda yake adua sai Allah yasa tasleem tace b'ata son auren, yasan in tace batason kilan baza forcing dinta ba, all he's still thinking is her naked chest, yasan kou ya aureta yanda yake mugun nuna mata girma da wuya ya iya zuwa inda take da sunan zai nemi wani abu wajenta, yasanta da saurin raini da kuma gulma, he's sure anything he tells her kowa sai yaji. Before yana tunanin she have nothing amma yanzu yasan she's more than yanda yake tunani. Yau Tuesday bayan ya tashi daga bacci with he's erection as hard as ever yake tunanin him together with tasleem, da sauri ya dauke wannan tunanin sai kuma ya tuna cewa gobe Wednesday day zaa saka bikinshi da ita, Dan shafa face dinshi yayi daga inda yake zaune a bakin gado yana tunanin who to marry as second wife, yasan ba zai taba yuwa after all he have planned ya kare da wannan lousy girl din kadai ba, idanuwa ya lumshe sai kuma ya Mike ahanakli ya shiga bathroom
"enough about her... " ya fadawa kanshi Don ya lura this days yana takura kanshi da tunanin da yawa, yasan shine namiji kuma yana da right din da zai auri mata kou hudu yakeso at the same time so dole zai nemi wata ya kara daita.
The following day rashida ta zauna Tana tunanin how to get close to tasleem, she thought of going to school dinta, b'ata san yanda zata farayi mata magana ba, tasan most people basu son Mai like masu, duk dare batayi bacci ba Tana tunanin yanda zata samu taje kusa da one tasleem take, tasan She's from a big family haka itama rashida iyayenta ba kananun mutane bane,
"rabbi help me through this... " ta fadawa kanta while arriving at a decision, gari na wayewa ta shirya ta fita ta tsaida Mai adaidaita ta fad'a mata ya kaita gidan Dan iyan garin gidan Alhaji mussadiq ba boyeyye bane, kowa yasan gidanshi saboda he's a well known man, sanda tazo gidan karfe takwas da yan mintuna, Mai adaidaita ta sallama tare da knocking a gate din, sanye take cikin long hijab har kasa Mai hannu, hannunta biyu waje and she have a wonderful innocent face that makes her look harmless, sake knocking tayi Mai gadi ya leka, ganin mace ce yasa ya bude small gate ta shigo ciki,
"Dan. Allah malam tambaya nake... " ta fad'a mashi
"Allah yasa na sani.. " ya amsa mata
"Dan Allah tasleem ta fita ne?.. " ta tambayeshi, shuru yyi yana kallonta saboda an fad'a masu jar suyi disclosing anything game da yan gidan to anyone, ganin irin kallon da yake mata yasa tace
"school din mu daya... " ta sake fad'a mashi,
"tou ki kirata mana... " ya amsa mata,
"na rasa layinta ne... Kou zaka taimaka min... " ta amsa mashi Tana fiddo wayarta,
"bani da number ta amma ga bangarensu chan... " ya fad'a yana nuna part din hajiya zainab, kafin ya sauke hannu sai GA tasleem ta fito da doguwar hijab mai jan kasa sannan Tana rungume da bag dinta ta gaba as usual,
"gata nan ma ta fito... " Mai gadin ya fada mata , da sauri rashida ta juya Don ganin the lucky girl, she's so younger, murmushi ta saki tare dacewa
"yauwa shikenan ma... "ta fadawa Mai gadin sannan ta fara takawa towards tasleem dake heading zuwa inda motarta ke tsaye, Tana tafiya ahankali taga wata ta nufota, hakan yasa ta Dan daina tafiya Tana kallonta, da sallama rashida ta karaso wajen tasleem, amsawa tasleem tayi Tana kallon face dinta kou she knew her amma sam. B'ata gane face din ba,
"sister kwana biyu... " rashida ta fad'a mata kaman ta Santa tuntuni,
"sai alkhairi... " inji tasleem dake kokarin gano kou ita wacece,
"irin wannan kallo haka ba dai baki gane ni ba... " ya fad'a mata sounding so real, goshi tasleem ta dafa sannna tace
"am Sorry siater... Ina da mantuwa ne... Sam ban gane ki ba... Dan Allah wacece.. Don't be offended... " tasleem ta fad'a mata wearing a friendly smile, Dan turo baki rashida tayi Tana cewa
"ashe ni kadai na damu dake ke baki Damu Dani ba... " tafad'a kaman zatayi kuka
"pls am sorry... Kar kice haka mana... " tasleem ta fad'a Tana dafa shoulder din rashida
"ba dole in fadi haka ba... Tunda na ganki nake son ki zama kawata... I think of you always.. It's been 5 months a gidan anty ummy ke da mum dinki kun zo suna... " Dan face tasleem ta b'ata Tana cewa
"sorry again.. Wacece anty Ummy... " ta sake fad'a mata holding her shoulder
"matar yarima abubakar... "
"Ayya... Ban taba sanin sunan matar yaya abubakar ba... "
"ai ni kanwar matar shi ce... Kuma ranar da kuka zo inq gidan.... Na GA Kinyi min and I want to be your friend... Dan Allah kar kice aa.. " ta fad'a kaman zatayi kuka, dadi tasleem taji da akace ana son zama. Friend dinta, wato she's very important haka,
"haba why zance no... Bazan taba cewa no ba... Yanzu ma Don ina sauri da mun koma ciki nayi introducing dinki to my mom..." Dan tsalle rashida ta daka tare da rungume tasleem Tana cewa
"nagode sosai... Har naji sanyi cikin raina... Na mance rabonda inji irin wannan dadin... Am so happy right now..." rashida ta fad'a cikin matsanacin farin ciki because it's so easy than she thought
"nima naji dadi dana samu more friends... "
"nidai kar ki sakani a jeren anyhow friends dinki because ni special friend ce... Kou me kike so zanyi maki... Baki ganin har takowa nayi gidanku saboda how special you're "
"na yarda am special kam... Insha Allah kema zan sakaki jerin special people... Nagode da kauna... " ta fad'a,
"wayyo my besty is saying ta gode da kauna... Nike da godiya da baki daga min kai ba... You're so classy... Am so lucky am with you now... " rashida ta fad'a mata, rufe face tasleem tayi Tana cewa
"you're making me feel More special wallahi..."
"Ashe Bakisan how special you're ba...wallahi you're very special even not to Anyone but to me... "
"aikam kema daga yau you're special to me... Kuma I will treat you likes special person... " inji tasleem that is careless and don't think before doing or saying anything,
"besty kar ki makara... Kawai bani number dinki zan kiraki... " rashida ta fad'a mata
"muje in ajiyeki along the way sai in wuce.. " inji tasleem, babu musu rashida ta bita suka shiga motar ta. Nanfa hira ya barke tsakanin su amma no body is talking about yarima, nan take rashida ta gane tasleem b'ata da sirri she even told her about tafiyar da zasuyi da hajiya zuwa India da kuma yanda ake koya mata girki da sauransu, saboda dadin hira har ta mance da zata ajiyeta a bakin titi Don ta hau keke ba ita kuma rashida was so happy that she doesn't mind following her bumper to bumper, she couldn't help but texted Amanda Tana cewa
"we're together...she's so easy to get... " ta tura mata. Nan fa suka cigaba da labari,
"wai me zakuyi da matar sarki a India... " ta tambayeta saboda ita kawai tana son story dinsu ya kasance cikin abinda ke tafe daita,
"b'ata lafiya ne... Shine zan rakata ganin dr... " ta amsa mata,
"oh I thought shopping zakuyo na bikin... " ta fad'a mata saboda taji what she will say
"eh zamuyi shopping tace...amma bana biki ba... Tace zan zabawa black mamba kayan lefe... " ta fad'a Tana Dan b'ata face,
"waye black mamba... " rashida ta tambayeta, dariya tasleem Tayi tace
"between me and you.. It's Aliyu... Haka nake ce mashi... " ta fad'a cikin whisper kaman ba su kadai bane cikin motar, idanuwa rashida ta zaro tace
"waye Aliyu kuma?.. "
"last born din sarki mana... Baki san kanin mijin yayarki ba?. " ta tanbayeta,
"ai ban sanshi ba. Why kike kiranshi da black mamba kuma... " ta sake tamabayarta, baki tasleem ta tabe before saying
"because duk duniya babu wanda na tsana kamanshi with his black and wicked mind... " ta fad'a mashi rashida couldn't help but wonder if tasleem ce Wanda zai aura because yanda take magana it seems babu komai tsakaninsu,
"oh shi zaiyi aure kenan.. "
"nidai ban sani ba.. Kawai ummah tace zan zaba mashi kayan lefe... Kilan aure zaiyi... Har na tausayawa matar da zai aura... Mutum ba kyau sai kuma shegen bakin hali... " ta fad'a hankalinta kwance, rashida zata bude baki tayi magana sai tasleem ta zaro idanuwa Tana cewa
"subhanallah.. Na mance ban ajiyeki ba.. Har na kusa zuwa school... " ta fad'a Tana dubawa if zata iya tsayawa, rashida da tayi confuse tace
"don't worry... Ai ina jin dadin hira dake ne... Shiyasa kou a jikina... " tasleem b'ata kara cewa komai ba tayi parking tana tare dacewa
"besty sorry... Ki samu abun hawa... Zamuyi waya... " ta fad'a mata, babu musu rashida ta fita tare da waving dinta. tsayawa rashida tayi Tana thinking if tasleem ce target dinta because it's confusing. Haka dai ta samu Mai adaidaita ta tafi inda take service dinta.
Tasleem her school friends about her new friend, babu abinda suka ce mata sai she should be careful.
Yau ita ta had'a masu lunch bayan ta dawo daga school. Sai da yamma suka shiga kitchen da mom dinta again for another meal,
"my love Kinga hajiya Tana son traditional food so zamuyi miyan gargajiya Mai dauke da nutrients masu yawa da kuma amfani a jikin mussanman jikin mata,...sunan miyan edikang ikong,...da pounded yam" Dan b'ata face tasleem tayi tace
"Meye haka kuma mummy.. " ta fad'a sounding so disgusting
"sunan Miya Wanda yan calabar sukeyi.. Amma kuma mazan arewa suna son biyan sosai in dai mutum ya waye kou yana fita wurare zai san miyan...so this is ourrm ingredients.. " ta fad'a Tana bude mata kayan da zasuyi amfani dashi wajen hada miyan, kifi ta gani kala kala tace
"mummy wanann duka cikin miyan zamu saka?." tq tambayeta,
"yes mana.. Kinsan banbancin mu da yan kudu kenan.... Su sun yarda su bawa cikinsu mu kumq mun yarda da kayan mata... Shiyasa in zakiga matansu very healthy and strong... Duk yanda suke basu cin abinci gaya kou lami dole sai sun saka Nama kou kifi at times both... " ta fad'a mata,
"Kinga wanann is socked stock fish,nayi socking dinshi ne Don yadanyi taushi saboda yana da wuyan dahuwa, sai dry fish, da boiled fresh fish, na zubda ruwan ne saboda ba kowa ke son karnin kifi ba, tare da cray fish, sai ganda, sai Maggi, garlic da ginger tare da pepper ...sai ga ganyen ugwu da water leaf Wanda Kinga na wankeshi tas na yanka, sai manja... Miyan bai son ruwa at all saboda haka zamu Dan sawa water leaf dinmu gishiri kadan sai mu dora kan wuta... " ta fada Tana juye water leaf dinta cikin tukunya ta Dan barbada gishiri sannan ta dora kan wuta, daga nan ta dora another pot ta zuba stock fish din tare da dry fish ta saka ruwa dan kadan ta dora kan wuta, bayan few minutes ta sauke water leaf din da ruwa ciki
"wow mummy naga baki saka ruwa ba kuma yanzu da ruwa ciki... " ta fad'a out of surprise and excitement,
"eh mana...baki ji sunan ganyen ba... Water leaf.. So yana da ruwa sosai... " ta fada Tana juye ganye cikin Dan Karamin basket Don ruwan ya tsane.
"tunda muna jiran kifin ya dahu sai mu fere doyanmu mu dora kan wuta... " ta fada mata, nan tq fiddo doya ta fere shi sannan ta yanka kanana ta dora kan wuta. After some time ta bude kifin sannan ta dauki ganda ta juye kan kifin dayayi taushi sosai ta dauki boiled fish dinta ta juye ciki sai ta zuba maggi